← Book details Sakatariya Ta Psrt 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 91

Sashe 26

Sakatariya Ta Psrt 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kaman ta nitse cikin office É—in haka ta ji sai dai ita Aisha Farida ce dole ta nuna dakewarta. Tukunna ma dama yana office lokacin da ta shigo? ko dai bayan ta shiga banÉ—akin ne ya shigo office É—in.

"Miss Salihu whats the meaning of this?"

Da ƙarfinta ta waiwayo bayan ta sauke ƙaramar ajiyar zuciya. Ita ɗin expert ce wajen waskewa, ta ce

"Daɗin abin ma kowa yana yi, abinda na yi ba farau ba ne akai na. Ni'ima ce da ubangiji ya baiwa bayinsa dan ya nuna ma na mu ɗin ba komai ba ne. Da Sarki da shugaban ƙasa da maikuɗi da talaka, malami da jahili, mai kyau da mummuna, mace ko namiji, fari ko baƙi. Dukkan mu muna da buƙatar wannan ni'ima. Abu ne ba babba ba yaro"

Ta É—an haÉ—e rai ta ce " yanzu haka Sir Najeeb kai ma wannan ni'imar sai da ka yi ta kafin ka zo office yau, ko tun jiya rabon da ka yi?"

The girl is really crazy, taya za ta yi abin kunya and pretend kaman ba komai. Masifa ya ke so ya ma ta amma maganganunta sai su ka kusa sa shi dariya. Ya daure ya ce " Miss Salihu a wani dalilin ya sa ki ka yi min amfani da banÉ—aki?"

"Saboda ya fi kusa da ni mana"

"This should be the last time da za ki yi haka"

"Ok Sir"

Har za ta wuce sai ta juyo ta É—an yi gyaran murya ta ce " Sir ina da magana"

Ido ya É—aga ma ta alamar miye.

"Sir, tsakani da Allah tusar da na yi É—azu ka ji ta?"

Kallon-kallo su ka tsaya yi. Har ga Allah tana son sani dan bayan ƙarar da tusar ta yi ba ƙaramin wari ne ya biyo bayan tusar ba.

"Get out of my offfice"...

*SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......

*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

*Last Free page*

0️⃣1️⃣5️⃣

"Mama har yanzu bai kirani ba, ina ga bai san ma na yi yaji ba fa" Aneesa ta faÉ—a cike da damuwa a ran ta.

"Ya ki ke so na miki? Na kira AbdulWahab na ce ka zo ka bada haƙuri matar ka ta yi yaji ko ya?"

"Mama do something please, ba zan iya sharing mijina ba"

"An riga an ɗaura auren Aneesa live with it. Ke ne za ki san yadda za ki riƙe gidan ki ta yadda yarinyar ba za ta samu kan shi ba"

Aneesa ta ɗan ɓata fuska ta ce "Mama ta ya zan yi hakan bayan bana zama a Lagos"

"Za ki ajiye aikin ki kenan?"

"Hell no. Ta ya zan bar career É—i na when i'm at its peak. Ko kaÉ—an"

Mama ba ta ce komai ba, to mi za ta ce. Itama mace ce da mijinta ba ya gabanta. Ta taso da aƙidar 'yan cin kai, yau tana Dubai gobe tana China wajen saro kaya, kasuwancin ta shine a gaban ta. Auren fari ta haifi Aneesa da Nazir, da ta auri Alhaji Abdullahi ma ɗa ɗaya ta haifa ta rufe haihuwa. Kuɗi kuɗi su kawai ta sa a gaba ba ta da lokacin kula da iyalin ta balle tarbiyyan yaran ta, shi ya sa ko kishiyoyin ta ba sa gaban ta, dama kuma kowa gidan ta daban...

.....................

Farida na zaune wani saurayi ya shigo neman Najeeb.
"Wa za a ce?" Ta tambaya lokacin da ta É—au wayar.

"Ki ce ƙanin shi"

"Sir wai ƙanin ka na neman ka"

Ajiye wayar ta yi ta ce " ya ce ka shiga"

Ba a jima da shigar wannan baƙon ba Anas ya zo shima ya shiga.

Dukkan su uku zama su ka yi ana taÉ—in bayan rabuwa.

"Big B tunda ka ƙi auruwa mu zamu shige gaban ka fa, dan na gaji da zama tuzuru"

"Shege yaushe ka dawo da za ka fara maganar aure. Anas see this small boy fa"

Anas dai murmushin ya ƙe yai dan ya san inda maganar za ta tsaya ba za ta ma sa daɗi ba.

Farida ta shigo ta samesu a haka, bayan Anas ba ta taɓa ganin Najeeb ya sake yana taɗi da wani ba. Sai dai kamar yadda wannan saurayin ya ce shi ƙanin sa ne ƙila su na da alaƙa tunda dai a yadda Anas ya gaya ma ta ƙanwar Najeeb ɗaya ce wato Najdah. Wata 'yar girman kan kaman yayan na ta.
Kai tsaye wajen Najeeb ta nufa a wajen kujerun da su ke zaune wanda anan ya ke saukan baƙin sa.

"Sir ga wannan ana buƙatar signature ɗin ka anan" ta faɗi lokacin da ta miƙa ma sa wasu takardu.

Ya amshi takardun ya fara dubawa.

"Kai Big B wannan hottie as a secretary ai za ta É—auke hankalin ma su zuwa wajen ka"

Najeeb ya É—ago ido ya ma sa wani kallo wanda ya sa yai saurin chanja magana da cewa.

