← Book details Sakatariya Ta Psrt 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 91

Sashe 25

Sakatariya Ta Psrt 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Kul. Ba na son jin wani magana, ki je ki nemi abinci ki ci ki samu ki huta"...

Ɗakin su Yakubu ta shiga ta ke cin abincin, ba wai daɗin abincin ta ke ji ba sai dai saboda Ummi ce ta takura sai ta ci. Gaba ɗaya zuciyarta na ma ta ɗaci. Duk yadda ta so ta basar da abin ta ka sa, kawai sai hawaye. Ta ya za ta manta da wannan rana a rayuwarta, ranan da ya kamata ace ya zamo ranan farin ciki amma kuma komai ya zo ya dagule, ya zamo ranan shine rana mafi baƙin ciki a tarihin rayuwarta. Sai da ta yi kuka mai isarta kafin ta share hawaye ta tattara kwanukan ta fita...

...................

Anyi Walima lafiya, sai dai duk yadda Farida ta ci burin ganin anyi komai da ita abinda ya faru daren jiya ya kashe ma ta jiki. Da farko ma shiri ta yi kawai za ta wuce office amma amarya Jiddah ta hanata.
"Dan Allah Anty Farida kar ki tafi, ki taimakeni ki tsaya ayi komai da ke. Ke ce support É—ina Anty"

"Na san kin ji abinda ya faru jiya, ba na son tsayawa anan wata ta gayamin maganan banza mu kwashi 'yan kallo. I dont want to ruin your day"

"Anty dan Allah ki mance da komai, Allah ina buƙatar ki kusa da ni fiye da kowane lokaci"

Da ƙyar Farida ta haƙura ta tsaya. An ci kuma an sha sannan an kira Malami ya yi wa'azi.

Washe gari Asabat ƙarfe shaɗaya aka ɗaura auren *Hauwa Maijiddah Musa Wase da AbdulWahab Bello Hassan Kachako*

Ɗaurin auren da ya samu halarcin manya-manya mutane, ta ɓangaren Alhaji Bello Kachako da shi kan sa AbdulWahab ɗin.
Da dare aka kai amarya gidan ta wanda kwana biyu kawai za ta yi su wuce Lagos...

Gidan Amarya Maijiddah kam bayan kowa ya tafi aka bar amarya da halayenta.
Tun safiyar yau ta ke gudawa saboda tsoro da fargaba.
Akwai mafiya yawancin mutane da idan su na cikin damuwa ko tashin hankali ko tsananin farin ciki ko baƙin ciki za ka ga yanzu-yanzu cikin su zai hautsine su fara ziryan banɗaki.
Maijiddah was nervous tun wayewar garin yau, abu ne da ta jima tana roƙo sai gashi ya tabbata, wai ga ta amarya. Ta sha Flagyl kam har ba adadi duk dan ta samu sauƙin wannan abun amma kaman tunda Maghriba ta do so abin ya fara ƙaruwa. Yanzu haka kafin Farida ta tafi sai da ta tabbatar ta sha magani amma yanzu da ta ke ita kaɗai sai ta ke jin cikin ta na ƙugi yana kuma murɗawa.

Tana cikin wannan yanayi wanda ta kira da ƙarshen kunya aka shigo ɗakin. Buɗe ƙofar ɗakin yai daidai da kukan da cikinta yai "ƙululululu"

A hankali ya tako wajen da ta ke ya ajiye ledar hannun sa akan drawer sannan ya tsugunna gaban ta ya sa hannu ya É—aga gyalenta sama yana mai yin Bismillah.
Jikinta rawa ya ke, sai zufa ta ke haÉ—awa. Na farko saboda tsoro na biyu kuma saboda yanayin da ta ke ciki.

"Alhamdulillah, finally Gimbiya Allah ya nuna ma na wannan rana"

Duk maganan da ya ke yi sama-sama ta ke jin sa. Kamar ta saki ihu ta ke ji saboda kunya da haushin kan ta. Ta ya za ayi daren farkon su ace ta ɓarke da gudawa, wannan abin kunyan har ina.

