← Book details Sakatariya Ta Psrt 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 91

Sashe 12

Sakatariya Ta Psrt 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yakubu girgiza kai kawai ya yi ya tada machine É—insa su ka tafi...

Sandy mai goge office É—in Najeeb ne ta cewa Farida Najeeb ya zo lokacin da su ka haÉ—u, za ta shiga lifter ita kuma Faridan ta fito.

Ta na ajiye jaka ta wuce office É—in sa. Yana duba wa su takardu ta shigo.
"Good morning Sir"
Ya ji shigowarta amma ya share ko É—agowa bai yi ba.

"Sir akwai aikin da zan yi ne?"

Sai a lokacin ya É—ago ya kalleta.
"What part of my message did you not understand?"

"Sir na ga saƙo ta email ranan Laraba wai an koreni daga aiki"

Ya É—aga ido ya ce "and?"

"Ban koru ba mana. Ba laifin da na yi sannan ko na yi laifi ma, tsarin da ka shirya min ya hana ka koreni"

"Listen Miss Salihu. Na san Saboda Anas ki ka dawo, but ki sani. This is my company, just like you Anas is my employee. So, na koreki ba abinda Anas zai iyayi akai. Now get out of this place bitch"

Fita ta yi daga office ɗin ba tareda ta ce ƙala ba. Minti biyu sai ga ta ta zo da takardu a hannunta

"Ga shi nan, wannan takardar shedar amincewarka ce da tafiyata. Wannan kuma kai ka amince zan yi aiki da kai na wata shida ba tareda ka koreni ba, idan har ka koreni to za ka dinga biyana salary har wata shida ta cika kuma......"

"Wait whats this? When did i sign this? I never signed this"

"Ka kalla dai da kyau Sir Najeeb Jibo. Ka san tabbas signature da ke jiki kai ka yi, you stamped and signed it"

"This is bullshit" ya faÉ—i tareda yaga takardun

Farida ta yi dariya ta ce " na nawa kuma wannan ma ba original É—in bane. Original É—in na nan, so ba inda zan je"

Ta fita daga office É—in...

Anas ne ya shigo office É—in ta da sauri "'yar uwa mi ya faru? Najeeb ya kira ni yanata kwarwa"

"Ce ma sa na yi bai isa ya koreni ba"

"Barin shiga na ji mi zai ce" ya shige office É—in Najeeb da sauri...

Yadda Anas ya ɗau alamarin fa ba da sauƙi bane. Domin Najeeb faɗa ya ke ma sa kamar tsohon zaki, cewa yai ya kawo ma sa mahaukaciya, yarinyar ba ta ganin girma ko darajar sa.

"Amma Najeeb we've talked about this ai, na roƙeƙa ka bata wani chance ɗin"

"To hell with her. I dont want to work with her, can you imagine wannan yarinya ta creating documents ta sa na signing ba tareda na san miye a ciki ba. The girl is a crook, she's just...."

"Haba yallaɓai. Duk wannan tashin hankalin akan mace, ban sanka da haka ba"

Najeeb ya kalli Anas ido cikin ido ya ce " get her out of this office or i will use force, and you know i will do it"

Ganin yadda Najeeb ya bircike ya sa ya fita ya samu Farida ya ce dan Allah ta koma gida zuwa gobe idan Najeeb ya huce zai kirata sai ta dawo. Farida ta tafa hannu ta riƙe ƙugu ta ce "Ya Anas ba inda zan je. Ai yau idan bai haƙura ba zai ga haukata muraratan. Ba ri ma kaga"

Ta wuce office É—in Najeeb.

"Ka ga Sir Najeeb kar ka bari na nuna ma ka haukata anan, kai shikenan ba dama mutum ya ɗan yi ƙaramin laifi sai ka ce kora, to yau ka gamu da gamonka. Ba inda zan je idan ka takura kuma na shigar da kai ƙara tunda da izininka na tafi hutu" ta san hakan zai iya faruwa shiyasa ranan laraba da ta zo ta typing documents ɗin ta haɗa cikin wasu da zai signing shi kuwa ko dubawa bai yi ba ya dinga signing ɗin su.

"Well lets see how tough you are" ya faÉ—i tareda É—aukar waya ya kira security.
Anas da ya shigo office ɗin ya fara bashi haƙuri. "please dont do this. Ba girmanka bane wallahi. Za ta bar maka aiki amma banda koran walaƙanci dan Allah"

Farida ta ce " Ya Anas ka barshi, security É—in su zo ina nan ba inda zan je"

"Farida ki yi shiru ki fita, i'll handle this"

"Yadda ya ke ji da taurinkai ni nawa ya ninka na shi. Mun fafata da arnan Jos ma balle shi"

Ana haka sai ga wasu murÉ—aÉ—É—un security sun shigo, dukkan su biyu da ka gansu ka san basu da mutunci da alama ma ba musulmai ba ne.

Najeeb ya tashi ya zo gaban Farida ya ce " for the last time, LEAVE"

"Allankatafir ba inda zan je"

Shi kam Anas baza ido kawai yai yana kallon wannan dramar.

Najeeb ya dubi securities É—in ya ce " throw her out of my company, i dont want to see her here again"

Ɗaya daga cikin securities ɗin ya nufo ta yana ƙoƙarin riƙe ta, aikuwa ta yi tsalle ta faɗa jikin Najeeb ta cukwuikuyeshi tana ihu tana faɗin wallahi ba zan fita ba ko za a kashe ni.
Najeeb ya rintse ido lokaci guda kuma hankalinsa ya tashi. Cikin zuciyarsa ya ke mamakin abinda ya faru, ba wai rungumeshin da ta yi ba, sai dai effect É—in da rungumar ya jawo ma sa. He cant believe he got erection because of this crazy girl.

