Sashe 35
Sakatariya Ta Psrt 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Na rantse da Allah, kai na rantse da mutuwata ita ta sani na je na ɓata abun nan na kuma sace takardun zanen, ba na baku takardun ba ɗazu"
Malam Muntari irin tsofin Najadun nan ne, wanda sun yi ƙuruciyar bariki tsufan su kuma ya zo ya zama a lalace.
"Malam Muntari munji bayanin ka za ka iya tafiya"
Sai da ya fita wani da ke gafen Najeeb ya ce " Miss Salihu kin dai ji abinda ya ce, mi za ki ce gameda abinda ya faÉ—a domin ki kare kan ki"
Ajiyar zuciya Farida ta yi sannan ta ce " ni ba abinda zan ce, tunda tsoho kamar wannan bai ji tsoron Allah ya faɗi gaskiya ba ai ba abinda zan ce. Allah ne shaida ta, ni ban san VESTAC ba, wannan tsohon kuma ban taɓa magana da shi ba"
"To Miss Salihu ki É—an bamu Minti biyar"
Har ta zauna a lobby É—in wajen ba ta daina maimaita kalmar Hasbunallahu wa ni'imal wakil ba.
Minti shabiyu ta yi a wajen sannan a ka kirata.
Tana zama wanda ke gafen Najeeb ya ce " Miss Salihu mun sameki da laifin ɓata sunan kamfani. Daga yau kin bar aiki a Najeeb Constructions sannan kamfanin nan tana bin ki taran miliyan biyu da rabi za ki biya cikin kwana talatin, idan ba ki amince da wannan hukunci ba ko kuma ki ka ƙi biyan wannan kuɗi to za mu shigar da ke ƙara kotu"
Kallon Sir Najeeb ta ke idon ta ya ciko da hawaye. Shima É—in kallon ta ya ke amma wannan karan ita kan ta ba ta san kallon tausayi ya ke ma ta ba ko kallon madallah.
"Sir ka na da abin cewa?" Wanda yai maganar É—a zu ya tambayi Najeeb...
*Allah ya kaimu daren yau da rai da lafiya sai ku ji mi Sir Najeeb zai ce*
*SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......
*Azizat......âœ*
*Wattpad @000Azee*
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
0ï¸âƒ£2ï¸âƒ£1ï¸âƒ£
"She stays" abinda ya faÉ—a kenan.
"Sir amma..."
"Za ta biya taran kamfani but she stays"
Daga haka ya tashi ya fita. Tana zaune a wajen ta kasa tashi, ji ta ke kamar an kafe ƙafafuwan ta a wajen. Tana ji su na wasu maganganu a kanta da Sir Najeeb amma kuma ba wannan ne damuwar ta ba. Ita da ta ke shirin aure ina za ta samu 2.5M, 'yan kuɗaɗen ta duk ta yi amfani da su wajen siye-siyen abubuwan biki. Ummi da Baffa Musa da wanne za su ji, da siya ma ta kayan ɗaki ko da biyan miliyan biyu da rabi.
Har su ka gama fita ba ta tashi a wajen ba sai da Yakubu ya zo.
"Farida wani hukunci su ka yanke?"
Maimakon ta bashi amsa sai ta ce "Yakubu kai ma ka yadda ni na yi abun nan?"
"Na san duk tsiyar ki iya maganar baki ta tsaya, wannan ba halin ki bane"
"Yakubu 2.5M ina zan samu?"
"Malam Muntari É—an giya ne, zai yiwu an biyashi dan yai miki wannan sharrin ne, amma Allah ya fisu koma waye ne"
"Ni kam aikin nan nawa ake bani da mutane su ka sa mun ido a kanshi haka?"
"Akwai Allah Farida, tashi mu tafi"
Office É—in sa ya kaita ta zauna yana daÉ—a ba ta baki, sai da ya ga ta samu nitsuwa kafin ya rakata zuwa office É—in ta.
