← Book details Sakatariya Ta Psrt 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 63 OF 91

Sashe 63

Sakatariya Ta Psrt 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wannan karon hawayen da Farida ke ɓoyewa kan su ke zirya a idon ta.
Najeeb ya zuba ma ta ido yana son gane a ina ya san ta amma ya kasa, kuma idon na ta ya ma sa kama da idon da ya ke yawan gani cikin baccin sa.

Hannu ya É—aga ya nuna Farida da yatsa ya ce "who is she?"

*SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......

*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

0️⃣4️⃣0️⃣

*jiya na ga comments ɗin ku na kuma sha dariya. Princess Salma shugaban 'yan team Farida, ina mai ban haƙuri😀. No brain injury is the same haka healing process ɗin ma ba ɗaya bane. Normally waɗanda su ka farfaɗo daga coma su na shiga wani yanayi da ake cewa traumatic brain injury. Ya danganta idan aka gwada mutum a samu ko mild ne ko acute ko kuma severe. Ko da wanda aka yiwa induced coma ba sa farfaɗowa a take su dawo normal. Wassu idan su ka farfaɗo manta komai su ke tundaga magana zuwa tafiya zuwa duk wani abu da su ka iya da. A hankali-ahankali ana sake koya mu su sai brain ɗin su ya dinga picking da sauri, waɗansu abun ma kafin a nuna musu sai su tuna da kan su. Najeeb ya fara tuna 'yan uwansa ne saboda sun fi kusa da shi. It will be odd ace daga farko-farko ya gane Farida tunda ba wai sun jima tare ba ne. Koda ya ke Najeeb ɗan duniya ne zai iya ganeta ma ya waske😂 i dont know, ba ri mu bi su mu ga ya za ta ƙare*

Najdah ne ta yi saurin cewa "she's your secretary" Daddy ya buge bakin ta.
Najeeb cigaba dai da kallon Farida yana son fahimtar miye ma'anar secretary da kuma dalilin da ya sa ita wannan secretary É—in ta ke tareda shi koyaushe.

Dr Kenneth ya ce "za ka tunata a hankali. Yanzu ka tuna ya aka yi ka zo nan?"

Najeeb ya girgiza kai still idon sa na kan Farida da idon ta ke cike da hawaye amma tana ta dannesu kar su zubo.

"Ba ka san ya aka yi accident É—in nan ya faru ba?" Najeeb ya sake girgiza kai.

"Ka tuna wani abu a iya kasancewar ka cikin yanayi na coma?"

"I dont know, there was darkness, then voices then her eyes" ya faÉ—a yana nuna Farida

"Za ka iya tuna voice É—in da ka ke ji?"
Najeeb ya girgiza kai.
Dr Kenneth ya miƙa ma sa wani littafi ya ce duk abinda ya tuna ya rubuta a ciki.

Kafin Dr Kenneth ya fita sai da ya tabbatar mu su da kada su dinga damun sa da tambayoyi, su bari a hankali zai dinga tuno komai. Za dai su iya dinga yi ma sa labarin abinda ya ke so ko kuma su dinga nuna ma sa abubuwan da zai sa ƙwaƙwalwar sa ta yi saurin dawowa dai-dai...

Najeeb ya buɗe littafin ya fara zane. Idan akwai abinda ya farayi bayan ya fara iya riƙe biro to zane ne. Dan har yanzu ma rubutun sa bai dawo dai dai ba.

Dukkan su su ka zuba mishi ido su na ganin yadda ya ke zanen wani gida. Duk da freehand sketch ne hakan bai hana gidan ya fito da kyau ba. Da ya gama sai ya zana wata mace a bakin gidan tana murmushi wanda yanayin fiskar ya É—an yi shige da fiskan Farida.

Farida kam ba zanen ta ke kallo ba tana tsaye ne amma ta yi nisan kiwo. Tunanin ta bai wuce ya za ta ji idan aka ce kwata-kwata Najeeb ya manta da ita kuma ya kasa tunowa da ita.

"Aisha" mom ta faÉ—a tana dafa kafaÉ—arta. Ta É—anyi firgigit ta kalli Mom, Mom ta nuna ma ta Najeeb.
Idon ta ya sauka akan Najeeb da ke miƙa ma ta takarda. Hannu na rawa ta karɓi takardar. Duban zanen ta yi sai ta fashe da dariya wanda ya sa hawayen da ta ke ta ɓoyewa su ka samu damar saukowa.
Shima Najeeb É—in murmushin yai.

Ba abin da ya fi ɗaukan hankalin Farida irin abinda ya rubuta a ƙasar zanen *Plz smile*

"Allah sarki yanajin ta ajikin sa ne fa" Daddy ya faÉ—a yana shafa kan É—an na sa.

Najdah ta cika ta yi fam, tana ta hararan Farida ta gefen ido.

Mom ta ajiye album a gaban sa ta buÉ—e tana faÉ—in duk wanda ta tuna a ciki ya faÉ—a. Hoton baby tana jinjira ne a farko, ya fi minti biyu yana kallon hoton kafin ya ce Baby. Gaba É—aya sai su ka sa dariya.
Hoto na gaba kuma na shi ne yana ɗan shekara huɗu anyi hoton a wani amusement park ne yana cikin motan wasan yara. Wannan kam bai ɗau lokaci ba ya nuna kan sa. Hoto na uku hoton shi da Sabreen ne lokacin da Sabreen ta yi graduation ɗin gama high school. Ya jima yana kallo, ya gane ta amma sunan ya maƙale ma sa. Kusan minti huɗu ya ce "Sa Sa Sabreen"...

