Sashe 7
Sakatariya Ta Psrt 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Æangaren turaruka ya nufa a Mall É—in saboda favourite perfume na shi ya kusa Æ™arewa. Kamar daga sama ya fara jin muryan ta, kamar ranan da ya fara ji yau ma masifa ta ke yi. Zuciyar sa ce ta raya ma sa ba ita bace amma kunnensa ya Æ™aryata hakan, domin kuwa muryar sak da wadda ya ji ranan a restaurant. Yana so ya maida hankalinsa kan abinda ya ke dubawa amma kuma idanuwan sa na Æ™waÉ—ayin gaskata abinda ya ke ji, shin yarinyar ranan ce? ko kuwa wata ce mai irin muryarta.
Kasa daurewa yai sai daya juya ya maida dubansa ga inda ya ke jiyo muryan. Ita É—ince dai, 'yar mitsilar yarinya mai shegen surutun nan. Ya kai duban sa ga wanda ta ke wa masifan ya ga ba saurayin ranan bane wani ne daban, haka kawai ya ji tsanar yarinyar dama ma su irin halinta kam ina za su iya kama kai.
He couldn't believe it, garin kallonta sai ga shi har turaren da ya É—auka yana shirin faÉ—uwa daga hannunsa. Yai saurin taro turaren tareda sake murmushi saboda wautar da yai, garin gulma. Abin haushin ma ba wai ya san yarinyar bane amma kuma gashi halayyarta ya dameshi. Ya saurin kauda kan sa lokacin da su ka zo za su wuce shi, tana tafiya tana surutu, kafaÉ—arta ya É—an gogi bayansa kaÉ—an, yai saurin juyowa ya bi bayanta da kallo amma she's too busy talking to even notice what happened.
"Lousy girl" ya faÉ—i a fili sannan ya É—au turaren ya bar wajen...
"Ni wallahi da na san É—an abinda za mu saya kenan da ban biyoka ba Yaya FaruÆ™. Duk abinda mu ka É—auka ka ce yai tsada. Dama ai abu mai kyau shi ake siya da tsada"
"Wallahi mijin ki ya shiga uku Farida, ke fa ki ka ce mu zo nan ba ni ba. In ba dan ke ba mi zai sa na zo siyayya a nan"
"Amma Yaya ai ba ka cemin ba ka da kuÉ—i ba ko!"
"Allah ya shiryeki dai"
Har su ka bar Mall ɗin ba ta dena complain ba, dama wasu kaya ne Yaya Faruƙ zai siya na bikin ƙannen sa. Ƙarshe dai daga Mall ɗin kasuwa su ka wuce...
......................
Ana zaune ana duba kayan da su Faridan su ka siyo Maijiddah ta shigo tsakar gidan da sallama, dawowarta kenan daga yiwa Hajiya Yelwa kitso. Kai tsaye É—aki ta nufa bayan ta gaishe su.
"Ke Jiddah zo nan" Farida ta kirata.
Ba mu su ta dawo ta tsugunna gefen Faridan ta ce "gani Anty"
"Kina gani kowa yana duba kaya yana sa albarka ke za ki tsallake ki shige ciki"
"Lah Anty zan cire hijabi ne na wanke hannuna sai na fito"
Zainab ta ce " ba wani, baƙin ciki ta ke ba nata kayan bane"
Farida ta wurga mata wani awarwaro wanda ya doki hancinta maimakon bakinta da Faridan ta yi niyya.
"Zan ci Ubanki agidan nan, sa'arki ce da zaki dinga yaɓa ma ta magana son ran ki. Na ce sa'arki ce!" Ta daka ma ta tsawa.
