← Book details Sakatariya Ta Psrt 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 91

Sashe 11

Sakatariya Ta Psrt 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan Maghrib ta kira numbar da Anas ya bata na wasu Sudanese da ke son haɗa hannun jari da Najeeb. Ta faɗa mu su meeting ɗin su da Najeeb gobe ƙarfe goma.

Su na cin abincin dare Baffa Musa ya aiko a kirata. A falonsa ta sameshi yana aikin lissafi a takarda. Ɗan nesa da shi ta zauna a ƙasa ta gaishe shi.

"Ya aikin dai"

"Alhamdulillah Baffa"

"Allah ya taimaka, iyayen yaron nan sun sameni kuma mun tattauna da su. Na ce su bani lokaci na yi bincike saboda kar a samu matsala irin na baya"
Farida ta rintse ido tana tuno abinda ya faru a baya. Ta ya za ta manta wannan babban al'amari daya faru a rayuwarta.
Maganar Baffa ya dawo da ita.

"Sun ce Asalin su 'yan Wudil ne amma kuma tunda Kakansa ya dawo cikin Kano da zama ya zamana 'yan uwan su sunfi yawa anan. Ina so idan komai ya daidaita da yardar Allah da ke da Maijiddah ƙarshen shekara ayi bikin ku tare. Tunda Allah ya sa Saminu ya amince. Na huta da yawan maganganu da ake akanta"

"Baffa wani Saminu kuma?"

"Yaron shagona"

"Baffa auren sadaka za ka yiwa Maijiddah, haba dan Allah sai ka ce wanda ta ke da wani aibu"

"Bance tanada aibu ba. Amma tunda har yanzu shiru ba wanda ya zo neman aurenta kinsan dai ba zan zuba ido ina ganinta haka har a gama auren ƙannenta ba"

"Wallahi Baffa kai bagidaje ne. Wai za ka aurar da ita wa yaron shagonka, irin ta yi kwantai É—in nan,cab É—i"

"Tashi ki bani waje. Ba shawararki na nema ba"

"Baffa dan Allah ka saurareni, Wallahi indai ka aurar da ita wa Saminu Jiddah ba za ta taɓa samun kwanciyar hankali ba. Walaƙantata zai yi dan ya san sadaka aka bashi ita"

"Ban nemi shawaranki ba. Tashi ki tafi "

"Baffa akwai wanda ya ke sonta fa"

"Waye?"

"AbdulWahab sunan shi, É—an gidan Hajiya Yelwa wanda Jiddah ke wa kitso"

"Hajiya Yelwa?"

"Cikakken sunan sa AbdulWahab Bello Hassan"

Baffa ya ajiye biro ya kalli Farida da kyau ya ce " na san ki da yawar magana amma ban sanki da sharri ba. Yaushe É—an gidan Alhaji Bello Kachako ya ce yana son Maijiddah"

"Allah Baffa da gaske na ke, ka tambayi Jiddah"

"Shi kenan, kiramun ita"

Ko da ta shiga É—aki Maijiddan ta samu tana waya. "Ki je inji Baffa"...

Farida na shirin kwanciya ta jiyo muryan Baffa yana faɗa. Da sauri ta zari hijabi ta fita saboda ƙaramar riga ce a jikinta.

" kin san ko waye shi kuwa?, babban ma'aikacin custom ne fa. Ba na son sharri Maijiddah ki riƙe matsayin ki"
Duka matan sun hallara a falon dan suma faÉ—an Baffa ya tado su daga matsugunninsu. Maijiddah kam ta kifa kai tana kuka dan ta tsorata da masifar Baban na ta.

"Ikon Allah! Yanzu dan ba ki da mashanshani sai ki yiwa bawan Allah sharri. Ba ki tsaya ma kusa ba sai chan nesa da ke ki ke hangowa. Ni dama na san yawan zuwa gidan Hajiya Yelwan nan kwaÉ—ayi zai sa miki" Anty Hanne ta faÉ—i tana tafa hannu.

