← Book details Sakatariya Ta Psrt 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 82 OF 91

Sashe 82

Sakatariya Ta Psrt 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Haba Saminu a bi a hankali mana"

Jin muryan mace ya sa Saminu ya fara washe baki yana faÉ—in sorry Hajiya.

"Suna na Farida ƙanwar Yakubu ɗan gidan Alhaji Musa Wase"

"Kai kai ashe Hajiya Farida ce. Ki gafarceni dan Allah na É—auka wani banzan yaro ne"

Farida ta ce ba komai

"Ina son ka min wani aiki ne ka É—an samu wani abokin ka sai ku zo. Za ku samu 'yan chanji na siyan kati"

Saminu ya sa ihu yana faÉ—in koma minene za su yi...

Farida ta yi murmushi ta ce "Naomi miji na ki ke so ko?. Fine, za ki same shi da kyau"...

...............................

Tana zaune tana duba kayyayakin da su ka siyo É—azu ta ji wayarta na ringing. Da sauri ta É—auka dan tunanin ta Najeeb ne ganin sunan Madam Farida ya sa ta yi tsaki. Ko me ta ke nema a wajena oho.
Kamar ba za ta É—auka ba sai kuma ta É—auka.

"Naomi Naomi, Naomi Masoyi. Naomi matar Najeeb ko?. Fatan kina lafiya? Ina son ganin ki ya za ayi ne?"

Naomi ta ja tsaki ta ce " ba za ki ganni ba. Na san plan É—in ki bai wuce ki dake ni ba"

Farida ta yi dariya ta ce "Allah ko? To barin zo sai mu ga ko dukan na ki da gaske zan yi"...

Naomi ta kashe wayan tana tsaki. Baifi minti goma ba sai ga shi Mrs Comfort na kiran ta akan ta zo ta buɗe ƙofa ana ƙwanƙwasa ƙofa.
"Mama ina Abel, ya je ya buÉ—e mu su"

Mrs Comfort ta É—aga murya tana faÉ—in " wai ba za ki fito ba. Abel baya nan fa"

Naomi ta yi tsaki sannan ta fito.

Mrs Comfort na zaune a kan keken guragu tana karanta bible Naomi ta zo ta buɗe ƙofa. Naomi ta zaro ido lokacin da ta ga Farida tsaye, bayanta kuma wassu samari biyu ne wanda da ka gan su ka san a buge su ke.
Ta ja da baya da sauri tana faÉ—in Mama.

Suna shigowa Farida ta ce "Saminu rufe min ƙofa dan Allah"

Naomi gefen Mrs Comfort ta tsaya jikin ta na rawa.

Farida ta kalli Falon na su da kyau sannan ta ce " Mrs Comfort ban san ko da sa hannun ki Naomi ta asirce min miji ba, har ta ke son auren shi"

Mrs Comfort ta zaro ido, Ita da ta tsani musulmai shi ne za ta bari 'yarta ta yi tarayya da musulmi. Ta dai lura da yawan kayyakin da Naomin ke zuwa da su kwana biyun nan, kuma ta yiwa Naomin magana amma ta ce saurayin ta ne ke siya ma ta.

"Ni ban san komai ba. Naomi wai mijinta ki ke so?"

"Madam Farida ki fita a gidan mu ko na kira police"

Farida ta kwashe da dariya ta ce " ina da numban comissioner of police zan baki sai ki gaya mi shi ƙorafin ki amma kafin nan..."

Ta kalli Saminu ta ma sa ishara da ido. Shi da É—ayan da su ka zo da ake cewa Maska su ka yi kan Naomi. Naomi ta yi hanyar É—aki tana ihu amma ko takun kirki ba ta yi ba, Maska ya cafko ta.

Kujeran da ke wajen ɗan ƙaramin dining ɗin su Saminu ya ɗauko. Aka zaunar da Naomi ana ɗaureta bayan sun fara rufe bakin ta saboda kuka da ihu da ta ke yi.

