← Book details Sakatariya Ta Psrt 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 91

Sashe 13

Sakatariya Ta Psrt 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Najeeb yarinyar nan 'yar iska ce, ƙila ma 'yar ƙwaya ce kaga ɗazu wai za ta yi kokawa da ni idan na ce zan shiga office ɗinka"

"So?"

"Najeeb ka koreta, ina wancan Joseph É—in nan da ya ke aiki da kai kafin na yi tafiya"

"Look Khalidah, i fire who i want to. For now that girl stays"

"Najeeb i demand you to sack that girl"

Da ƙarfi ya buga desk ɗin gaban shi.

"Look Khalidah, dan mahaifinki yanada 8% share a kamfanin nan doesnt mean you can make rules here. I owned 75%, i make the rules here. Understand that or ask your father, he'll explain to you. Now get the hell out of my office"

Khalidah ta fice fuuu cikin fishi.

.............

Cikin sati uku da Farida ta fara aiki a Najeeb constructions ba wanda bai santa ba. Wanda su ke tunanin ba za ta jima ba sai gashi har sati uku, shi kan sa Anas yai mamakin yadda Najeeb ya haƙura da Farida. A zuciyarsa kuma yana ganin kamar akwai lauje cikin naɗi.

Babban matsalar Farida a office ita ce Khalidah, a second floor ta ke amma kusan koyaushe tana third floor. Magulmatan kamfani su ka sanar da Farida cewa Khalidah son Najeeb ta ke, lokacin da ta zo ta yi service ɗin ta a Kamfanin ta haɗu da Najeeb tun daga lokacin kuma ta ƙi tafiya, da ke dama mahaifinta na da share a kamfanin sai ta samu ɗaurin gindi. Shekararta uku a Najeeb constructions amma ba alamar nasara sai dai ta ƙi haƙura...

Ta gaji da cin abincin canteen kullum sai kashe kuɗi ga abincin a zuba ma ka kamar kana roƙo duk da ma mafi yawancin lokuta Engr Mathew ko Arch Hamza wani cikin abokan Yakubu ke siya ma ta. Ba ma wannan ba abincin ma bai ma ta yadda ta ke so ba.

Ta zuba faten doya da ya ji ganyen alayyaho da kifi a plate. Gaba ɗaya ƙanshi ya baɗe office ɗin, ta na ci tana korawa da zoɓonta mai sanyi a haka Najeeb ya shigo. Bai ma ta magana ba ya shige office ɗin sa, yana shiga ta ji kira. Tsaki ta yi ta ce " yana gani fa abinci na ke ci" haka ta ajiye ta shiga office ɗin sa.

"Miss Salihu. The next time you eat in the office, 10% zan cire a albashin ki. Is that clear?"

"Ok Sir " ta faɗi ta fita tana ƙunƙuni...

.....................

Farida ta zaunar da Baaba Sabuwa ta yi ma ta bayanin abinda ke faruwa tsakanin AbdulWahab da Maijiddah. Da kuma ƙudurin AbdulWahab ɗin na son turo iyayen sa.
Baaba Sabuwa ta ce idan dai da gaske ne za ta sanar da Baffa Musa sai ya basu lokaci.
Farida ta ce " yanzu Baaba Sabuwa ba ki yarda ba kenan?"

"Farida na fi kowa damuwa da rashin auren Maijiddah, sai dai maganar AbdulWahab É—in ne ta zo kamar almara"

"Addu'arta ne ya ƙarbu. Kin san tunda na zo gidan nan kullum dare Maijiddah sai ta fi awa ɗaya tana sallah tana roƙon Allah ya bata miji. Ko ba ta sallah sai ta tashi ta roƙeshi. To Ubangiji mai jin ƙan bayinsa sai ya kawo ma ta wanda ba ta taɓa tsammani ba. Baaba Sabuwa ki godewa Allah kawai ki cigaba da yi ma ta addu'a"

Cikin satin Alhaji Bello Hassan Kachako da wa su wakilan AbdulWahab su ka zo. Bakin Baffa Musa kasa rufuwa yai, shi ba dan ya gani zahiri ba ko lokacin da Baaba Sabuwa ta gaya ma sa bai gama yarda ba. Su zuwan da su ka yi idan an basu Maijiddah su na so bikin kar ya É—au lokaci.

