← Book details Sakatariya Ta Psrt 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 91

Sashe 46

Sakatariya Ta Psrt 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ni ka bar ni, ka san abinda ke damuna ne?"

"Get up" ya faɗa da ɗan ƙarfi.

Ibrufen tab ya miƙa ma ta tareda ruwan ɗumi, ta amsa ta sha.

Ya ce " ki shanye ruwan"

Ta cigaba da shan ruwan ɗumin har ya ƙare. Ta miƙa ma sa mug ɗin ya karɓa ya ajiye a saman bedside drawer.

"Kwanta"

Kwantawa ta yi da bayan ta tana kallon idon sa. Rigan baccin da ta sa riga da wando ne masu laushi, wandon iya gwiwa ya ke.
Hannu ya sa ya kamo ƙafafuwanta biyu. Ta challa ƙara " Sir Najeeb me ka ke shirin yi?"

Wanni kallo ya watsa ma ta ta yi shiru. Ƙafafuwanta ya kama sannan ya tanƙwasu ta yadda cinyoyinta sai da su ka taɓa cikinta gwiwan kuma na taɓa nonuwanta. Ya sake stretching ƙafafun sannan ya sake tanƙwasasu. Haka ya ke yi har sai da yai kaman sau goma sannan ya sauke ƙafafun, ya sake ɗaga ƙafa ɗaya ya tanƙwasashi gefe. Ƙafar ta yi kaman triangle, sannan ya tanƙwasa ta koma ɗaya ɓangaren haka yai ta yi har sau goma sannan yai wa ɗaya ƙafan ma haka. Hannu ya sa zai ɗaga hips ɗin ta sama Farida ta yi saurin cewa "Sir Najeeb ina abu fa, kuma ba a abu idan ana abu"

Ya gimtse dariyar da ta zo ma sa ya ce " Bakin ki ne abu ai, ni ma ba na abu idan ba na so na yi abu musamman ma da wadda ba ta da abu"

Ya tallafo hips É—inta ya É—an É—aga sama sannan ya mai da su ya sake É—aga su a haka sai da yai sau goma.
Yana sake wani form of stretching É—in ta yi saurin cewa " Sir Najeeb ka yi a hankali wandona zai yage"

Tsayawa yai yana kallon ta. Sometimes yana mamakin wai yarinyar nan ta yi makaranta. Most at times tana yin wassu abubuwan kamar 'yar ƙauye.

Sai da ya gama yi ma ta yoga dan ta samu relieve sannan ya kashe wuta ya kwanta.
A cikin duhun Farida ta dubi gefen sa ta ce "Sir Najeeb ya aka yi ka iya wannan abin, Allah na ji sauƙi sosai"

"Sleep Mrs Jibo" ...

...................

Kamar yadda Sabreen ta nema haka washe gari aka ware ma ta office a second floor. Da ta zo ta gani ta ce ba ta so sai a top floor inda office ɗin Najeeb ya ke. Anas ya ce sai dai ta yi manage ahaka zuwa kwana biyu. Ba ta da haƙurin kwana biyu dan haka ta ce ba za ta zauna ba.

Kamar yadda Anas yaiwa Farida alkawari hakan ya sa ya kira Yakubu su ka fara reviewing É—in case É—in Farida da aka yi kwanan baya.

Najeeb ya jima yana zaune yana aiki, Sabreen ta sa shi a gaba da kallo. Ya ce ta tafi ta ƙi tafiya sai yai kamar bai san da zaman ta ba a wajen.
Farida ba ta office lokacin da Sabreen ta zo ta wuce. Ta dawo daga kai saƙo ta zauna tana yin aiki sai ta tuna ya kamata ta chanja pad. Ta ɗau jakar ta ta nufi office ɗin Sir Najeeb tunda banɗakin sa ya fi clean.

Yana zaune ya ji hannun Sabreen a kafaÉ—ar sa. Ya juyo a fusace.
"Whats the meaning of this?"

