← Book details Sakatariya Ta Psrt 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 50 OF 91

Sashe 50

Sakatariya Ta Psrt 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ganin reply É—in ta ya sa shi murmushi. Ya É—an jima kafin ya tura ma ta "Mrs Jibo sleep"

Good night kawai ta sake turowa daga nan ba ta kuma turo da wani saƙon ba. Shi ma ya ajiye wayar sa gefe ya kwanta.

.......................

Safiyar Sunday ya aika ma ta da Iliya driver akan ya je ya É—auko ta. Ita kam tana chan tana kan haÉ—a kayan tsaraba da za ta zo da shi. Sai da Iliya ya kusa isa cikin Jos sannan ya kira ta ya ce ya kusa isowa.
Wani matsayi ta ke kuma hangowa kan ta idan ta koma Kano. Ya sa an kawota da mota ya kuma turo ma ta driver ya dawo da ita. Wannan karramawar sai Mrs Jibo ai...

Lokacin da su ka isa gida ana kiran sallar maghrib. Iliya ya je ya kira Friday su ka shiga da buhun dankalin turawa da ta zo da shi da kuma wata ƙatuwar jakan ghana-must-go.

ÆŠakin Mom ta je dan ta gaidata ta samu ba ta nan, ta wuce É—aki ta shirya ta yi sallar la'asar da magariba...

Ƙarfe tara ta sauko ƙasa dan ta nemi abinda za ta ci, ba komai a dining ɗin hakan ya sa ta shiga kitchen shi ma wayam. Yunwa ta ke ji dan haka ta tsaya ta girka noodles da soyayyan ƙwai, ta fito ɗauke da plate ɗin shi kuma Najeeb ya shigo.

"Sir Najeeb" ta kira sunan sa. Juyowa yai ya ganta tsaye riƙe da plate da cup

Sai da ya gama kallon ta daga sama har ƙasa sannan ya juya ya tafi. Ta bi bayan sa da baki buɗe.

A dining ta zauna ta ci abincin ta dan idan ta haura sama za ta ji ƙiwuyar saukowa, sai da ta gama ci sannan ta wuce ɗaki.

"Sir Najeeb irin ba ka ji daÉ—in ganina É—in nan ba, ko sannu da zuwa babu"
Bai kulata ba hakan ya sa ta gane akwai abinda ke damun sa dan bayan bai kulatan ba fiskar sa ya nuna yana cikin damuwa.

"Sir Najeeb ba ka da lafiya ne?"

"Please stop talking" abinda ya iya faÉ—a kenan ya gyara kwanciya a kan gado.
Tabbas akwai abinda ke damun shi dan Najeeb ba ya bacci da wuri, sannan duk rintsi sai ya yi wanka ya sa kayan bacci kafin ya kwanta.

Kaman yadda ya buƙata ɗin, shirun ta yi tana tunanin ko me ke damun shi.
Har ta kwanta Najeeb bai tashi ba, ba kuma baccin ya ke ba dan idon sa a buɗe lokacin da ta leƙa shi...

Washegari da ta shirya ta fito ne ta haÉ—u da Tasallah a kitchen wanda ke shaida ma ta Mom ba lafiya an ba t gado.
"Ayya ashe shiya sa jiya da na dawo na ji gidan shiru. Ya jikin ta?"
Tasallah ta ce da sauƙi. Maimakon office da ta yi niyyar zuwa sai ta wuce asibitin lokacin Iliya ya kawo Adama za ta ɗauki wassu kayan buƙatu sai su ka tafi tare.

Ta yi mamakin yadda Mom ta faɗa haka. A wajen Najdah ke cewa " tunda yanzu ke ki ke juya Big B sai ki sa ya zo ya ga Mom. Kin wani yanko ƙafa kin zo irin son a sani ɗin nan"

Farida ta kalli Najdan sannan ta kalli Mom da ke kwance tana bacci.

"Na san da cewa ba kya son ganina tareda yayan ki, amma ki sani shi ya kawo ni gidan ku ba ni na kawo kai na ba. Tun farko-farkon zuwa na ki ke ta ƙananun magana akai na, ban tanka mi ki ba. Kar ki sa na kalle ki da idon Aisha Farida dan ba za ki ji daɗi ba. Ki bini a hankali mu tafi a yadda mu ke yanzu"

Najdah ta yi tsaki, ta É—au waya ta fara latsawa.

Farida ta fice daga É—akin gudun kar ta fara masifa ta tada Mom daga bacci. Amma tabbas za ta ware lokacin Najdah nan ba da daÉ—ewa ba...

Kai tsaye Najeeb constructions ta wuce sai dai da ta je office É—inta kama baki ta yi saboda chanji da ta gani, office É—in ta da na Najeeb ya koma kusan guda É—aya, maimakon gini da ke tsakanin su yanzu wani tinted glass ne ya raba su wanda daga office É—in sa yana iya hango komai a na ta office É—in amma ita kuma ba za ta ga na sa ba.

" ba dai wannan Sir Najeeb ya ke nufi da matsayi ba"

Ba ta gama zama ba Najeeb ya shigo ran sa a ɓace. Yanzu ya fito daga board meeting.