Ta zauna ne amma kaman a ƙaya ta ke, ko da ta cigaba da aiki anan, hankalinta ba zai kwanta ba domin kowa da wannan abun za a dinga ganin ta.
Tana cikin wannan tunanin Anas ya shigo.
" 'yar uwa dan Allah ki yi haƙuri, wallahi ban yadda ke ki ka yi abin nan ba. Zan cigaba da bincike har sai na gano gaskiya"
"Ba komai Yaya na. Allah shi ne shaidata"
"Kin yi magana da Najeeb ne?"
"A'a"
"Barin sameshi"
Anas na shiga office É—in ta yi ajiyar zuciya sannan ta jawo wayan ta ta fara dube-duben hotuna. Sai da ta kai kan hotunan modelling É—in nan sannan ta tsaya. Hoto kawai ta je É—auka ga shi ya zame ma ta jaraba. Tana kallon hoton ba ta san lokacin da hawaye ya fara zubo ma ta ba, hawayen da ba ta yi É—azu ba shi ta ke yi yanzu...
"Na ji hukunci da aka yanke, amma Najeeb kai ka san Farida ba za ta iya samun 2.5M cikin 30 days ba"
Yai ajiyar zuciya ya ce "zan biya ma ta"
"No need"
"Ban gane ba?"
Najeeb yai dariya wanda ya fi kama da dariyar yaƙe.
"Ni ta yiwa laifi, so only i gets to punish her. Wannan duk formalities ne na Kamfani and i've cleared it up"
"Wait, ka biya ma ta 2.5M É—in?"
"Ina da abinyi Anas, so get out"
"Najeeb are you inlove with her?" Tambayar da ta sa Najeeb ya tashi tsaye lokaci guda, cikin fushi ya ce "how dare you say that to me"
"Dude, abin ne da mamaki. Tunda Farida ta zo kamfanin nan ka chanja, when it comes to her ba ka iya taɓuka komai. What could that be if not love"
"Get out, get the hell out of here"
Anas dai ya fita ne amma zuciyar sa ta gama amincewa da Najeeb na son Farida. Its so obvious all this while bai gane ba...
"Wai wani irin magani ki ka yiwa Najeeb ne? Duk abinda ki ka yi sai ya shanye. Gaya min wani malamin ki ka riƙe?"
Takaici ma ya sa Farida ba ta tanka ma ta ba.
"Farida da ke na ke magana"
Wannan karan ba za ta É—auki cin fuska daga wajen Khalidah ba.
"A wajen uwar ki na ke karɓan magani. Ki fita min a office kafin ki ga rashin mutunci"
"Its not over yet Farida" ta snapping a dai dai fiskarta sannan ta fita.
"Kai ya Allah daga wannan sai wannan. Ni da na san wannan cin fuskan zan fiskan ta a wannan kamfani da tun farko da Sir Najeeb ya koreni na tattara koli na na tafi"
Ba ta idda zancen zuci ba wayar ta ta fara ƙara.
Tana É—auka ya ce " to my office"
Saɓanin ɗazu da ta ganshi a wancan hall ɗin yanzu fiskar sa ta sauya akwai ɗan fara'a a tattare da shi.
"Ki fixing meeting da team Alpha anjima"
"Sir Najeeb ba abinda za ka gayamin, ba za ka tambayeni gameda gaskiyar lamari ba"
"Miss Salihu, ba yau na fara gaya mi ki ba. Our relationship is strictly professional, anyi investigation kuma an sameki da laifi, kuma an hukunta ki. What else do you want me to say?"
"Sir Najeeb ko da na cigaba da aiki anan, daraja na ta zube, mutunci na ya zube"
"Wanni daraja ki ke da shi dama? You are just a secretary, my secretary"
"Shikenan tunda abinda ka ce kenan. Amma duk min daren daÉ—ewa gaskiya za ta fito kuma da kai da sauran ma'aikatan na ka duk sai kun ji kunya"
................