Har lokacin da Farida ta zame jiki ta bar ɗakin ba su ankara ba. Tafiya ta ke amma ba abinda ke yawo a ƙwaƙwalwarta irin sunan da Najeeb ya ambata.
Wato ya iya tuna Sabreen amma ita bai tuna ta ba, Sabreen fa!...

Hoton Aisha aka buɗe ma sa lokaci guda idon sa ya fara kawo ma sa hoton ta kwance cikin jini. Dafe kan sa yai yana numfashi da ƙyar nan kuma seizure ya kama shi ya fara jijjiga. Su Najma su ka fita kiran likita, bayan seizure ɗin ya tsaya Dad ya gyara ma sa kwanciya ya maida shi kwance ta gefen sa...

...................

Tana zuwa ɗakin su gado ta hau, kukan ma da ta ke son yin ma ta kasa. Zazzaɓi ne ya rufeta tun tana rawan sanyi har bacci ya tafi da ita. A ƙalla ta yi awa uku tana bacci kafin ringing ɗin wayar ta ya tashi.

Ta É—au wayar tana mai goge gumin da ke goshinta da É—aya hannun.

"Aisha ki na ina?"

"Ina gida Mom"

"Yaushe za ki dawo?"

"Sai dare"

"Ok"

Sai da ta ajiye wayan ta tashi da ƙyar. Ko'ina a jikin ta ciwo ya ke a haka ta shige banɗaki dan ta yi wanka...

Da dare da ta isa ta tarar da abun mamaki. Mom na tsaye gaban Najeeb tana hawaye tana bashi haƙuri, shi kuma ya kauda kai gefe.
Daddy baya nan dan ya bar asibitin tun da yamma. Najdah ne a wajen bayan Mom, itama Sallah ta ke yi.

Mom ta zagayo gaban Najeeb ta tsugunna har ƙasa. Da gudu Farida ta ƙarasa wajen tana ƙoƙarin ɗaga Mom.
"Mom so ki ke ki ja ma sa bala'i. Bai kamata ki tsugunna ma sa ba"

"Ki bar ni Aisha, ya tuno abinda na yi ya ce baya son ganina. Plz ki ce ya yafe min, ba zan iya rayuwa ba tareda ina kusa da shi ba"

Farida sai da ta tabbatar ta É—aga Mom kafin ta sa hannu ta fara goge ma ta hawaye.
"Dan Allah ki dena kuka, kukan ki masifa ce a gareshi"
Da ƙyar Mom ta iya haɗiye kukan ta yi shiru.

Farida ta juya ta kalli Najeeb da ya ƙura ma ta ido, cikin ɗaga murya ta ce "kai Sir Najeeb, ka kiyayi fushin mahaifiyar ka. Kar ka ga dan kana cikin wannan yanayi ana tausaya ma ka ka maida mu bamu san mi mu ke ba, ka sanni sarai zafi gareni, kuma idan ba ka shiga taitayinka ba duk abinda ke cikin ƙwal..."

"To kashe ma na shi. Munafuka, kin san yana cikin wani hali amma ba za ki bari hankalin sa ya kwanta ba, kashe shi tunda abinda ki ke so kenan, dan ki gaji dukiyar sa ko"

"Najdah!" Mom ta daka ma ta tsawa.

"Mom ki ga abinda ta ke ma sa fa, anan É—azu ya shiga wani hali saboda wani abu ya tuno amma yanzu ta dinga ma sa masifa kaman wani É—an ta"

Shikan ido ya ke bin su da shi. Yadda Farida ke masifa haka ya dinga ji ƙwaƙwalwarsa na tuno ma sa wassu masifan da ta yi a baya. Abin ya confusing na shi, domin yana ta ƙoƙarin gano a ina abubuwan nan su ka faru kuma yaushe su ka faru.

"Ki tafi ki bamu waje zamu iya jinyar sa" Najdah ta faÉ—a tana kallon Farida ido cikin ido.

"Yarinya kenan, ki je ki yi aure za ki fahimci minene tsakanin miji da mata. Jinya kuma ko uwar da ta haifeshi ba ta ma sa É—awainiyar da na ma sa ba."

"Mom kin ji maganar banzan da ta ke yi ko?"

Mom ta ce "gaskiya ta faÉ—a. Babu wanda yai wa Najeeb hidima kaman ta, kuma ba abinda za mu saka ma ta da shi sai addu'a. She's the only one that never stop believing in him kuma na tabbata da ya yi shekaru a haka to a hakan Faridan za ta jira shi"

Najdah haushin maganan Mom da ta ji ya sa ta je ta É—au jakan ta fuuuu ta fita ko sallama babu.

"Koyaushe haka ki ke da faÉ—a?" Najeeb ya tambaya yana kallon Farida

"Haka na ke, a haka ka sanni dan haka idan za ka tuno ka tuno, idan ma ba ka tuno ba to zamu cigaba daga inda mu ka tsaya"

"Son please forgive me" Mom ta faÉ—a tana haÉ—a hannun ta alamar magiya.

"Ka san Allah Sir Najeeb ba inda za ta je sai ka ce ka yi haƙuri"

Dariya yarinyar ta bashi.
"A matsayin ki na wa?"

Confidently ta ce "a matsayina na matar ka"

"Mata na?" Ya tambaya looking confused

"Yes ni matar ka ce" ...

.........................
Chapter 63 · 0% Book details