← Book details Sakatariya Ta Psrt 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 53 OF 91

Sashe 53

Sakatariya Ta Psrt 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wata baƙar Marcedez benz ce ta shigo Kamfanin Najeeb constructions. Lokacin da motar ta tsaya an kai kusan minti biyu kafin aka buɗe ƙofa. Wata haɗaɗɗiyar mata ce ta fito daga ciki ta owners corner. Tun daga takun ta ka san mace ce mai aji da kuma girma. Kai tsaye ta shige kamfanin security ɗin wajen yana mata good morning ta amsa ma sa ta hanyar ɗaga hannu.
Anas ne ya nufota yana gaisheta lokacin da ta iso top floor É—in. Tare su ka jera su ka wuce conference hall É—in inda za ayi board meeting.

Kujeran da ta zauna an rubuta CEO a jiki waje ne da Najeeb ke zama lokacin yana da lafiya. Waje ne da bayanshi ba wanda ya taɓa zama a wajen idan ana taro haka.

Sai da ta ja numfashi ta sauke sannan ta ce *"suna na Aisha Farida Salihu, Mrs Najeeb Adam Jibo kuma acting CEO Najeeb constructions har zuwa lokacin da miji na zai samu lafiya ya dawo"*
Ta kalli fuskokinsu mai cike da tarin tambayoyi ta ce *ko da me ja?*....

*Tantarantarantaran. Daga secretary sai CEO wannan ƙarin matsayi har haka @team Farida kuna da aiki a gaban ku. @team Najeeb, sorry Najeebullahi ya tafi hutu, sai kun ganshi kawai dan nima ban san ranan dawowar sa ba😀*

*SAKATARIYA TA*
.......(My Secretary).......

*Azizat......✍*
*Wattpad @000Azee*

*BISMILLAHIR RAHMANIR RAHIM*

0️⃣3️⃣3️⃣

*wannan labarin na kuɗi ne, dan Allah kar a fita da shi, ga mai so zai iya tuntuɓar 08137311900*

"Excuse me, ba za mu amince da wannan ba. Ta ya za ace za ki jagoranci kamfani kamar wannan ki na matsayin sakatariya. I bet wannan kamfani za
ta ruguje kafin nan da wata É—aya. Duk da ki na matsayin matar Sir Najeeb hakan ba zai sa ki ma ye gurbin sa a wannan kamfani ba. You are incompetent and clueless" wani a ciki ya faÉ—a yana huhhura hanci.

Ba tareda ta karaya ko nuna damuwa ba ta kalli mutumin ta ce " mi ye matsayin ka a wannan kamfani?"

Mutumin ya É—aga kafaÉ—a ya na faÉ—in " I'm Festus Ogonna the F....."

"Get out!" Farida ta daka ma sa tsawa wanda kowa a wajen sai da ya sha jinin jikin sa, hatta Anas da ke gefe sai da ya ji wani dum. She sounds exactly like Najeeb.

"Mr Ogonna ba za mu iya zama da wawa kuma jahili ba. Tambaya É—aya na yi ma ka amma ka fara ba da tarihin rayuwar ka. Who cares about your name?, a wannan kamfani matsayin ka shi ne identity É—in ka and that's what i asked ba sunan ka ba"

Kallon-kallo aka fara yi, yadda ta ke magana da faÉ—a-faÉ—a ka ce kamfanin na ta ne tun fil azal.

"Get out!" Ta sake daka ma sa tsawa tana kallon sa ido cikin ido.

Mr Ogonna aƙalla zai kai 45yrs amma Farida ba ta kalli girman sa ba balle ta ji kunyar idon sa.

Mr Festus ya yi kasaƙe yana kallon ta. Ya buɗe baki amma ya kasa magana.

Phone da ke gabanta ta É—auka ta danna wassu numbers. Ba su ankara ba sai ji su ka yi tana faÉ—in security su zo su fita da wani mahaukaci.

"You cant do this, you dont have the right" Mr Ogonna ya faÉ—a cikin masifa.
Farida na zaune ba ta ce komai ba sai ma duba takardu da ke gaban ta da ta fara yi. Mr Ogonna ya cigaba da kumfar baki yana faÉ—awa sauran su sa baki, Farida ba ta da matsayin da za ta jagorance su balle har ta koreshi daga wannan meeting É—in. Sai dai ba wanda yai magana. Sai kallon juna su ke su na magana da ido amma ba wanda ya furta wani abu.
Su na zaune har securities biyu su ka zo su ka fita da Mr Ogonna yana ta zage-zage.

Ta gane Mr Ogonna sarai, sau dayawa idan anzo meeting tun lokacin Najeeb yana É—aya daga cikin wanda duk abinda aka faÉ—a sai ya kushe. Ya fi so ayi abinda ya zo da shi.
Najeeb bai cika sauraron sa ba, yana tashi zai yi magana Najeeb zai ce ya zauna. Wassu lokutan kuma sai ya bari ya gama bayanin sa sai Najeeb ya gwaleshi da cewa sun ƙayatu da labarin wasan kwaikwayon da ya gama ba su.
Mr Ogonna irin ma su son cigaban kan su kaÉ—ai ne. Ba su da wani interest akan aiki indai ba zai jawo ya samu wani matsayi ko wani kamashon kuÉ—i ba.

