Sashe 87
Sakatariya Ta Psrt 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mutane ba kaÉ—an ba su ka halarci waliman wannan suna, tun daga mutanen Gombe zuwa na Wase da Jos kowa ya karkaÉ—e jiki ya zo. Sabreen da Lukman ma saura kwana É—aya suna su ka dira a Kano. Yaro ya samu kyaututtuka ba adadi.
Sorveniers sa aka raba ba za su irgu ba. Saboda gudun evil eye, sunan yaro kawai aka sa babu hoto. Washe gari aka yi abincin sadaka aka kai Iskalin Almajirai sunfi ishirin...
Rayuwa ta cigaba da tafiya hakanan soyayyar Najeeb da Farida tana tafiya gwanin sha'awa. Baby Yaman ba ƙaramin gata ya ke gani a wajen iyayen sa ba, ga uwa uba kakannin sa. Kowa son ɗaukan sa ya ke idan aka fita da shi, amma miskilin yaro ba kowa ya ke yarda ya ɗauke shi ba. Ko Tasallah da ƙyar ya ɗan saba da ita ya dena kuka idan ta ɗauke shi...
Kamfanin Najeeb sai daɗa bunƙasa ta ke yi, yanata samun buɗi ta ko'ina...
Wannan zuwan Farida gida lokacin Yaman yana ɗan wata huɗu ta lura da cikin Ummi. Ko ya akayi ma ba ta lura da shi ba sai yanzu oho dan aƙalla cikin zai kai wata shida.
"Ummi dan Allah ki haifo mace na samu ƙanwa nima"
Ummi ta ma ta daƙuwa, Farida ta sa dariya, dan ta gane Ummi kunyar cikin ta ke ji...
....................
Aneesa da Maijiddah sun saita kan su, sun dena kishin hauka. Aneesa ta yadda duk makaman yaƙinta, sosai ta ke kula da miji da yaranta tunda yanzu ba inda ta ke zuwa. Ciki ma ta ke da shi amma ta kasa sanar da Abdulwahab dan kar yai zaton ƙarya ta ma sa irin wancan karan.
Daren wata Monday AbdulWahab yana ɗakinta ya ke ma ta maganar wani abokinsa da ya buɗe sabon kamfani, yana yi ma sa tayi akan ya bar Aneesa ta jagoranci ɓangaren sales and marketing saboda experience da ta ke da shi.
"Mi ki ka gani?"
"Duk abinda ka ce Sweetheart" ta faɗa tana kai hannunsa daidai cikinta. Jin ɗan tauri-tauri da cikin yai ya sa shi duban Aneesan da kyau yana neman ƙarin bayani. Ta ɗaga ma sa yatsu huɗu tana murmushi.
"Da gaske?"
Ta gyaÉ—a ma sa kai. Ya jawota jikin sa sosai yana hamdala...
Bisa amincewar AbdulWahab ta fara aiki wanda 8am-2pm za ta dinga yi duk rintsi zuwa uku da rabi ta dawo gida randa ba ta samu traffic sosai ba ma kafin ƙarfe uku ta iso gida. Cikin be zo ma ta da wani laulayi ba shiyasa ta ke gudanar da lamuranta cikin sauƙi. Ita kuwa Maijiddah sosai Al'amin ɗinta yai wayo, kowa na son yaron a gidan ba ma kamar yayunsa Baby da Alizah, indai su na gida sun dinga faɗa akan sa kenan kowa na son ɗaukan sa...
Bayan wata biyar Aneesa ta haiho yarinyar ta mace. Yadda bata wahala a renon cikin ba sai ya zamana ta wahala wajen haihuwa, dan awa takwas ta yi tana labour ƙarshe sai da aka sa mata ruwan naƙuda kafin haihuwan ya taso gadan-gadan.
Itama wannan jaririyar a Kano aka yi sunanta, yarinyar ta ci suna Khadijah su ka sa ma ta inkiyar Mujahida...
............................