Security É—in ya kai hannu zai janyo Farida daga jikin Najeeb, Anas ya daka ma sa tsawa ya ce su fita daga office É—in.

Najeeb har lokacin idonsa a rufe, ya rasa ya zai yi, he's afraid of pushing her away saboda Anas da securities za su ga yadda engine ɗinsa ta miƙe. He cant embarrass himself infront of this crazy girl dan haka cikin hikima ya sa hannu ya turata da ƙarfi before you knew it ya juya da sauri yai hanyar banɗaki.

Anas da ke recording abinda ke faruwa yai kan Farida da ta faɗi ƙasa warwas. " sorry 'yar uwa, tashi" da ƙyar ta miƙe da taimakon Anas saboda ƙugunta da ya bugu sosai...

Ya ƙara zuba ruwa a fiskarsa a karo na ba adadi. Ya kalli kan sa a madubi sai lokacin ya ga yadda jacket na shi ya ɓace da janbakinta.

"This girl is a witch. How could this possibly happen?"Rabon shi da shiga yanayi irin wannan ma ya manta....

"Oga ka fito ayi magana, ka haƙuran ne ko dai" muryan Anas ya katse shi.

Ajiyar zuciya yai sannan ya fito riƙe da jacket a hannunsa yadda ya riƙe ka ce kashi ne ajikin jacket ɗin. Yana fitowa Anas ya sa dariya.

"Get out Anas, i dont want to see anyone"

"Ka huta mutumina irin wannan al'amari sai da hutu ai"
Najeeb ya wurga ma sa jacket É—in. Anas ya chafe ya ce " wannan jacket É—in ta tarihi ce"
Sai da ya kai bakin ƙofa ya ce " kar ka manta za ka saurari presentation daga Team D ƙarfe goma. Zan sa sakatariyarka ta tuna ma ka idan lokaci ya yi"

Najeeb ya ce " Anas i'll kill you"....

Anas na fita ya samu Farida ya ce " gaskiyar Yaks da ya ce ke da Najeeb fire and fire ne sai dai gaskiya ta ki wutar ta fi tasa zafi. Kar ki bari kowa ya shiga office É—in sa sai nan da 1hr kafin nan ya huce"

Farida ta amsa da " ok"

Ko ajikinta dan ta san haƙarta ya cimma ruwa...

Yana zaune ya sa hannu a ƙirjinsa yana shafawa ashe yarinyar nan har cizonsa ta yi, da ya duba wajen a madubi yai wani jaa abinka da farin mutum.

"She'll pay for this, i'm not sending her away. Not until she suffer, i'll make sure she cry and cry and cry"

Yana zaune ya kunna laptop É—in sa " lets see what the witch is doing"

Tana zaune tana danna waya ga biscuit agefe tana ci. Har zai kashe sai ya tsaya saboda shigowar Khalidah da ya gani. " another bitch" ya faÉ—i a ran sa...

Kai tsaye hanyar office É—in Najeeb ta yi Farida ta ce " Malama tsaya"

A gadarance Khalidah ta juyo "and who are you?"

"Idon ki dai bai makance ba ina?. Kin san dai aikin wanda ke zama a kujeran nan ko"

"Ya kamata ki sani, matsayin ki bai kai ya hanani shiga office É—in Najeeb ba"

Farida ta taso " Sir Najeeb ya ce bai son ganin kowa sai nan da awa É—aya dan haka. Ko ke wacece sai dai ki dawo anjima"

"Ki hanani shiga idan kin isa?" Khalidah ta faɗi tana ƙoƙarin shiga. Farida ta sa hannu ta jawota da ƙarfi.

"Ki riƙe matsayinki Malama, ko kuma wallahi ni da ke sai mun kwashi 'yan kallo"

"Ki matsa na shiga. Ke kin ma san ni wacece a kamfanin nan?"

"Najeeb constructions na gani ba Najeeba constructions ba dan haka duk matsayinki a ƙarƙashin mai kamfanin nan ki ke"

"Hmmm za ki sha mamaki yarinya, ko kwana ɗaya ba za ki ƙara anan ba Najeeb zai koreki, wanda su ka fi ki nitsuwa ma ba sa daɗewa balle ke shashasha"

"Eh na ji dai. A bi doka a zauna lafiya"

Khalidah ta yi tsaki ta fita. Sai da ta tafi Farida ta ja numfashi ta ce " wai! na sha da ƙyar. Wannan matar fa ta riƙe ni ba ƙaramin jin jiki zan yi ba. Allah ya yi halitta anan"

Najeeb da ke kallon komai ya ce "scary bitch"...

..............

Ƙarfe goma saura minti biyar ya fito daga office ɗin sa.
"Sir na biyo ka ne?"
Bai kulata ba ya fita bayan ya harareta.

Da ya tafi ta ce " ka ji dashi, ni kam kujeran nan tawa ce ina nan daram da kai"

Lokacin da zai dawo tare su ka dawo da Khalidah. Su na shiga office ta cigaba da bayanin abinda Farida ta ma ta sai dai hankalin sa ma baya gareta yanaga takardun da ya shigo da su.

"Najeeb ba ka ce komai ba"

"She's doing her job" ya faÉ—i ba tareda ya kalleta ba
Chapter 12 · 0% Book details