← Book details Sakatariya Ta Psrt 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 91

Sashe 52

Sakatariya Ta Psrt 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Lah ba mu ma gaisa ba" ta faÉ—a tana tsugunnawa ta na mi shi ina kwana.

Tausayin ta ne ya kama Daddy. A yadda ya ga Najeeb É—azu zuciyar sa ta karaya. Yanzu idan Najeeb ya rasu wanni hali Aisha za ta shiga? Auren da bai wuce sati shida ba.

"Aisha ki shirya yanzu, idan na fito za mu je asibiti Najeeb ba lafiya"

Dum ƙirjinta ya buga "Najeeb ba lafiya, mi ya same shi?. Allah sarki ashe shi ya sa bai kwana a gida jiya ba." Tambayar da ke yawo a kanta kenan.
Amma duk yadda aka yi rashin lafiyar Najeeb mai tsanani ce dan kuwa Daddy ba zai damu har haka ba idan minor abu ne.
Komawa É—aki ta yi dan ta É—au gyale da jakar ta...

Iliya ne ya ke jan su, cikin motar shiru ka ke ji. Ganin yadda Daddy ke ta yawaita faɗin Lahaula Wala Ƙuwwata Illah Billah lokaci zuwa lokaci sai Farida ta ƙara tsorata da lamarin. Ba dai Najeeb ya rasu ba ne, idan Najeeb ya rasu ina za ta sa kan ta...

Sai da su ka isa asibitin sannan Daddy ya ce " 'ya ta ina so ki kwantar da hankalin ki dan Allah. Insha Allah komai zai zo da sauƙi, Najeeb ya yi hatsari jiya da dare"

Dafe ƙirjinta ta yi da sauri lokaci guda kuma numfashin ta ya tafi hucin gadi na 'yan wasu sakanni.
Hawaye ne su ka fara zirya a idon ta su na gangarowa.

"Ba kuka za ki ma sa ba, addu'a za ki ma sa Aisha"

Tafiya su ke amma ƙafafuwanta ji ta ke kaman ba ajikin ta su ke ba, she's not feeling them ko kaɗan.
Har su ka isa wajen su Anas hawaye ta ke. Yadda ta ga an cika wajen sai hankalin ta ya ƙara tashi.

Daddy ya tambayi ɗanuwan sa ko likitan ya ce wani abu. Uncle Sulaiman ya ce sun ce ƙarfe tara za a ma sa CT-scan aga mi ya hana shi farfaɗowa dan sun ce su na zargin ƙwaƙwalwar sa ta kumbura ne.

Anas ya raka Farida gallery na theater room ɗin inda ta hango Najeeb kwance ansa ma sa life support system. A lokacin ta fashe da wani irin kuka mai taɓa zuciya. Anas ya ɗan dafa ta ya ce " dan Allah ki dena kuka addu'a za ki ma sa abinda ya ke buƙata kenan"

"Mutuwa zai yi ko?, mutuwa zai yi tun ban nuna ma sa yadda na ke son shi ba ko?, Ya Anas ba zan iya jure rashin sa ba"

Shi ma dai Anas daurewa kawai ya ke amma ya karaya da halin da ya ga abokin na shi....

Zuwa yamma an tabbatar mu su da cewa akwai jini da ya daskare a ƙwaƙwalwar Najeeb wanda idan ba acire ba ƙwaƙwalwar za ta yi ta kumbura ne har kuma ta iya jawo ta dena aiki gaba ɗaya wanda ƙarshen zancen dai mutuwa ce.

