← Book details Sakatariya Ta Psrt 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 91

Sashe 19

Sakatariya Ta Psrt 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ƙarfe uku sai ga kiran Anas ya shigo wayar sa. Lokacin su na hanyar dawowa. Yana ajiye wayar ya kalli Farida da ta yi lanƙwas a motar ya fara faɗa.

"Miss Salihu are you nuts?"
(Miss Salihu kin yi hauka ne?"

"Kin fixing meeting da Mr Abraham ƙarfe uku ba tareda kin gayamin ba a wani dalilin?"

"Sir, ba ka ce min za ka fita ba ai. Kuma mantawa na yi"

"To hell with mantuwar ki. Miss Salihu, akwai dubban mutane da su ke neman aikin nan, idan ba za ki yi aiki da kyau ba zan kore ki"

Shi kan sa sai abin ya zamo ma sa banbaraƙwai wai 'zan kore ki' ba ma 'na kore ki ba' kamar yadda ya saba faɗi.

"Sir Najeeb dan Allah ka dena É—aga min hankali, dududu yaushe na dawo aiki bayan wannan iftila'in da ya sa me mu. Irin wannan rashin godiyar ne ya sa wallahi aikin nan ke fita min a ka. Ga shi mutum duk ya fiffige saboda aiki amma ba ka gani. Ni mutum ce kuma ba abun aibi ba ne ace na yi mantuwa tunda yana kan kowa"

Yana son maida ma ta martani amma ya rasa me zai ce. Yawan maganarta shi ne abu na farko da ya ja hankalinsa ranan da ya fara ganinta a restaurant, haka nan har yau bakin nan na nan. A kowani lokaci tana da abin faÉ—i choichoichoi. Tunowa da yai da kama su da aka yi da irin surutun da ya sha, ya sa ya san wannan Aisha Faridan a ko ina sai ta yi magana ba ta iya yin shiru......

............................

Tana zaune tana typing memo Anas ya shigo office É—in ta.
Sir Najeeb ya jima da fita kuma a yadda ya ce ya tashi kenan saboda zai daɗe. So ta ke ta ƙarasa abinda ta ke yi ta tafi itama duk da kuwa ƙarfe biyu ne saura. Ciwon cikin period ke damunta tun safe shiyasa ta ke nan laƙwas ba kuzari sosai duk da kuwa ta sha magani ya lafa ma ta kaɗan.

" 'yar uwa yau ba zoɓo ne? Kin san i'm addicted to your zoɓo"

" Ya Anas ban yi ba yau. Ni zoɓon ma zan dena gaba ɗaya tunda Sir Najeeb ya nuna indai na cigaba da sana'a a office to cikin albashina"

"Ya Najeeb zai ma na haka kuma?"

"Hmm kaman ba ka san shi ba, watan da ya wuce da ya zare 40% ai har yau shiru ka ke ji. Wai jiya Halima tana duba gwanjo anan da ya shigo ya gani haka ya dinga faɗa har da cewa wai ya ƙara ganin na buɗe hajata a office zai cire 10% a cikin albashina. Kuma fa ya Anas lokacin break ne ba wai a lokacin aiki ba"

Anas yai murmushi ya ce " kin fara gajiya da shi ne Farida? Ko za ki bar aikin?"

"Yaya kenan. Ni fa idan ka ga na ajiye aikin nan to aure na yi, na gano take-takensa ai, dama so ya ke na yi wani abu ya koreni. Mutum sai shegen taurin rai"

"Well, ni na ga alamun tun fara aikin ki da shi ya chanja, he's becoming more tolerant now. Allah! Farida da Najeeb É—in da ne da tuni kin bar aiki a nan"

"Hmm shi ya sani, wai ace mutum yai ta haɗe rai shi kaɗe ya ƙi shiga jama'a. Ai jama'a Rahama ne"

"Kowa da irin rayuwarsa 'yar uwa"

Har zai fita ya ce " ki ji har na manta. Akwai baƙin da za su zo gobe wajen Najeeb, ki scheduling lokacin meeting da su sannan ki sanarwa Najeeb on time kar ayi irin ta ranan"

"Ai ranan na sha kwarwa. Allah, Ya Anas na É—auka mari na zai yi yadda ya dinga banbamin nan"

"Sai ki kiyaye"...