"Tsirara za ku ma ta" Farida ta faɗa da ƙarfi.

Maska ya yaga vest É—in da ke jikinta, mini skirt É—in ma ya yage ta ya saura daga ita sai pant.

"Shi ma ku cire" Farida ta faÉ—a ba alamar wasa a fiskarta.

"Plz Madam Farida, i beg you. Naomi za ta bar mi ki mijin ki, plz dont kill her" Mrs Comfort ta faÉ—a tana kuka.

"Ni ba kisa zan yi ba, zan dai É—anÉ—ana ma ta kaÉ—an daga azabar da za ta ji duk ranan da ta sake neman mijina ne"

Ta kalli Saminu ta ce "bar ma ta pant É—in, zai ma sa cirnakun su ci gindinta sosai"

Handglove ta cire ta miƙawa Saminu. Saminu ya ce " Hajiya barshi zan sa hannu kawai"

"A'a ka dai saka É—in"

Ya karɓa handglove ɗin yana sawa. Daya gama Maska ya fito da wata leda wanda kwalbar Bama mayonnaise ne aciki cike da cirnaku baƙaƙe da jajaye.

Saminu ya É—ebo cirnakun nan ya sa hannu cikin pant É—in ta ya zuba su. Har da cuccusawa cikin abun ta.
Da ya gama ya zuba sauran a cinyayyen gashinta, dama ta riga ta cire wig É—in da ke kan ta. Sauran ya sa a bayanta....

*SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......

*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

0️⃣5️⃣4️⃣

Naomi sai zazzare ido ta ke yi tana kici-kici akan kujera, idonta yai ja ga gumi da ke ta tsatstsafowa a jikinta. An ɗaure hannu da ƙafa ga bakin ma an kulle ba halin kuka.

Mrs Comfort ta turo kekenta zuwa wajen Farida da ke tsaye tana kallon Naomi.

"Plz Madam Farida, i beg you in the name of the Almighty God stop this. Naomi za ta bar mijin ki i promised you that"

Jin yadda Mrs Comfort ke roƙo tana hawaye ya sa ta ɗan ji tausayin ta.

Ta ciro Shentos insecticide a jaka ta miƙawa Saminu.
"Fesa ma ta su mutu, tunda uwarta ta roƙi alfarma"

Saminu ya ƙarɓa ya fara fesa wa Naomi a kanta da bayanta. Yana shirin feshe wajen abun ta, Farida ta ce "tsaya-tsaya Saminu. Cire ma ta pant ɗin za su faɗo"

"Hajiya ki bari na fesa a wajen za su fi mutuwa da wuri"

Farida ta girgiza kai. Saminu ya cirewa Naomi pant ɗin wanda ke cike da cirnaku wasu sun mutu wasu kuma suna ta mutsu-mutsu a jiki. Cikin minti ɗaya kusan duk cirnakun sun mutu saboda ƙarfin maganin. Wanda su ka tsira ma to sun nakasa sosai.

Farida ta kalli Mrs Comfort ta ce "ki jawa 'yar ki kunne, duk abinda ta yiwa mijina ta warware idan ba haka ba. Nan gaba ba'a cirnaku kaɗai zan tsaya ba, sai ta ƙwammace ba ta zo duniya ba"

Ta cilla ma ta wani tube na magani ta ce " idan ta wanke jikinta da kyau ta shafa wannan. Zai taimaka wajen rage raÉ—aÉ—i"
Ta kalli su Saminu ta ce su kunce ta. Ana kunce bakin Naomi ta ɓarke da kuka, ihu ta ke kamar wadda aka aikota saboda azaba. Ana gama kunceta ta fita da gudu sai banɗaki, tana zuwa taga ba ruwa a ciki ta fito ta wuce kitchen da gudu tana sosa gabanta da bayanta zuwa kanta duk lokaci guda. Suna ji ta buɗe randan ruwa ta fara kwararawa kan ta tana yi tana kuka...

