Sashe 59
Sakatariya Ta Psrt 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Son ka ga abinda matar ka ta yi ko? She is a fighter, she's a winner. Matar ka iron lady ce. Ka tashi ka ji, ka tashi ku gina rayuwar ku tare" ya kissing goshin sa yana shafa gashin sa.
"Daddy Mom ta dawo?"
"Sai next week" ya amsa ma ta.
"Allah ya dawo da ita lafiya"
Su ka amsa da Amin.
Anas kam kunya ta hanashi magana sai kau da kai ya ke. Daga baya Daddy ya bar su ya ce zai je yai magana da likita.
"Ya hanya" Anas ya katse shirun na su.
"Alhamdulillah mun je lafiya mun dawo lafiya. Sauro bai cize mu ba haka Cinnaka ba ta cize mu ba balle ayi tunanin mun wahala. Kuma dai girma ya faÉ—i"
"Farida dan Allah ki yi haƙuri. Na san ba ni da hujja akan abin da na aikata amma ki yi haƙuri ki yafe mun"
"Ya Anas a nan ka zo ka roƙe ni Allah Annabi akan na zama CEO amma mi ka yi bayan na zama CEO. Ka bauɗe min, ka ƙi goya min baya har ka na ganin gara ka bar aikin da zama na CEO ko?"
"Ba haka ba ne Farida, kawai dai ba na so kamfani ta shiga matsala ne"
"Da kyau, saboda ga Aisha Farida mai farar ƙafa ko?"
"Duk abinda ki ka ce i deserve it. Ban riƙe amanar abokina ba, i'm truly sorry"
"Ka san mi ake cewa namiji matsoraci? To Ya Anas kai matsoracin namiji ne kuma ragon namiji. Idan ba ka dena sa tsoro a lamurran ka ba to ba inda za ka je a rayuwa. Kuma ko a gidan ka za ka samu matsala. Kana ganin da ina da tsoro zan kai yadda na kai da Najeeb, ka san da ni matsoraciya ce da tun ranan da Najeeb ya koreni da na bar aiki a kamfani kenan. But i fight back, na nuna ma sa ni ba ƙwallo ba ne da zai dinga bugawa duk lokacin da ya ke so. Ka san miyasa Najeeb ya ka sa korata? Because he needs me. Najeeb na son mutum mai zafi, mutum da ba ya da tsoro ko kaɗan"
Ya ji haushin kiran sa rago da ta yi amma kuma gaskiya ta faÉ—a, sau tari ta inda su ke samun matsala da Najeeb kenan.
"Ki yi haƙuri dan Allah"
" na ji haushi kuma har yanzu ina jin haushin ka. Ka bani lokaci na huce tukunna"
"Ba komai, amma dan Allah ki yafe min"
"Na yafe"
Ba su sake wani maganan ba har Daddy ya dawo su ka tafi.
"My champ ka ga abokin ka ko, ka ganshi ko" ...
......................
Washe gari tana shigowa kamfani aka fara tafi, ana ma ta congratulations.
Duk wanɗanda su ke ma ta wani gani-gani to yanzu sun sha jinin jikin su. Madam Farida kamar yadda yanzu aka fi kiran ta ta zama Boss lady. Tundaga lokacin da ta ƙarɓi matsayin CEO kowa ya shiga taitayin sa saboda ita ma zafi gareta kamar Najeeb. Wani zubin ma gara Najeeb ɗin dan shi idan ya ma ka tsawa shi kenan amma wannan sai ta bika da baƙar magana wani lokacin idan ta yanko ma ka magana sai ka ji kamar ka kama kai ka rusa kuka.
Ga wanda ya bita sannu kuma tana da sauƙin kai...
Su Mr Vladimir bayan ya tabbata Farida ta leading team kuma anci gasa ba ƙaramin baƙin ciki su ka yi ba. Neman sulhu su ka fara yi dan kar su rasa 5% da au ka yi alƙawari amma kuma Farida ta ce bata san zance ba. Su su ka faɗi sharaɗi kuma dole su bi shi yadda ya ke. Haka dai ba tareda sun so ba su ma sa hannu a takardar da ke shaidar sun ba da 5% shares ɗin su a Najeeb. Ranan Farida sai da ta yi hawaye saboda hango farin cikin da ta yi a idon Najeeb idan ya farfaɗo ya ji abinda ta yi...
......................
Gidan AbdulWahab kam yanzu zaman lafiyan ba kamar da ba. Tunda Aneesa ta dawo Lagos da aiki sai komai ya chanja. Kullum cikin taƙalar Maijiddah ta ke yi, duk da ma yanzu Maijiddan ta dena tsoron ta kuma ta na ɗan maida ma ta magana amma still wassu lokutan shiru ta ke ma ta. Aksarin lokaci Maijiddah tana burin inama ace itama ta iya magana kaman Farida da za su dai-dai ta tsakanin ta da Aneesa.
Haka kawai ta hana yaran shiga harkan ta, duk da yaran na so amma abinka da uwa da ɗa sai ya zamana ta yi musu tsawa shikenan. Ɗan gara ma Alizah wani lokacin tana ƙin bin umurnin Maman na su.
AbdulWahab na iya ƙoƙarin yin adalci tsakanin su duk da ma yanzu Maijiddah ta fara ganin chanji a tattare da shi lokacin da Aneesa ta dawo. Tana renon cikin ta lafiya amma wani lokacin gani ta ke tunda Aneesa ta dawo kaman yanzu AbdulWahab ya rage ba ta kulawa da kuma ɗokin cikin da ta ke ɗauke da shi.
Cikin ta na wata bakwai Aneesa ta fara laulayin ciki. Ta gano hakan ne ranan su na zaune suna cin abinci ta fita da gudu tana amai a banÉ—akin da ke guest room.
