← Book details Sakatariya Ta Psrt 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 91

Sashe 43

Sakatariya Ta Psrt 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Najdah ta É—aga ido ta kalleta sai kuma ta sauke ido. Shi kam Najeeb bai ce komai ba ya san fitina ta ke nema and he's not ready for that.

Ta ajiye tray ta shiga banɗaki ta watsa ruwa, lokacin da ta fito Najdah ta fita. Ba ta san mi ya sameshi ba amma ta ga ko kayan jikin sa bai cire ba ya miƙe akan gado yana kallon sama.

"Sir Najeeb ba ka da lafiya ne?" Shiru

"Sir Najeeb ka tashi mu ci abinci"

Ta gama duk surutun da za ta yi amma bai ce komai ba sai daga baya ya tashi ya shige banÉ—aki...

.....................

Sati ɗaya kenan da fara zuwa aikin ta, ba za ta ce komai na tafiya dai-dai ba ba za kuma ta ce akwai matsala ba. Yawanci ma Najeeb ba ya zama a office ya kan fita supervising ayyukan da kamfanin sa ke yi kuma ya ke so a ƙarasa kafin hutun ƙarshen shekara.

Safiyar yau da ta shiga kitchen ta samu Mom na decorating wani chocolate cake, sai ƙanshi ya ke yi.
"Mom wa ke birthday?" Ta tambaya.

"Ya kamata a ci taran ki tunda ba ki san birthday É—in waye gobe ba" Mom ta faÉ—a tana murmushi.

"Najdah?"

Mom ta girgiza kai, Farida ta leƙa cake ɗin ta ga shekarun da aka rubuta "wai-wai ashe na babban mutum ne"

Mom ta yi murmushi ta ce " he likes chocolate cake"

Farida ta ce "Ayya, cake É—in ya yi kyau kuma"

"Akwai surprise family dinner da za ayi gobe da yamma. But dont tell him, idan ya sani ba zai zauna a gida ba"

"Allah ya kaimu gobe Mom"

....................

Safiyar asabat bayan ya iddar da sallah bacci ya koma. Haka kawai ta tsinci kan ta da kallon kyakykyawar fiskar sa, ta jima tana kallon sa, she cant believe he's 35yrs. Gaskiya jindaɗi da hutu na ɓoye shekarun mutum...

Da ta É—an tattare É—akin sai ta fita dan ta taimakawa su Adama da aiki.

Lokacin da ta dawo ɗakin kusan azahar ya riga ya fita. Ta buɗe akwatin kayan ta tana duba kayan da za ta sa. Mom ta ce iyalen gidan Uncle Sulaiman za su zo ga su Hajia Fatima, dole ta yi shigar da ba za a raina ta ba. Tana cikin duba wannan ta ajiye ta sake dubawa ta ajiye aka ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin,
Ta je ta buÉ—e ta ga Mom ne.

"Mom ki shigo"
Mom ta miƙa ma ta wani paper bag ta ce "ki sa wannan and please wear the dimond necklace"

Ta amshi bag É—in tana ma ta godiya...
Ba ƙaramin kyau gown ɗin ciki ya ma ta ba tareda takalmi da purse wanda su ka shiga da kayan.

Ƙarfe huɗu ta fito bayan ta shirya cikin doguwar riga pink da Mom ta ba ta. Lokacin gidan an fara hayaniya, ta sauko ƙasa tana gaisawa da su Hajia Fatima...

Ya na gidan sa Dad ya kirashi akan maza-maza ya zo gida. Ya san ƙila surprise party su ka shirya ma sa. But he has no choice ba ya iya yiwa Dad mu su. Haka ya rufe gidan ya shiga mota ya dawo. Tundaga motoci da ya fara cin karo da su ya san hasashen sa ya tabbata.
Da sauri ya haura sama yana avoiding wata ƙaramar cousin ɗin sa 'yar shekara biyar da ke cewa ya ɗauketa.
Zuwa yai ya shirya a gurguje dan text É—in Najdah da ya gani akan ya zo Garden su na jiran sa a wajen.
Komai sauri-sauri yai tun daga wanka zuwa sa kaya. Yana buɗe ƙofa ya gan ta a bakin ƙofa. Daga sama har ƙasa ya kalleta, she look beautiful, ga dimond necklace da ta sa da ya ƙara fito da ita.

"A ka ce na zo na kira ka"

* a surprise page gobe for team Najeeb*

*SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......

*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

0️⃣2️⃣7️⃣

Da farko ya shagala da kallon ta amma tunda ya ƙyalla ido ya ga sarƙan da ke wuyan ta sai ya janye idon sa yana cewa "matsa na wuce"

"Sir Najeeb Happy birthday"

Bai amsa ba kawai wucewa ya yi. Ta bi bayansa tana cewa " Dan ma ka samu na wishing na ka Happy Birthday ɗin" yana takun sa na ƙasaita ta na bin sa a baya, da ke heel ta sa sai ya zama ba ta iya sauri ba sai ta ɗan sa gudu-gudu sauri.

Sai da su ka kusa isowa wajen sai ya tsaya, tana iso shi sai yafara tafiya a hankali ta yanda za su jera tare.

Su na shiga wajen aka sa tafi. Wani cikin cousins É—in sa ya ce " ka ga salon soyayyar manya. Har ta tafiyar su iri É—aya ce"

Najdah ta zo ta kama hannun Najeeb ta ma sa jagora zuwa inda zai zauna. Yana zama itama Farida ta zauna gefen sa.

"Happy Birthday babban yaya" Uncle Sulaiman ya faÉ—a yana kallon Najeeb da ke kujeran su na opposite.