"Munafukai anzo gulma. To ta Allah ba taku ba" ta kalli Baffa ta ce "Baffa ina ni na ce ma ka AbdulWahab na son ta, to ka manta da na yi maganar. Idan gaskiya ce ai ba za ta ɓuya ba idan ma ƙarya ne za a gani. Jiddah ta shi mu tafi"

Jiddah kam tana tsugunne a wajen ko motsawa ta kasa yi. Haka Farida ta zo ta ja ta su ka bar falon...

"Dan Allah ki bar kukan nan, tukunna kukan mi ki ke yi? Saboda Baffa bai yarda da ke ba? Shareshi idan AbdulWahab ya turo ai za su ga zahiri"

Cikin kuka ta ce "Anty Farida wai Baba cewa yai idan ma asiri na ke son yi akan shi gara na bari. Allah ya bani miji Saminu, ta ya mahaifina zai min wannan zargin. Har rashin miji zai sa na koma asiri"

" Jiddah ki godewa Allah, domin addu'arki ta ƙarbu Insha Allah. Ba ga ni ba, ko kin manta abinda ya faru da ni shekaru uku da su ka wuce, i was exactly your age lokacin. Wani surutu ne ba ayi ba, an zage ni an zagi Ummi, hatta Abbana da ke kabari sai da ya samu kason shi. Dan haka ki cigaba da addu'a kuma ki yi ƙum da bakin ki. Duk lokacin da AbdulWahab ya turo su za su ji kunya ai"

"Na gode Anty"

Ta gode Allah da Anty Farida ta yadda da ita lokacin da ta ji record É—in hiran da su ka yi a waya. Ta rintse ido tana tuno abinda ya faru tsakaninsu duk da kuwa alokacin ba ta cikin hayyacinta saboda firgicewa da ta yi da ganin kyanwa.

Hiran su ta tuno wanda ya sa duk wani baƙin ciki ya kau daga zuciyarta.

*" Hauwerh za ki iya auran tsoho?"*

*"Mi zai hana?"*

*"wannan tsohon fa shekarunsa É—ai-É—ai har arba'in da É—aya, ga yaran sa har biyu"*

*"ai ba tsoho ba kenan"*

*" haka ki dai ki ka ce gimbiya Hauwerh"*

*"zan samu amsata anjima ko?"*

*"sai bayan kwana uku"*

*"wai-wai har 3days. To, Allah ya kaimu"*

*amin*

Gaskiyarsa ya fi komai birgeta. *" ina son matata sosai Hauwerh, sai dai umurnin Hajiyata ne akan lallai in ƙara aure kafin shekara ta ƙare. Kuma kallo ɗaya na mi ki na ji kin birgeni"*

Ta sha ji ana hiran sa idan ta je yiwa Hajiya Yelwa kitso. A yadda ta fahimta matarsa na aiki a Abuja shi kuma da yara su na Lagos, sai ƙarshen wata ta ke zuwa mu su. Wannan ne dalilin da ya sa Hajiya Yelwa ta sa shi ƙara aure.

Kamar yadda Anty Farida ta ce za ta yi shiru har sai ya aiko gidan su. A da tunanin da ta yi shine gobe da safe ta playing record É—in hiran su wa Baabar ta ta ji saboda ta yadda da maganarta ta kuma yiwa Baba bayani...

........................

Washe gari ma shigar atamfa ta yi duk da kuwa a dresscode ranar Jumua'a ne kawai aka amince asa kaya native.
Yana shigowa ta bi bayan sa da sauri.

"Sir kana da meeting da Sudanese ƙarfe goma. Sannan akwai wani Mr Habib Olalekan da ya kira ya ce yana buƙatar ganinka na ce ya zo ƙarfe tara"

"What about the files that i asked you to arrange?"

" na gama Sir"

"Bring them here"...

.........

Sati ɗaya kenan da fara zuwa aiki. Duk wani kafa da Sir Najeeb ya ɓullo da shi dan ya muzguna ma ta tana shanyewa, acewarta dole ta jure kar ya ɗauka ta gaza aikinta ne. Tsawa da masifa kam tana shan shi kullum.