Ummi ma ta haihu namiji amma kwanan sa biyu yaron ya koma. Farida sai da ta yi kuka ranan tamkar ita ta yi haihuwan.
Baffa Musa ma ya ji mutuwar yaron dan yadda ya ke ji da Ummi to haka ya ke jin son abinda za ta haifo ma sa. Sai dai ƙaddara ce da ta riga fata...
Yau Jumma'a da wuri ya dawo daga office. Ɗakinsa ya fara shiga amma ba ta nan. Ya rage kayan jikin sa sannan ya wuce ɗakin ta. Abin mamaki sai ya ganta durƙushe bakin gado tana kuka. Da sauri ya ƙaraso wajenta dan tunanin sa wani abu ne ya samu Yaman.
"My Queen mi ya faru? Ina Yaman?"
Ɗaga hannu ta yi ta nuna wajen gadon yaron. Ya ƙarasa gadon da sauri, ya kalli Yaman na bacci hankalin sa kwance, sai a lokacin ya ji hankalin sa ya kwanta. Ya shafa kan yaron sannan ya koma wajen Farida da ke kuka.
Ya jima yana rarrashin ta kafin ta yi shiru ta miƙa ma sa PT strip ba tareda ta ce ma sa ƙala ba. Bai gane ba ya tambayeta " what is it?"
Ta É—ago jajayen idanun ta ta kalleshi ta ce " i'm pregnant"
Allahu Akbar Najeeb ya faÉ—a tareda yin sujjada a gefenta. Har ya É—ago ba ta dena kallon sa ba.
"Kai i'm happy Aysherh, kin min komai a rayuwa ban san mi zan miki na saka miki ba"
Hararansa ta yi ta ce "it seems ka manta shayarwa na ke. Yaman is only 7months"
"So?"
"Da ke ba kai za ka yi wahalan ba ai"
Jawota jikinsa yai ya ce " Aysherh aren't you happy, mutane nawa su ke neman haihuwa ido a rufe amma Allah bai ba su ba. Amma ke kin samu kina kuka, let me ask you something. KuÉ—in kula da su ne ba mu da shi ko kuma me ne?"
Skt 59
Maimakon ta bashi amsar maganar sa sai ta fashe da kuka. Har cikin ransa ya ke jin haushin kukan ta, dan shi bai ga abin kuka a nan ba.
"Ban yi aure da wuri ba Aysherh, i had my first child at 37yrs. Ina da abokai da 'ya'yan su na fari suke shekara goma, takwas, bakwai. Kai Cousin É—ina Bilyamin da ke Gombe, shekara É—aya aka haife mu, but his first daughter will be thirteen this year. Ba kya son haihuwa da ni ne?"
Shiru ta yi dan ba ta da abin cewa. Ita dai ta san tana son hutu, haihuwa ba wasa ba ne.
"Shekarun baya cikin wauta na tsara wa kai na iya 'ya'ya biyu na ke so. Amma yanzu i've changed, ina son 'ya'ya dayawa. Allah ya kawo mana ko nawa ne, da taimakon Ar-Rahman za mu kula da su, mu tarbiyantar da su bisa tafarkin addini, za mu yi komai dan mu inganta rayuwar su in har muna raye"
"Dole ka ce in haihu dayawa ai, salon nan da 'yan shekaru kaÉ—an idan na gama yin laushi ka je ka ce za ka auro wata sabuwa tunda na tsufa. Wallahi lokacin ne za ka san Aisha Farida ka auro"
Lallai Farida har yanzu da sauran shirmenta, abin da ya ke hanga daban abin da ta ke hangowa daban. Cigaba da magana da ita a wannan lokacin ma shirme ne.
Miƙewa yai ya je ya ɗau Yaman da ke bacci ya ce "ka da abinda ya samu baby na Aysherh. Or else..." ya sa kai ya fita ba tareda ya jira mi za ta ce ba.
