← Book details Sakatariya Ta Psrt 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 91

Sashe 18

Sakatariya Ta Psrt 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Waya ya samu Anas na yi lokacin da ya shigo, ya samu waje ya zauna yana kallon sa.

"Miss Salihu ta bar aiki ne?" Ya faÉ—a da harshen ko in kula lokacin da Anas ya gama wayar.

"Ka fara kewar ta ne?" Anas ya amsa ma sa

"Oh please, ka amsa min tambayata ba na son shirme"

Dariya Anas yai sannan ya ce " well, ta ce za ta dawo amma sai Monday"

"Monday is too far"

"Mutumina da alama ka ƙagu ka ganta ko?"

Tashi Najeeb yai ya ce " idan ba ta dawo Monday É—in ba, ka nemo min wata sakatariyar"

Anas ya É—an yi dariya ya ce " kamar da gaske"......

...........

Ghana-must-go manya guda biyu ne a gabanta tana faman jera kayan gwanjo da ta saro da za ta kai Kano.

Adiyya wata jikar Nanna ta miƙo ma ta waya wai ana ta kiranta tun ɗazu.
Amsa wayar ta yi ta ranƙwashi kan yarinyar wadda ba za ta wuce shekara takwas zuwa tara ba. "Na hana ki ɗaukan wayata ba kya ji ko. Yanzu jiba yadda kuka cinye min chaji"

"Allah Anty ba ni kaɗai bane har da Mubashshir, shi ne ya ke game, ni kallon hotuna kawai na ke yi" yarinyar ta faɗa tana shafa wajen da Farida ta ranƙwasa.

Duba wayar ta yi ta ga missed call ɗin Maijiddah ne da na sister Munibat sai saƙo guda ɗaya wanda wani number ya turo. Numbar na yawan damunta da saƙo tun lokacin da ta yi welcome back ɗin layinta. Ta buɗe saƙon ta karanta kamar haka.

*fatan ki na lafiya Aysherh? Ina so ki yadda da ƙaddarar da ta same ki, ki ɗauke shi a matsayin jarrabawar Ubangiji. Zai fi ki koma al'amuran rayuwar ki kamar da, ba tareda wani tsoro ba. N J*

Tsaki ta yi ta ce " shi wannan N J ɗin sai shegen naci, ka kira ba za ka kira ba, sai gatan tura saƙo kamar kamfanin Airtel."

Ta tura masa reply kamar haka *" Malam NJ ko Mr NJ, koma wa ka ke dai, ina ma ka gargaɗi da ka dena turomin saƙo, saboda ni matar aure ce. Idan ka cigaba kuwa duk inda ka ke, mijina zai nemoka kuma ba za ku wanye lafiya ba"*

Sai da ta tura saƙon ta ke ƙara alhinin wannan NJ ɗin wanda take tunanin ƙila cikin abokan Yakubu ne da su ke aiki tare a Najeeb constructions. Idan ba haka ba ta ya NJ zai san an kidnapping ɗin ta har ma ya san ta ji ciwo a ƙafa. Ƙafarta ya fara tambaya ranan da ya fara turo saƙonsa wanda kuma ta san idan ba Yakubu da Anas ba ba wanda ya san ta ji ciwo a wajen aikin su. Ta kawar da tunanin ta hanyar kiran Maijiddah dan ta ji mi ye labari...

Yana zaune ya ji ƙarar shigowar saƙo. Ya ɗauki waya ya duba, sai da ya karanta sannan yai murmushi dan ya san yanzu kam ta samu lafiya tunda har ta iya ma sa reply.

.........................

Yau sammako yai a office dan ko mai shara ba ta yi aikinta ba lokacin da ya shigo. Fakewa yai da cewa wasu ayyuka zai ƙarasa a office ɗin lokacin da Najdah ta tambayi dalilin fitarsa da wurwuri haka. Duk da kuwa dama shi ɗin mai fitar wuri ne amma na yau daban ne...