Wata É—aya kenan da ya wuce. Aiki a Najeeb constructions ya zamewa Farida sabuwa, zuwa kawai ta ke amma ba ta jin aikin a ranta. Ko da Anas ya ce ma ta Sir Najeeb ya biya ma ta kuÉ—in ba ta ma sa godiya ba. Ta so ajiye aikin amma sai ta yi tunanin idan ta bari to wanda basu yarda akwai hannunta a abinda ya faru ba ma za su yarda, shiyasa ta cigaba da zuwa. Dama niyyarta da zaran saura wata É—aya auren ta za ta je ta rubuta takardar barin aiki.
Sir Najeeb bai chanja ma ta ba, yadda ya ke da ɗin haka ya ke, wani lokaci yai ihu yai faɗa wani lokaci kuma yai magana a hankali. Saɓanin da da ta ke maida ma sa magana yanzu kam ko mi zai ce ba ta kulashi.
Ta koma ba ruwan ta da kowa aikinta kawai. Ko sallah a office É—in ta ta ke, balle wajen cin abinci kam ta dena zuwa...
"Sir ga resignation letter É—i na" ta faÉ—i lokacin da ta ajiye ma sa takardar a gaban sa.
"Ok" iya abinda ya faÉ—a kenan ko É—agowa bai yi ba balle ya kalli idon ta.
Ta yi mamaki dan Najeeb É—in da ta sani da ba zai yi shiru ba.
"Allah ya sada mu da alkhairi Sir Najeeb. Na gode da taimako da kulawar ka"
Cikin zuciyar sa ya amsa da amin.
*SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......
*Azizat......âœ*
*Wattpad @000Azee*
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
0ï¸âƒ£2ï¸âƒ£2ï¸âƒ£
WaÉ—anda ta ke mutunci da su kawai ta je ta yiwa sallama. Lokacin tashi yai ta haÉ—a yanata-yanata ta tattara office É—in,ta É—auko office laptop da Najeeb ya ba ta dawo ma sa da shi.
"Sir Najeeb zan tafi, ka yafeni dan Allah, na san a zaman da mu ka yi na yi laifuffuka dayawa amma ka yi haƙuri. Allah ya yafemu gaba ɗaya"
Shiru ne ya ratsa office É—in na lokaci mai tsawo. Tun tana ganin Sir Najeeb zai buÉ—e baki yai magana har ta cire rai ta fita daga office É—in.
Sai da ta fita daga office É—in sannan ya É—ago idon sa ya ce " i'm not done with you yet Miss Salihu"....
Office ɗin Anas ta je dan ta ma sa sallamar ƙarshe.
"Yanzu ƙanwata shikenan kin bar aiki da mu?"
"Yaya na ai ana tare ko da bana aiki anan"
"Gaskiya ban ji daÉ—i ba, yanzu idan ki ka tafi wa za mu samo ya replacing É—in ki. Ke ce the second longest surviving secretary a wajen Najeeb"
"Ya Anas kenan, ai da ƙyar mu ka sha mu ɗin ma"
" ba wani, da ƙyar dai Najeeb ya sha a wajen ki"
Dariya ta yi sannan ta ce " ya Amaryar ta mu?"
"Tana nan sai rigima"
"Ta kaini rigima"
Anas ya zaro ido yana dariya "ai Farida idan ta kai ki rigima bulaguro zan yi a garin. Irin ki ai sai su Najeeb"
"Hmm Ya Anas kenan. Nikam ina abokin adawar ka? Ko ya janye ne?"
"Ai tunda Daddy ya sa min stamp na yaƙice shi. Ga shi dama gimbiyar wannan ɗan baƙin kaɗai ta ke gani"
"Allah ya kaimu lokacin biki Yaya na"
"Amin ƙanwata, kar a manta da IV ɗin mu fa"
"Ai kune ƙarɓan fari".....
...................