"I know you missed my touch Noory" ta faɗa tana ƙara shigewa jikin sa.

"To karuwancin har a office" muryan Farida ta dakatar da ita.

Dukkan su su ka kalli Farida da ke tsaye ta sa hannu a kafaÉ—a.

"Miss celebrity you're stepping beyond your boundary" ta ƙaraso har gaban ta ta nuna ta da yatsa.
Kamar yadda ta ce mata she has his heart haka itama ta kwaikwayi maganan ta ta ce " fuck off old woman, i am his wife"

Sabreen ta cize leɓe tana huci.

"As as as, mai guri ta zo sai mai tabarma ta naÉ—e"

"Wow! I like your courage" ta faɗa tana haɗiye duk wani baƙin ciki da ta ke ji.
Har ta fita Farida ba ta bar cewa as as as ba.

Ta juyo ta kalli Najeeb da ya zuba ma ta ido yana ganin shaƙiyancin da ta ke wa Sabreen. Not minding ko waye Sabreen ɗin.

"An dai ji kunya, mace ta gudu ta barka shekara takwas amma ka gan ta yanzu jikin ka ya fara rawa kamar mazari" ta yi wani juyi sannan ta wuce banÉ—aki.

....................

A hankali ta fara barbaÉ—a tankaÉ—aÉ—É—en yajin da ke hannunta, tun daga pillow zuwa duka bedsheet É—in. Bedsheet É—in ba fari bane balle a gane. Tana gamawa ta fice daga É—akin ta maida roban yajin zuwa kitchen. Ta haura sama abinta.
Sabreen ta dawo tayi wanka ta shirya cikin rigan baccinta ɗan filili da shi. Ta kwanta akan gado. Juyawar da za tayi sai ta ji zafi a wuyanta da cinyoyinta da ke buɗe. Ta sa hannu ta sosa wuyar ai sai ya zama kamar ƙara zafi ta yi wa wajen. Ta yi wuf ta tashi tana sosa ko'ina ajikinta...

Farida ta baza kunne tana sauraron ko saƙonta ya kai inda ya ta ke so, saboda haka ma ba ta kunna Tv ba, Shi kuma Najeeb na aiki a laptop. Lokaci ɗaya su ka ji an kurma ihu.
Da farko Najeeb ya ɗauka ko ƙaran daga TV ɗin Najdah ne tunda ya ga Farida ba ta kunna Tv ɗin su ba. Ihu da ƙaran ya cigaba da ƙaruwa hakan ya sa ya miƙe zumɓur ya fita, Farida ta bi bayan shi da sauri.
Lokacin da su ka isa ƙasa su Daddy da Mom ma sun iso ƙasan su na kan Sabreen da ke ta soshe-soshe tana ihu...

*SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......

*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

0️⃣2️⃣9️⃣

*wannan labarin na kuɗi ne, dan Allah kar a fita da shi, ga mai so zai iya tuntuɓar 08137311900*

Sabreen na ganin Najeeb, ta yi kan sa tana sose-sose, ya riƙeta yana tambayar miya ke damunta amma ba magana sai kuka tana ƙara shigewa jikin Najeeb kaman jikin sa ne zai ma ta magani.
Mom ta tafi da gudu É—auko car key. Chak ya É—auketa za su fita dai-dai nan Farida ta sa kuka itama tana wayyo cikina wayyo cikina.
Najeeb ɗauke da Sabreen ya juyo ya ga Farida har ta kai ƙasa tana riƙe da ciki.

Dad ya ce ajiyeta ka É—auko matar ka.
Sabreen ba ta ji mi aka ce ba amma ganin Najeeb na shirin sauketa sai ta sake ƙanƙame wuyan Najeeb tana kuka.
Chan gefe ma Faridan kuka ta ke yi Mom ta yi kan ta tana ƙoƙarin ɗagata tana tambayar miya sameta.
Tunanin Najeeb ko dai ciwon cikin period ne amma kuma she was normal throughout yau, tunda yau kwana na uku kenan da farawanta.

