← Book details Sakatariya Ta Psrt 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 86 OF 91

Sashe 86

Sakatariya Ta Psrt 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Farida ta kira Adama ta tayata haÉ—a kaya, da su ka gama ta kai ma ta su cikin mota. Da ta shirya ta je ta yiwa Mom sallama sannan ta shiga É—akin Sabreen. Waya su ke da Lukman lokacin da ta shigo, tana kallon ta da jaka ta sa dariya har da hawaye.

"Ni ba na son gulma, Mom ce ta ce na koma" Farida ta faÉ—a tana haÉ—a rai.

Sabreen ta ce " to Allah ya kiyaye hanya sai mun zo karɓan tsaraba"...

Saloon ta fara wucewa aka ma ta gyaran gashi da lalle sannan ta wuce gida. Ko'ina na nan tsaf-tsaf saboda Tasallah ba ta wasa da gyaran gidan.

Lokacin da ta shiga É—aki wanka ta yi ta feshe jikin ta da turaruka.
Ƙarfe biyar na yamma Abdullahi ya faɗa ma ta zai je ya ɗauko Najeeb a airport yanzu kuma ƙarfe huɗu da kwata.
Gyara É—akinta ta yi kafin ta wuce na shi É—akin. Yana nan a gyare amma sai da ta cire zanin gado ta sake sa wani sannan ta shiga banÉ—aki dan ta wanke...

Tun ƙarfe biyar da kwata ta ke tsaye jikin balcony na falon sama tana jiran dawowarshi amma Abdullahi bai shigo gidan ba sai ƙarfe shida saura minti goma. Tana ganin ya fito daga motan ta yi saurin barin wajen. Ɗakin sa ta shiga ta fara gyara arrangement na turaruka da mayukan sa...

Ta ji shigowar sa amma ta dake ba ta kulashi ba ta cigaba da gyaran har da faÉ—in " duk an bar É—aki a hargitse. Komai gashi nan ba tsari kaman ba mutum ke kwana a É—akin ba"

Yana tsaye yana kallon ta bai ce komai ba duk da farin cikin da ya mamaye zuciyar sa.

Ya ajiye jakar sa ya shige banɗaki ba tareda ya ce ƙala ba. Tana binsa da wutsiyar ido har ya shige banɗakin.

Ta ɗan yi ƙaramar tsaki ta ce " koma ya nuna ya gannin nan"
Ta zauna bakin gado tana jiran sa. Ya jima a banÉ—akin kafin ya fito sanye da bathrobe fari.

"Ni fa kar mutum ya ga na zo ya nemi yi min walaƙanci Mom ce ta ce na zo."

Shiru Najeeb bai ce komai ba. Ta É—aga ido ta kalleshi yana tsaye gaban mirror yana shafa jikin sa da mai.

"Allah na gani sai na tafi tunda ba a son ganina, dama ba wai da son rai na na zo ba"

Najeeb ya ajiye man da ke hannun sa ya je ya buɗe ƙofar ɗakin ya ce " a gaida Mom da su Sabreen. Allah ya kiyaye hanya"

"Kuturun Uban chan. Au'uzubillahi har ka sa ina zagi"
Ta tashi fuuuu ta ce " zan tafi É—in koma ba za ka sake ganina ba"

Sai da ta zo shigewa ta ƙofan ya riƙe hannun ta.

"Ni ka sake ni in tafi, ka sake ni na ce"

Ya jawota jikin sa yana kallon ƙwayar idon ta. Itama ɗin kallon sa ta ke ƙirjin ta na bugawa da sauri-sauri ba abinda jikinta ke muradi irin tajita kwance kan faffaɗan ƙirjin sa.

"My stubborn Mrs Jibo. Na san duk maganan nan cika baki ne kawai, you miss me, i see it in your eyes"

"Ba wani. Ni dama taimakon ka zan yi tunda Mom Allah Annabi ta roƙeni akan na dawo"

"Oh really?" Ya faÉ—a tareda sunkuyo da kan sa, ganin yana matso da bakin sa kusa da nata bakin ya sa ta lumshe ido tana jiran haÉ—uwar bakin su.