Har ƙarfe takwas da rabi ba ita ba alamarta. Haka dai ya ke aikin na shi ba tareda samun kwanciyar hankali ba...

Tun takwas saura ta zo, ta fara biyawa tana tallen gwanjon da ta saro a office-office da ke hawa na farko da na biyu. Sannan ga uwa uba labarin kidnapping ɗin su da ta ke bayarwa ga duk wanda ya ma ta jaje. Ba ta ankara ba tana office ɗin sister Munibat ta ga ƙarfe tara har da kwata.

"Kai ashe haka lokacin ya tafi barin je na kama aiki kafin Sir Najeeb yai ƙuli-ƙulin Kubra da ni"...

"Najeeb na samo ma ka wani secretary, he's a good guy idan ka amince zai fara aiki gobe"

Ya kalli Khalidah kallon ki na da hankali kuwa.

"Ban sa ki wannan aikin ba. Idan ina buƙatar secretary na san inda zan nema"

"Najeeb, sati ɗaya kenan wancar shashashar ba ta zuwa. Na san abinda ya faru ne ya sa ta ƙi dawowa, ni wallahi da da su...."

"Out"

"Najeeb.."

" i said get out"

Khalidah ta kai maƙura wajen ɓacin rai amma ba yadda ta iya dole ta kwantar da kai idan tana son samun Najeeb.

"Shi kenan zan fita amma ka yi tunani"

Tsaki ya ja sannan ya cigaba da aikin da ya ke akan system É—in sa.

Shigowar Farida kenan Khalidah ta fito daga office É—in Najeeb.

"Ina kwana Anty" Farida ta faÉ—a dan abinda ta ke kiran Khalidar da shi kenan idan tana son tunzurata. Khalidah irin matan nan ne da Allah yai wa baiwar jiki da tsayi.

" da kin rufawa kan ki asiri kin bar aikin nan da zai fi mi ki, dan ni Khalidah sai na sa Najeeb ya kore ki daga aiki"

"haba Anty! daga zuwa na. Ba ga ruwa balle ya hanya?" Farida ta faÉ—i tana farfari da ido.

Khalidah tai tsaki ta tafi...

"Sir Najeeb Ina kwana" ta faÉ—i lokacin da ta shigo office É—in sa. Bai ce komai ba bai kuma É—ago ba.

"Miss Salihu you are late"

" na san ba ka son latti Sir, a min afuwa na yau ne kawai"

Sai a lokacin ya É—ago idon sa ya kalleta.
Shigar riga kalar maroon ta yi sai wando kalar ash da jacket shima kalar ash, ta yi É—aurin turban da É—ankwali kalar maroon.

"Sir Najeeb ka gama kallon da kyau. Duk haɗuwar da na yin nan gwanjo ne ajikina, grade one ma kuwa. Kuma akwai irin su-irin su da na saro ko da za ka ɗaukawa ƙanwar ka ko..."

"Miss Salihu, go back to your office" ya faÉ—i yana sauke idon sa

"Haba Sir, ba sannu, ba ya jiki, ba..."

Wani file ya miƙa ma ta ya ce " ina son aikin nan cikin minti goma"

Ƙarɓan file ɗin ta yi a hannunsa tana kumbure-kumbure har ta fice daga office ɗin...

*💮SAKATARIYA TA💮*
.......(My Secretary).......

*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

*Free page*

0️⃣1️⃣1️⃣

A kishingiɗe ta ke a kan kujerarta bacci ya sace ta. Tun ƙarfe goma da ta gama aiki ba abin da ta ke yi, chatting ta ke yi a waya baccin ya sace ta.

"Miss Salihu...Miss Salihu" ta yi firgigit ta farka. Kallon sa ta farayi tana murza ido.

