Sashe 51
Sakatariya Ta Psrt 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Cikin Aisha na wata takwas abin ya faru. Immediately Adam ya saki Nabilah ta tattare yaranta ta bar ma sa gida. Sai dai hakan bai sa Najeeb ya dena zuwa wajen Aisha ba. Idan ya taso daga makaranta chan zai wuce sai dare ya dawo. Mom ta ma sa faÉ—an amma baya ji.
Ana haka sai ɗaya daga cikin ma su kula da Aisha ta yi tafiya saboda Maman ta da ta mutu. Ganin haka ya sa Najeeb ya dawo wajen Aisha da zama duk da kuwa akwai Mrs Beverly tareda ita. A kwana na uku da ya koma wajen Aisha, Mom ta zo da ƙarfin tsiya ta tafi da shi gida ta hana shi zuwa wajen Aisha. Abu da renon turawa sai ya fara maida ma ta magana akan ba ta isa ta hana shi fita ba, Ya fita da gudu.
Mom ta nemi restraining order daga kotu akan ba ta yadda ɗan ta ya je gidan Aisha ba saboda tana tunanin Aisha za ta ma sa lahani. Da ke Najeeb under 18 ne sai ya zama dole yana ƙarƙashin kulawar iyayen shi. Ranan da letter ɗin ta fito haka Mom da jami'an kotu su ka je su ka ɗauko Najeeb tareda faɗawa security ɗin gidan ko da wasa kar ya bari Najeeb ya shiga gidan.
Daren ranan yai wani mummunan mafarki akan Aisha ta mutu hakan ya sa da safe ya kira Daddy da ke Belgium a kan ya sa baki yana son zuwa wajen Aisha.
Mom ta ce indai ya na America yara za su zo wajen sa amma Yaran ta ba za su je wajen Aisha ba. Da Najeeb ya fita school bai je ba sai da ya fara biyawa wajen Aisha ya ga tana lafiya kafin ya tafi.
Yammacin ranan da ya dawo ya samu Mom tana masifa akan Aisha ta dameta da kira. Najeeb bai kulata ba sai da Najma ta dawo ta ke ce ma sa yau ta ji tausayin Aisha domin ta kira kusan so biyar amma saboda ba ta magana ba ta iya ba da saƙon da ta ke son faɗa ba. Ƙila tana son ganin ka ne.
Hankalin Najeeb ya tashi, tunda su ka raba gida Aisha ba ta taɓa kira ba. Ta kira sau biyar kam yana nufin tana cikin matsala ne. Haka ya fita da gudu ya je ya ɗau keken sa ya tafi gidan Aisha duk da kuwa Mom tana ƙwala ma sa kira akan ya dawo.
Da ya je gidan tun daga falo ya fara kiran Aisha amma ba ta fito ba ya duba Mrs Beverly a kitchen ba ta nan sai ya haura sama da gudu. Kai tsaye ɗakin Aisha ya shiga. Amma mi sai ya ji kukan jinjira, yana duba gefen sa ya ga Aisha kwance ga jini duk ya ɓata wajen. Irin jinin da ya gani sai da wani jiri ya kusa kada shi ya dafe gini na wasu mintuna kafin ya ƙarasa wajen ta yana jijjigata amma ba ta tashi ba. Cikin kuka ya je ƙasa da gudu ya kira emergency line na police...
Yana tsaye aka zo aka É—auke gawan Aisha, duk abinda idon sa ke sa ma sa shine Mom ce ta kashe Aisha. Ranan shima asibiti ya kwana dan yana tsaye a wajen bayan ansa gawar Aisha a mota ya faÉ—i ya suma...
Ko da bayan autopsy na Aisha ya fito kan ba kashe ta aka yi ba, haihuwa ta yi ita kaÉ—ai jini ya tsinke ma ta kuma rashin Mutum a kusa da ita ya sa ba a kawota asibiti da wuri ba har ta mutu.
Najeeb bai daina ganin Mom a matsayin wanda ta kashe Aisha ba. He was very traumatized a lokacin da har ta kasance baya iya bacci sai da magani. Ya jima yana visiting therapist kafin daga baya aka ce ya dawo normal amma still a hakan bai koma dai-dai da Mom ba.
Rasuwan Aisha ya sa Mom ta saduda da rayuwa, ta nemi Adam ya maidata dan ta kula da Najdah...
"She wanted her dead all along, she's evil" abin da ya faɗa kenan ya buga steering ɗin motar. Idon sa na buɗe amma duhu ya ke gani, yana ƙoƙarin saita motar ta shi wata babbar mota ta zo ta buge motar sa, motar Najeeb ta yi sama sannan ta dawo ta faɗi ƙasa...
*SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......
*Azizat......âœ*
*Wattpad @000Azee*
*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*
0ï¸âƒ£3ï¸âƒ£2ï¸âƒ£
*wannan labarin na kuɗi ne, dan Allah kar a fita da shi, ga mai so zai iya tuntuɓar 08137311900*
*wannan page É—in na ki ne ke kaÉ—ai Anty nah Surayyah. Wishing you health, wealth, peace, grace, mercy and joy amin. Allah ya Æ™arawa rayuwarki ta Oga da ta yaran ki albarka amin. Happy birthdayðŸ¾ðŸ¥‚🎂*
Tana zaune sai cika ta ke tana batsewa, abu É—aya ta sani shi ne ta ajiye aiki da Najeeb sannan kuma dole ta rama abinda Sabreen ta ma ta. Ba za ta bar karuwan nan ta sha banza ba.
Tun tana duba agogo tana jiran Najeeb har bacci ya É—auketa akan Sofa...
Daddy kam bayan fitan Najeeb kiran matar sa yai su ka yi hira, da ke jikin tan da sauƙi, dan likitan ya ce za'a iya sallamarta gobe.
