← Book details Sakatariya Ta Psrt 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 6 OF 91

Sashe 6

Sakatariya Ta Psrt 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Waye ya girka abincin nan?" Tambayar da ta yiwa waiter kenan.

"Any problem ma'am?" Ya tambaya with politeness.

Farida ta kalli abincin ta kalle shi sannan ta ce "abincin ku shine problem É—in ai. Na san wadda ta girka abincin nan ko tantama babu Bayarabiya ce. Idan ba haka ba taya za'a yi jollof rice a restaurant kuma a cika ma sa yaji. An gaya mu ku kowa ne ke son yaji? ko kuma dai so ku ke mutum ya ci ya koma gida yana gudawa. Da a garin da ba zafi ne sai ace ya yi dai-dai amma wannan Kanon na ku da shegen zafi kuma ku dafa abinci mai yaji kuna ba wa mutane. Mi ku ke nufi?"

Waiter É—in bai gama fahimtar maganar Farida ba, saboda ba wani hausan kirki ya iya ba. Shekaran sa na uku kenan a Kano. Ya dai gane kalmar 'Yaji' dan haka ya ce " ma'am with due respect, i dont think the food is pepperish"

Farida ta hangame baki " Yo ƙarya na ke yi kenan?"

"Sorry ma'am"

Rayyan ya girgiza kai ransa a ɗan ɓace ya ce " Farida dan Allah ki barshi haka, bari a kawo mi ki fried rice"

"A'a Ray, sai ya taɓa abincin nan ya ji dan ya tabbatar da magana ta"

Wani matashi wanda tun shigowar su Farida ya ke ankare da yadda ta cika wajen da surutu ya taso ganin dramar da ake yi.

"Haba Madam. Tun É—azu ki ke damun mutane da surutu fa, kar ki manta nan public place ne"

Kallon sama da ƙasa ta ma sa sannan ta ce " Malam sa'ido,gulma da munafurci. Kunnen ka bai jiyo surutun da ke fitowa daga TV ba sai nawa. Tsabar ha'inci ka bar matarka da cin garau-garau , ka zo ka tisa tumbinka a gaba kana cin fried rice da chicken, Allah wadai"

Kunyar da Rayyan ya ji ko wanda aka yiwa maganar bai ji ta ba. A ƙalla mutumin nan zai kai shekara Arba'in, amma Farida ba ta ga girman sa ba ta ke yaɓa ma sa magana.

Mutumin ya zuba ido yana kallon ta kawai tsabar mamaki.

"Kalleni da kyau Malam na fi ƙarfin ka, inma kana ƙungiyar mafiya ne to jinina fau-fau ya fi ƙarfin ka"

Mutumin ya kalli Rayyan ya ce "ɗan uwa gaskiya kana ƙoƙari. This girl is fire" sannan ya koma table ɗin sa.

Ta ce "Ba fire ba Volcano. Mtsww"

Ta kalli waiter ta ce "taste this food before i loose my temper"

Da sauri ya ɗau sokali ya ɗeba abincin ya taɓa. Irin masifan da ta yiwa mutumin nan wai ta ce ba ta loosing temper ba to idan ta yi ya za ta zama kenan.

Tabbas abincin ya É—an fito da taste É—in yaji amma bai kai har yadda Farida ta kururuta ba.

"Sorry ma'am, i apologise on behalf of our kitchen...."

Lokaci guda Najeeb ya miƙe tsaye hakan ya bashi damar ganin fiskar budurwar wanda alokacin ke yiwa waiter bayanin abinda zai kawo ma ta a madadin jollof rice mai yaji da su ka kawo. A yadda ta ke masifa ya ɗauka zai ganta gabjejiya sai ya ganta 'yar mitsila bai fi mutum ya mangajeta ba amma sai shegen baki. Kallo ɗaya ya ma ta ya ɗauke idon sa ya fice daga restaurant ɗin.
A mota ya jira Anas wanda shi kam sai da ya ci yai naÆ™ sannan ya fito.

"Mutumina ka san yarinyar nan ta bi waiter har kitchen É—in su. Na ji tausayin saurayinta wallahi, haka yai wani lafau da shi abin tausayi"

Najeeb ya ce " its his fault ai, ta ya zai dating lousy girl kamar wannan"

"Yarinyar tana da kyau ba laifi, sai dai surutu kam Tabarakallah ko gidan radio iya ka ci" ...

Rayyan da Farida kuwa ba su suka bar restaurant É—in ba sai da Farida ta sauke masifar ta ta huce. Shi Rayyan abincin ma kasa ci yai, ita kuwa aka kawo ma ta fried rice ta naÉ—a harda take away ta yi.

....................

"Gaskiya Yaks idan na ce ma ka akwai vacancy a ƙasa na yi ƙarya, sai dai ka bani lokaci nan zuwa next week zan bincika, idan ma ba ta samu anan ba zan iya nema ma ta a wani wajen. Ai ƙanwar mu ba za ta rasa aiki ba Insha Allah"

Yakubu yai ma sa godiya sannan ya fice daga office É—in.
Anas kenan, yana da sauƙin kai ba kaman Oga kwata-kwata ba, wanda mulki da girman kai ya hanashi sakewa da mutane. A shekarun sa na uku da fara aiki a Najeeb constructions sun saba da Anas sosai, tamkar yayansa haka ya ɗauke shi...