"Sir Najeeb ashe Mom ba lafiya shi ne ba ka gaya mun ba"

"Get back to work Mrs Jibo"
Gwiwanta yai sanyi ba dai duk wani zumuɗi da zaƙalewan da ta ke yi a kan sa duk na banza ba ne.

"Noory" muryan Sabreen ya dawo da ita daga tunanin da ta ke.

Murmushi Sabreen ta yi ganin Farida a wajen. Da alama itama daga wajen da Najeeb É—in ya fito ta fito.

Ganin Sabreen ya sa ta ma tuna da zancen ta, ita harga Allah ta manta da wata Sabreen.

"Noory, you are just taking it personal, i'm here to work"

"Kar ki sake kirana da wannan sunan. Here and anywhere else i am Najeeb to you"

Ta É—an ji haushi saboda a gaban Farida ya faÉ—a. Amma ta dake ta ce "fine"

Farida ta fice daga office É—in ta koma na ta duk da ta san daga inda ta ke su na kallon ta.

Wani yanayi ta tsinci kan ta ciki. Sabreen ta fara aiki anan, mi hakan ya ke nufi? Kenan watarana Sir Najeeb zai aiketa wajen Sabreen ko Sabreen ɗin ta ba ta saƙo dan ta kaiwa Sir Naheeb. Ba zai yiwu ba, dole ta ajiye aikin nan. Ba za ta yi aiki tana ƙarƙashin Sabreen ba, wannan cin fuska ne.

"Congratulations 'yar uwa. Finally gaskiya ta fito" muryan Anas ya doki kunnen ta.

"Wani gaskiyar?" Ta tambaya tana ƙoƙarin ɓoye damuwar ta.

Zama yai zai ma ta bayani sai ga Sabreen ta fito.

Tana ganin su ta yi wani murmushi sannan ta juya tana catwalking ta fita.

Anas ya juyo ya kalli Farida wanda itama bin bayan Sabreen É—in ta yi da kallo.
Ya ce "asirin wanda su ka kitsa mi ki sharri ya tonu. Gaskiyar zance ta fito"

"Haba! Yaya na wani É—an Alatsinen ne ya ke son ganin baya na"

"Wallahi Khalidah ce"

"Ban yi mamaki ba dan za ta rina"

Nan ga shiga labarta ma ta yadda aka yi gaskiya ta fito.
Da kotu za su shiga amma an settling case ɗin tsakanin Kamfani da su saboda Alhaji Matawalle ba ya so a je kotu domin ya na siyasa kuma ya na son fitowa takaran senator. Na biyu kuma Alhaji Tukur mahaifin Khalidah ba ya son wargaza alaƙar sa da Najeeb, 8% shares na shi a kamfanin shi ya san kuɗin da ya ke samu, shi ya sa shima ya zaɓi teburin sulhu.

Alhaji Matawalle zai biya kamfani taran miliyan ishirin ita kuma Khalidah za ta biya Farida miliyan biyu.

" 'yar uwa mun yi kuÉ—i fa. Dan Allah ayi kason da mu"

Farida murmushi kawai ta yi dan ba wannan ba ne damuwar ta.

Ranan duk wani É—okin dawowa Kano da ta yi ta ji Kanon ya fita ma ta a kai. Da yamma bayan ta dawo Baba Sabuwa ke kiran ta akan 'yan uwan Najeeb sun kawo lefen ta yau da safe. Su kan su ba su san da zuwan ba ko karramawar kirki ba a mu su ba.
Farida kin ga kaya ki godewa Allah gaskiya domin an zuba dukiya a lefen ki. Yanzu ya za ayi? Za a kawo mi ki shi chan gidan kun ne ko ya?

"Baaba Sabuwa duk yadda ku ka yi" ta faÉ—i hakan ne saboda ko kaÉ—an maganar lefen bai sa ta ji raÉ—aÉ—in da ta ke ji ya ragu a zuciyar ta ba...

........................

Yana shigowa Daddy ya kirashi tambayar sa yai ko ya je ya duba Mom ya ce bai je ba.

"Yanzu Najeeb ka kyautawa kan ka, da girman ka da ilimin ka amma ba za ka kyautatawa mahaifiyar ka ba. Duk abinda ta yi ma ka bai kai ace tana kwance a asibiti yau kwana uku ka kasa zuwa ka dubata ba. Najeeb tsinuwa ka ke nemawa kan ka?"

Maganganun Daddy su na shiga su na fita ta ɗaya kunnen ne, saboda ba jin su ya ke ba hankalin sa ya tafi wani wajen. Jini kawai ya ke gani malale a ƙasa ga kuma gawar Aisha...

Daddy ya gama ma sa wa'azi sai Najeeb ya tashi ya fita ba tareda ya ce komai ba...

Tuƙi ya ke amma zuciyar sa na tuno ma sa abun da ya faru shekaru da su ka wuce. Duk da yanzu ya girma kuma ya san ƙaddarar Aisha ne ta zo da haka amma wannan trauma ɗin da ya dasu a ransa tun yana yaro ya ƙi sake shi...

***
Chapter 50 · 0% Book details