Baffa Musa kam zani ne ta tadda muje. Dan haka ya amince da sauri.
Sati na zagayowa aka kawo sadakin Maijiddah, dubu ɗari da hamsin. Wata uku aka sa biki su ka nemi a dawo da shi wata biyu Baffa Musa ya amince. Duk da kuwa bashida kuɗi a ƙasa dan ya gama kashe kuɗi wajen bikin su Salima. Sai dai ba zai bari damar da ya ke nema tun da jimawa ya kuɓuce ma sa ba. Allah na gani ya so a haɗa bikin Maijiddah da Farida sai dai hakan bai yiwu ba. 'Yan uwan Rayyan sun ce Rayyan yana so ya haɗa ginin sa kafin ayi biki...

Wannan babban al'amari ya sa kishiyoyin Baaba Sabuwa kowa yai tsit dan abin ya ba su mamaki, duk cikin yaran da aka aurar ba mai sa'an Maijiddah. A gaba É—aya yaran ma Yayar Maijiddah wadda ita Maijiddan ta biyo wato Bilkisu ita kaÉ—ai ta auri wanda yai boko sosai kuma ya ke da hali yana aiki a kamfanin insurance, sai gara-gara mijin Kulthum wanda shima ma'aikacin Kamfanin Airtel ne.

Abu kamar mafarki fa yadda su ke tsokanarta da Matar Custom sai ga shi har sadakinta an bayar saura a É—aura aure kawai.

......................

Tana kwance wayarta ya fara ringing tana É—agawa ta ga Sir Najeeb. Mi zai sa ya kira a wannan lokaci? Ta dai É—auki kiran.

"Miss Salihu, i asked you to send me a copy of the proposal before you leave. What happen?"

"Ya Allah! Na manta zan turo ma ka yanzu"...

Yana zaune yana sipping tea ɗin sa ta turo ma sa saƙon. Sai da ya duba ya ga aikin bai yi kyau ba akwai gyararraki. Nan ya sake kiran ta.
Tana amsa waya ya fara faɗa "Miss Salihu what is this? Mi ki ka turomin? Haka na ce ki yi?" Jin ƙorafin yai yawa ya sa ta ce

"Domin kai ƙorafi danna ɗaya, domin neman ƙarin bayani gameda aikin da aka maka danna biyu, domin magana da Aisha Farida kai tsaye danna uku...."

Ba ta gama ba ya kashe wayar.
Farida ta yi tsaki, " shi agidan ma ba za ka huta ba aiki, ya san da ya na yi wannan É—in. Wallahi ba za ka kasheni da aiki ba"

Najeeb ya cillar da wayar yana cize leɓen sa na ƙasa. He's waiting for the perfect time ya aiwatar da ƙudurinsa, just a perfect time. Yarinyar nan sai ta raina kanta...

*💮SAKATARIYA TA💮*
.......(My Secretary).......

*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

*Free page*

0️⃣0️⃣8️⃣

Washegari a office Najeeb bai ma ta maganar shaƙiyancin da ta ma sa ba, iya kaci tana nuna ma sa proposal ɗin ya ce ta je ta gyara.

Tana aiki sai ga Sister Munibat ta shigo.

"Sister Farida ya aiki"

"Alhamdulillah"

"Sir Najeeb yana ciki?"

"Eh ki shiga"

Minti biyar sai ga ta ta fito har za ta wuce ta ce " Sister Farida ɗan bani ruwa mai sanyi ma na, fridge ɗin office ɗina ya ɓaci"

Farida ta miƙa ma ta satchet water mai sanyi.

