Sashe 5
Sakatariya Ta Psrt 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tun kafin Adam Jibo ya dawo Nigeria dama ya riga ya gina wani ƙaton gida a Kano. Anan iyalen sa ke sauka idan sun zo hutu Nigeria. Ƙannen sa sun yi aure suma da nasu iyalin Fatima na aure a Kano yayinda Ruƙayya ke aure a Katsina. Suma ƙannen sa 'ya'yan Alhaji Mustafah sun yi aure da iyalen su. Sulaiman yana Kano yayinda Abubakar ke Abuja. Duk wata su kan haɗu ayi meeting a gidan tsohuwa wato Hajiya Mama. Alhaji Mustafah ya jima da rasuwa tun kafin rasuwan Aisha. Hajiya Mama tana nan a gidan Alhajin sai fama da jikoki. A gefen gidan Alhajin duka Sulaiman da Abubakar su ka yi gininsu. Shi Adam ne gidan sa yai nisa da su. Sai dai shima indai yana gari to kullum sai ya je ya gaida Hajiya Mama wannan ya zamo ma sa al'ada. Hajiya Mama ita ya sani a matsayin uwa. Goggon su ta jima da rasuwa bayan rasuwar Mahaifin su ta sake wani auren a Ashaka inda wajen haihuwa ta rasu. Haƙiƙa Hajiya Mama uwa ce ta gari. Ba ta haifi nata ba amma ta riƙe yaran mijinta tsakani da Allah wanda har yau suna darajata. Inda ace ta ha'ince su da tuni sun watsar da kashinta musamman bayan da Alhaji Mustafah ya rasu.
Duka karatun Najeeb a ƙasar waje ya yi su. To dama a ƙasar wajen aka haife shi. Yai degree na shi na farko a MIT (Messacheusettes Institute of Technology ) inda ya karanchi Engineering and Technology daga nan ya sake wani degree ɗin a ɓangaren Architecture. A London yai Masters na shi kafin ya tafi Korea yai Phd na shi.
Ya fara aiki a Korea da wani construction company kafin ya ajiye aikin ya je yai wani course a India, lokacin Mahaifinsa Professor Adam Jibo ya dawo Nigeria da zama. Bayan ya ƙare course ɗin ne ya dawo Nigeria ya buɗe Kamfanin sa mai suna *Najeeb constructions* shekaru bakwai da su ka wuce kenan.
Ya taso cikin kuÉ—i kuma ya nemi kuÉ—i ya samu. A shekarun sa talatin da huÉ—u, ba abinda ke gaban sa da ya wuce kamfanin sa. Zai iyayin komai saboda samun É—aukakar kamfanin sa.
Anas shi ne babban aminin sa, jinin su ya haɗu sosai duk da kuwa Najeeb ya girmeshi da shekara uku, amintar su ta sa lokacin da ya buɗe kafanin sa ya jawo shi gefen sa su ka haɗu su ka ɗaukaka kamfanin saboda shima Architect ne. Bayan Daddy da Najdah wanda ya ke kira Baby to Anas shi ne mutum mafi kusa gareshi idan ka ɗauke Hajiya Mama. Sun jima da baran-baran da yayarsa Najma a kan ƙin Mahaifiyar su daya ke yi wanda har yau babu wanda ya san dalili abu kusan shekaru ishirin kenan.
*SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......
*Azizat......âœ*
*Wattpad @000Azee*
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
*Free page*
0ï¸âƒ£0ï¸âƒ£3ï¸âƒ£
Kamar kowani lokaci idan ta zo Kano ɗakin Inna ta ke kwana, wannan karan ma hakan ce ta faru, sai dai yanzu Maijiddah da Zainab ke kwana a ɗakin bayan rasuwar Inna. Daga zuwan Farida ta kori Zainab a ɗakin tace ba za su kwana su uku ba. Zainab ta fice daga ɗakin tana ƙuƙuni.
