← Book details Sakatariya Ta Psrt 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 91

Sashe 31

Sakatariya Ta Psrt 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Lokacin Najeeb yana ji da kan sa matashi ɗan shekara ashirin da bakwai. Sai dai kash! Saura kwana biyar a ɗaura aure Sabreen ta gudu bayan ta ajiye wasiƙa akan Najeeb yai haƙuri tana son sa amma ba ta shirya aure yanzu ba. Wannan shi ya ƙara birkitar da al'amarin Najeeb. Cikin ƙanƙanin lokaci ya lalace ya koma mara haƙuri mara fara'a kwata- kwata.
Wannan dalilin ne ya sa ya dawo Nigeria ya buɗe kamfanin sa, kuɗin da ya ke da shi da kuma aron kuɗi da ya ƙarɓa a wajen Daddy da su ya haɗa ya tada Najeeb constructions har ta zama abun da ta zama a yanzu. Shekaru bakwai kenan da su ka wuce ana cikin na takwas. Ba abin da ya ƙara ɗasawa Najeeb tsanar Sabreen irin bayan wata takwas da guduwa da ta yi sai ga shi an saki film ɗin da ta yi cikin turawa har tana kissing ɗin wani ƙaton kafiri a cikin film ɗin....

*SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......

*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

0️⃣1️⃣8️⃣

Farida na zaune a office wani babban mutum ya shigo office É—in. Cikin fara'a ta gaida shi saboda irin su ne idan sun zo wajen Najeeb su ke ba ta alkhairi idan za su tafi.

"Barka da zuwa ranka shi daÉ—e"

"Yawwa beauty, sannu da aiki"

"Wa za ace ya zo?"

"Alhaji Matawalle"

Ta É—au phone ta kira Najeeb. Yana É—auka ta gaya ma sa ga Alhaji Matawalle ya zo.
Tana ajiye wayar ta ce " ka shiga"

Sun ɗan gaisa kafin su ka fara tattaunawa kan abinda ya haɗa su. Kusan 30mins suna magana kafin su ka cimma matsaya ɗaya. Najeeb ya ƙarɓi takardun hannun Alhaji Matawalle yana dubawa kafin yai signing.

"Na ce ba, wannan sakatariyar kan nan..." bai ida maganar ba Najeeb ya É—ago ido ya ma sa wani kallo.

Maganar da Alhaji Matawalle ke son faÉ—a daban amma dole ya haÉ—iyeta ya buge da cewa

"matar aure ce?"

"Alhaji Matawalle ka zo waje na ne ko wajen sakatariya ta ka zo?"

"Kai Allah yarinyar nan tana da kyau ga fara'a ga...."

Najeeb ya ture takardun hannunsa gefe ya ce " idan ka shirya aiki da ni sai ka dawo"

"Haba Najeeb, wanni irin magana ne wannan?"

"Ka jini da kyau Alhaji Matawalle, now leave"

"Shashashan banza shashashan wofi. Har ni za ka kora a office É—in ka. Za ka gani"

Alhaji Matawalle ya É—au takardun ya fita fuuuu...

............

Ranan Jumma'a bayan an dawo daga sallar jumu'ah Najeeb ya kira ta.

"Ki shirya, za mu je Lagos ranan monday"

"Haba yallaɓai ai ko ni buhun gawayi ce iya ka ci. Haka kawai ka ce in shirya mu je Lagos ba tareda na san abinda za muyi ba"

Ya ɗan yi shiru na wasu daƙiƙai kafin ya ce " akwai 2days bid da za'ayi a Lagos and its important for this company"

"Zan tambayi Baffa, idan ya barni to idan bai barni ba shike nan sai ka je kai kaÉ—ai ko ka É—au wani ku je tare" daga haka ta fita daga office É—in.

Da dare ta samu Baffa Musa da maganar amma ya ce ba za ta je ba.