Anty Hanne wanda ita ce ta biyu a matan Baffa Musa kuma Umman Zainab ta ce " Yo ba gaskiya ta faɗa ba. Anyi auren ƙannenta biyu yanzu za a sake wasu biyun. Ai abin kunya ne ace ko mashinshini ba ta da shi"
"Da kyau, dama Zainab ai daga nono ta sha. To barin gaya mu ku, tafi ƙarfin tayi baƙin ciki da bikin ƙannenta saboda duk cikin su ba wanda yake auren mijinta. Na ta mijin na nan zuwa, za ku ganshi handsome gentleman da shi"
Hajara ta ce " waya ga handsome mijin shortie" gaba ɗaya sai aka sa dariya banda 'yan ɗakin su Maijiddan wanda su ke tausayinta. Maijiddah ta fashe da kuka ta tashi za ta bar wajen Farida ta riƙe hannunta ta ce " ba inda za ki je. Ki tsaya ki kalli kowacce ido cikin ido ki maida mata martani daidai da ita"
"Anty Farida gaskiya su ka faÉ—a, na yi kwantai"
"Ji mim shirme, inba dan ke da su ɗin duk 'yan ƙauye bane dan kina 20yrs ba ki yi aure ba shine kin yi kwantai. Tukunnama ke za ki aurar da kan ki ne? Ko mijin ya zo kin ce bakya so"
Ta kalli Hajara da ke dariya ta ce " ke kuma fantsararriya, za ai aurenki at 16yrs ba abinda ki ke hangowa sai kwanciyar aure saboda abinda ki ka sani kenan. Gaya min me ki ka iya? Wacce sana'ar ki ka iya? Jakar banza kawai, yanzu haka wankar tsarki mai kyau ba ki iyaba, tun tasowar ki ke daƙiƙiya ce, shiyasa ko jarrabawar WAEC ma ki ka ce ba za ki rubuta ba. Har mijin da za ki aura abin alfahari ne, ina shi ma wani tunkuzan ne kamar ki, ba ilimin Arabi bare boko"
"A hakan dai auren za ta yi, ta fi wasu da maneman ma ba ta da su" Anty Hanne ta faÉ—i tana hararan Farida
"Wallahi Jiddah ta fi ƙarfin ta auri miji kaman Haladu, mi za tai da irin su Haladu ai shi kam sai jaka irin Hajara. Mijin Jiddah ɗan gayu kuma mai ilimi ne Insha Allah"
Tuni wajen ya kaure da hayaniya, Baaba Sabuwa dama tuni ta shige ɗaki saboda takaici, ita ɗin kanta ba daɗin ganin Maijiddah ta ke agidan ba. Anyi auren ƙanwarta Murja duk da kuwa tsakaninta da Murjan shekara ɗaya ne to yanzu ga Salima ma za ayi na ta amma ita shiru. Tana jin hayaniyar su amma ko leƙowa ba ta yi ba.
Farida kam duk ta inda aka ɓullo kare Maijiddah ta ke ta hanata tafiya kuma ta hanata kuka. Ƙarshe dai sai gajiya su ka yi su ka barta dan indai wajen ɗasa magana ne to Farida ta kere su...
Da dare da za su kwanta Farida ta sa Maijiddah a gaba da masifa.
"Ke sai ana magana ki fara kuka, ba dole su raina ki ba. Ai su na magana ki na magana, wanda ya gaji ya bari. Tukunna ma ke idan za ki fita sai ki dinga saka dogin hijabai kamar matan Malam, a haka kam ai ko mutum zai tsaida ke a hanya ma zai É—auka ke matar aure ce ya fasa"
" Lah na saba ne ai"
"A wannan zafin, to kul, kisa É—an dai-dai amma banda dogin nan, idan ba haka ba zan sa almakashi na rage mi ki tsayin su"
"Kai Anty"
"I'm serious"
Maijiddah ta sa dariya...
Washe gari da sassafe Farida ta shirya za ta bi Yakubu wajen aiki saboda interview da ya ce za a ma ta yau. Sai da za ta fito daga É—aki taga Maijiddah na shiryawa itama da alama fitan za tai,
" 'Yan mata ina zuwa da sassafe haka"
" Hajiya Yelwa ce ta kirani wai dan Allah na zo na yiwa jikokinta kitso yau za su tafi"
"Ba za dai ki gyara ba ko"
"Mi na yi Anty?"
