← Book details Sakatariya Ta Psrt 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 91

Sashe 49

Sakatariya Ta Psrt 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Lokacin da ya gama abubuwan da zai yi yana kishingiÉ—e a kan gado ya ji gadon ya ma sa daban. Tun da ta zo kullum za su kwanta akwai pillow a tsakanin su, jiya ne kawai su ka kwana ba pillow.
A hankali ya sa hannu ya fara shafa gefen da ta ke kwana wanda ya ke empty yanzu. Ya tuno ranan farko da za su kwana a kan gadon faɗan da su ka yi, daga ƙarshe da tunanin kissing ɗin da su ka yi jiya bacci ya tafi da shi.

Washe gari da safe Daddy ya ce su je su yiwa Baffa Musa ta'aziya. Tare su ka je a chan ne ana taɗi wanda tsakanin Daddy da Baffa Musan ne dan shi banda ya haƙuri da ya ce bai kuma cewa komai ba. Cikin taɗin su Baffa Musa ke kawo rayuwar da Farida ta yi. Daga wannan gida zuwa wannan gida kafin daga baya ta zauna a wajen Kakannin ta.

Daddy ya tambayeshi ko miyasa bai ɗauki Farida tun da wuri ba. Baffa Musa ya ce "Hmm Faridan, tun tana yarinya ta ke da baki. Ko hutu aka kawota sai ta yi ta ƙorafi, Baffa garin ku akwai zafi, ba zan zauna ba"...

Lokacin da za su tafi Baffa ya ce da Najeeb " ka kula min da ita dan Allah. Ka da ranan gobe Ubanta ya ce ban riƙe amanar tilon 'yar sa ba"

Najeeb ya ce Insha Allah...

........................

Yau sati ɗaya kenan da ba ta nan. Cikin sati ɗayan nan ya rasa ganewa kan sa. Bai ma cika son fita ba, dama wajen aiki ke ɗebe ma sa lokaci to yanzu ana hutu. Sabreen washe garin da Farida ta tafi itama ta yi tafiya, bai san inda ta je ba kuma bai damu ba dan shi idan ta tashi ne to kar ta ƙara dawowa.

Yau da ya je wajen Hajia Mama ne ta ke cewa ya kira ma ta Farida ta ma ta ta'aziya.

Kwana uku da Farida ta yi a Jos ta yi su cikin rashin jin daÉ—i, na farko ga rashi da su ka yi, na biyu kuma Sir Najeeb da ya shareta. Kullum da tunanin sa ta ke kwana ta tashi, amma shi ko text bai ma ta ba balle ya kira ya ma ta ta'aziya. Duk da kuwa ranan da ta taho ta tura ma sa text akan sun isa lafiya amma ko reply bai yi ba. Wasu lokutan har mafarkin suna tare ta ke, haka kawai tana zaune sai ta ji kaman muryarsa a kunnen ta yana faÉ—in "kiss me" har tunanin ko ta fara hauka ta ke yadda waÉ—annan kalmomin biyu ke sa ta jin wani nishaÉ—i da farin ciki...

Tana ganin wanda ya kirata mamaki haÉ—e da wani farin ciki ya mamayeta, sai da wayar ta kusa katsewa sannan ta É—auka.

"Sir Najeeb shi ne sai yau?"

"Aishatu, kuna lafiya ya haƙuri?" Muryan Hajia Mama ya doki kunnen ta maimakon muryan Najeeb...

Hajia Mama na kashe wayan ta kaiwa Najeeb sanda.
"Ashe ko ta'aziya ba ka je mu su ba. Kakan matar ta kan"

"Kai Tsohuwa, ba munje gidan uncle É—in ta ba. Miye sai mun je har Jos. Will that bring back the dead?"

Hajia ta sa ke É—aga sanda yai gefe da sauri yana dariya...

Kaman yadda Hajia Mama ta nema kuma ta sa Daddy ya ma sa magana dole ya shirya zai je Jos. Shi sau ɗaya ya taɓa zuwa garin kuma aiki ne ya kaishi.

Ya fito kenan ya tarar da Anas da Najdah a falo su na magana.
"Kai ba na son takurawa fa, she's still in school" Najeeb ya faÉ—a yana hararan Anas.

Anas ya ce " an gaya ma ka ni irin ka ne da sai na zauna har 35yrs. Ai ni kafin watan shidan sabuwar shekaran nan zan angonce"

"Shege, to Baby sai ta ƙare karatu tukunna"

"Wallahi ba ka isa ba, ka san tun yaushe mu ke shan ruwan kanwa kuwa"

"ÆŠan iska, to ka bi ni a hankali ko in hanaka, dama Musty yana gaba dani saboda na hana shi, ka ga idan ka yi wasa sai na bashi ita"

"Kai na a ƙasa babban yaya, mu na neman tubarrakin ku"...

Sai da su ka jima su na wasa da dariya kafin daga baya bayan Najdah ta bar falon Anas ya shiga bayanin abinda ya kawoshi.

"Najeeb, Farida ita ke da gaskiya da kai da kamfani you owed her apology"

Najeeb ya gyara zama yana sauraron sa.

"Khalidah da Alhaji Matawalle su su ka kitsa komai. The money from VESTAC inc. Alhaji Matawalle ne ya sa aka tura supported by Khalidah. Shi ya shirya yadda za a sace ma ka takardun zanen ka a kuma ɓata modelling da ka yi. On the other hand kuma Khalidah ita ta kawo shawaran a framing Farida. Duka evidences da mu ka haɗa yana nan" ya miƙa ma sa wata ƙatuwar envelope.

Idon Najeeb ya rine yai ja tsanar Khalidah da Alhaji Matawalle na ƙara shiga ran sa.