"Baffa ni da Oga na ne fa"

"Ogan na ki mijin ki ne da za ki bi shi har Lagos da sunan aiki, ku je kuna kwanan hotel"

"Baffa daÉ—ina da kai gidadanci"

Daƙuwa ya ma ta ya ce "zan ci uban ki Farida"

"Yo Baffa ai kai ne Uban nawa, sai ka ci kan ka, kawai"

Baffa ya taso zai mangareta ta fita daga falon da gudu tana dariya.

"Wannan yarinya wannan yarinya, Allah dai ya shirya min ke"

Baffa bai amince da tafiyar ba sai ranan Lahdi bayan ta ma sa alkawarin a gidan Maijiddah za ta kwana ba a hotel ba.

Ranan monday Najeeb da Farida su ka wuce airport da sassafe, wanda dreban Daddy ne ya kai su, ba su jima ba jirgin su ya lula sama.
Wannan karan ne farkon hawa jirgin Farida, ta dinga surutu tana cewa " dama ance albarkacin Kaza ƙadangare kan sha ruwan kasko, Sir Najeeb na gode Allah ya samu a damshin ku, irin wannan matsayi haka. Wa ya ga Aisha Farida ta shiga jirgi"

As usual bai tanka ma ta ba dan ba ya da abinda zai ce. The girl talks too much...

Kamar yadda aka tsara É—in su na gama taron na ranan dreban gidan AbdulWahab ya zo É—aukan ta.

Da za ta tafi ta ce "Sir Najeeb ka zo mu je a rage ma hanya"

Idon sa ne ya ba ta amsa ba baki ba. Ta san ma'anar Kallon na sa dan haka ta ce "Allah ya ba ka haƙuri, sai gobe"...

Gidan Maijiddah ya ma ta kyau ɗakuna shida ne a gidan. Uku a sama uku a ƙasa, ɗakin AbdulWahab Aneesa da kuma yara su ne a sama ita Maijiddah kuma na ta na ƙasa.

Saboda traffic ba su isa da wuri ba duk sai da ta gama gajiya kafin su ka iso.
Maijiddah a É—akin ta ta sauketa, tana tsananin farin cikin ganin ta.

"Barin kawo miki abinci Anty Farida, kafin nan ki ɗan watsa ruwa, ga banɗakin" ta nuna ma ta ƙofar banɗakin da ke cikin ɗakin.

"O'o su Jiddah Amarya, muma dai za mu zo wajen"

Har Maijiddah ta kai bakin ƙofa ta ji Farida na salati. Ta juyo da sauri "Anty miya faru?"

"Jiddah ashe duk jan kunnen da na miki duk a banza. Dan Allah a ina kika samo wannan bujen kayan"

Maijiddah ta kalli kan ta, pakistan ta saka riga da wando amma wandon irin mai buje É—in nan ne.

"Anty a cikin kayan lefe na ne"

"Ki na amarya auren wata biyu da 'yan kai, ki ɗauko wannan bujen wandon ki saka, dan Allah dan Annabi. Wallahi ko ni budurwa ba zan sa bujen wando haka ba balle ke matan aure, ga pakistan ma su pencil wanduna ba ki sa ba sai ki sa mai bujen wando. To maza ki cire kuma idan ba wai kin kai an shaping wandon ba kar ki ƙara saka kayan nan"

"Anty na ji, ki shiga ki yi wanka ina zuwa"...

'Yan kwana biyu da Farida ta yi a gidan Maijiddah ta sha faÉ—a kaman ba gobe, musamman da Jiddan ta ba ta labarin irin kayan da Aneesa ke sawa idan ta zo.

"Ke me ya hanaki sa irin kayan?"

"Anty Farida, a gaban yaran sa sai insa ƙananan kaya 'yan ficil-ficil ɗin nan. Idan uwar su ba ta da kunya ni inada shi"

"Lallai ke jaka ce Jiddah, dama ustazan nan yawancin ku sai a hankali. Wacce ayar ce ta hana ayiwa miji shiga ta ado da jan hankali"

"Anty Farida ba fa mukaÉ—ai ba ne a gidan"

"Maza na shigowa ne?"