"Biyo ni"

Kafin ta wartsake ta tattara office É—in tuni ya fita.
A hawa na farko ta sameshi yana yiwa wasu bayani. Anas ne ya ce ma ta yana ƙasa, dan da ba ta san inda yai ba.

Tana tsaye tana ƙoƙarin saita kan ta saboda har lokacin ba ta gama wartsakewa ba ta ga yai hanyar parking lot na kamfanin. Da sauri ta bi bayan shi tana jiran ƙarin bayani amma bai ce komai ba. Sai da su ka iso wajen motar sa ta ce "Sir fita za mu yi ne?"

"Shiga mota" abinda ya iya cewa kenan. Sai da ta zauna da kyau sannan ta kalleshi ta ce "Sir da ka gayamin fita za mu yi ai da na ɗan gyara fiskata ko. Yanzu ko ɗan hodan nan ban ƙara tisawa fiskata ba, fiskata ta yi wani bauu"

" Miss Salihu ina so ki sa a ran ki cewa wannan kamfani ba fashion industry ba ne inda ake gudanar da fashion shows. This is a constructions comp...."

"DaÉ—ina da kai Sir Najeeb akwai wasge mutum. Kuma dan ina aiki a kamfani irin wannan sai ba zan yi ado ba. Yanzu idan a yamutse na ke fitowa kai kan ka ba za ka ji daÉ—in aiki da ni ba, balle ma su zuwa wajenka kullum"

"Miss Salihu..." ya faɗa da ɗan ƙarfi

"Sir Najeeb ina neman alfarma dan Allah"

Ɗan juyowa yai ya kalleta na ɗan daƙiƙai sannan ya maida hankalin sa ga tuƙin da ya ke yi.

"Sir dan Allah ka dena kirana da Miss Salihun nan. Shi fa Salihun nan yana chan kwance cikin kabari amma ka dinga kirana da sunan sa. Ga Aisha ga Farida duk bai maka ba, sai ka kirani da Salihu" ta ɗan yi ƙasa-ƙasa da murya ta ce "Salihun ma fa a hoto kawai na ganshi ban ganshi a zahiri ba, amma abi a dameni da Miss Salihu Miss Salihu"

Wannan karan muryarsa a kausashe ya ce " our relationship is strickly formal Miss Salihu. So ba abinda zai sa na kira ki da first name na ki"

"Abin ai son kai ne. Ita sister Munibat ai Miss Munibat ka ke kiranta ba Miss AbdulHamid ba. Ga wancan ƙatuwar nan Khalidah, itama sunan ta ka ke kira. Sai ni ne za a raina a dinga wani yaɓa mani Miss Salihu kamar wata marar suna. Gaskiya Sir ka dinga kirana da suna na nima"

"Or what?" Ya faÉ—i yana kallon ta

"Sir ni dai ka gyara dan Allah"

Bai sake cewa komai ba har sai da su ka iso inda za su je. Ya ce ta fito kuma ta kimtsa kan ta baya son yawan surutu. Wani É—akin taro ya shiga ya barta a reception wai ta jira shi.

Kusan awa ɗaya yai a wajen sannan ya fito. Tunda su ka bar wajen su ke tafiya tun tana shiru-shiru har dai ta kasa jurewa ta ce "Sir Najeeb wai garin za mu bari ne kam?" Bai kulata ba sai ma ƙara volume ɗin kiɗan da ke tashi a motar da yai.
Haka ta haƙura ta yi shiru har su ka isa wajen. Tana fitowa a mota ta fara miƙa tana cewa " kai! yau na zaunu gaskiya. Irin wannan nisan waje haka"

Wani site ne da kamfanin su ke ginawa ya zo dubawa. Bayan zaunuwa to Farida ta taku domin kaf wajen sai da su ka zaga duk girman shi. Su kan tsaya da wasu ma'akata yai mu su tambayoyi da 'yan bayanai. Anan ta ke ɗan rubuta wa su abubuwa kamar yadda ya buƙata.
Chapter 18 · 0% Book details