"Na gode sister" har za ta tafi Farida ta ce " yawwa idan kina son zoɓo ko kunun aya, gobe zan fara zuwa da shi"

Sister Munibat ta É—an yi dariya ta ce " a cafeteria za ki dinga ajiyewa?"

"A'a anan office É—ina, mai so sai ya zo ya siya"

"Toooo, ke da Sir Najeeb kunfi kusa, amma bana tunanin zai amince da haka"

"Sister Munibat ke dai ki sanar da 'yan wajen kun nan kawai"

Sister Munibat tace "Allah ya kawo kasuwa" Farida ta amsa da Amin...

Washe gari Farida ta haɗa zoɓo gora shabiyar da kunun aya gora goma. Tun kan ta shigo ta ɗan bibbiya wajen mutanenta ta sanar da su, wasu a lokacin su ka ƙarɓa dan wa ya ke da garajen zuwa har Office ɗin Sir Najeeb siyan zoɓo...

Tana aiki a computer Najeeb da Anas su ka fito.

" 'yar uwa sannu da aiki ko"

"Na gode Yayana"

Har zai shige ta ce " Ya Anas ga zoɓo fa, harda kunun aya"

" ƙanwata kenan, kina sha'aninki"

"Yaya ai mai neman kuɗi kam kowani ƙofar samu ya gani shiga ya ke"

"Well Hakane, Allah ya kawo kasuwa"

"Na kawo ma ka zoɓo ko kunun?"

"Ki bari anjima yanzu zamu fita wani waje nida mutumunki ne"

Kafin ya gama surutun sa Najeeb kam ya yi gaba...

.....................

Tana tsugunne gaban fridge tana duba sauran zoɓonta wanda na Anas ne da na Sir Najeeb da ta ajiye mu su, yanzu Yakubu ya zo ya ƙarɓi na sa.

"Miss Salihu"

A firgice ta juyo dan ba ƙaramin tsorata ta yi ba.
"Ya Allahu! Sir Najeeb ai sai ka sa hawan jinin mutum ya tashi. You scared the hell out of me"

"To my office, Now"

Yana shigewa ta fara mimicking na sa " Miss Salihu, to my office now nnnnnnaa. Mtsww"

Ta ɗau zoɓo ɗaya wanda yai sanyi sosai ta shiga da shi.
Tana zuwa ta ajiye ma sa akan table ta ce "Sir na san kafi son shan tea ko coffee amma wannan zoɓon one in town ne. Albarkacin haƙƙin maƙotaka za ka dinga samun kyautar goran zoɓo ɗaya"

Tunda ta fara magana ya zuba ma ta ido har sai da ta kai aya. Duk yadda ya ke jin tsanar yarinyar nan wannan quality na ta na rashin tsoro yana impressing na shi. Idan ka cire Anas duk girman Kamfanin nan babu wanda ke iya tsayawa gaban sa ya faɗi magana son ransa sai ita. People fear him, but this skinny girl idonta ƙyam ya ke duk lokacin da ta ke gabansa babu tsoro ko fargaba a tattare da ita.

"Sir ka taɓa zoɓon ka ji, Allah sai ka yi santi"

"Miss Salihu, duk wani rules and regulations na wannan Kamfani yana da muhimmanci. But na ga alama ba ki É—auke su da daraja ba. You dont wear cooperate clothes, you eat in the office you... you... you and only you Miss Salihu"

"Haba Sir, tun ranan da kace na dena cin abinci a Office fa na dena"

"Oh really, and that yellow thing you ate in the morning yersterday?"

"Kai Sir ya akayi ka gani? Ban karya ba na fito shine na karya a office"

"I see. And this" ya nuna goran zoɓo da ta ajiye"

"Alakoro na kawo ma ka fa. Tunda dai Allah ya haɗamu maƙotaka"
Chapter 13 · 0% Book details