Ranan gaba É—aya É—auke ma ta wuta yai dan har raba wajen kwana su ka yi, ya kwana a É—akin sa ita ma ta kwana a na ta.
Washe gari ma ko kulata bai yi ba. Tana gaishe shi ma sama-sama ya amsa ma ta. Haka su ka ci breakfast ba tareda wani ya yi wa É—an uwan sa magana ba. Yana gamawa ya tashi ya fita...
.............................
Yau kwana biyu kenan ma'auratan ba sa wani magana da junan su. Najeeb na dawowa daga office zai maƙalewa Yaman yana wasa da shi. Idan ya lura yana jin yunwa kuwa Tasallah zai kira ko matar Abdullahi su miƙawa Farida.
Najeeb na dawowa daga sallar Maghrib ya ga su Tasallah na fito da kayan Yaman ana sawa a boot ɗin mota. Farida na tsaye ɗauke da Yaman wanda ya sha kayan sanyi ma su kyau saboda yanayin garin akwai sanyi, itama Faridan da ganin shigarta fita za ta yi. Bai ce komai ba ya tsaya yana kallon ikon Allah. Farida ma kau da kai ta yi kaman ba ta gan shi ba tana jira su Tasallah su ƙarasa fito da kayan.
Sai da su ka gama Farida ta ce " ba'a manta komai ba ko?"
Tasallah ta ce duk kayan da ta ce a É—auko an É—auko.
Farida ta sa kai ta shiga mota dreba ya ja mota su ka fita a compound ɗin. Najeeb na tsaye a wajen yana ganin ikon Allah. Ran sa kuwa yai matuƙar ɓaci, mi Farida ke nufi da shi.
Ya isa cikin gidan da ƙyar saboda ciwon kai da ya fara ji saboda ɓacin rai. A hankali ya ke maimaita Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'oun saboda ya samu nitsuwa...
........................
Farida kam gidan su Najeeb ta wuce da Yaman. Da ta je a falo ta samu Mom da Najdah suna hira, itama ta zo gida.
"Oyoyo angona" Mom ta faɗa tana ƙarɓan Yaman a hannun Farida.
Shigowa da kaya da Danliti ya farayi ne ya sa Mom tambayar ko lafiya.
"Na kawo miki É—an yaye ne"
"ÆŠan yaye?" Mom ta faÉ—a tana sake kallon Yaman da ke hannunta. Yaron da watan shi bakwai da sati biyu ne a duniya.
"Mom yaron bai damu da nono ba, shima rashin son cin abinci kaman uban sa. Shi ne na ce gara na yaye shi"
"Amma Anty Farida da kin bari ya cika shekara ɗaya, Yaman fa bai da wani ƙwari" Najdah ta faɗa tana kallon Yaman ɗin da ke murmushi saboda Mom da ke ma sa wasa.
"Kema kina hanya ai za ki ji yadda ake ji. Allah ya kaimu nan da wata biyu lafiya"
Najdah ta yi shiru dan itama fama ta ke yi da kanta. Ta wahala sosai da wannan cikin tun yana ƙaramin sa har yanzu kuwa.
"'yata ki bari Yaman ya kai 10 months mana, Najeeb ma a wata goma na yayeshi"
"Mom ki yi haƙuri dan gaskiya na yaye shi daga yau"
Mom ta kalli Faridan da kyau ta yi murmushi dan ta lura kaman Faridan na É—auke da ciki ne...
Sai bayan sallar Isha Farida ta dawo gida. A falon sama ta samu Najeeb yana zaune sanye da baƙar jallabiya yana jan carbi.
"Barka da hutawa" ta faɗa tana ƙoƙarin tafiya ɗaki tunda har yanzu ba wai sun shirya ba ne.
"Aysherh" ya kira sunan ta a hankali.
Tsayawa ta yi tana jiran mi zai ce.
"Zo ki zauna?"
Ba musu ta dawo ta zauna a gefen sa.
"Ina ki ka kai min É—a na?"
"Gidan kakannin sa"