Daga baya kuma Aneesan ta fara tsirface-tsirfacen abubuwa irin na ma su ciki.
Lokaci guda hankalin AbdulWahab ya koma kan Aneesa. Ranan su na cin abinci da ke Maijiddan ne ta yi girki, Aneesa ta fara kushe abincin akan an hana ta yawan cin mai a asibiti kuma ga shi abincin Maijiddan ya cika mai.
"Sweetheart ba ka gaya ma ta abinda likita ya ce ba ne?" Ta faÉ—a tana kallon Maijiddah.
"Anny zan gaya ma ta ba yanzu ba akwai yara a nan"
"Na san ba za ka iya gaya ma ta ba. To Malama Maijiddah ciki ne da ni kamar yadda ki ka sani, kuma likita ya ce saboda mahaifata tana da rauni na guji aikin wahala da yawan stress na kuma rage cin wassu abubuwa saboda kar cikin ya zube. Sai ki kiyaye nan gaba"
Maijiddah ta buɗe baki da hanci tana ganin wannan cin fuskan. Ƙarin haushin ma AbdulWahab bai yi magana ba.
Ajiye cokali ta yi ta bar wajen. Da ya ke kwanan ta ne AbdulWahab da ya zo sai ya ke ƙara gaya ma ta report ɗin da likita ya ce gameda cikin Aneesa.
Haushi ya kawo ma ta har wuya, ka sa shiru ta yi ta ce "amma Abban Alizah ni ma fa ciki gare ni kuma ko da babu likitan da ya gindayamin sharaɗi, dai a matsayin da na ke yanzu ina buƙatar kulawa ta musamman"
"Hauwerh dont get me wrong please, ba wai ina nufin ke baki buƙatar kulawa ba ne..."
"Sai yanzu na gane gaskiya. Dama saboda matar ka ba ta nan ka auro ni, to yanzu ta dawo ban da matsayi ko?"
"Shhhhh, kar ki sake faÉ—in haka Hauwerh ki na da matsayi babba a rayuwata"
" a rayuwar ka haka ne amma a zuciyar ka Anny ce kaÉ—ai"
Kamo hannun ta yai ta wafce hannun.
"Plz Gimbiyata, ki yi haƙuri. Ki na da matsayi a zuciyata da rayuwata gaba ɗaya"
Ranan dai AbdulWahab da ƙyar ya shawo kan amaryar sa...
.....................
Ko mi zai ma ta ba za ta koma Lagos ba. Gara ya dinga zuwa yana dubata duk ƙarshen wata. Ta bar mu su waje su sakata su wala yadda su ke so. Sai da motar su ta ɗau hanya sannan ta jingina kanta da seat tana hawaye. Babbar motar Macapolo ta shiga da zai je Kano daga Lagos. Duk da kasancewa dare ne hakan bai sa ta ji wani fargaba ba. Su na tafiya tana tuno maganganun AbdulWahab...
Sai da su ka dawo daga asibiti sannan ya je ɗakin Maijiddah dan ya bata haƙuri tsawan da ya ma ta ɗazu. Ya sani sarai bai kyauta ma ta ba. Duk abinda ya faru bai kamata ya gaya ma ta magana haka ba.
Wayam É—akin ba kowa. Ya duba ko ina ba ta nan. Mai aikin su dama ba ta nan ta yi tafiya. Fita yai ya je ya samu mai gadi inda ya sanar ma sa Maijiddah ta fita. FaÉ—a ya fara ma sa akan miyasa zai barta ta fita ita É—aya da tsohon ciki. Maigadi ya ce shi ya je ya samo ma ta taxi ma domin kuka ta ke yi ta ce an musu rasuwa ne za ta je gida kuma kai ka ce ta tafi saboda kun fita da Madam Babba.
Tsaki yai ya koma ciki. Ya kira numbarta sau ba adadi amma a kashe. Ba dai Maijiddah gida ta tafi ba.
Aneesa na kwance sai nishi ta ke ita a dole ta yi ɓarin ciki kuma kishiyar ta ce sanadi. AbdulWahab ya shiga tashin hankali sosai ina ya san zai nemi Maijiddah da daren nan...
Washe gari da safe ya samu labarin ta shiga mota ta tafi Kano. Kiran Hajiyar sa yai dan ya ji ko ta iso sai ya ga Hajiya ba ta ma sa maganar ba sai ma tambayar sa da ta ke ina Maijiddah. Sai alokacin ya waske da cewa ai tana hanyan Kano ma yanzu.
"Ko kai fa amma ka ce wai ta zauna a chan ta haihu"
Dama Hajiya Yelwa ta nemi ya bar Maijiddah ta haihu a kano ya ƙi shiyasa ba ta kawo komai aran ta ba.
Ƙarfe goma na safe su ka isa Kano inda direct gidan su mijinta ta wuce. Yanayin yadda Hajiya Yelwa ta ganta ya sa ta gane ba tafiyar jirgi ta yi ba.
"Lafiya Hauwa na ga kin kumbura, duba ƙafafuwan ki"
"Ba komai Hajiya zama ne kawai ya sa yai haka"
Hajiya Yelwa ta kira AbdulWahab tana ma sa faÉ—a akan barin Maijiddah da yai ta zo ita É—aya sannan a mota ba a jirgi ba.
Hamdala yai lokacin da ya ji Maijiddah ta isa gida lafiya. Ya bawa Hajiya haƙuri akan ayyuka su ka ma sa yawa.
"Hajiyata ki É—an bawa Hauwa wayar na kira numbar ta baya shiga ina ga wayan ya mutu ne"
Hajiya ta miƙawa Maijiddah wayar wanda ganin idon Hajia ya sa ta karɓa.