"A'a"

"To wallahi ki shirya zama boyi-boyi a gidan nan, very soon idan kin gama amarcin nan za a ajiye ki gefe saboda ƙauyanci da gidadanci da ya mi ki yawa"

Maganganun Farida shi ya ke ta yawo a ƙwaƙwalwarta lokacin da ta ke dudduba ƙananun kayan da Faridan ta ba ta lokacin auren ta.
Ranan laraba su Farida su ka tafi ita kuma Aneesa ta zo ranan Alhamis da dare. Duk cikin weekend É—in nan a takure ta yi shi. Dama tsarin AbdulWahab É—in ko na Aneesan ne ma oho, duk lokacin da Aneesa ta zo to yana É—akinta har sai ta tafi, ita kuma sauran ranakun na ta ne.

Yau da safe Aneesa za ta koma Abuja. For once a rayuwarta tana so ta cire kunya da tsoro.

Ta tuno faÉ—an Farida lokacin da ta ce kunyan saka kayan ta ke ji.
"Shegiya kunya ya ƙare a abinda kukeyi da dare. Miye bai ganiba ajikin na ki da za ki dinga ɓoye ma sa"

Ta ɗauko micro mini skirt na blue denim jeans ta saka, cikin tops ɗin da Faridan ta haɗo da shi ta ɗauki wata fara wanda ta fi kama da vest amma V-neck gareta. Ta tsaya jikin madubi tana kallon kan ta, da ke guntuwa ce sai ƙananun kayan su ka amsheta sosai. Ta tufke gashinta da ta sawa ribbon ta nannaɗe shi kamar doughnut. Idan akwai abu ɗaya da ta san mijinta na so kuma ya ke ja ma sa hankali bai fi gashin ta ba. Dama Farida ta gaya ma ta kowanni namiji akwai abinda ya fi attracting na shi a jikin mace. Wa su ƙirji, wa su hips, wa su ƙafa wa su gashi da sauran su. To itakan ta san dogon gashin ta ne, AbdulWahab ba ya gajiya da shafa gashinta yana sa fiskarsa ciki yana shaƙar ƙanshin sa.
Takalmi mai ƙasan wedges ta saka dan ba ta iya tafiya da heel ba...

Su na cin breakfast a dining ta fito. Alizah ce ta fara hangota ta ce " Wow! Anty you look beautiful"

Ta É—an yi murmushi ta ce "Thank you dear"

Sai da ta zauna Baby ta ce " i love your hair Anty"

Maijiddah ta yi murmushi, ta sa hannu tana wasa da gashin na ta ba tareda ta yi yunƙurin ɗiban abinci ba.

Normally idan Aneesa na nan ba ta zama ta ci abinci da su amma yau tana so ta rama abinda Aneesan ke ma ta ne.

Shi kam AbdulWahab tunda ya ɗaga ido ya kalleta bai iya saukewa ba. Sandwich da ya riƙe tuntuni shine bai sauke ba kuma bai ci ba. Sai da Aneesa ta yi magana sannan hankalin sa ya dawo jikin sa.

"Sweetheart za ka dropping É—ina a Airport ko?"

" No Anny, zan makara idan na kai ki"

Ta gama gane mijin na tan ya ɗan bircike akan Maijiddan. Ta san mijinta na son ya ga mace ta sa sexy ƙananan kaya, shi ya sa duk lokacin da ta zo ta ke sawa dan hankalin mijinta ya tsaya a kanta, sannan a tunanin ta Maijiddah ba za ta iya saka irin waɗannan kayan ba dan tun day one da ta ganta ta ke ma ta kallon local girl. Sai ga shi kuma yau ta proving na ta wrong.
Chapter 31 · 0% Book details