Yana fita ta cigaba da aiki, tana so ta ƙare ta tafi gida da wuri dan kar ta yi staining dan ba ta zo da pad ba, ta ajiye a bakin gado za ta sa a jaka ta manta shi a wajen.

Minti ishirin ta haÉ—a komai sannan ta turawa Najeeb lokacin meeting É—in sa ta email. Tana kan tattare kayanta Halima ta shigo.

Halima Baballe tana aiki a hawa na ɗaya ne a HR department. Halima irin matan nan ne ma su gutsuri tsomi, 'yan haɗa waje. Bazawara ce aurenta biyu tana fitowa. Tun farkon zuwan Farida ta ke ƙoƙarin manne ma ta sai dai Faridan ba ta bata dama ba. Yawanci su ka haɗu a masallaci haka za ka ga tana liƙewa Farida tana kawo gulma da zunɗen mutane duk dan ta samu fada a wajen Farida tunda Farida sakatariyar Sir Najeeb ce, kuma kusan kowa a kamfanin yana son samun kusanci da Sir Najeeb.

"Anty nah Anty nah, ba dai kin tashi ba" ta faÉ—i tana washe baki

"Zan tafi gida, Sir Najeeb ba zai dawo ba kuma na gama aiki na"

"Sai na ga kin min wani lakwas, lafiya kuwa?"

"Halima yau ba na jin magana. Mi ya kawo ki?"

" Anty na kenan, baƙon wata ya zo kenan"

Farida ta yi tsaki ta saƙale jakarta a kafaɗa ta ce " mi ya kawo ki?"

"Anty na, za a yi bikin 'yar yata nan da sati biyu kuma wallahi adashen da na ke jefawa akwai mutum uku a gabana kafin na amsa shine na zo ko za ki ara min kuÉ—i?"

Kallon sama da ƙasa Farida ta ma ta sannan ta ce " kar ki kawo min rainin hankali nan wajen. Yaushe mu ka haɗa hanya da ke da har zan ba ki aron kuɗi na?"

Halima ta yi dariya tareda ɗan dafa kafaɗar Farida ta ce "ƙawata kenan..."

"Cire hannun ki a jikina tukunna" Farida ta katse ta

" duk yadda na ɗauke ki da zuciya ɗaya amma ke har yau ba ki ɗauke ni haka ba. Ita Sister Munibat ɗin da ki ke maƙalewa an gaya mi ki son ki ta ke? Kwanaki fa har cewa ta yi ke 'yar ƙwaya ce"

"Dalla gafara daga nan. Ba na son munafurci, halin ki na haÉ—a guri ya sa ba na son mu'amala da ke, idan da ba ki sani ba ki sani"

Halima ta ɗan haɗa rai ta ce " na rantse da Allah Munibat ta ce wai ke 'yar ƙwaya ce"

Farida ba ta ce komai ba ta ce biyo ni.
Tiryan-Tiryan su ka wuce office É—in Sister Munibat inda ta ke ta faman aikin zane.

"A'a Sister Aisha ke ce tafe, ban ganki a masallaci ba ko lafiya?"

Farida ta kalli Sister Munibat sannan ta kalli Halima ta ce " maimaita abin da ki ka faÉ—a a office É—ina"

Halima ta ji ras dan ba ta É—auka abinda Farida za ta ce ba kenan. Ta É—auka su na zuwa za ta fara yiwa Sister Munibat masifa.
Sai dai kamar yadda ta ke pro a wannan ɓangare sai ta dake, ta kalli Sister Munibat ta ce " cewa na yi Sister Munibat ta ce ke 'yar ƙwaya ce"

"Astagfurullah" Sister Munibat ta faɗi da sauri tana yin wiki-wiki da ido tana ƙara cigaba da istigfari a zuciyarta.

