← Book details Sakatariya Ta Psrt 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 85 OF 91

Sashe 85

Sakatariya Ta Psrt 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Najeeb bai farfaɗo ba sai kusan ƙarfe ɗaya na rana. Yana buɗe ido ya ga matar sa zaune. Kamar wadda aka tsikara haka ya tashi zaune da sauri. Ganin ta haɗa rai lokacin da su ka haɗa ido ya sa ya tashi tsaye ya iso wajenta. Tana zaune akan kujera ko gizau ba ta yi ba balle ta tashi sai ma juyar da kai da ta yi.
Tsugunnawa yai a gabanta yana kallon gefen fiskarta.

"Na sani abinda na yi is unforgivable. Na sani kina da hujjar da za ki yi fushi da ni. Amma Dan Allah my Queen ki yafe min, I love you, only you"

Juyowa ta yi ta kalli ƙwayar idon sa wanda ke nuna tsananin so da begen ta. Ba abinda ta tuna irin yadda ta tsugunna gaban sa tana hawaye tana roƙon sa amma yai watsi da ita.

"I forgive you" ta faÉ—a a hankali. Ya taso da sauri zai kissing É—in ta ta sa hannu ta tare bakin sa ta ce " i forgive you amma kuma..."

..........................

Kafin a samu a kamo Naomi sai washe gari a chan wani bola tana kwance duk kayan jikinta a yayyage. Kai tsaye gidan Pastor Chukudi aka wuce da ita, wanda ya ke shine pastor ɗin church ɗin da su ke zuwa. Maureen ce ta faɗi silar haukan Naomi shiyasa aka wuce da ita gidan Pastor ɗin. Ita kan ta Maureen ta tsorata da yadda ta ga haukar ƙawar na ta, acewarta su koma wajen Ifagbemi ya basu magani amma Mrs Comfort ta ce ba za su aikata saɓo biyu ba. Ga saɓon zuwa wajen Boka dan asiri ga saɓon neman magani a wajen boka. Ita ta yarda Jesus zai warkar da 'yarta.

Annointed water da oil kam Naomi ta sha su kamar ba gobe amma shiru ka ke ji kaman an suka dusa. Ba sauƙi balle ayi tunanin za ta warke. Da dare Pastor Chukudi da tawagar su su wuni akan Naomi suna ma ta holighost fire amma su na yi tana ƙara rikice mu su...

.......................

Cikin kwana biyu Najeeb ya fita hayyacin sa. Farida ta ƙi dawowa. Ta ce ta yafe ma sa amma ya bata lokaci ta yi tunani. Mom ma ta goya ma ta baya akan ya barta ta huta.

Yau ma dai gidan ya zo roƙo amma ba ta nan, Adama ta ce sun fita da Sabreen.

Ya zauna a falo yana jiran dawowar su duk da kuwa Adaman ta ce ba su jima da fita ba.
A falon Daddy ya dawo ya sameshi lokacin har ya fara bacci. Jin takun mutum ya sa ya farka.
Gaishe da Daddyn yai yana faÉ—in yana son magana da shi. Daddy ya ce ya biyo shi. A falon Daddy su ka ya da zango inda Daddy ke tambayar ko lafiya.

"Dad ka sa baki dan Allah. Ta ce wai sai ta haihu kafin ta dawo. 3 months yai yawa, ba zan iya jure rashin ta ba"

Daddy yai murmushi ya ce " so ka ke na sa ta tayi abinda ba ta so?"

"No Dad amma idan ka ma ta magana wallahi ba za ta ƙi maganar ka ba"

" Son kenan, wannan tsakanin ka da iyalin ka ne ba ni da wani hurumi a ciki. Ka bata lokaci kaÉ—an za ta sauko, she went through alot saboda kai dan haka ka bi ta a hankali"

Najeeb ya haÉ—a rai dan bai ji daÉ—in maganar Dad ba, maimakon ya supporting É—in sa sai ya ke maganar wai ya amince da hukuncin da ta yanke...

Lokacin da su ka dawo ma haka ta wuce shi, yana magana ko uhum ba ta ce ma sa ba ta haura sama.

"Sabreen please help me talk to her" ya faÉ—a yana haÉ—a hannu.

Kaman Daddy itama cewa ta yi ya ba wa Farida lokaci.

ÆŠakin su ya wuce ko zai samu daman magana da ita amma ya samu ta kulle É—akin.

"My Queen please ki bari na ganki ko na minti É—aya ne"

Tana zaune akan gado tana jin magiyar sa amma ko ajikinta duk da chan ƙasan ranta tana son kasancewa da shi amma ba za ta janye ƙudirinta na son horashi kaɗan ba. Haka ya gama magiyar sa ya bar wajen....

Bayan kwana biyar da haukar Naomi Pastor ya bada shawaran a je a bawa wanda ta yiwa magani haƙuri saboda idan su ka yafe hakan zai sa Naomi ta samu sauƙi.
Mrs Comfort, Pastor Chukwudi da Saint Janet suka je gidan su Najeeb. Maigadi ne ya sanar da su Farida tana gidan au Najeeb, su ka karɓi address a wajen shi su ka wuce chan...

Mrs Comfort kuka ta dinga yi wiwiwi a gaban su Farida tana roƙon su gafartawa Naomi. Daddy ya ari bakin Najeeb da Farida ya ce sun yafe, Najeeb ya haɗe rai dan shi plan ɗin shi ma sai Naomi ta je jail.