Abun ka da ma su dukiya tuni aka kira Dr Sajid Usman Abdallah dan ya zo ya jagoranci aikin da za a ma sa. ( ga wanda ba su san Dr Sajid ba an bar ku a baya 😂 ku karanta Mutum mugu ne. Yana nan a wattpad, za ku ga yadda Angon Zaytunah da Naziha ya sha goggonmayar rayuwa. Yai fama da zafin kishin Zayty da kuma rashin kamun kan ta. Sannan ya zo yai dakon soyayyar Ziha yarinyar da shekara ashirin da biyar cur ya ba ta, But aka ce love is blind☺)

Ranan Alhamis aka saka aikin kuma har lokacin Najeeb is in comatose. Kwana biyun nan Farida ta yi su ne akan sallaya. Kaso biyu cikin uku na daren sun tafi a sallah da roƙon Allah ne sauran kaso ɗaya kuma ya tafi a kuka da tunani.
Mom ma da aka sallamota wani tashin hankalin ta shiga dan sai da ta suma lokacin da ta je ta ga É—an ta kwance a asibiti rai a hannun Allah...

Sun yi aikin awa shaÉ—aya akan Najeeb kuma Alhamdulillah an cire jinin da ya daskare ba matsala.
Sai dai Dr Sajid ya ce akwai yiwuwar Najeeb zai cigaba da zama cikin coma na tsawon lokaci. Amma, ba abinda ya fi ƙarfin addu'a...

Wata ɗaya kenan da ta wuce, wata ɗaya na kuka da roƙon Allah, wata ɗaya da tun ana cewa zai iya farfaɗowa gobe har aka zubawa sarautar Allah ido.
An tabbatar da case É—in Najeeb ta shiga PVS (persistent vegetative state) yanzu kam sai randa ya farfaÉ—o kawai amma ba maganar ana tsammanta zai tashi nan kusa.

Duk wani wanda ya san Najeeb Adam Jibo sai da su ka tausaya ma sa. Shi ba mai bacci ba, shi ba mutuwa ba. Yana nan yana numfashi amma gashi a kwance ba abinda zai iya yi.

Wannan wata ɗayan da a ka yi Farida ta zama certified nurse a wajen kula da Najeeb. Tunda aka dawo da shi ɗaki na musamman da aka gyara saboda shi Farida ta koma kwana da shi. Duk yadda Daddy ya hana ta ƙi. Ita ke goge ma sa jiki safe da kuma yamma, har turaren sa ta je ta kwaso tana fesa ma sa. Ta ce Sir Najeeb ba ya son ƙazanta kuma yana son ƙanshi.

Zuwa yanzu ta rage yawan kuka da ta ke. Tana asibiti yanzu 24/7 duk da kuwa an ce ba sai an zauna da shi ba tunda ba wai tashi zai yi ya buƙaci abu ba kamar normal mai jinya. Idan ka ga ta je gida to ta je ɗauko wassu kaya ne. Kullum da safe da kuma dare sai Daddy da Mom sun zo sun duba ta tareda duba Najeeb da fatan cewa ko da na ɗan ƙaramin lokaci ne zai buɗe idon sa.

Farida ta chanja ta zama silent. Ko Sabreen ne ta zo duba Najeeb ba ta kulata, fita ma ta ke ta ba ta waje har ta gama tsiyarta ta tafi. Wanda iya ka daÉ—ewar ta minti ishirin ne...

Yau ma ta na kwance gefensa tana ɗan shafa gashin sa da ya fara tohowa saboda lokacin da za a masa aiki aske gashin aka yi yai ƙwaranƙwal.
TaÉ—i ta ke ma sa kamar yadda ta saba yi.

"Sir Najeeb a ina ma mu ke"

Ta ɗan yi murmushi ta ce "yawwa na tuna, ranan da na fara jin wani abu gameda kai shine ranan da aka zo aka rescueing na mu daga hannun su Joseph. Ban ganewa zuciyata ba tun daga ranan. Ko da na dawo office kullum idan na kalli idon ka sai na ji wani abu ya taso min daga chan ƙasan zuciya ta, shi ya sa ko ina magana da kai na ke avoiding haɗa ido da kai. Ko da yaushe ina ƙoƙarin yaƙi da zuciyata saboda wani sabon al'amari da ya dinga taso min da shi gameda kai ba mai yiwuwa ba ne, na dinga tabbatar wa kaina ka fi ƙarfi na, na dinga nunawa kai na, Najeeb Adam Jibo ya fi ƙarfin Aisha Farida Salihu. Amma ka san me? Bayan ƙaddarar aure ta shiga tsakanin mu sai...."