Ƙarfe shaɗaya na dare wayar sa ta fara ringing, daga kan gado ya sa hannu ya lalubota ya ɗara a kunne dan ko gama gane numban da ya kira bai yi ba.
Abin da aka ce ma sa ne ya sa ya tashi zaune yana maimaita Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raju'oun jikin sa na ɓari.
ÆŠaukan key yai ya fita daga É—akin da sauri duk da kuwa pyjamas ne a jikin sa...
Tunda aka shigo da shi ake ƙoƙarin tsaida jini, yadda jini ke zuba a jikin sa da ma gefen kansa ka ce duka jikin sa zai tsiyaya zuwa ɗan ƙanƙanin lokaci.
Wani na ganin Najeeb Adam Jibo a jikin ID card É—insa ya gane ko É—an waye, shi ya sa aka kira numban Daddy...
Yadda Daddy ke jinsa gani ya ke ba zai iya jira har Iliya ya taso daga BQ ya zo ya kai shi ba duk da an hana shi tuƙi da dare saboda idon sa.
Yana fitowa yana ƙwala sunan Malam Aminu maigadi akan ya buɗe gate, yadda ya ke kiran, shi kan sa Maigadi sai da ya tsorata... Ikon Allah ne kawai ya kai shi asibitin lafiya amma ƙila da shi ma hatsarin zai yi.
Yana zuwa aka ce har lokacin likitoci na kan sa. Jikin sa rawa ya ke bai iya zama ba yana safa da marwa zuciyar sa cike da addu'o'i. Tsabar rikicewa ko fitowa da wayar sa bai yi ba daga mota...
Anas ƙarfe huɗu da rabi na asuba aka kira shi, ya fito daga banɗaki kenan ya yi alwala ya ji kira kafin ya ɗauka ta katse. Ganin Daddy sai hankalin sa ya tashi, lokaci guda zuciyar sa ta raya ma sa ƙila Mom ce ta rasu. Duk da kuwa jiya da ya je dubata ya ga jikin ta da sauƙi sosai, to amma mutuwa ko da ciwo ko ba ciwo sai an tafi. Yana ƙoƙarin sake kiran Daddy kiranshi ya kuma shigowa ya ɗauka da sauri.
Maimakon Daddy ya ce ma sa wani abu ne ya samu Mom sai yai ma sa maganar Najeeb, Najeeb da su ka rabu lafiya ƙalau jiya.
"Daddy ya rasu ko?" Ya faÉ—a hawayen da su ka cika idon sa su na gangarowa.
Daga ɓangaren Daddy ya ce " a'a, yanzu likitocin su ka fito amma bai farfaɗo ba har yanzu"
Yai hamdala tareda cewa gashi nan zuwa...
Zuwa ƙarfe bakwai na safe asibitin ya cika da 'yan uwa. A wannan lokacin ne Uncle Sulaiman ya sa aka maida Daddy gida saboda ya chanja kaya.
.....................
Farida ba ta farka ba sai ƙarfe biyar lokacin da alarm ɗin ta yai ta ruri ba kakkautawa. Da ƙyar ta sa hannu ta jawo wayar ta katse alarm ɗin. Mafarki mai daɗi ta yi, itada Najeeb su na zaune a wani lambu, kanta na kan cinyar sa yana wasa da gashin ta.
" I love you Aysherh" ya faÉ—a idon sa cikin na ta.
"I love you too Sir Najeeb"
Hannun sa ya sa ya É—an matse bakin ta ya ce "ba na hana Sir Najeeb É—in nan ba"
"Sorry my champ"
Ta É—an É—ago kanta ta kissing goshin sa sannan kumatun sa sannan hanci. Ganin ta tsaya ya sa yatsa ya nuna lips É—in sa.
Ta girgiza kan ta. Ya ɗan yi ƙanƙan da ido alamar tausayi. Murmushi ta yi tareda haɗe bakin su...
Ta tashi jiki a mace ta shige banÉ—aki, wannan mafarki da ta yi ya sa ta sassauta jin haushin sa da ta ke ji.
Lokacin da ta zo gaban madubi, kallon kanta ta yi ta fara gwada maganan da za ta yiwa Najeeb ta yadda zai tabbatar ran ta ya ɓaci ya kuma ɗauki maganarta serious.
A hankali tana fari da ido ta ce "Sir Najeeb, gaskiya idan Sabreen za ta yi aiki a kamfanin ka to ni zan ajiye aiki na"
Ta yi tsaki ta ce ba haka bane barin sake. Wannan karan ta haÉ—a rai ta ce "Sir Najeeb zan ajiye aiki na"
Sai ta kwaikwayi muryan sa ta ce " good for you"
"Good for you kawai za ka ce min? Ka na tunanin idan na ajiye aikin akwai wanda zai iya yi ne?"
Da muryar sa ta ce "dayawa ma"
" Sir Najeeb, Allah ni kaÉ—ai ce za ka iya jura. Ba wanda zai iya juran faÉ—an ka. Kai ba mace ba amma sai shegen mita"
"Aysherh" ta ji muryan sa a bayanta. Da sauri ta juya amma ba kowa. Ta rufe ido tana tuno kiss É—in su na ranan...
Saboda ta tsara ba za ta koma aiki ba shiya sa da ta gama azkar É—in ta ta sauko dan ta taya Adama aiki.
Tana saukowa ta haÉ—u da Daddy wanda shigowar sa kenan, ganin sa sanye da kayan bacci ga kuma damuwa shimfiÉ—e a fiskar sa ta yi tunanin ko wani abu ne ya samu Mom.
"Daddy ya jikin Mom" ta faÉ—a cike da tararrajin mi zai ce
"Alhamdulillah da sauƙi 'ya ta"