Daddy ya ce " kar ka kumbura ma sa kai, wannan taron domin 'ya ta aka yi ba shi ba"

Najdah ta É—auko cake ta kawo gaban sa. Ta kissing goshin sa ta ce " Happy birthday sweet Bro"

Murmushi yai sannan ya amshi wuƙar yanka cake ɗin ya sa zai yanka.
Aminu babban É—an Uncle Sulaiman ya ce " ka yanka tareda amarya ma na mu san yanzu kam ka bar tuzuranci"

Juyowa yai ya kalli Farida wanda itama shi ta ke kallo.
" he's right, 'yata help him cut the cake" Daddy ya faÉ—a yana kallon yadda Najeeb ya haÉ—a rai.

A hankali Farida ta ɗau hannun ta ta ɗaura akan na Najeeb. Ido ya ƙura ma ta ita ma cikin idon sa ta ke kallo. A haka har wuƙar ya nitse cikin cake ɗin. Sai da aka fara tafi sannan su ka cire ido cikin na junan su.
Da ya yanka ma cewa aka yi Farida ta sa ma sa cake É—in a baki bayan ta sa aka ce shima ya ba ta, relunctantly dai ya sa ma ta.

Ba a jima ba aka fara serving abinci ana yi ana taÉ—i ana dariya. HaÉ—a kujeru aka yi da table sai ya zama kaman a dogon table ake cin abinci. Sun jeru straight akan kujerun.

Anwar É—an Hajia Fatima ya tashi ya ce " aga aga?"

Aka amsa ma sa da aga

"Aga waye yai aure @35yrs?"

Aka nuna Najeeb.

Aminu ya tashi "Aga Aga" aka amsa da aga

"Aga waye yai ƙwacen mata?"

Aka nuna Najeeb, wassu na dariya ƙasa-ƙasa.

Wani kallo ya watsawa Aminun dan ya girmeshi kusan shekara shida amma shi ya yi aure harda yarinyar su É—aya.

Aminu ya zauna yana dariya.

Anas ya tashi ya ce "aga aga?"

Da aka amsa ma sa ya ce "aga waye yai auren soyayya da sakatariyar sa?"

Wassu su ka nuna Najeeb wassu kuma wanda ba son auren Najeeb da Farida su ke ba, su ka fara hararan Farida, irin su Najdah da Afrah wanda tunda ta dawo daga weekend ta tarar da auren Najeeb ta tattara ta koma gidan Uncle Sulaiman.

"Barin nuna wani short video clip na wannan masoya, there first fight and probably there first love"

Idan da yadda Najeeb zai yi ya je ya make Anas a inda ya ke tsaye da ya je. Dan wani mugun kallo ya ke aika ma sa daga inda ya ke zaune.

Anas ya ɗaga Tab ɗin sa sama ya playing video ɗin. Video compilation ne na wajen da Farida ta fara zuwa aiki har ta hana Najeeb shiga office, da wajen da ya koreta ta ƙi tafiya har ta rungumeshi lokacin da ya kira security. Sai wajen da Najeeb ya zo ya zauna akan superglue. Tun a clip na farko aka fara dariya, Daddy har da tari tsabar dariya. Wassu da ke gefe su ka dawo wajen da za su ga video ɗin da kyau.
Lokacin da video ɗin ya ƙare Anas ya ce " Thanks to CCTV footage na kamfani mun samu wannan video na masoya mai cike da tarihi"

Najeeb ya rintse ido ya cize leɓen sa na ƙasa. Wannan embarrassment ɗin da me yai kama. A gaban su Daddy da ƙannen sa, dan duk wajen idan ka cire iyayen to ya girme mu su.

A lokacin aka fara cewa ya tashi ya duba kujeran da ya zauna ko akwai superglue a kai. Wa su kuma su na kwaikwayon maganar Farida su na "Sir Najeeb ya dai?"

Farida kam idon ta na ƙasa saboda ta ji kunya. Duk uban mutanen da ke wajen nan sun ga asirin ta.

Uncle Sulaiman yana dariya ya ce " kai gaskiya Alhaji ka iya matchmaking. Ka haÉ—a Najeeb da dai-dai da shi"

Aminu ya ce " ai yanzu da take gidan sa idan yai mata laifi da ruwan borkono zai yi tsarki"

Anwar cikin dariya ya ce " sai ya zama tsuliyar Big B is on fire kenan"
Gaba É—aya wajen kowa dariya idan ka cire Najeeb da ya cika yai fam.
Farida ma da ta sunkuyar da kai É—an dariyan ta yi...

Ana cin abinci ana sake gulman abinda aka gani. " Hajia Fatima har da cewa immediately Anas ya tura ma ta video za ta forwarding wa Najma da su Uncle Abubakar da ba sa nan...

Daddy ya ce " kar ku sa 'ya ta a gaba. Idan ɓera na sata to daddawa ma na wari"

Yadda hannun Najeeb ke shaking, Farida da ke gefen sa sai da ta tsorata. Ta leƙa ta ga hannun sa ɗaya da ya sa akan cinyar sa ya tamke shi kamar mai shirin kai dundu amma still hannun na rawa, ɗaya hannun da ya riƙe tsokali da shi kuwa yai wa sokalin riƙon makami ne.

Ana cin abinci amma Najeeb ba ya ci. Farida ma tunda aka playing video É—in nan ta ka sa cigaba da cin abincin.

Lokaci guda hayaniyar da ake ta tsaya chak. Wanda su ke opposite da su Najeeb su su ka ga matar da ta doso wajen da ake taron ita da Adama da ke riƙe da tray za ta kawo wani nau'in abincin.
Chapter 43 · 0% Book details