Farida ta kalli Mrs Comfort ta ce "ki jawa 'yar ki kunne ko kuma jikinta ya gaya ma ta" daga haka su ka fice a gidan.

Gaba ɗaya ruwan randar ta ƙarar a jikinta still ba ta ji sauƙin komai ba. Sai ihu ta ke yi, Mrs comfort ta ɗau waya ta kira Abel ƙanin Naomi akan maza-maza ya zo gida.
Naomi ta zama tamkar mahaukaciya a cikin gidan, ta shiga nan ta fita chan, ta kasa zama ta kasa kwanciya sai kuka da soshe-soshe...

Ƙarfe shida na yamma Naomi na kwance tsiraran ta tana hawaye tana nishi sama-sama, gefenta ƙawarta Maureen ne ke ma ta fifita a gabanta. Maganin da Farida ta bayar aka shafa ma ta, ya ɗan taimaka wajen samun sauƙin raɗaɗin da ta ke ji. Ilahirin jikinta duk ya cika da tabon cizo.

"Na God go Punish that woman" Maureen ta faÉ—a tana tsaki

Mrs Comfort da ke gefe tana ganin 'yartata ta ce "ba laifin Madam Farida ba ne. Laifin Naomi ne, mi ya kaita soyayya da musulmi hakan ma married man"

"Mama ki dena faÉ—in haka. Ko ma mi Naomi ta yi ba ta chanchanci wannan punishment É—in ba. This is pure cruelty"

Mrs Comfort ta girgiza kai tana tunanin idan Naomi ba ta ji sauƙi ba za su wuce asibiti kawai...

.............................

Hankali kwance Farida ta koma gida, zuciyarta saƙayau, ko ba komai Naomi za ta yi jinyar kwana biyu.
Ƙarfe shida saura sai ga Anas da Najdah sun zo ma ta.
Anas dai haƙuri ya ba ta kan wannan magana tareda nuna ma ta suna tareda ita ɗari bisa ɗari.
"Akwai wani Malami da na yiwa magana ya ce zai tayamu da addu'a. Insha Allah za mu ga ƙarshen wannan al'amari"

Farida ta ce " Ya Anas na gode sosai Allah ya saka da alkhairi"

Najdah ta cire girman kai ta ce " Anty Farida, Big B yana son ki sosai, ba zai taɓa walaƙanta ki cikin hankalin sa ba, Please kar ki yi fushi da shi"

" Na gode Najdah, ku dai cigaba da tayamu da addu'a"

Najdah ta ce Insha Allah.

Sun É—an jima kafin su ka tafi. Su na ma tunanin Najeeb zai dawo ya same su amma har su ka tafi bai dawo ba...

A ɓangaren Najeeb kuwa zuciyarsa tafarfasa ya ke lokacin da ya isa gidan su Naomi ya isketa kwance. Maureen ce ta kira shi ta sanar da shi komai.

Lokacin da Mrs Comfort ta ga Najeeb ya shigo gidan su hankalin sa a tashe ta fara tunanin kaman maganar Farida gaskiya ne. Idan ba haka ba Sir Najeeb ɗin da ta sani ɗan ƙwalisa mai ji da kan sa ba zai taɓa kallon Naomi ba balle ya damu da ita ko kuma ya so ta.

Tana gani ya É—auki Naomi a hannun sa su ka fita tareda Maureen. Tana faÉ—in su tsaya amma ba wanda ya kulata cikin su...

Da su ka je asibiti gado aka ce ta kwanta sannan Likita ya duba ta daga sama har ƙasa. Da ya gama examining na ta ya nemi bahasin abinda ya faru har cirnaku su ka cize ta haka musamman a ta wajen abun ta. Maureen ta fara koro bayani akan ai wata Ogar Naomin ce ta sa ma ta cirnaku a jiki.

"Saboda me? Wannan ya kamata akai case É—in nan gaban 'yan sanda" Likitan ya faÉ—a cikin faÉ—a.
Maureen ta ce yanzu ma daga asibitin police station za su wuce.
Chapter 82 · 0% Book details