Sashe 21
Sakatariya Ta Psrt 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
"Najeeb wanni walaƙancin ne wannan? Ga wacce ta ma ka sharri amma ba ka ɗau mataki a kanta ba sai Halima. Ka manta Wannan Jakar har dukan Halima ta yi. You're supposed to sack her"
" ina ganin ba ki shiga office ɗin ki ba har yanzu. Go back to your office akwai saƙo da na sa aka ajiye mi ki"
"Najeeb i'm serious bai kamata ka kori Halima ba she didnt deserve it"
Ko kallonta bai yi ba ya ce " ki je office ɗin ki ki duba saƙona"
Ta juya a fusace ta bar office É—in.
Farida ta fara dariya dan ta san saƙon, tunda ita ya ce ta typing suspension later ɗin Khalidan.
Ganin dariyan na ta ya ƙi ƙarewa ya sa ya daka ma ta tsawa.
"Miss Salihu!"
"Sorry Sir" ta faɗi tana ƙoƙarin gimtse dariyan...
Ta gama abinda ta ke amma ta fake dan tana son ganin reaction É—in Khalidah idan ta dawo.
Ai kuwa sai ga Khalidan ta zo a rikice.
Ta cilla wa Najeeb takardar hannunta tana faÉ—in " Najeeb explain this"
" ba ki iya karatu ba ne ko me?"
"Najeeb one month suspension a kan me?"
Shiru yai bai kulata ba.
"Najeeb a wani dalilin za ka min haka"
Still Najeeb bai yi magana
"Najeeb magana fa na ke. I'm calling my Dad right now"
Tana ƙoƙarin kiran mahaifin na ta ta ji Najeeb yana magana.
"Alhaji Tukur na bawa 'yar ka Khalidah Siraj Tukur suspension na wata É—aya, ko kana da ja akai?"
Saboda wayar a handsfree ta ke sai kawai Khalidah ta ji Babanta yana cewa "ba ni da ja My Engineer. Komai ka yi dai-dai ne"
Najeeb ya sa hannu ya katse kiran ko ɗagowa bai yi ba balle ya ga yadda Khalidah ta taƙune fiska.
"Shikechar inji wani almajirin mu. Asha hutun wata ɗaya lafiya ko, dama ance idan za ka gina ramin mugunta ka gina dai-dai kai" ta ƙarasa maganar tana dariya
Khalidah ta zo gaban Farida ta nunata da yatsa ta ce " sai na ga ƙarshen ki Farida, you'll see"
"Allah raka taki gona Anty Big"
Tsaki Khalidah ta ja sannan ta fice a office É—in.
Tana cikin dariya Najeeb ya daka ma ta tsawa.
"Get out"
Simi-simi ta fita a office É—in sa.
..............
An kawo lefen Maijiddah kuma ba ƙarya AbdulWahab ya kashe kuɗi wajen haɗa kayan nan. A wajen ƙarɓan kaya ma Farida ta ka sa ta tsare dan ganin komai ya tafi dai-dai.
Anty Hanne ƙiri-ƙiri ta nuna kishinta a fili saboda kayan da akaiwa Maijiddah ko rabinsa ba aiwa 'ya'yanta da aka aurar ba.
Baaba Sabuwa kam farin ciki fal ranta.
Ranan sunday da dare AbdulWahab ya zo yiwa Maijiddah sallama da ke ya zo weekend.
Farida ce ta tsarawa Maijiddan kwalliya ta kuma zaɓa ma ta kayan da za ta sa.
Falon Baffa Musa aka saukeshi. Wannan zuwan sa gidan kenan na biyu tun haÉ—uwar su.
Tareda Farida su ka zo bayan sun gaisa da shi sannan ta fita ta basu waje.
"Ina yini" ta faÉ—a a hankali dan ita har yanzu ta kasa sake jiki da shi.
"Lafiya gimbiya ta"...
Hiran na su yawanci shi ya ke maganar dan Maijiddah kam kunya ta hanata sakewa.
Ya ɗan taɓa abinda aka kawo ma sa sannan ya tashi akan zai tafi.
"Allah ya tsare hanya, ya kai ka gida lafiya. Ka gaida su Baby da Alizah"
"Amin tawan. Shikenan gimbiya ba wani É—an abu da za ki bani"
"Abban Alizah mi ka ke so"
Ɗan matsowa yai kusa da ita ya riƙe hannunta ɗaya yana ɗan murzawa. Ya sa hannu ya saukar da gyalen da ta yane kan ta da shi sannan ya tufke ɗankwalin,
warware gashin da ta tufke yai sannan ya fara shafa gashin wanda ya zubo har tsakiyar bayanta ƙanshin man da ta shafa wanda ke fitar da ƙanshin mint leaf kaman kuma lemon grass. Ya kai hancinsa yana shaƙar ƙanshin.
Hannunta da ke trembling cikin na sa da kuma yadda bugun ƙirjinta ya ƙaro saboda closeness na su ya sa ya saita kan sa yai gyaran murya bayan ya miƙe tsaye sannan ya ce " Allah ya kaimu kwana ashirin da tara gimbiyata"....
....................
Yakubu ta sa ya ciro ma ta kuÉ—i bayan ta ga cikakken alert É—in ta wannan karan Sir Najeeb bai cire komai ba.