"Jiya mi na gaya mi ki?"
"Kayya Anty"
Farida ta je ta binciko ma ta wani hijabi cikin kayanta wanda bai da tsayi ta miƙa ma ta. "Sa ka wannan"
"Anty da kin barshi, skirt É—in da na sa fa ya É—an kama ni"
"Saka!"
Ba mu su ta amsa hijabin ta saka, da ke ita É—in guntuwa ce ya kusa kai ma ta gwiwa.
Haka su ka jero su ka fito, É—akin Baaba Sabuwa kawai su ka shiga su ka gaisheta sannan su ka fita...
..............................
A office ɗin su Yakubu ta zauna wanda shi da colleage ɗin sa Engr Mathew su ke sharing. Tun a office ɗin ta dinga sa Mathew dariya da surutunta. Ƙarfe tara da rabi Yakubu ya dawo office ɗin ya ce Farida ta biyoshi. Kai tsaye office ɗin Anas su ka je. Da sallama su ka shiga office ɗin lokacin Anas na duba wasu takardu. Ɗagowar da zai yi ya ga yarinyar ranan, ta ke murmushi ya suɓuce ma sa cikin ransa yana ayyana abubuwa dayawa.
"Bismillah zauna" ya faÉ—i yana nuna ma ta kujera.
Yakubu ya ce " sir ni zan wuce office"
" Ok Yaks"
Sai da Yakubu ya fita sannan ya kalli Farida ya ce " Aisha Farida Salihu right?"
"No" ta faÉ—i tana kallon cikin idon sa.
"No kuma, ba sunan ki kenan ba" ya faÉ—i da mamaki
"To yallaɓai ka ga takarduna ka ga sunan da ke jiki kuma sai ka sake tambaya"
"Hmmm. Well na ga takardun ki kuma ba laifi i'm impressed. Sai dai aikin da za ki yi babban aiki ne kuma aiki ne da sai kin yi haƙuri sosai"
"Rayuwar duniya kanta sai da hakuri, balle aiki a ƙarƙashin wani" ta amsa tana kallon laptop ɗin da ke gaban Anas
"Da alama dai Yaks bai yi ƙarya ba gameda yarinyar nan, tabbas za a sha kallo tsakaninta da Najeeb" abinda Anas ya faɗi a zuciyarsa kenan. A fili kuma ya ce
"Malama Aisha, kasancewa muna buƙatan Secretary da sauri so gobe za ki fara aiki. Kafin nan zamuje ki ga office ɗin ki sannan zan nuna mi ki yadda za ki dinga gudanar da ayyukan ki"
"Abin da sauri-sauri haka?" Ta tambaya
"Ko ba za ki iya ba ne?"
"Kana ganin Ogan ka zai iya korana ne? Dan ance mini abu ƙiris mutum zai yi ya koreshi"
" I see, ashe kinada labarin wanda za ki yi aiki a ƙarƙashinsa. Kin san ba ya ɗaukan raini, Malama Aisha"
Farida ta ɗan yi murmushi ta ce "ni kuma banda mutunci ba, ga rashin haƙuri kamar zawo"
Anas yai murmushi sannan ya miƙe ya ce " welcome to Najeeb constructions miss Aisha Farida"
"Thank you" ta faɗi tareda miƙewa itama...
Ta yi mamakin ganin girman wajen da aka nuna ma ta a matsayin office ɗinta, cikin ranta tana ayyana irin shagalin da za ta yi a wannan waje, ga ƙaramar fridge ga AC, kai aiki cikin jin daɗi haka.
"Ehmm, Ogan ki bai ƙaraso ba tukunna so zuwa gobe idan kin fito za ki ganshi. Ba sai an nuna mi ki shi ba kina ganin sa za ki ganeshi" maganar Anas ya dawo da ita daga tunanin da takeyi.
"Ba matsala Sir Anas"