← Book details Sakatariya Ta Psrt 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 91

Sashe 54

Sakatariya Ta Psrt 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Sannun Anty, barka da yammaci" ta faɗa tana ajiye jakarta a kan ƙaramin fridge da ke ɗakin.

" an samu abinda ake so ko? Shi ne yanzu ba za a iya zama da shi ba" Najma ta faÉ—a tana mata wani kallo.

"Big sis ai dama kukan munafurci ne, neman attention ta ke yi kuma ta samu shine ta guje shi. I cant believe wai Daddy ne ya ce ta zama CEO ko mi ta sani oho"
Ta rasa cikin yayar Najeeb da ƙanwar sa wanne cikin su ta fi tsanarta. Mom da Daddy du ka sun karɓeta hannu bibbiyu kuma ba su da girman kai amma Najma da Najdah kam sai a hankali, ƙiri-ƙiri su ka nuna ma ta ba sa yinta, ba kamar Najdan ma.

Farida ba ta ce ƙala ba, ta ƙarasa bakin gadon da Najeeb ya ke kwance kamar mai bacci. Ta manna ma sa kiss a goshin sa ta ce " My Champ, ka ga na jima ko? Aiki ne ya min yawa. Ka san sai yanzu na gane ba ƙaramin wahala ka ke sha ba a office ɗin nan. Da ni kullum gani na ke kana zaune kan kujera mai laushi ga AC ba ka da wata matsala, ashe abin ba sauƙi. Yau har irin zamanka na yi dan kawai na ba su tsoro, na nuna mu su cewa kana tareda ni. Kuma Wallahi sun tsorata. Ka san yanzu kai ni ne, ni ma kuma kai ne"

Najdah ta ja doguwar tsaki Najma kam ido da baki ta sake tana kallon ta. Ba su sha mamaki ba ma sai da ta ce "dan Allah tunda kun riga kun gaisa da shi ku bamu ware, miji da mata su na son keɓewa da junan su"

"Heeeee wonders shall never end, shegiya ke a suwa ki koremu a wajen É—an uwan mu"

"Ni É—in ce dai matar Najeeb"

Najdah ta kalli Najma ta ce " Big sis ki ji abinda ta ke faÉ—a fa, wai mu fita a É—akin Big B"

Najma ta tashi ta ɗau jakar ta ta ce " ba laifin ta ba ne Najdah. Laifin Daddy ne da ya je ya kakaɓo wata 'yar ƙauye ya haɗata da Najeeb, har ta ke ganin matsayin ta yana dai-dai da namu"

Har su ka fita ko kallon su ba ta yi ba. Ba ta da lokacin su, idan fitina su ke nema su jira Najeeb ya warke su ga ikon Allah.
Ta zauna ta sa kanta a gefen sa ta na shafa hannun sa. Bai jima ba bacci ya É—auketa a haka...

Da dare su Daddy su ka zo anan Mom ke ma ta sallama akan jibi za ta wuce za ta je Umurah ta yi wa Najeeb addu'a. Farida ta yi farin ciki da hakan tareda addu'an Allah ya kai ta lafiya ya dawo da ita lafiya.
Fitan su ke da wuya tana zaune ta zubawa Najeeb ido, ta kai hannu za ta kama hannun sa sai ta ga ya motsa yatsun sa biyu. Wani ihu ta ƙwalla tana kiran sunan Daddy.

"My champ da gaske kai ka motsa yatsun ka? Da gaske yatsun ka ne su ka motsa?"

Ganin ba wani reaction da ya sake yi ya sa ta fita da gudu tana kiran su Daddy.

Sun yi nisa da É—akin dan sun kusa fita a asibitin kafin ta taro su.

"Daddy ku tsaya Sir Najeeb ya motsa yatsun sa yanzu" ta faÉ—a tana haki.

Daddy da Mom É—in kowa sauri ya ke ya je ya ga shalelen É—an na su.

Koda su ka zo É—akin Najeeb yana nan dai yanda ya ke.
Kallon da Daddy ya ma ta ne ya sa ta san ba su yarda da maganarta ba

"Allah Wallahi Daddy ya motsa yatsun sa, Allah"

Tana maganan tana hawaye. Mom ta kamo hannun ta ta ce " Farida it's ok, addu'ar mu kullum shi ne ya tashi ɗin. You're just hallucinating ki kwantar da hankalin ki, Bi izni kun fa ya kun zai tashi nan ba da daɗewa ba" jin haka Farida ta tubure akan wallahi Najeeb ya motsa yatsar sa. Ƙarshe dole aka kira likita wanda ya zo ya sa aka kunna mu su video footage ɗin wajen. Dama babban amfani na sa cctv cam ɗin kenan saboda a dinga bibiyar shi ko da zai iya motsawa ko ya farfaɗo ba tareda wani na wajen ba.

Lokacin da su Daddy su ka gani su ka gan hakan ne ta faru Najeeb ya motsa yatsun sa, farin ciki su ka ji marar misaltuwa tareda ƙara samun hope akan Najeeb zai tashi.

"Daddy zai tashi, yana so ya tashi Daddy zan ajiye aikin nan kar ya tashi ba na kusa da shi" ta faÉ—a tana goge hawayen da ke zubo ma ta.