A ɓangaren Maijiddah kam tunda sauran 'yan gidan su su ka ji labarin abinda ya faru sai su ka koma tsokanarta da habaici da Matar custom. Abin yana sosa ma ta rai sai dai ba yadda za ta yi tunda dama sun saba tsokanarta. Bisa umurnin Farida ta amince da AbdulWahab. A yadda ya tsara immediately zai tura iyayensa ayi maganar sai dai ta ce ya bari a gama bikin ƙannenta tukunna.

Da sati ta zagayo ta je yiwa Hajiya Yelwa kitso, kunya duk ya cikata lokacin da Hajiyar ta kira ta da 'surkuwa ta' da kyar ta iya ƙarasa kitson saboda yadda ƙannen AbdulWahab su ka sa ta agaba da tsokana.

Shirye-shiryen biki ake ba kama hannun yaro. Dan asabat za a É—aura aure...

Kallon rainin hankali ya ma ta sannan ya ce "repeat what you just said"

"Sir Najeeb ina son É—aukan leave na kwana uku. Ba zan zo aiki ba ranan Laraba Alhamis da kuma Jumma'a"

"You are crazy right? Yaushe ki ka fara aiki da za ki É—au 3days leave?"

Ta yi shiru

"Answer me!" Ya daka ma ta tsawa.

"Sir, bikin ƙannena za ayi kuma..."

"And so?"

"Sir...."

"Get out of my office"....

Washe gari laraba ya ɗauka ba za ta zo ba sai ya ganta. A zuciyarsa ya ce ashe ta san mi ta ke yi. Sai dai ƙarfe ɗaya na yi da aka fita sallah ta yi tafiyarta.

Da ya dawo daga masallaci ya shiga office ya ga takarda akan desk É—in sa.

*Sir na tafi, sai Monday zan dawo. Ka yi haƙuri wannan hidimar ta gida ce dole ayi komai da ni*

Duƙunƙuna takardar yai sannan ya cillar " crazy bitch"
Ya É—au waya ya kira Anas.

"Hello mutumina ya aka yi?"

"Find another secretary"...

*💮SAKATARIYA TA💮*
.......(My Secretary).......

*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

*Free page*

0️⃣0️⃣7️⃣

Hankali kwance Farida ta ke hidiman biki. Anas dai ya kira ya ma ta faɗa akan tafiyarta, acewarsa kwana uku yai yawa sannan ya sanar da ita Najeeb ya koreta sai dai kar ta damu ta zo ranan Monday ɗin kafin nan zai roƙe shi. Ita kam ko ajikinta dan ta san abinda ta shirya wa Najeeb.

Ranan Jumma'a su Ummi su ka zo daga Jos, murna wajen Farida ba'a magana. Ranan Asabat aka É—aura auren *Hajara Musa Wase da Haladu Iliyasu* sai *Salima Musa Wase da Jabir Muhammad*

'Yan uwa daga Wase da GiyaÉ—e duk sun zo, da ke Baffa Musa da Baaba Sabuwa duka 'yan Wase ne. Ita Anty Hanne kuma 'yar GiyaÉ—e ce.
Haka aka sha hidima lafiya, duk da an ɗan samu rikici ranan yini saboda magulmata wanda su ka tisa Baaba Sabuwa a gaba kan rashin auren 'yarta Maijiddah. Maijiddah ta yi kuka har ta ƙoshi duk da ta san akwai alamun kukan na ta ya kusa ƙarewa amma kuma madamar ba auren ta yi ba, ita ko Baabarta ba wanda zai samu sukuni...

.......................

Shigar Abaya ta yi mai adon duwatsu kalar gold. Gyalensa ta yi rolling da shi sannan ta É—au jakarta ta fito, gidan dai an watse sai 'yan tsiraru. Ummi ma ta tafi jiya saboda aiki da za ta koma.

"Allah dai ya sa Sir Najeeb ya haƙura idan ba haka ba kuma kin gama aiki kenan a Najeeb constructions"

"Ya ma isa ya koreni. Lallai! ai Yakubu ka zuba ido kawai ka sha kallo amma yau ko ana ha maza ana ha mata bazan ajiye aiki ba"
Chapter 11 · 0% Book details