Farida cikin kuka ta fara cewa "Mom ulcer, ulcer na ne ya tashi"

Bai san ko maganar Daddyn ne ta shige shi ba, ko kuma dai ya zaɓi tallafawa Farida ne akan Sabreen ɗin. Amma tsintar kan sa yai da sauke Sabreen ya nufi wajen da Farida ke murƙususun ƙarya a ƙasa. Daddy da Mom su ka tallafawa Sabreen su ka fita da ita. Daddy na cewa yai sauri ya ɗauko Farida. Faridan na hannun sa ya ce su tafi da Sabreen zai taho da Farida.
Ba tareda ya ji nauyin ta ba haka ya haura da ita sama dan ya É—auko key É—in motar sa, har da ce ma ta sorry.
Ya ɗauki key ɗin su ka fito still yana ɗauke da ita. Kafin su isa wajen motar sa motar su Daddy ta fice daga gidan. Sai da ya ajiyeta sannan ya zago da gudu ya shiga wajen zaman driver, yana ƙoƙarin tada motar ya ji ta ce "Sir Najeeb mu koma cikin gida, idan na sha Gestid ma zai lafa mun"

Kallon ta ya tsaya yi cike da mamaki da takaici, sai yanzu ya lura fiskarta ba É—igon hawaye ko É—aya. Lokaci guda zuciyar sa ta ankara da cewa lallai Farida na da hannu wajen abinda ya samu Sabreen, yanzu haka wani abin ta sa ma ta a É—aki.

"You lied?" Ya faɗa da ɗan ƙarfi

"Sir Najeeb Allah Wallahi ina da ulcer, na ji alamun zai tashi ne shi ne ya sa na tareshi tun kafin ya zo"

Zaro ido yai waje lokaci guda kuma ya kwashe da dariya har da dukan steering.

"Now i'm very certain that you're crazy Mrs Jibo"

"Sir Najeeb da laifi idan mutum ya tari rashin lafiya ne?"

Sai da ya sha dariyar sa sannan ya ce " faÉ—amin gaskiya mi ki ka yiwa Sabreen?"

"Ni ba abin da na ma ta. Ance idan duka yai yawa na kai ake karewa. Da ka je kana dakon ɗaukar wata ƙatuwar banza ba gara ka ɗauke ni ba, har lada za ka samu a hakan fa"

"So, kin ƙirƙiri ciwo ne kawai dan na ɗauke ki?"

"Allankatafir ba haka ba ne. Ciwon a jikina ya ke tun asali"

" Ok ok, so yanzu mi za ki ce da su Dad? Su ma za ki gaya mu su taro ciwo ki ka yi?"

"Cewa zan yi na sha magani na warke"

"Ni kuma sai na kai ki asibitin, a taro miki ciwon da kyau"

Ganin yana ƙoƙarin ta da motar ne ya sa ta yi saurin buɗe ƙofa ta fita da gudu. Yana gani ta fita ya kwantar da kan sa ajikin kujera yana murmushi. Shi kan sa mamaki ya ke, a da ya tsani yawan surutun ta amma yanzu ya na jin nishaɗi idan tana yin wasu abubuwan.

Ya jima a cikin motar yana tuno wassu abubuwa da su ka faru a baya. Yana fitowa zai koma cikin gida Daddy ya kirashi yana tambayar ya aka yi ba su iso ba. Cewa yai cikin Faridan ya lafa ta ce ba sai anje asibiti ba.
Daddy ya ce "to Alhamdulillah, Allah ya ƙara lafiya"

Yana kashe wayar ya fara mamakin ƙaryar da yai saboda Farida.
Duƙunƙunewa ta yi ajikin bargo tana tsoron mi Sir Najeeb zai yi dan ta tabbata ya gane ita ta yiwa Sabreen wannan abu.
Yana shigowa ta sake duƙunƙunewa ta na rintse ido.

"Ki gayamin gaskiya mi ki ka sa ma ta?"
Chapter 46 · 0% Book details