Hannunta ya kamo yana wasa da yatsunta bayan ya zauna kusa da ita.
"Bari mu yi sallah sai mu ci abinci, na san baki ci wani abin kirki ba yau"

A karo na ba adadi cikinta ya sake yin ƙugi, wannan karan kam AbdulWahab ya ji.

"Sorry princess yunwa ko?"

Idan ta cigaba da shiru za ta cutu haka nan da kunya ace ta gaya ma sa matsalarta sai dai ya za ta yi.

"Ki shiga ki yi alwala ni inada alwalata" ya katse tunanin ta

Ai da sauri ta miƙe ta shige banɗakin. Duk yadda ta so ta daure ta yi alwala amma hakan bai yiwuba dole dai sai da ta je ta zauna a toilet. Ƙarshen kunya sai ga shi ƙaran gudawan na fitowa da ƙarfi wanda tabbas ta san AbdulWahab da ke ɗakin ya ji.
Ta gama amma kunya ya sa ta kasa tashi ta yi flushing, ta jima tana zaune daga baya ta yi ta maza ta tashi ta flushing na shi sannan ta yi alwala. Sai dai ka sa fitowa ta yi daga banÉ—akin dan ba ta san da wanni ido za ta kalli AbdulWahab ba.

Jin shiru kuma ta ƙi fitowa ya ce " gimbiya ko na zo na fitar da ke ne?"

Ta sauke ajiyar zuciya sannan ta fito. Daga bakin ƙofa ta tsaya kanta a ƙasa ta ce a hankali " I'm sorry, cikina ne ya ruɗe Yaya"

Tasowa yai har wajen da ta ke tsaye ya kamo hannunta ya ce " There's nothing to be sorry about my dear, mun riga mun zama É—aya ai"

Sai da ya zaunar da ita sannan ya ce "kinsha magani?" Ta É—aga ma sa kai.

"Barin haÉ—o mi ki tea sai ki fara sha"
Fita yai daga É—akin wanda cikin minti shabiyar da ya É—auka sai da Maijiddah ta sake zagayawa banÉ—aki.

Lokacin da ya dawo ya sameta a ɗan kwance gefen gado. He know she's nervous shiyasa ta ke experiencing wannan abun. Ya tuna akwai wani abokinsa mai irin wannan, ko exam za su yi sai ya ɓarke da gudawa, a ranan da za su fara exam na Waec shekaru da dama da su ka wuce sai da Hussaini ya makara saboda ruɗewa da cikinsa yai.

A yadda ya ganta she's already weak, idan yai yunƙurin yi ma ta wani abu that will label him a cruel man.
Taimaka ta yai ta tashi ta sha tea ya haÉ—a ma ta da kaza.
"Ki kwantar da hankalin ki ba abinda zan miki, ki ci ki samu ƙarfin jikin ki"

Shi da kan shi ya fara ba ta naman a baki har ta ƙoshi. Ya ce ta shiga ta yi wanka ta ce na yi.

"Kinga yanzu jikinki ya tsatstsafo da gumi saboda tea da ki ka sha. Ki je ki watsa ruwa"

Gaba É—aya kunya sai ya sake rufeta. Ta tashi ta shiga ta sake wanka da ta fito ba ta same shi ba ya tattara wajen. Ta yi saurin buÉ—e closet ta nemo kayan bacci riga da wando ta sa, sannan ta É—aura hijab akai.

Da ya dawo a zaune a bakin gado ya sameta.
"Hauwerh cire hijabin nan akwai zafi"

Ba mu su ta cire hijabin ta sunkuyar da kai tana wasa da bakin pyjamas É—in ta.

"Ya cikin na ki?"

"Da sauƙi"

"Ki kwantar da hankalin ki ba abinda zai faru kin ji"

Ta gyaÉ—a kai.

