Sashe 10
Sakatariya Ta Psrt 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Miss Salihu is that clear!" Ya daka ma ta tsawa.
"Yes...yes Sir"
"Good, now get out of my office"...
Tafi minti goma ta rasa yadda za ta arranging files É—in da ya bata, kamar da gayya aka hargitsa files su ka zama haka. Tana cikin yi kira ya shigo, ta yi tsaki kafin ta É—auka.
"In my office now"
Doguwar tsaki ta ja sannan ta tashi ta wuce office É—in sa.
Ce ma ta yai yana da meeting ƙarfe shabiyu. Baƙin ciki ya zo ma ta har wuya. Maimakon ya gaya ma ta da ya kira sai da ya bari ta sha wahala ta zo har office ɗin sa.
"Why are you still standing, get out?"
"Sir, na san kai Oga na ne kuma zan ba ka girman ka amma kuma wallahi ba zan ɗau walaƙanci ba. Sir daga zuwa na na yi jelen tsakanin office ɗinka ya fi sau goma. Haba dan Allah, indai saƙon magana ne idan ka kirani sai ka gaya min ba wai sai na zo har nan ba. Wannan ai salon mutum ya samu ciwon baya ne"
Ganin ya miƙe ya sa tai shiru. Har gabanta ya tako ya tsaya. " Miss Salihu, i know you are a lousy crazy girl but that should stop outside this company. Here, you are just a secretary, so work like one" yana gama faɗin haka ya fice daga office ɗin ya bar Farida baki buɗe.
"Allah ya isa na, mugu kawai. Daga ranan farko a addabi mutum da aiki kaman Jaki" ta yi tsaki sannan ta fice daga office É—in...
...........................
Ƙarfe sha biyu saura minti biyu ya fito daga office biye da shi kuma sakatariyar sa Farida, tana ɗauke da wasu files a hannunta. Lifter su ka shiga saboda a second floor za a yi meeting ɗin. Ƙanshinsa ne duk ya bi ya cikata, ta rasa wannan ƙanshin na shi, its so inviting, so cool.
Kiiiinnnnn. lifter ta tsaya su ka fito yana gaba tana bin bayan sa har su ka shiga hall É—in.
Kowa ya hallara a wajen dama shi ake jira. Dokar Najeeb ne lateness is a punishable offence.
Ta samu kujera kusa da mace É—aya da ke wajen ta zauna bayan ta ajiye files a gaban Najeeb.
Duk yawancin bayanan su ba ganewa ta ke yi ba, ko dan maganar ta fi karkata zuwa ga ayyukan gine-gine da kamfanin ke yi ne...
Ƙarfe ɗaya saura minti biyar aka rufe meeting,su ka fito.
Yanzu ma bayanshi ta bi su ka haura. Sai dai ta yi laushi sosai tana ajiye files akan table ta kwantar da kanta.
Rufe ƙofar da yai ya sa ta ɗago idon ta. Ya cire suit ɗin sa, farar shirt ɗin ne kawai ajikinsa yana warware hannun rigar da alama dai alwala yai. Su na haɗa ido ya ƙara haɗa rai...
Sai da ya tafi ta fara ƙoƙarin neman banɗaki dan ta yi tsarki ta yi alwala. Office ɗin ta dai babu, ƙoƙarin fita ta ke matar ɗazu ta shigo office ɗinta.
"Assalamu Alaikum sister"
"Wa'alaikissalam, 'yar uwa sannu da zuwa"
"Suna na Munibat AbdulHamid, i'm an Engineer. Office É—ina na second floor"
"Masha Allahu. Suna na Aisha Farida, sabuwar sakatariyar Sir Najeeb"
"Na ce dama ko zamu sauka mu je sallah. Akwai masallaci a ƙasa"
"Wallahi na gode, kamar kin san abinda ke raina kenan , dama banÉ—aki na ke nema"...
Fita su ka yi Sister Munibat ta nuna ma ta inda banÉ—akin mata ya ke, sannan su ka sauko su ka wuce masallaci. Anan Farida ta ga wa su ma'aikata matan duk wanda tacewa ita sakatariyar Sir Najeeb ce sai su ce "Hmmm, Allah ya sa ki iya dan Sir Najeeb Sai a hankali"
Ita kam ba ta ce komai ba dan tun kafin su faÉ—i haka ta ji a wajen Yakubu da Anas.
Daga masallaci canteen ɗin kamfanin su ka wuce, su na shiga Farida ta hango Yakubu da wasu su na cin abinci dan haka ta yi saurin ƙarasawa wajen table ɗin su.
"Yaya Yakubu ka siya min abinci yunwa na ke ji"
Yakubu ya harareta ya ce " idan ba ki da kuɗin siya ki je ki karɓi ruwa, ruwa is free for all the workers here"
"Haba dan Allah, na ce ma Yayan ma ba za siya mun ba"
"Yayan ai ba na Allah Annabi bane. Na cin hanci ne"
Engr Mathew da ke gefe ya ce " sister ki zauna za'a siya miki abinci. You are our beautiful sister ai"
Farida ta je ta jawo kujera ta zauna. Yakubu ya ce "Matt, wannan yarinyar ci ta ke kamar gara ga ta da shegen son bati. Idan za ka bi shawarata ka barta ta siya da kanta idan ba haka ba kullum kai za ta maƙalewa"
"No problem, this beauty deserve to be serve like a Queen"
Farida ta yiwa Yakubu gwalo...