Pastor ya mu su godiya sannan su ka tafi. Duk da wannan yafiya da aka yi bai sa Naomi ta warke ba. Kwana biyu da dawowar su daga gidan su Najeeb ta tsere daga gidan Pastor ta shiga gari. Wasa-wasa aka baza neman ta amma har sati guda ba labarin inda ta ke...

.........................

Shirye-shiryen bikin Sabreen ake yi duk da kuwa Sabreen da Lukman ɗin sun amince akan ba za ayi hidima ba amma Mom da Farida sun ƙi. Wata guda aka saka har yanzu kuma saura sati uku.

Fitowarta kenan daga wanka ta kalleshi zaune akan gado. Mantawa ma ta yi ba tarufe ƙofan ba.
"Ni fa ba na so ana shigo mini É—aki ba izini"

A hankali ya taso ya zo ya tsugunna gaban ta ya kamo hannunta biyu ya riƙe gam. Kallon sa ta ke yi yadda idon sa yai ja.

"Aysherh I cant, ba zan iya ba. Kafin 3 months É—in nan zan iya mutuwa idan ba kya tareda ni. Please ki manta da komai ki dawo gida mu cigaba da rayuwar mu. I promised to make it up to you, ba zan sake É—aukan sakatariya ma ce ba, yalla yarinyace ko tsohuwa. Zan dage da addu'an dare saboda kar wata ta kuma samun galaba a kaina. Zan yi duk abinda ki ka ce amma please come back to me. I love you"
Ya kai hannun ta kan kirjin sa ya ce " My heart beats for you Aysherh, only for you. Ki taimakeni ki taimaki zuciyata kar rashin ki kusa da ni ya min illa. Na É—auka zan iya jurewa amma Wallahi ba zan iya ba, its being 2 weeks amma gani na ke kamar 2 years ne. I miss you Aysherh, I miss us. Please my Queen..."

*team Farida kun karɓi haƙurin Najeeb ko ya?*

Skt 57

"Ka yi haƙuri amma ba zan koma yanzu ba" ta faɗa a hankali duk da kuwa maganganun sa sun karya ma ta zuciya.

Ya cize leɓen sa na ƙasa yana huci, bayan 'yan daƙiƙai ya miƙe tsaye ya ce "tunda abinda ki ke so kenan zan jira ki"...

Ba ta iya É—aga ido akan sa ba har ya fita daga É—akin.
Anya ta ma sa adalci kuwa? Ta tambayi kan ta. Sai dai kuma ta rasa gane amsar da za ta bawa kan ta...

Yinin ranan sai sintiri ta ke tsakanin falo da É—aki amma Najeeb bai dawo ba. Washe gari ma bai zo gidan ba...

Su uku ne a dining su na cin breakfast lokacin da Najeeb ya shigo. Kwana biyu kenan bai zo gidan ba.
Wajen Mom ya je ya gaisheta, ta shafa gashin sa tareda ma sa peck a goshi.

Ya duba Sabreen ya ce "amarya ya shirye-shirye"

Sabreen ta yi murmushi ta ce "shiri ai sai su Mom da Ayshah, su ke ta komai"

"Allah ya kaimu lokacin"

Mom ta amsa da amin yayinda Sabreen ta sunkuyar da kai tana murmushi.

"Zan wuce Abuja, i'll be there for two days"

Mom da Sabreen su ka ma sa addu'ar Allah ya kiyaye.
Farida tunda ya zo ta ke binsa da ido amma bai ko kalli wajen da ta ke ba.

Ganin ya juya zai tafi ya sa ta yi saurin sake mug ɗin tea da ta riƙe, Mug ɗin ya faɗi kan tile ya ɗan fashe.

"Ouch...Ouch ... Wayyo zafi..." Farida ta faÉ—a saboda tea É—in ya É—an fetsu ma ta.

"Sannu Ayshah, sannu, ba ki ji ciwo ba ko?" Mom ta faɗi tana ƙoƙarin riƙe hannun Farida.
Farida kam idon ta na kan Najeeb wanda ta ke tunanin zai zo da gudu ya dubata. Sai taga saɓanin haka tsayawa kawai yana kallon ta.

ÆŠan gyaran murya yai ya ce " na tafi"

Farida na jin haka ta fashe da kuka.
Sabreen mi za ta yi banda dariya. Mom ma dariyan ta ke son yi amma ta gimtse.

Har ya fita Farida bata dena kuka ba. Sabreen ta ce "someone is missing her husband"

Farida ta kalleta ta galla ma ta harara. Mom kam yi ta yi kaman ba ta san sunayi ba, Adama ma ta kira akan ta zo ta tattare wajen da Mug É—in ya fashe...

Ƙarshe haushi ya sa Farida tashi daga wajen ba tareda ta gama cin abincin ba...

...........................

Tana jiran kiran sa ko text amma shiru. Baƙin ciki ya tokare ma ta maƙoshi, kowa ma haushin sa ta fara ji a gidan. Sabreen kuwa indai su ka haɗu sai ta tsokaneta akan Najeeb.

Ranan da zai dawo ta samu Mom a É—akin ta da su ka gaisa ta ce "Mom zan je na É—au wassu kaya a chan gida"

Mom ta yi murmushi dan ta gano Ayshah na son komawa gidan ta ne. Ta ce " 'yata ni inaga horon ya isa haka, Son zai cutu idan ki ka cigaba da zama a nan"

"Amma Mom..."

Mom ta katseta da cewa "ki yi haƙuri ki koma kin ji"

Farida ta yi ajiyar zuciya ta ce "shikenan zan koma saboda ke"

Mom ta ce na gode. Sai da Farida ta fita sannan Mom ta yi murmushin manya...
Chapter 85 · 0% Book details