Maimakon kiss a baki sai ya kissing kumatun ta. Ta buÉ—e ido a hankali gaba É—aya ta yi laushi saboda wani mugun sha'awar sa da ke taso ma ta.

Murmushi ya ma ta ya sake matsowa da bakin sa wannan karan kam tuni ta yi saurin matsawa da nata bakin, bakin su ya haÉ—e waje guda...
Sun jima suna aikawa junan su hot kiss kafin ya jawota zuwa kan gadon. . Wata ɗaya da 'yan kwanaki rabonta da shi, ba ƙaramin missing ɗin sa ta yi ba. Yadda ya ke sarrafata haka itama ke mayar ma sa da martani, sun jima su na gogar junan su saboda an jima ba a gamu ba...

Bayan komai ya kankama da su ka yi wanka Najeeb ya ce " ki shirya na maida ki wajen Mom na haƙura ki huta a chan"
Duka ta kai ma sa ya goce yana dariya...

..........................

Rayuwan masoyan gwanin sha'awa, kullum su na manne da juna. Duk dare sai sun tashi sun gudanar da sallah sun roƙawa junan su addu'an samun zaman lafiya da kuma samun 'ya'ya ma su albarka. Duk Jumu'ah Farida ba ta fasa yin sadaka ba...

Ranan Asabat aka É—aura auren Sabreen da Lukman. Daddy ne ya zama alwalin Sabreen 'yan uwanta sun zo ba laifi, wannan karan har mahaifiyarta sai da ta zo. Anyi walima kuma anyi family dinner a gida. Washe gari Sunday kuma aka wuce da Sabreen Abuja. Farida ta so zuwa amma Najeeb ya hana saboda yanzu ta yi nauyi.

Duk cikin 'yan uwanta babu wanda ya nuna damuwar sa da asalin Lukman, su daÉ—in su ne ma Allah ya shirya mu su Sabreen har kuma ta yi aure hankali kwance...

.......................

Wanda su ka kawo Sabreen mutum huÉ—u ne Mom ce da Najdah sai Aunt Mouna da wata cousin É—in Sabreen É—in Nihaya. Ba su fi awa biyu a gidan ba suka koma bayan sun yiwa Sabreen 'yan nasihohi.

Ƙarfe biyar Lukman ya shigo gidan na su. Cike da farin ciki, finally shima ya zama ango...

Ƙarfe takwas saura su ka gabatar da sallan Isha tareda sallar godiya sannan Lukman ya gabatar ma ta da kazarta. Tare su ka ci kazar su ka ƙoshi sannan Lukman ya tattare wajen...

Kunyar Lukman ta ke ji, ta sani ita ba irin matar da ta dace da Lukman ba ne. Ya fi ta daraja da kima duk da kuwa ta fishi asali.

"Ka yi haƙuri ba nida abin da kowane ango ke farin cikin samu a rana irin ta yau. Na yi rayuwa marar daɗi a baya, na zubda mutuncina a idon duniya, na ɗauka rayuwa mai kyau na ke yi, rayuwa ta 'yan ci da jin daɗi amma a gaskiya rayuwar ƙunci na yi a baya. Ka yi haƙuri dan Allah. Ina godiya da Allah ya bani kai. Ba ka dubi yawan shekaruna ba, ba ka dubi rayuwar bariki da na yi a baya ba amma ka amince da ni ka amince na zamo sashen rayuwar ka. Thank you Lukman"

"Shhhhhh" ya faÉ—i tareda haÉ—e bakin su...

Sabreen ta sha gyara sosai, duk da ta saba amma Lukman ya bata mamaki saboda yadda ya birkitata da salon sa, sai takejin ba ta taɓa tarayya da wani da yai kusan sa a iya sarrafa mace ba....