Farida ta ce " to kin ji mi tace?"

Kafin sister Munibat ta yi wani magana Halima ta amsa da cewa " za ki ce ba ki faÉ—i haka ba, ranan a masallaci. Idan kin manta ni ban manta ba"
Ta ƙarasa maganar tana matsowa kusa da ita kamar za ta maketa.
Jikin sister Munibat ya fara ɓari musamman da ta tuno abinda ya faru.

"Kin gani ai ta ka sa magana saboda ta san gaskiya ne, munafuka, kina jikinta kina zaginta"

Farida ta kalli sister Munibat ta ce " ki faÉ—a min gaskiya. Kin faÉ—i haka ko baki faÉ—i haka ba?"

Sister Munibat ta buÉ—e baki za ta yi magana sai hawaye.

"Shikenan! Kukan munafurci. Dama yare, yare ai sai a hankali, dukkan su munafukai ne"

"Yi min shiru" Farida ta daka ma ta tsawa. Ta kalli sister Munibat ta ce " kin bani mamaki. Ina É—aukan ki da daraja ina mugun mutuntaki. I consider you an older sister"

Ta juya ta fita saboda ba ta da ƙarfin yin masifa.

.......

Ƙarfe bakwai na yamma sai ga sister Munibat a gidan su Farida. Duk hayaniyar da ake na lissafe-lissafe a tsakar gidan, Farida ba ta ciki. Ƙarshen sati aka ce za a kawo lefen Maijiddah.
Tana chan kwance ta gama murƙususu akan gado saboda ciwon ciki. Maijiddah na gefe tana yiwa wata ƙaramar ƙanwarsu kitso.

"Anty Farida ga ƙawarki ta zo" Sadiq ya faɗa lokacin da ya faɗo ɗakin da gudu

Da ƙyar Farida ta ɗaga kai lokacin da sister Munibat ɗin ta shigo ɗakin su.

Sai da su ka gaisa da Maijiddah sannan ta zauna a gefen gado ta fiddo da ƙur'ani izub sittin ta ce " Sister Aisha na riga na yi alwala kafin na taho. Zan rantse mi ki akan abinda ya faru ranan da sister Halima ta ke faɗi"

Farida ta ɗan tashi jingine ta ce " bai kai har ga haka ba 'yar uwa. Ke dai ki gyara halin ki, zato zunubi ne ko da da gaskiya a cikinta. Sannan ki sani saka dogon hijabi ba shine ke nuna taƙawa ba"

"Na rantse da Allah sister Aisha ba abinda na faɗa ba kenan. Ranan da ba ki zo ba farko-farkon fara aikin ki, inaga lokacin bikin gidan kun nan ne. Ana taɗi shine aka kawo maganarki, cikin maida zance sai na ce *' sister Aisha kam wani lokaci idan ta yi wani abu kamar 'yar ƙwaya'*. Na rantse da Rabbil Arshi iya abin da na ce kenan"

Ta ja numfashi ta ce "dan Allah ki yafe ni sister Aisha"

"Ba komai, ya wuce. Sai ki kiyaye gaba, ki dinga taka tsantsan da mutane, dan abu É—aya za ka ce ace ka faÉ—i goma. Ita kuma Halima Baballe gobe sai na ci ubanta tunda haÉ—i ta ke son yi tsakanin mu"

"Kin yafe min?" Ta tambaya kamar za ta yi kuka

"Wallahi na yafe mi ki, nima ki yafe ni" Farida ta faɗa tana ƙara kwanciya akan gado...

............................
Chapter 19 · 0% Book details