Daddy zaunar da ita yai yana ƙara ma ta nasiha akan tashin Najee. Ko ta na kusa da shi ko ba ta kusa zai tashi Insha Allah, kuma zai fi jin daɗi idan har ya tashi ya ga ta kula ma sa da Kamfanin sa.
Ranan su Daddy ba su bar asibitin ba sai wajen ƙarfe sha biyu na dare.
Farida kam bayan sallah da ta tashi ta yi ba abinda ya sa ta É—auke idon ta akan Najeeb gaba É—aya daren ranan ji ta yi kamar zai buÉ—e ido ya ma ta magana. Ka sa bacci ta yi saboda kar ya buÉ—e ido tana bacci...

..........................

Su uku ne su ka zo domin yin wannan yarjejeniya. A ɓangaren team ɗin Najeeb constructions kuwa su biyar ne Madam CEO tana tsakiyar su.

Dogon bayani Mr Smith yai wanda du ka bayanan sa kan yadda su za su fi samun riba ne ba komai ba. Da ya gama Mr Nokovic ya karɓa ya fara magana amma shi maganar da yai akan wai ba su yadda da shugabancin Farida ba ne.

Da su ka gama ta su bayanin Farida ta karɓa ta fara bayani.

" a duk bayanan ku abu biyu na fahimta. Na farko ba ku yadda na zama CEO ba na biyu kuma ku na son cire hannun jarin ku"

Mr Nokovic ya ce " mu na son ƙara siyan hannun jari ba wai cire hannun jari ba"

"Oh really, ashe har kun tsorata kenan. Ni abinda na gani a rubuce shi ne kuna son ƙara siyan hannun jari ko kuma ku cire hannun jarin ku. So ni na riga na yadda maganan siyan hannun jari yanzu batun hannun jari da za ku cire za mu yi magana akai. So nawa za ku siyar ma na"

Kallon-kallon su ka farayi suna mamakin yadda lokaci guda ta juya abun kan su.

"Ba ni da lokaci da yawa, kaman yadda ku ka sani ina da majinyaci a asibiti wanda ke buƙatar kulawata"

"Mrs Jibo (ya faÉ—i jibon kaman wani *Jaebo*) mun san halin da kamfanin nan ke ciki ba za ta iya siyan shares É—in mu ba."

Farida ta yi murmushin yaƙe ta ce " waya gaya mu ku Kamfani ba ta da halin siya. Ni nan ni zan siya kunga abu ya dawo gida kenan. So mu fara cinikin $200,000,000 mi ku ka ce?"

"Mrs Jibo" Mr Smith ya kira kafin ya ƙara da wani abu Farida ta ce " $205,000,000 wannan fa?"

Shiru su ka yi dan ba su zo don su siyar da shares É—in su ba dama burga da barazana ne kawai.

"Ku na cewa ba ku yadda na shugabanci wannan kamfani ba a wani dalilin? Saboda ina mace?"

Mr Vladimir wanda bai yi magana ba tun É—azu ya ce "mun yarda ki shugabanci wannan kamfani a bisa sharaÉ—i É—aya"

Farida ta É—an gyara zama ta ce " wanni sharaÉ—i"

Mr Vladimir ya ci gaba da bayani " akwai bidding da za ayi a Abuja nan da sati huɗu. Manya-manyan kamfanoni za su shiga wannan bidding su submitting picth ɗin su saboda duk wanda ya ci contract ɗin, its worth billions. Sau ɗaya wannan kamfani ta taɓa winning contract mai tsada kamar haka, but wannan ya ma fi wanchan da aka yi a Lagos.
Mu na so ki yiwa wannan kamfani register ki kuma jagoranci wannan kamfani har ta winning wannan contract É—in. Idan Najeeb constructions ta samu wannan project, mu mun amince za mu sayar mi ki 5% na shares na mu amma idan wannan kamfani ta shiga gasan nan ta faÉ—i to za ki sayar ma na da 10% na shares É—in ki"

"Idan kuma na ƙi shiga gasar fa?"

"Za mu cire duka 11% shares na mu wanda ka iya kassara wannan kamfani saboda halin da ta ke ciki"

Tsawon minti biyu ba wanda ya sake magana. Sai murmushi turawan su ke ganin sun sa ka Farida a wani hali.

" Najeeb constructions za ta shiga wannan gasa kuma za ta ci Insha Allah"

Anas ya kalleta yana faÉ—in "Farida akwai matsala, ba za mu iya..."

" Ni Aisha Farida Mrs Najeeb Jibo, na amince za mu shiga wannan gasa kuma za mu ci da yardar Allah"

*SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......

*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

0️⃣3️⃣4️⃣

***
Tana shiga office yana biyota.
"Farida kin san abinda ki ke faÉ—a kuwa, a halin da wannan kamfani ta ke ciki shine za ki samu cikin gasa. Do you have any idea irin manya-manyan kamfanin da za su shiga wannan gasa, ko da Najeeb yana nan chance É—in winning is very low balle kuma baya nan"

"Ya Anas so ka ke na ƙasƙantar da mu a gaban yahudawan turawan nan?"

"A'a so na ke ki cire girman kai, ki ce ba za mu yi gasan ba. Idan sun cire shares na su ko Daddy za mu iya neman taimako a wajen sa"

"Ya Anas kenan, mutanen nan sun san mi su ke fa, ɗaurin goro su ka ma na. By all means so su ke mu faɗi, mu ji kunya. Ni ban shirya turmusa wannan kamfani a ƙasa ba"

Wannan karan a hankali yai maganar ya ce " kin zaɓi a shiga gasan nan mu faɗi, Najeeb ya rasa 10% na shares na shi?"
Chapter 54 · 0% Book details