"Ba wanda ta kai sweety na kyau ai. Najdah is the epitome of beauty ba ƙarya"

Gyaran murya Anas yai sannan ya ce "Musty zan wuce office, sannu da zuwa"
Musty ya miƙa ma sa hannu su ka gaisa. Idon Farida na kan Anas wanda ta ga ya chanja lokacin da Musty yai maganar Najdah. Tun farko-farkon fara aikinta ta san Anas ya na son Najdah, duk da kuwa Anas ɗin bai iya buɗan baki ya faɗawa Najdan ba har yau.

"Ya Anas dan Allah ka É—an jirani minti biyu" ta faÉ—a tana murmushi.

Sauke idon da za ta yi domin ƙarɓan takardun da Najeeb ya gama signing sai ta ga idon shi chul akan ta. Ba ta san ma'anan wannan kallon ba amma ta fassara shi da cewa kallo ne da ke nuni da zan gamu da ke.
Da ta amsa takardun ta ce "Allah na gani ni ban ci bashin kowa ba, kurwata kur"

Har ta fita daga office É—in bai daina kallon ta ba.
Musty cikin fake American accent É—in sa ya ce " Your secretary is funny and cute"

"Ba ka daina halin na ka ba ko?"

"Sorry Babban yaya"

Tana fita ta tadda Anas na tsaye yana jiran ta. Gaba É—aya fiskar sa ta chanja bisa yadda ta san shi da, shi ba kaman Najeeb bane kullum fiskar sa a sake ta ke gashi da son barkwanci.

"Yaya na ban gane wannan É—an adawar ba fa, shi waye?"

Murmushin ya ƙe yai ya ce "ɗan ma su gida ne. Mustafah Sulayman Jibo kenan"

Kalmar da ya faÉ—a ta 'É—an ma su gida' ya sa ta tuna da audion da aka ce ta yi kwanakin baya inda ake cewa shi É—in É—an Maigadin gidan su Najeeb ne, kenan da gaske ne.

"Ya Anas kar ka damu mu akai za mu dangwalawa. Idan da so ai ya share komai"

"Ki na ga Najdah za ta tsallake ɗan uwanta ta zaɓe ni ko kuma Daddy ne zai watsar da zumunci ya zaɓe ni?"

"Ya Anas da wannan ma amma tun farko kai ka yi sake. Da ka gina soyayyar ka a zuciyar ta da tuni an wuce wajen"

Girgiza kai yai ya ce " Farida ba za ki gane ba"
Wucewa yai ya bar office É—in ran sa ba daÉ—i...

Najeeb na zaune da Musty ne amma hankalin sa na kan tunanin mai Farida za ta faÉ—awa Anas. The girl is mischievous, yanzu haka wani gulma ta ke yi.

A wajen cin abinci Farida ta samu Anas shi kaÉ—ai, bai ordering abinci ba, ruwa ne kawai a gaban sa, yana zauna amma hankalin sa yai nisa cikin tunani.

"Ya Anas yau da garau-garau na zo, za ka ci" Farida ta ajiye kular tana ƙoƙarin buɗewa.

" 'yar uwa yau ba na jin yunwa" ya faÉ—i ba tareda ya kalli abincin ba.

"Allah sai ka ci, nan nan na hana Yakubu abincin nan na ce a yaya na zan kaiwa amma ka gwaleni ba ka isa ba"

Ta fara zuba abincin a plate tana faɗin "Ya Anas yajin ya ji maggi fa, ga man ma sai ƙanshin albasa ya ke"

Sai da ta gama haÉ—awa ta tura gefen sa ta ce " dan Allah ka ci"

Ba yadda zai yi dole ya É—au spoon ya fara ci. Ita ma ta haÉ—a na ta ta fara ci. So ta ke ta ma sa maganar Najdah shi ya sa ta zo.

"And what is the meaning of this?" Muryan Najeeb ya gauraye ilahirin wajen.

"Anas miye haka?, babu respect tsakanin Oga da mere secretary. Ta ya za ka bari ta zauna a inda na ke zama na ci abinci. Are you trying to disrespect me kamar yadda ta ke disrespecting É—i na"

"Najeeb is not..."

"Shut up" Najeeb ya katse Anas da tsawa. Wannan ya ja hankalin kowa ya koma kan su.

Ta shi Anas yai zai bar wajen. Farida ta ce "Yaya dan Allah ka tsaya ka ci abincin ka, ni barin bar ma sa wajen"

"Bar shi na gode Farida" ya faÉ—i sannan ya bar wajen.

"Girma ya faÉ—i, kuma wallahi an ji kunya"

Hannu Najeeb ya kai zai ma ta mari sai kuma ya tsaya yana huci hannun na reto a sama " I'm warning you Miss Salihu, ki kama matsayin ki ko kuma na nuna mi ki"

Haɗiye miyaun da ya tokare ma ta maƙoshi ta yi lokacin da Najeeb shi ma ya juya ya bar wajen. Ta gama sadakarwa Najeeb marin ta zai yi. Har ta hango yadda fiskarta zai koma idan da marin ya sauka a fiskarta.

Ranan dai ita ɗin ma ka sa cin abincin ta yi. Mi ya ke damun Najeeb da har zai yiwa Anas haka, hakan ma agaban jama'a wanda duk a ƙasan Anas ɗin su ke...

Kai tsaye office É—in Anas ta wuce da ga canteen. Yana zaune yana ta kan zane a takarda wanda da ka gani ka san yana zanen ne saboda huce haushi.

"Yaya na kar ka ce na cika gulma amma anya Sir Najeeb yana da lafiya kuwa. Gaskiya a binciki ƙwaƙwalwar sa"

"Lafiyar sa ƙalau Farida, kawai dai he has a rough life ne. Mahaifiyar sa then Sabreen, su suka maida shi haka"

"Sabreen?" Farida ta faÉ—a da alamar tambaya.

"Macen da Najeeb ya fara so ba"
Chapter 26 · 0% Book details