← Book details Sakatariya Ta Psrt 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 91

Sashe 48

Sakatariya Ta Psrt 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ba'a jima ba aka taho da Farida. Yana ganin ta ya ƙarasa wajen ta da sauri. Ya riƙe hannunta kawai sai ta faɗa jikin sa ta fara kuka.
Duk wani formalities Anas ne ya tsaya zai yi, dan Najeeb kan jan hannun matar sa yai su ka bar wajen. Sabreen ta bi bayan su tana faɗin ba zai yiwu Farida ta tafi haka ba bayan abinda ta yi ma ta. Najeeb bai kulata ba har su ka isa bakin mota. Zai taimakawa Farida ta shiga Sabreen ta riƙe ma sa riga, ta fara kukan munafurci.

"Noory she wanted to kill me, ita ta sa min yaji a gado jiya. I almost died Noory"

Bai yi yunƙurin yafce hannunsa daga riƙon da ta ma sa ba illa matsawa yai kusa da Farida ya ɗan sukuyo dai dai saitin fiskarta. Ba tareda wani tantama ba ya haɗe bakin su. Farida ta ƙwalalo ido saboda mamaki da shock da ta ji lokaci guda.

Sabreen ta sake rigan Najeeb tana kallon yadda Najeeb ke kissing Farida zuciyarta na tafarfasa, ji ta ke kamar zuciyar zai bulluƙo ya fito.

Farida ta yi saurin janye bakin ta saboda tunowa da ta yi a public place su ke. Da rinannun idanun sa da su ka ƙanƙance ya ce "kiss me" ba ta san ya akayi ta jefar da kunyar ba kawai ta tsinci kan ta da haɗe bakin su not minding a inda su ke...

*SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......

*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

0️⃣3️⃣0️⃣

Murmushi kawai ta ke yi tunda su ka fara tafiya. Idon ta na gefen titi amma hankalin ta ba a titin ya ke ba. Har yanzu tana jin taste ɗin zaƙin bakin sa a nata bakin. Ba ta taɓa sanin haka kiss ke da daɗi ba sai yau. Lokacin su na soyayya da Lukman ya taɓa kissing hannun ta da goshi amma banda lip to lip kiss. Shi kam Rayyan ba su taɓa irin haka ba, Rayyan ya na tsoro da shakkar Farida shi ya sa ko hannun ta bai taɓa riƙewa ba sai dai ko a rashin sani.
Yau ta samu first kiss É—in ta, kuma da Sir Najeeb, Sir Najeeb fa. Ta sa hannu ta rufe bakin ta saboda tsikar jikan ta da ya tashi lokacin da ta tuna abinda ya ce "kiss me".

"Did they hurt you?"

Ai ta tafi duniyar tunani ba ta ma ji abinda ya ce ba. Duk wani cin mutunci da ta shirya za ta yiwa Sabreen lokacin ta na cell ta watsar da shi. Ƙwaƙwalwarta ba abinda ya ke tunowa sai wannan moment ɗin.

Chan ƙasan zuciyar sa ya ke neman dalilin da ya sa ya kissing ɗin ta amma ya rasa. Chan ya baiwa kan sa amsa da Sabreen. Yes ya yi haka ne saboda Sabreen, saboda ta gane cewa he's over her now. Amma must he resort to kissing her? Yanzu sai ta rena shi. Wata zuciyar ta ce but it was the best kiss you ever had. Ko dan ya jima bai yi kiss ba ne, dama da Sabreen ne kawai, no one else. First kiss na shi in 8yrs felt different. Kaman wani ƙaramin yaro haka ya lashe lips ɗin sa da harshe. Garin haka ma saura kaɗan ya buge wani mai Keke.

Har su ka isa gida ba wanda yai magana. Farida ce ta fara shigowa dan ta fita ta bar shi a mota. Tana tafiya tana jin ta a sama fiskar ta É—auke da murmushi.

Najdah ne da wata tsohuwa a falon lokacin da ta shigo. Ba ta ma lura da su ba sai da tsohuwar ta ce "amarya lafiya?" Farida ta juyo sai ta ga tsohuwar duk da kuwa kuɗi sun ɗan ɓoye tsufan, amma kuma a yadda ta gan ta za ta haifi Daddy.

Ta yi saurin ƙarasawa wajen ta ta tsugunna "Hajiyata dan Allah ki yi haƙuri ban gan ki ba ne"

"Na ga alama ai, kin tafi birnin soyayya ko. Ina angon" kafin ta ba ta amsa sai ga Najeeb ya shigo.

Yana ganin Hajiya Mama ya washe baki " tsohuwa yaushe a gari?"

Yana ƙarasowa wajen ta ta ɗauki sandarta ta ɗaga sama za ta kwaɗa ma sa ya ja baya da sauri.

" ke fa tsohuwa kin dawo kenan za ki fara cin zalin mutane"

"Ungo na ka Najeebullahi, tun jiya na dawo amma shi ne ba za ka kawo min amarya na gan ta ba"

"To ke kiji da ƙafar ki ma na, amma sai shegen yawo"

Farida dai kallon Najeeb da Hajia Mama ta ke da su ke dramar su na Kaka da Jika. Najeeb was jovial amma ba kaman tsakanin sa da Mom ba wanda tun zuwan ta abin ke É—aure ma ta kai.

Hajia Mama ta kalli Farida ta ce "kin ga mijin kin nan ke ce rufin asirin sa. Haka yai ta yawo ƙaton tuzuru da shi, sai da Allah ya kawo ki"

Farida ta yi murmushi.

"Sai ki kula da shi sosai dan É—an duniya ne"....