"Kai ka san wani mataki ko hukunci za ka É—auka idan aka koma aiki ranan monday" ...

..............
Ba dan ya riga ya shirya tafiya ba da ba abin da zai sa ya tafi. Ƙusan ƙarfe uku ya isa Jos, address ɗin da Yakubu ya bashi ya bi, da tambaya kuma ya isa har layin su. Bai gama shan mamakin layin ba sai da ya isa gidan. He cant believe a irin wannan gida Farida ta yi rayuwa. Ba wai dan bai saba ganin gidaje haka ba a'a sai dan yadda Farida ke gudanar da rayuwar ta with boldness and cofidence, ba ta shayin shiga ko'ina. A ko yaushe ji ta ke dai-dai ta ke da kowa, duk daraja ko kuɗin ka kuwa.

Yaro ya kira ya ce a ma sa magana da Farida dan tun a bakin layi ya ajiye mota saboda mota ba ta shiga layin.

Ana yiwa Farida kitso yaro ya shigo wai ana sallama da Anty Farida.

"Ni kuma? Waye?"

"Bai gaya min ba"

"Ya yake" Farida ta sake tambaya tana sawa ranta kwaÉ—ayin ya kasance Sir Najeeb ne ya zo.

Yaron ya ce " fari ne, dogo, kaman balarabe ya ke amma ya iya Hausa" ai yaro bai gama bayani ba ta tashi daga gaban Umma Binta ƙanwar Ummi da ke ma ta kitso.

"Ka je da gudu ka ce ma sa ina fitowa yanzu"

"O'o amaren zamani kenan, Farida wannan zumuÉ—i haka"
Ai ba ta ji me Umma Binta ke cewa ba ta riga ta shige É—aki za ta É—au hijabi...

Ya bawa ƙofan gidan baya yana tsaye hannayen sa duka biyu su na cikin aljihu, hankalin sa ya tafi wajen wassu yaran Birom da ke wasa a ta wajen kwata yana mamakin yadda yaran ba sa ƙyanƙyamin wajen.
Yana sanye da baƙar shirt da baƙin hoodie jacket sai baƙin jeans.

"Sir Najeeb" muryan ta ya doki kunnen sa. A hankali ya juyo yana kallon ta, ba ta wani chanja ba sai dai idon ta ya É—an nuna rama may be saboda kuka ne dan ya san ba ta wasa da abinci.

"Ashe za ka zo, shi ne ko ka faÉ—a min. Mu shiga ciki"

Sai da ya É—au minti É—aya ya na kallon ta kafin ya bi bayanta su ka shiga gidan...

Da ke kwana na tara kenan da rasuwan duk an watse sai iyalin sa kawai. A daddafe ya gaisa da su. Kusan awa ɗaya yai a gidan saboda yadda 'yan uwa da maƙota ke zuwa gaida mijin Farida wanda yawanci gulma su ke zuwa saboda su ga mutumin da ya sa aka fasa aurenta da Rayyan, su ga ya ya ke. Sai dai kowa ya zo da Masha Allah ya ke tafiya baki buɗe. Sun ga kyau, sun ga kuɗi, sun ga aji, sun ga ƙasaita...

Lokacin da zai tafi bayan ta raka shi wajen motar sa ya ce " za'a koma aiki monday yaushe za ki dawo?"

"O'o ni Aisha Farida, dan aiki kawai za a neme ni. Ni kam dole idan na koma a chanja min matsayi ya kamata a upgrading É—i na, na bar matsayin sakatariya"

" ki na son ƙarin matsayi ne?"

"Haba Sir Najeeb wa ya ƙi cigaba a duniya"

Bai san ya ake zuwa gai da sarakai ba shi ya sa bai zo da komai ba. Ya dai bar musu dubu ɗari a gefen ɗrinks ɗin da su ka kawo ma sa wanda ko taɓawa bai yi ba...

Har motar sa ta ƙule Farida ba ta bar wajen ba. Tana ƙissima abubuwa dayawa a ranta. Zuwan Najeeb ya sa Najeeb ya ƙara samun wani matsayi na daban a zuciyar ta...

*SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......

*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

0️⃣3️⃣1️⃣

*wannan labarin na kuɗi ne, dan Allah kar a fita da shi, ga mai so zai iya tuntuɓar 08137311900*

Yana hanya ta kirashi lokacin koma fita daga Jos bai yi ba. Ya saƙala bluetooth ya amsa kiran.

"Sir Najeeb shi ne har da ɗawaiyina haka. Mun gode Allah ya ƙara buɗi. Allah ya kai ka lafiya"
Amin kawai ya ce ya kashe kiran.

Da ya isa Kano yana so ya kira ta amma ya ka sa. Sai ya É—auko wayar zai danna numbar ta sai ya fasa ya ajiye, ana huÉ—u da yai haka sai ga text É—in ta ya shigo tana ma sa ya hanna da fatan ya isa lafiya.
"Na isa" kawai ya daure ya rubuta ya ma ta reply da shi. Maimakon ta haƙura a haka sai ta kuma turo da wanni text ɗin.
"Sir N mi zan taho ma ka da shi? ina son zuwa Wase gobe"

Bai san ina ne Wase ba, dan haka ya minimizing wayar ya browsing sunan nan ya gane wata ƙaramar hukuma ne a Jos.

Ya ma ta reply da "ok"

Ta sake turo wani saƙon " Sir N ba ka faɗi abinda zan kawo ma ka ba"

Ya na so ya ajiye wayar ya shareta amma zuciyar sa ta hanashi

"Kan ki" ya tura ma ta ba tareda ya gama tantance ma'anar faÉ—in hakan ba.

"Kan kifi? Sir N kan wani irin kifi?"
Chapter 49 · 0% Book details