"Now breath in and breath out"

Ba ta gane ba har sai da ya nuna ma ta yadda za ta yi da kan sa sannan ta yi yadda ya ce. Sai da ta yi kusan sau goma kafin ya ce ta kwanta.

Kafin ya shimfiÉ—a sallaya yai sallar nafila tuni bacci ya sace amaryar sa. Da ya idar sai ya gyara ma ta kwanciya sannan ya kwanta bayanta ya musu addu'a ya kashe wutan É—akin...

Washe gari da kunyar sa ta tashi tunowa da tai da abinda ya faru jiya. Sai dai shi kam ko ajikinsa, nuna ma ta yai wannan shine amfanin auren domin sun riga sun zama É—aya. Duk wani matsalarta na shi ne, haka nan duk matsalarsa na ta ne.

Da dare su ka je gidan su sallama, daga nan su ka wuce gidan su Maijiddan. A wannan lokacin Farida ta tambayeta ko gudawar ta tsaya kafin ango ya shigo. Maijiddah ta ce "inaa, Anty ni kam ai na sha kunya" a taƙaice ta gaya ma ta abinda ya faru Faridan ta yi ta ma ta dariya.
Ba su jima ba su ka wuce saboda da sassafe jirgin su zai tashi.

Daren ranan ya gaya ma ta basic abubuwan da ya kamata ta sani gameda airport da jirgi. Sannan ya jaddada ma ta ba abinda zai faru yana tareda ita.
Ko breakfast ba ta iya yi ba saboda kar ta ci wani abu ya dameta. Ƙarfe tara jirginsu ya wuce Lagos. Kuma Alhamdulillah Maijiddah ba ta yi gudawa ba, sai dai ta tsorata kam lokacin da jirgin zai tashi, ba dan AbdulWahab na riƙe da hannunta yana kwantar ma ta da hankali ba ƙila da ta yi kuka. Sai da jirgi ya lula sama sannan ta ɗan samu nitsuwa kaɗan...

Asha amarci lafiya Maijiddah (banda gudawa plz😁)

.........................

Safiyar Monday Farida ta fito aiki duk da kuwa gajiya bai saketa ba, sai dai kamar yadda ta yiwa Maijiddah dariya sai gashi itama tana tsaka da aiki cikinta ya hautsina. Da farko sharewa ta yi tana mita " mutum ya yi ta ciye-ciyen mai kwana biyu ba dole ciki yai ta kuka ba"

Sai dai fa lokaci guda ta kasa yin komai ta tashi ta nufi office É—in Najeeb da gudu dan nan ne kusa da ita sannan ta É—auka baya office É—in dan ya fita É—azu ya je meeting. Abinda Farida ta manta shine ya riga ya dawo tuntuni.
Da gudu ta zo ta wuceshi yana zaune yana aiki, kafin ta ƙarasa ma ta saki tusa a hanya.
Yana shirin buɗe baki yai magana kan shigo ma sa office da ta yi da gudu ya ji ƙaran tusan da ta yi...

Hankali kwance Farida ta zauna ta zazzage kayan cikinta, dama tun ran asabat rabon da ta yi, ga shi ba ƙaramin abinci ta ci ba a bikin nan. Ta jima a ciki kafin ta wanke ta yi flushing, kasancewa banɗakin yai gum sai ta ɗau air freshner ta feffesa ta ƙara buɗe windown banɗakin da kyau saboda iska ya ratsa.

Ta fito tana ɗan daddanna ciki tana faɗin "kai abubuwan da na ci a bikin nan ai sai barka. Kashi rahama ne Allah, ka ji yadda na ji wani saƙayau lokaci guda"

Cak ta tsaya da tafiya lokacin da muryan da ba ta taɓa tunanin ji ba a wannan lokacin ya doki kunnenta

"Miss Salihu"
Chapter 25 · 0% Book details