Sashe 83
Sakatariya Ta Psrt 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Magani ya rubuta mu su na sha da na shafawa sannan aka sallamesu bayan ya rubuta mu su report da za su kai police station.
Daga asibiti Najeeb ya ce Abdullahi ya kai su police station. Abdullahi dai mamaki ya cika shi dan bai gane wannan al'amari ba daga asibiti sai police station. Ya dai cika umurni ya wuce da su...
Ganin report É—in da su ka kawo da kuma testimony da Naomi da Maureen su ka bayar ya sa aka haÉ—a su da police biyu dan su je su arresting wannan muguwar mata da aka kira da Madam Farida.
Cikin su Naomi ba wanda ya ambata cewa Madam Farida matar Najeeb ne. Shi kuma Najeeb yana zaune kaman wawa duk abinda Naomi ta faÉ—a to daidai ne...
Motar su na gaba motar police na baya har su ka isa gida. Abdullahi dai bai san mi ya ke faruwa ba.
Maureen sai kumfar baki ta ke tana faÉ—in "today she go know say our madness pass her own"
Naomi kam maƙalewa ta yi jikin Najeeb wanda ke ta ce ma ta sorry...
Bayan tafiyar su Anas, wanka Farida ta yi ta gabatar da sallar Isha. Tana ma kan sallayar tana addu'a Tasallah ta shigo É—akin da gudu tana haki.
"Baaba Tasallah lafiya?" Farida ta faÉ—a ganin yadda ta tsorata.
"Folisawa a falo, Folisawa suna neman ki Hajiya"
"Police kuma"
Tasallah ta gyaÉ—a kai.
"To ki je ina zuwa"
Tasallah ta fita, still tana tsoro dan ganin Najeeb ne ya zo da su ya sa ta ƙara tsorata da lamarin.
Farida ta cire hijabin sallar ta ta je ta ɗauko ƙarami ta saka dama gown ɗin material ne a jikin ta.
Najeeb da su Naomi na zaune a falon su kuma police É—in su na tsaye.
Ganin Naomi ya sa ta gane dalilin zuwan police.
"Suna na Sergeant Iliya. Mu na tambaya ko ke ce Madam Farida Salihu?"
Farida ta kalli Najeeb wanda ko wajen da ta ke tsaye bai kalla ba sannan ta kalli sergeant É—in ta ce "eh ni ce"
"Madam you are under arrest"
Farida ta yi murmushi ta ce "mu je ko"
Tasallah da ke chan wajen dining ta fashe da kuka tana faÉ—in "Alhaji ka yi wani abu dan Allah. Za su tafi da ita"
Ko gizau Najeeb bai yi ba balle ya sa baki.
Maureen na faÉ—in "evil woman. You'll rot in jail for this"
Haka Farida ta bi bayan su suka fita. Tasallah na ihun matar gidan ne fa, mi ta yi?.
Ganin ba wannan ba ne zai fishsheta ya sa ta nufi É—aki ta É—au wayarta ta kira Mom...
Ganin gidan Najeeb ya ƙara haukata Naomi. Duk ciwon da ta ke ji sai ya zamana ta watsar da shi gefe, babban burinta shi ne yadda za ta mallaki wannan gida ita kaɗai...
...........................
Tun kan su isa police station É—in Daddy ya fara kiraye-kirayen waya. Su na zuwa ma ba wani dogon bayani kawai sake Farida aka yi. Domin Comissioner of police ne ya kira ya ce a saketa.
Abinda ya ƙara sa Daddy ya tsorata da lamarin shine jin cewa Najeeb ne ya zo ya bada report sannan ya ce a arresting Farida. Gaskiya Najeeb yana buƙatar addu'a.
Farida kam har su ka iso gida ba ta ce ƙala ba. Mom ce ma ke ta aikin ba ta haƙuri.
Daddy ya ce wa Mom gobe Tasallah ta kwasowa Farida kayanta. Daga yanzu a nan za ta dinga kwana tunda abin ya kai ga haka kar su wayi gari Najeeb ya kashe Farida.
Farida sai da ta shiga tsohon É—akin su sannan ta fashe da kuka. Tun É—azu ma tanajin kukan, kawai ta daure ne saboda su Mom. Wai ita ce yau Najeeb da kan shi ya ke kawo ma ta police har gida.
Najeeb É—in da lokacin da Sabreen ta sa aka kamata haka hankalin sa ya tashi ya zo police station yana masifa kaman zararre. Ta tuna first kiss É—in su a ranan. Shi ne yau Najeeb ke gani ana tafiya da ita amma ko ajikin sa, kai duniya!...
..........................
Washegari kamar yadda Daddy ya ce haka Tasallah ta É—ebo wa Farida wa su daga cikin kayan ta. Daddy ya ce ta fita hanyar Najeeb kar ya illata ta tun da abin ya kai ga haka.
Addu'a aka ci gaba da yiwa Najeeb dan addu'ar ce kaɗai garesu. Tasallah ba ta fasa sawa Najeeb ruwan zamzam a abinci ba kaman yadda Farida ta buƙata...
A ɓangaren Naomi duk faɗa da wani masifa da Mrs Comfort ke yi ba wanda ya shigeta. Tun da su ka shiga ɗaki ita da Maureen su ka fara shirya yadda za su kawo ƙarshen Farida saboda ma kar a samu matsala a gaba...