Ta fito daga wanka bayan sallar Isha ta fara jin hayaniya a ƙasa. Ba ta tantance ko muryan su waye ba ne amma daga yadda maganar ta ke haɗakar larabci da turanci ta san ba zai wuce Sabreen ba ne...

"Big B mi ya sa ka ke bin bayan ta, kai kan ka ka san ita ta yi wannan abin and she needs to be punished for that"

" walau ita ta yi walau ba ita ba, dukkan ku biyu babu wanda ya ke da ikon arresting É—in ta, especially you Sabreen. Ina so ki nisanci iyalina"

"Big B amma..."

"Najdah!" Ya daka ma ta tsawa. Kallon shi ta yi sannan ta haura sama da gudu.

Ya juyo ya kalli Sabreen ya ce "next time ki ka yi ƙoƙarin taɓa lafiyar mata ta, i wont take it lightly"

Cike da tuƙuƙin baƙin ciki ta ce "you dont love her, do you"

HaÉ—iye miyau yai sannan ya ce "go back to Hollywood you dont belong here"...

Ɗakin Najdah ya fara zuwa Lokacin da ya haura sama, amma ta ki buɗe ma sa ƙofa. Dan haka ya juya ya shiga ɗakin su.

Yana shiga ɗakin ya gan ta bakin gado tana kuka. Jikin sa yai sanyi ya ƙarasa wajen ta yana tambayar minene dan a tunanin sa ko a cell ɗin an mata wani abu ne.

"Mi ya faru?"

Tana kuka tana jan majina ta ce "Baba ya rasu"
Kan sa ya ɗaure dan Anas ya taɓa ce ma sa Farida marainiya ce to yanzu kuma wani Baban ne ya rasu.

"Your father?" Ya sake tambaya.

"Kaka na ne"

Ya jawota jikin sa yana lallashin ta.

"Yanzu Ummi ta kira ni, dan Allah Sir Najeeb zan je Jos gobe"

Ya gyaÉ—a kai ya ce "its ok"

Sun jima tana kwance a jikin sa tana hawaye tana faɗa ma sa kyawawan halayen Baba. Bai bar wajen ta ba sai da ta yi bacci, lokacin kusan sha biyu saura na dare. Da ya gyara ma ta kwanciya sannan ya je yai wanka ya shirya cikin kayan bacci sannan ya zo ya kwanta amma kafin yai bacci sai kusan ƙarfe biyu. Tunani ya cika ma sa kwanya.

Washe gari da sassafe ta shirya, ya sa Iliya ya kaita har Jos. Lokacin da motar ta bar cikin compound ɗin ƙarfe shida da rabi na safe. Yana shigowa cikin gida Daddy ya kira shi, da ya je tambayar sa yai gameda abinda ya faru jiya dan ya ji maganar a wajen Mom.
Bayan ya ma sa bayani sai Daddy ya ce " ka yi katanga tsakanin ka da Sabreen, ban hana ka ƙara mace ba idan ka ga ba za ka iya zama da Aisha ita kaɗai ba, amma ka sani. Ba zan taɓa amincewa da Sabreen a matsayin suruka ba. Ba wai dan ta rabu da kai ta dawo ba, sai dan ba zan bari ka haɗa zuri'a da macen da zata iya gurɓata ma ka rayuwa ba. Ina sane da lokacin da Mahaifiyar ka ta ke kuka kullum saboda Sabreen ta na shirin auren wani kafiri ɗan ƙwallon ƙafa har ta ke sukan addinin musulunci da ya hana aure tsakanin kafiri namiji da mace musulma. A hira da aka yi da ita shekaru uku da su ka wuce, cewa ta yi sallah na takura ta, wai anata abu ɗaya kullum ba hutu. Wannan ba macen aure ba ne. Idan har ka nuna za ka auri Sabreen to za ka yi nisa da ni da iyalina. Za ta zauna a nan ne kawai saboda alaƙa ta jini da su ke da shi da Nabilah amma bayan nan ba na so wani abu ya kuma shiga tsakanin mu"

Najeeb ya gyaÉ—a kai.

"Ya maganan gidan ka, anyi interior decoration É—in?"

"An kusa a gama"

"Ok Allah ya nuna ma na"...

Yau dai throughout a office jin sa ya ke wanni iri. Musamman idan ya zo fita ya ga ba ta kan kujeran ta.

Da ke Jummu'a ne kuma ranan hutu ne an haɗa ƙwarya-ƙwaryan party amma bai iya tsayawa a wajen ba. Anas ne ya tsaya ya wakilce shi, daga sallar jummu'a gida ya wuce yana jin jikin sa ba daɗi. Ba wai ba shi da lafiya ba ne amma kuma jikin sa is weak.
Yana shiga ɗakin sai ya ji ɗakin ya ma sa faɗi kaman ba ɗakin sa ba, there's something missing. Ƙanshin ɗakin ya sauya tun zuwan Farida saboda haɗuwar turarukan sa da na ta kalolin turaren. Har ta fasalin ɗakin ya sauya. Ya tuna ranan da ya shigo ya ga tana chanja arrangement na wasu abubuwan a ɗakin.
"Sir Najeeb ɗakin ka yana buƙatan polish"

Ya tuna yadda yai ta gwaleta yana cewa ta hargitsa ma sa É—aki.

Ya na shiga wajen closet ya tuna ranan da ya ke chanja kaya ta shigo lokacin gajeren wando na jeans ne a jikin sa ba riga.

" Sir Najeeb, idan ka na gida sai ka yi ta sa gajerun wanduna kaman wani É—an firamare"

Yai murmushi tunowa da yai da kalolin tusa da ta lissafto ma sa ranan...
Chapter 48 · 0% Book details