Skt 58

*ina roƙon duk wanda ya karanta wannan shafin yai wa Mijin Maman Durratu addu'a, Allah ya jiƙan sa da rahama, ya haskaka ƙabarin sa, ya gafarta ma sa ya kuma bawa iyalen sa haƙuri da juriyan rashin sa, Amin. Wanda su ka rigamu gidan gaskiya Allah ya jiƙan su da rahama, muma idan tamu ta zo Allah ya sa mu cika da imani amin*

Yau tun safe ta ke jin ta ba dai-dai ba. Ta dai daure ta cigaba da ayyukan da ta saba. Yana fitowa daga wanka ta riga ta cire ma sa kayan da zai sa. Ita ta shafa ma sa mai sannan ta taimaka ma sa ya shirya. Tana gyara mi shi tie É—in ya ce "my Queen lafiya? You look dull this morning"

"Just ƙafafuwa na ke ciwo" ta faɗa dan kawai kar ta tada ma sa hankali

"Ko za mu je ki ga likita?"

"No, zai yi sauƙi zuwa anjima"
Ta ɗan bugi ƙirjin sa kaɗan ta ce " mijina ka ga yadda ka yi kyau. Dan Allah ban da dogon hira da mata, banda lumshe mu su ido, ban da yi mu su murmushi, ka ji nawan"

Ya É—an ja kumatunta ya ce "na ji your highness zan kiyaye duk abinda ki ka ce" light kiss ya manna ma ta a baki kafin ya ja hannunta su ka bar É—akin...

Tafiyar Najeeb office da awa uku Farida ta fara naƙuda. Ɗanliti sabon dreban ta ya wuce da su asibiti. Tun a hanya Tasallah ta kira Mom ta gaya ma ta. Su na zuwa asibitin ko minti arba'in ba ta cika ba ta haihu.
Abin ya zo ma ta da sauƙi gaskiya, kuma Alhamdulillah ba wata matsala...

Tana kwance an kaita É—akin hutu Mom na gefe tana kallon jaririn mai kama da uban sa. Cikin zuciyarta ta ke godiya wa Ubangiji da ya sa ta ga É—an Najeeb.
Mom ta miƙawa Farida jaririn tana faɗin "he look just like his father"

Farida tana kallon jaririn tana godiya bisa wannan ni'ima da Allah ya ma ta...

Bayan minti talatin da haihuwar kafin Najeeb ya iso asibitin. He cant believe it sai da ya ga jaririn, Mom ce ta kirashi ta ma sa albishir da haihuwan. Bai kawo haihuwa ba tunda ya bar Farida lafiya gashi kuma EDD É—in ta saura kwana shida. Sai dai al'amari na Allah yafi gaban kowa.

Ya ɗau yaron yana murmushi tareda kissing goshin yaron. Alhamdulillah ya ke ta maimaitawa a fili, bakin sa ya ƙi rufuwa saboda farin ciki.

Ƙarfe huɗu da rabi aka sallame su daga asibitin su ka dawo gida. Kafin dare gidan na su ya cika da Jama'a. Kowa na zuwa ganin babyn Farida.

................................

Gidajen biyu sun kasance cikin farinciki bisa wannan ƙaruwa da aka samu. Da farko Mom ta so Farida ta dawo wajenta amma gogan sam bai ba da dama ba.

Mom za ta je gidan su tun safe sai dare ta tafi. Ita ke yiwa Farida wanka. Ummi ma kullum sai ta zo duba Farida da jikar ta.

Kafin ranan suna gidan an cika shi da tarkacen yara. Wassu abin ma jaririn kafin ya iya amfani da su sai ya shekara uku amma an siye su tun yanzu.

Ranan suna yaro ya ci sunan *Muhammad Yaman*
(Finally Farida an zama Umm Muhammad🤓)
Chapter 86 · 0% Book details