Su na cin abinci Najeeb da Anas su ka shigo, nan wajen yai tsit. Kai tsaye wani gefe su ka je su ka zauna inda wajene da aka tanada ɗan gefe da sauran mutane. Kujerun wajen da table ɗin ya fi sauran ƙayatuwa. Wajen cin abincin Sir Najeeb kenan, da ke Anas shi ne na hannun daman sa sai ya zamana tare su ke zama su ci a wajen.
Jin wajen yai shiru ba kamar yadda ta fara shigowa ba ya sa Farida cewa " ni kam mutuwa ce ta wuce ne? Na ga kowa yai shiru sai ƙaran sokala da fork kawai"
Yakubu ya taƙaleta ya mata nuni da ido. Sir Najeeb da Anas ta hango su na cin abinci.
Ta gane saboda Sir Najeeb ne kowa ya nitsu a wajen. Sakamakon da da ake cin abincin ana hira yanzu kam kowa abincin ya ke ci baki gum.
"Ya Anas...Ya Anas" muryarta ya karaÉ—e wajen.
Anas da ya ke kurɓan juice ya ajiye glass ɗin ya juyo da sauri. "A'a 'yar uwa ke ce, ya aiki"
"Lafiya yayana. Yaya wai ni an saka dokan hana magana ne anan? na ga anyi shiru"
Anas ya ce " ni ma ban sani ba amma ki tambayi Ogan ki"
Farida ta maida kallonta wajen Najeeb da ya cika ya kumbura kamar zai fashe. Ta ce " Sir Najeeb ka hana magana a nan ne??" Tambayar ta fi kama da gatse ko shaƙiyanci kuma da gangan ta yi hakan. Tashi Najeeb yai ya bar wajen. Yana fita daga canteen ɗin aka sa ihu. Wasu sai a lokacin su ka san miye aikin Farida, ta burge kowa, sai dai dayawa sun ji tausayinta dan a tunaninsu ƙarshen aikinta ya zo kenan. Harta Anas sai da yai dariya, shi kam sai da ya cinye abincinsa kafin ya tafi.
Suna fitowa a canteen É—in Yakubu ya ce " tunda aikin ne bakyaso shikenan. Idan ya koreki za ki san zafin neman aiki ai"
"Haba Yakubu, mutumin nan fa mutum ne amma yadda ku ke zuzuta shi ku ke tsoronsa sai ka ce wani ifritun Aljani"
"Ni dai na gaya mi ki"
Wai da su ka taho da Sister Munibat ma harda ba ta addua'ar da za ta yi idan ta shiga office, ita kan dariya kawai ta yi ta wuce.
..........................
Tana zama a kujerar ta aka kira, as usual dai cewa yai ta zo.
"Sir gani"
Kallon walaƙanci ya ma ta sannan ya jefa ma ta takardar da ke hannunsa.
"Read it"
Tsugunnawa ta yi ta É—auko takardar ta fara karantawa a zuciyarta.
"Read it loud" ya daka ma ta tsawa
Haka ta fara karanta ma sa daga farko har ƙarshe. Sai da ta tsaya sannan ya ce " i'm sure lokacin da aka baki takardar ɗaukan aiki an haɗa mi ki da wannan takardar, but you are so dumb to not have read it. Now, daga gobe ki fara shiga irin yadda aka tsara a dress code ɗin nan. This is a construction company not a fashion show"
"Sir, ni banda kuɗin siyan kaya irin wannan, kuma dai yau na fara aiki balle ace zan samu albashi dan haka sai ka yi hakuri har na karɓa albashi tukunna"
"Miss Salihu you are stepping beyond your limits, dont you dare talk back to me again" ya nuna ta da yatsa
"I gave you a week to find cooperate clothes. A week Miss Salihu"
"Ok Sir"
Hannu ya É—aga ma ta ta juya ta tafi.
Ta É—auka zai ma ta maganar abinda ya faru a wajen canteen sai ga shi bai yi ba. Ita kan bonus É—in ta dama ta riga ta tanadi amsar da za ta bashi idan ya ma ta magana...
Aiki dai ta aikatu dan da gayya ma ya ke sata wasu ayyukan. Sai dai tunda ranar farko ce haka ta haƙura ta dinga binshi a hankali kar ya ce ma ta lazy.
A haka su ka ƙare aikin ranan, ƙarfe huɗu za su dinga tashi dan haka ƙarfe huɗu saura kwata ta fara haɗa kayanta. Kiririnkiririn sai ga telephone na ƙara.
"Mtsww sarkin naci" ta É—auka fiska É—aure kamar tana gaban Sir Najeeb É—in.
Ajiye wayar ta yi ta shiga office É—in sa. A ranta tana ayyana abin da za ta ce idan wani aikin zai ba ta.
Tana shigowa ya nuna ma ta wata laptop ya ce ta ɗauka ta tafi da shi gida wanda za ta dinga ƙarasa aiki da shi a gida kenan.
"O'o ni Aisha, wato agidan ma ba hutu za kai ba"
"What do you say?"
"Babu, na ce Thank you Sir"
Sai da ta juya za ta fita ya ce "Miss Salihu"
HaÉ—iye miyau ta yi tareda dunkule hannunta É—aya ta juyo.
"Fix a meeting with the Sudanese tomorrow"
Wa su Sudanese kuma? Ta faÉ—i a zuciyarta a fili kuma ta ce "Ok sir"
Ta san ko ta tambaye shi ma ba gaya ma ta zai yi ba dan haka ta bari akan za ta samu Anas ya ma ta bayani...
......................
Gaba ɗaya a gajiye ta isa gida, Yakubu sai dariya ya ke ma ta wai indai a haka za ta ci gaba ba za ta jima da Sir Najeeb ba dan shi kam aiki ya ke so a mishi tuƙuru.