Anas na tattara wa su files kiran Najeeb ya shigo wayar sa, dama files ɗin wajen Najeeb zai kai su dan haka ya amsa wayan da sauri dan ya san abokin na sa da gajen haƙuri.

"Mr Man yanzu na ke shirin kawo ma ka files É—in"

Cikin huci Najeeb ya ce " Anas ka san that stupid boy bai zo ba, and numbar sa ba ta shiga. Find a replacement, ba zan iya da shi ba"

"Calm down Yallaɓai, barin zo office ɗin sai mu yi maganar...

Duk yadda Anas ya so Najeeb ya ƙarawa Joseph lokaci hakan bai yiwu ba, ƙarshe dai cewa yai ya nemo ma sa wani ko wata.

"Gaskiya you need to change abokina, this guy is good, and kai ma tsakani da Allah ka san kwana ukun da ka bashi ya yi ma sa kaÉ—an"

"I dont bloody care. Zaman shi a chan ba zai dawo da wanda ya mutu ba neither will it profit him in anyway. So why will he risk his job for that"

"It's his mother's burial, kuma kasan al'adun su da namu ba É—aya bane"

"And so freeking what?. Just ka nemo wani kawai"

Anas ya kalli abokin na sa cike da takaici ya ce " ba kowa ke da mummunan ra'ayi irin taka ba Najeeb, just because ba ka É—auki mahaifiyar ka a bakin komai ba doesnt mean kowa ma haka ya ke. Joseph yana son mahaifiyar sa, shiya sa ya tsaya yaiwa mahaifiyar sa proper burial kaman yadda al'adar su ta tanada. I hope you understand that"

"Oh please Anas! Not this talk again"

"Ka na so, ba ka so, gaskiya ce dole na faÉ—a ma ka duk min É—acin ta kuwa"

"Find another secretary for me Arch Anas Ali Almustafah"

Kallon-kallo su ka yiwa junan su kafin Anas ya fice daga office É—in.

*💮SAKATARIYA TA💮*
.......(My Secretary).......

*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

*Free page*

0️⃣0️⃣4️⃣

Ranan Tuesday sai ga Joseph ya zo office, ya sani sarai Najeeb zai yi fushi da shi amma bai ɗauka abin zai kai ga kora ba. Infact, irin koran walaƙancin da Najeeb ya ma sa sai da yai dana sanin fara aiki da Najeeb. Tun farkon zuwan sa kamfanin ya samu labarin halin maigidan na sa a wajen sauran ma'aikata, sai dai bai ɗauka abin na sa ya kai yadda ake faɗi ba sai da ya gani muraratan.

Anas dai ba yadda ya iya ne amma ran sa ya sosu da abinda Najeeb yai wa Joseph.

"Sir, he gave me 3 days, only 3days. I left Kano on tuesday morning, i reached my village on wednesday. My mother was buried on saturday and i make sure i squeezed myself and came back to Kano on Monday night. But he wont listen"

Joseph ya faÉ—i yana goge hawaye. Shi takaicin sa ma bai wuci yadda Najeeb ya nuna halin ko in kula da mutuwar mahaifiyar sa ba.

Anas ya kalle shi ya ce "please dont take it personal, Najeeb doesnt even respect his own mother. I'm sorry about your loss Joseph, i lost my mother when i was only 7yrs so i know how you feel"

Kalaman Anas su suka kwantarwa Joseph hankali har ya ƙarɓi check ɗin da Anas ya bashi sannan ya tafi...

.....................

Ido Yakubu ya zaro lokacin da Anas ya gaya ma sa akwai vacancy na ɓangaren secretary ɗin Najeeb.

Indai kana aiki da Najeeb Constructions to dole ne ka san halin Najeeb balle kuma jiya-jiya Najeeb ya gama koran Joseph wanda harda kira ma sa security su fita da shi, ba dan Anas ya sa baki ba Allah kaÉ—ai ya san halin da Joseph zai shiga.

"Kana tsoron kar a walaƙanta ƙanwarka ko?" Anas ya jefa ma sa tambaya

"Na ma ka alkawari zan yi ƙoƙari na ga ƙanwarka ba ta walaƙanta ba, za tai aiki da Najeeb na lokaci kaɗan ne ana samun wani vacancy ɗin zan chanja ma ta aiki"

Yakubu ya sauke ajiyar zuciya ya ce " Aikin Farida da Sir Najeeb ba mai yiwuwa bane, idan Farida ba ta ƙona shi ba to shi zai murɗe ma ta wuya ya kasheta. Ka san Farida kuwa? Ai Najeeb da Farida su ka haɗu anan kamfanin inaga ƙonewa kawai zai yi dan wuta da wuta ne"

Dariya Anas yai ya ce " har akwai yarinyar da za ta iya karawa da Najeeb? Gaskiya zan so ganin wannan Faridan"

"Hmm, na san halin Sir Najeeb na kuma san 'yar uwata Farida, amma wallahi duk inda Sir Najeeb ya kai da jin kai da miskilanci to Farida ta taka shi. Maganar ta zama Sakatariyar sa ma bai taso ba. Farida Farida Hmm..."

"Wallahi ni kuma da ka yi bayanin nan sai na ga sun dace gara a samu wacce za ta iya taka ma sa birki ko zamu huta da halin san nan"

"Allah akwai matsala idan Farida ta yi aiki da Sir Najeeb, yaƙi za'ayi fa a kamfanin nan"

"Kar ka damu mutumina, ka turo ta kawai na ma ta interview"

...........................
Chapter 6 · 0% Book details