Karfe goma saura kwata ta shiga falon Baffa dan bai jima da dawowa ba, sai da ta ba shi lokaci kafin nan ya ci abinci.
ÆŠan gefe da shi ta zauna suna gaisawa.
"Baffana na kai na. Allah ya ja zamaninka ya ƙara ma ka lafiya amin"
"Amin 'yar Baffa"
Hannu biyu ta sa ta miƙa ma sa kuɗi. "Baffa a sa mana albarka"
" wannan bai yi yawa ba Farida"
"Baffa na so ya fi haka ma sai dai ka san mu mata sai a hankali, kuÉ—in na wa na sayo gwanjo da su kuma ban gama haÉ—a kan kuÉ—in ba"
"Allah ya miki albarka Farida" ta amsa da amin.
"Dubu hamsin yai yawa Farida, ba dai duka albashin na ki ki ka kawo ba?" Baffa ya faÉ—a lokacin da ya gama irga kuÉ—in.
"A'a Baffa"
Shiru ne ya biyo baya na minti biyu kafin ta ce " Baffa dama na ce tunda wannan shekaran ka yi bikin su Salima ga na Jiddah nan da wata É—aya mi zai hana nawan a barshi wata shekaran kaga kafin nan ka tara wani abu"
" A'a Farida, idan na yi haka na ci amanar mahaifin ki. Duk cikin 'ya'ya na ba wadda ta wuce shekara ashirin na aurar da ita, Maijiddah ce ma har ta kai ishirin ɗin. Idan ba ƙaddara da ta faɗa miki ba ai da tun shekaru uku da su ka wuce anyi bikin ki"
"Baffa Allah ba matsala ka bari irin watan uku na wata shekara sai ayi kafin nan komai ya dawo normal"
"A'a Farida ko da duka gonakaina zan sayar dan na samu kuÉ—in yi miki aure zan sayar. Ai idan na bari wata shekara sai duniya ta zageni. Idan ba su iyayen yaron sun ce bai gama shiryawa ba ai da tareda Maijiddan zan haÉ—aki"
"Baffa dai" ta faÉ—a kaman za ta yi kuka.
"Tashi ki je ki kwanta. Allah ya kaimu watan December"
"Baffa nikam..."
"Tashi na ce" ya faɗa da ɗan ƙarfi.
Ta tashi tana guna-guni ta bar falon.
Sai da ta fita Baffa ya ƙara godewa Allah domin halin Salihu na kyauta kam Farida ta ɗauko, dan lokacin yana raye bashida rowa ko kaɗan, zai iya bayar da abu shi ya rasa kuma hakan bai dame shi ba...
................
Lagos
Ranan Monday da safe ya isa Lagos, kai tsaye office ya wuce kasancewa dama shi ɗaya ya je ya bar su Alizah a gidan maƙocin sa kuma abokin aikin sa Mr AbdulRazaƙ.
Bai ɗauka Aneesa za ta zo ba tunda ya gaya ma ta zai je Kano kuma zai bar yaran a wajen maƙota.
Ƙarfe takwas da rabi na dare ya isa gidan Mr AbdulRazaƙ dan ɗauko yaranshi. Sai dai da ya je ake ce ma sa Aneesa ta zo ta ɗauke su.
A take a wajen ya kira Aneesa amma ba ta ɗauka ba. Hankalinsa bai tashi ba sai da ya je gida mai' aikin su ta ce Aneesa ta wuce da yaran Abuja. Yai ta kiran numbar Aneesan amma ba a ɗauka. Ƙarshe dole ya kira numbar ƙaninta Nazir ya ce ya kaiwa Aneesa.
Minti biyar sai ga kiran Aneesa a wayarsa.
"Wannan wanni irin iskanci ne Aneesa za ki É—auke min yara ba tareda kin sanar da ni ba"
"Iskanci kuma AbdulWahab, Ni da 'ya'ya na. For your information, kai da su Baby sai ka janye maganar auren ka. Ko kuma su zauna tare da ni anan amaryarka ta haifa ma ka wasu"
"Anny kin san yaran nan suna Makaranta fa"
"And so, zan sa su a wani anan"
"Look Aneesa, ki maido min da yarana gobe-goben nan ko kuma..."
Ƙiiit ta kashe kiran.
*SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......
*Azizat......âœ*
*Wattpad @000Azee*
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
*Free page*
0ï¸âƒ£1ï¸âƒ£3ï¸âƒ£
Kwana biyu Aneesa ba ta turo ma sa yaran ba dan haka dole ya kira Alhaji, mijin Maman Aneesan kenan, ya ma sa bayanin komai shi baya ma gari dan haka bai san su Alizah na gidan sa ba. Ya jima yana yiwa Aneesa faɗa akan ta ajiye aiki ta je ta zauna da yaranta amma ta ƙi. Kasancewa Maman ta ba ta bashi goyon baya ba shi ya sa yai shiru ya zuba mu su ido. Ya auri Hajiya Salma ne lokacin Aneesa na da shekara goma shabiyu ƙaninta kuma na shekara tara. Bai taɓa banbanta su da 'ya'yan sa na cikin sa ba, makaranta mai tsada su ka yi da ta gama sakandare ya turata karatu ƙasar waje.