Maijiddah 'yar Baaba Sabuwa ce, kuma duk cikin yaran gidan tafi su hankali, kasancewa anyi auren ƙannenta biyu gashi za'ayi wasu biyun ya sa ake goranta mata rashin miji, kullum a takure take, dududu shekarar ta ishirin amma yadda ake mata gori a gidan ka ɗauka ta shekara talatin ne ba tayi aureba. Wai har 'yar Zainab da ke shekara shahuɗu tanada samari ita ba ta da kowa. Duk masu zuwa wajenta ba sa jimawa su ke guduwa. Islamiyya kaɗai ta ke zuwa yanzu, sai kuma takan taɓa ɗinki a keken Baabarta sannan tana sana'ar kitso. Dan wani lokaci har gida ake zuwa a kirata ta je ta yi kitso, domin gaskiya Allah ya bata baiwar iya kitso.
Shekarar ta uku da gama secondary, dokar Baffa Musa ce, sai dai mace ta yi karatun gaba da secondary a gidan mijinta amma ba a gidan shi ba, shi ya sa Maijiddah ba ta yi wani hoɓɓasa domin ta cigaba da karatu ba, saidai cikin ran ta tana ƙwaɗayin hakan. Ba wai muni gareta ba tana da kyau dai-dai gwargwado sai dai gaskiya guntuwa ce. Dan harta Zainab da bata gama tsayinta ba, ta fita tsayi.
Maijiddah tafi ganin gajartar da Allah ya mata a dalilan da ya sa ta rasa manema...
Suna sallar Asuba Maijiddah ta gaida Farida sannan ta fara gyara ɗakin su har lokacin Farida na yin azkar. Da ta gama ta fita dan ta fara hidiman cikin gida. Lokacin da Farida ta fito daga ɗaki Maijiddah kaɗai ta samu a tsakar gida tana shara. Cikin isa ta riƙe ƙugu tace " Jiddah ina batun dokokin dana sa a gidan nan wancan zuwana Kano?"
"Anty Farida kin san yau Lahdi ne ba a tashi da wuri"
Murya sama-sama ta fara magana. " Tab! wato dan bana gidan shine aka watsar da dokokina ko. To ku sani Wallahi duk wanda ya san yau ranan aikinsa ne bai fito ba ganinan zuwa har É—akin uwarsa in dakeshi kuma ba abinda zai faru. Zan irga uku É—aya....biyu...." sai ga yaran suna fitowa daga É—akunan su da gudu. Da ke sun manta tsarin da ta musu, kowa sai ya fito dan kar ya zama ranar sa ce kuma bai fito ba ta bishi É—aki ta zane. Ba yau Farida ta fara zane yaran gidan ba, yanzu haka yadda su ke tsoronta ko su Yaya Yakubu iya kaci.
Maijiddah ta ɗan yi murmushi lokacin da ta ga ƙannen nata na fitowa da gudu.
...............................
Ba tareda ya ɗago ya kalli Joseph ba ya ce " three days" Joseph ya haɗiyi yawu moƙot saboda ba shi da ta cewa, amma taya kwana uku zai ishesa ya je Enugu burial na Maman sa ya dawo a kwana uku, bayan Enugun ma chan cikin wani ƙauye mai nisa su ke.
"Anything else?" Muryar Najeeb ta dawo da shi daga tunanin da ya ke. Joseph ya girgiza kai da sauri ya ce "no sir". Da hannu Najeeb ya ma sa nuni da yai waje. Joseph ya bar office É—in da sauri...
Tare su ka fita da Anas, sunje sun duba wani site da kamfanin su ke ginawa. A hanyar su ta dawowa Anas ya nuna yunwa ya ke ji dan haka dole su ka tsaya a wani restaurant da ke kusa.
Fiskar san nan tamau ta ke kamar bai taɓa dariya ba a tarihin rayuwar sa. A haka su ka shiga wajen cin abincin, shi idan ba dan Anas ba ba abinda zai sa ya tsaya a irin wannan waje. The restaurant is not even classy.