Sallamar Anas ya katseta daga labarin da ta ke wa Najeeb.

Sai da su ka gaisa ta ke tambayar sa ya aiki?

" 'yar uwa abubuwa fa ba daɗi. Riƙe kamfani kaman Najeeb constructions sai ma su zafi irin Najeeb ɗin. Kin san Allah daga jin zancen halin da Najeeb ya ke sai kowa ya fara fidda asalin halin sa. Aka dena bawa aiki mahimmanci ana sako-sako da duk wani ayyuka da ake yi. Can you imagine wai anyi board meeting akan wai ba su yarda na jagoranci kamfani ba"

Farida ta zaro ido " to amma Ya Anas ba kai ke riƙeta ba idan Najeeb ba ya nan?"

"Haka ne amma kin san na 'yan kwanaki ne wannan. Najeeb bai taɓa tafiyar da ta wuce sati biyu ba. Yanzu kuma wata ɗaya da sati uku kenan ba ya nan. Farida abubuwa sun fara ja baya. Ba ni da zafi kaman Najeeb hakan ya sa kowa ya fara abinda ya ga dama"

"Amma ka gayawa Daddy?" Ta tambaya tana mamakin wannan al'amari, ba mutuwa Najeeb yai ba amma har an fara juya ma sa baya, Mutane kenan

"Mun tattauna da Daddy kuma ya amince da shawarar da na kawo, ya ce mu yi magana da ke É—in"

Ta É—an gyara zama dan ta fahimci zancen sosai.

"Farida riƙe Najeeb constructions ba zai tafi dai-dai ba sai iron man kaman Najeeb. Ki na da zafi, za ki iya taka kowa sannan za ki iya shugabanci. Kin zauna da Najeeb kin ga yadda ya ke gudanar da al'amuran sa i'm sure kin tsinci ilimin shugabanci a tareda shi. Farida ki koma aiki, wannan karan ba matsayin sakatariya ba sai matsayin CEO"

"Allah ya kiyaye Ya Anas. Wani zance ne wannan. Saboda ni ce na kawo son shugabanci duniya sai mijina na asibiti ba lafiya sai na tsallakeshi na tafi wajen aiki" ta goge hawaye ta ce " ina nan da shi anan har ranan da zai farfaÉ—o"

"Farida na san ki na so ki kasance tareda Najeeb, amma ba kya ganin kina da hakki akan kula da dukiyar sa. Barin gaya mi ki halin da mu ke ciki yanzu. Kamfanin da ta ke da major shares bayan Najeeb tana so ta janye hannun jarinta ko kuma mu mu sake sayar ma ta da kaso arba'in a ciki. Kin san mi hakan ke nufi? Yana nufin su na so su mallaki kamfanin ta ƙarfi, zai zama Najeeb 35% ne kawai na shi a ciki kuma kinga kamfani ta bar hannun Najeeb. Ke 'yar kasuwa ce kin san yadda za ki yi ki kawo cigaba a wannan kamfani ki kuma ceceta. Ni Architect ne ban da wani ilimi mai zurfi a wannan fanni. Najeeb da ki ke gani bayan karatun Engineering da Architecture da ya yi yana da degree a fannin kasuwanci sannan yana da certificates dayawa a ɓangarori ma su yawa musamman leadership. Hakan ya sa komai ke tafiya ma sa dai-dai"

"Ya Anas ba zai yiwu ba. A nemi wani ko cikin cousins É—in Najeeb amma ban da ni. Ba zan iya ba"....

"Farida......"

.................................
Chapter 52 · 0% Book details