Bayan kwana biyu
Maureen da Naomi su ka sake duƙufa gaban Boka Ifagbemi.
Lokacin da Naomi ta gama kwararo buƙatunta Boka ya kece da mahaukaciyar dariya. Sai da yai mai isar sa sannan ya ce "a kasheta? Ko kin manta annurin matar sa ya ke gani a idon ki, ko kin manta duk ranan da Matar sa ta mutu zai dena miki kallon so?"
"To Baba ya za ayi tunda idan aka kasheta maganin zai warware?"
Boka ya fara buga ƙirji yana surkulle sannan ya ɗago ya kalli Naomi ya ce "akwai abinda za a yi amma da ɗan wahala"
Naomi ta ce ko minene za ta yi.
Boka ya miƙa ma ta wani ƙaramin ƙwarya ya ce " ki samu gashinta ko farcenta ki sa a cikin wannan ƙwarya sai ki rufe. Da ƙarfe ɗayan dare ki toni rami ki sa wannan ƙwaryan a ciki sai ki saka saurayin kare wanda bai taɓa hawa mace ba akan ƙwaryan ki bisine tare. Yadda karen nan ya danne ƙwaryan nan haka za ta ƙarasa rayuwarta a kwance ba za ta taɓa tashi ba har sai idan wani ne ya tone ramin ya ɗaga karen daga kan ƙwaryan shi ne za ta tashi"
"Baba taya za mu gane saurayin kare da be taɓa hawa mace ba?" Naomi ta faɗa cike da fargaba.
Boka ya kwashe da dariya...
Sai da ya gama mu su bayani ya ce " ikilo pataki. Kar ki yarda wani mutum ya gan ki lokacin da ki ke businewa"
Naomi da Maureen su ka haɗa kai wajen cewa wannan mai sauƙi ne...
..........................
Bayan sun dawo Kano tunanin samun gashin Farida ko farcenta ya sa su ka shiga ruɗani dan da sun ɗau abin da sauƙi. Daga baya Maureen ta ba ta shawara akan su je gidan ko za su samu. Hakan kuwa aka yi. Naomi ta tambayi Najeeb ya kai ta gidan shi. Ba tareda ya musa ba ya amsa ma ta.
Suna zuwa É—akin Farida ta ce ya kaita. Tasallah ganin tare su ke da Najeeb ya sa ba ta iya hana Naomi ba...
Su na zuwa wajen dressing mirror ɗin ɗakin ta je tana dube-dube. Ta jima tana dubawa ko za ta ga gashin Farida ko da tsilli ɗaya ne amma ba ta gani ba. Har za ta tafi ta lura da wani baƙin Comb da ke wajen da kyau ta ga akwai tsillin gashi guda biyu a jiki ta yi murmushi ta cire su...
Bayan kwana É—aya...
Tun da yamma ta je bayan gidan su ta tone shi da É—an zurfi. Ta sa kwali da buhu ta rufe wajen.
Ƙarfe ɗaya saura ta ɗau ƙwaryan da Boka ya bata ta fita. Karen da ta siyo na kwance a wani keji gefen ramin da ta tona. Dama tun da yamma ta ma sa alluran bacci saboda Boka ya ce ba matacce za ta sa ba.
Lokacin da ta sa ƙwaryan a cikin ramin dai-dai agogon hannun ta ya cika ƙarfe ɗaya na dare. Ta cicciɓi karen za ta sa a cikin ramin aka dallota da torchlight.
"Anty Naomi what are you doing there?" Muryan ƙaninta Abel ya doki kunnen ta....
Skt 55
Naomi ta É—ago ido ta kalli Abel da ke nufo wajenta. Lokaci guda ta ji wani abu ya shiga kunnen ta, ta fara girgiza kai da sauri-sauri.
"Anty Naomi..." kafin ya ƙarasa maganar sa Naomi ta cilla ma sa Karen da ke hannun ta, ya goce da sauri har torchlight ɗin hannun sa sai da ta faɗi.
"Yirrrrrrrrrr, Ah Ah Ah, Chinkokoko kokokokoko Chichichichi..." waƙar da Naomi ta fara kenan tanayi tana rawa.
Abel ya tsaya yana kallon ta tareda kiran sunanta amma sam ba ta san yana yi ba sai tiƙar rawa ta ke yi, tana yi tana dariya.
Ganin fa ba dena rawar za ta yi ba, ya je ya kamota da ƙarfi yana faɗin "stop this nonsense please"
Naomi ta yi wani kuka sannan ta wancakalar da Abel ta baya ya faɗi ƙasa yana haki, "i'm coming oo i'm coming oo" abinda ta ke faɗi kenan kafin ta ranta a guje. Shi kuwa Abel ya fara ƙwala wa Maman su kira...
Ƙarfe ɗaya saura na dare ta tashi fitsari. Ganin idan ta koma bacci za ta iya kasa tashi ƙarfe biyu kamar yadda ta saba ya sa ta yi alwala kawai ta fara sallah. Ba ta kwanta ba sai ƙarfe uku da rabi bayan da ta ji ƙafafuwanta sun ma ta nauyi...
....................................