Sai da su ka zauna waiter ya zo dan ya ƙarɓi order ɗin su. Da sanin Najeeb ya faɗi wani kalar girki wanda baya cikin menu ɗin su. Saurayin ya ɗan tausasa murya ya ce "sorry sir, we dont have that in our menu"
Najeeb ya smirking ya ce " then, water will be fine"
Har zai tafi Anas ya tsayar da shi ya ce ya kawo wa Najeeb irin abinda ya ordering.
"Seriously!" Najeeb ya faÉ—i yana É—an girgiza kai.
"Mutumina kai fa ba engine ba ne, tun safe fa ba abinda ka ci. Gara ni naci ɗumame na ƙoshi kafin na fito, amma kai na san bayan tea ba abinda ka sa a baki"
"Did i complain?"
"Idan kai ba za kula da kan ka ba, i'll help you do that"
Kafin a kawo abincin wayar Anas ta yi ringing ganin mai kiran ya sa ya ce da Najeeb yana zuwa. Fita yai daga wajen don ya samu daman magana sosai.
Wata budurwa da saurayi su ka shigo wajen cin abincin . Hankalin Najeeb na kan wayar sa dan haka bai lura da su ba, sai dai table É—in da ke kusa da na su su ka zauna, da ke budurwar ce ta bashi baya dan haka bai ga fiskarta ba sai dai ya ga na saurayin lokacin da ya É—ago zai É—au ruwan da waiter ya ajiye mishi.
Surutun da budurwar ke yi ya sa ya ƙara tsanar wajen saboda hayaniya da ta cika shi. Tukunnama, ta ya mace za ta dinga surutu haka in a public place kamar wannan. Tun da su ka shigo siririn muryanta ya gauraye wajen. Kafin saurayin da su ka shigo tare yai magana ɗaya budurwar ta yi ɗari. A haka Anas ya shigo ya same shi, su na fara cin abincin Najeeb yai tsaki ya aje fork da sokali sannan ya ɗau tissue ya goge bakin sa.
"Abincin bai ma ka ba ko?" Anas ya tambaya yana kallon sa. Najeeb ya É—au ruwa ya kora batareda ya bawa Anas amsa ba. Tsakani da Allah ba wai abincinne bai ma sa ba, ba kuma yunwanne ba ya ji ba. Sai dai surutun wannan budurwane ya cika ma sa kunne. A rayuwarsa ya tsani hayaniya balle kuma yawar magana.
Kamar Anas ya gane damuwarsa ya ce a hankali "wannan yarinya ba dai surutu ba. Kamar radio"
Najeeb ya cigaba da danna wayarsa ba tareda ya ce komai ba...
..........
"Ka san Allah, idan na yi wata ɗaya a garinkun nan toyewa zan yi. Irin wannan zafi haka!. Da wayona Ray ban taɓa fin sati uku a Kano ba, ina ma zan iya"
Farida ta faɗi tana kora ruwa amaƙoshinta saboda tunda su ka zauna ta ke ta zuba surutu.
Rayyan ya ce "gashi É—an Kano za ki aura ba"
"Ai ka ji inda matsalar ta ke, ina ga fa sai dai kai ka dinga zuwa Jos, dan ba zan tare a Kano ba. Tukunna Ray, wai a garin nan ka taso cikin wannan zafin?"
Rayyan ya langwaɓe kai dan wannan tambayar kusan karo na uku kenan da za ta yi shi a ɗan zaman su a wajen nan.
" My Farida mu ci abincin nan, zai yi sanyi fa"
A hankali ta fara tauna jollof rice É—in wanda ko loma uku ba ta kai ba ta ajiye cokali. Ta yiwa wani waiter hannu akan ya zo.
Rayyan ya ma ta kallon mi ke faruwa amma ta kauda kan ta ta yi kamar ba ta gani ba.