Bayan an fita da shi Farida ta sake tambayar su ko da mai ja, wannan karan ba wanda yai ƙwaƙwƙwaran motsi balle magana.

"Good, now what's next?"

Anas yai gyaran murya ya gabatar da matsalar da ke gaban su a yanzu. Maganan French investors É—in su da ke son siyan kaso arba'in na kamfanin yai tareda neman minene mafita.

Farida ta bada dama a kawo shawara. A wajen kashi saba'in sun ba da shawaran a sayar da 40% É—in sauran kashi talatin É—in kuma su ka bada shawaran a kan kada a siyar a bari su janye 11% É—in su. Duk da kuwa kamfanin za ta shiga wani yanayi amma idan aka jure aka kuma bi matakai masu tsauri za a farfaÉ—o daga faÉ—uwan da kamfani za ta yi. Cikin wanda su ka ba da shawaran a bari su cire hannun jari har da Anas. Bayan Mrs Najeeb Jibo ta gama sauraron su sannan ta ce
"11+40?"
Kallon kallon aka farayi dan ba a gane me ta ke nufi ba. Ganin ba ta kuma cewa komai ba ya sa wani ya ce "its 51"

"Exactly 51" ta faÉ—a tana buga table.

"Taya 51% zai kasance shares ɗin wassu turawa, mun amince mu sallama mu su kamfani kenan?. Ta ya za mu bar wa wassu turawa kaso mafi tsoka cikin wannan kamfani, bayan shekaru bakwai kenan ku na yiwa wannan kamfani hidima ace kun kasa riƙeta har sai wassu baƙin haure sun zo sun mu ku jagoranci. Miji na baya nan hakan bai sa komai zai tsaya ba, dukkan mu mu na da hakki akan wannan kamfani. Maganar ma a saida mu su shares ba ta taso ba. We will fight, we will fight with everything we've got. Tsoro ba na mu ba ne, the moment mu ka sa tsoro to mun faɗi, we will all fight this together"

Gaba É—aya wajen aka sa tafi.

Anas yai murmushi tareda ma ta thumbs up...

A hankali ta buɗe ƙofar office ɗin, office ɗin na nan yadda ta san shi. Ba wani chanji illa kawai mai office ɗin da baya nan. Ta ƙurawa kujeran sa ido tana ganin kaman Najeeb na zaune a wajen sai dai wannan karan maimakon yadda fiskan sa ke tsume koyaushe to yanzu murmushi ya ke ma ta.

"Sir Najeeb" ta faÉ—a a hankali.

"Aysherh" ta ga ya faÉ—a ma ta yana ma ta thumbs up.

"Farida" muryan Anas ya dawo da ita daga tunanin da ta ke.

Ta juyo tana kallon sa.
"Gaskiya kin yi ƙoƙari, sai dai da sauran aiki saboda jibi za su zo kuma ba mu shirya komai a kai ba"

"Ya Anas su zo ma na, su É—in mala'ikun mutuwa ne da za mu ji tsoronsu?"

Anas ya girgiza kai.

"Wancan Mr Ogonnan ka sa a rubuta ma sa suspension na sati biyu. Ba ma son ɓata gari irin sa"

"Amma Farida ba kya ganin this is extreme".

Farida ta zauna akan kujera tana mai faÉ—in Bismillah a zuciyar ta.

"Lokacin da na ce ba zan karɓi aikin nan ba mi ka ce min?"

Anas yai ajiyar zuciya sannan ya ce "Shikenan Farida, zan yi yadda ki ka ce"

" na gode Yaya na" fita yai daga office É—in yana mai fatan zuwan Farida zai yi gyara ne ba lalata lamura ba.

Ta san dole za a samu matsala dama, shi ya sa tun farko ta ce ma sa ba za ta yi ba, saboda za su samu matsala da shi. Za ta iya bada umurnin da bai ma sa ba yai magana. A lokacin ya ma ta alkawarin duk abinda ta ce zai bi matuƙar bawai a harkan zane-zane ba ne tunda ba ta da masaniya a kan wannan harka.

Tana juyi a kan kujeran tana tuna hiran su da Daddy shekaranjiya.

" 'ya ta, Anas ya faÉ—a min ba za ki kula da kamfanin Najeeb ba, mi ya sa?"

Ta sunkunyar da kai ta ce "Daddy, aikin ya min girma kuma ban da ilimi a wannan harka"

Murmushi yai ya ce " Kamar ba Aisha Mai Gwanjo ba"

Farida ta yi saurin É—ago ido ta kalle shi cike da mamaki

Ya cigaba "Aisha mai turare, Aisha mai takalma, Aisha mai jakukkuna, Aisha mai zoɓo roto one in town.... and the list goes on. Aisha Baffan ki ya gaya min yadda tun ki na yarinya ki ka fara siye da sayarwa. Ko ba ke ba ce kina shekara tara ki ka saro goruba da taura ki ka zo da shi hutu kano, Baffan ki ya hanaki sayar wa ki ka ce ai ba za ki yi asara ba sai dai ya siye ya biya ki kuɗin hajar ki"

Farida ta sunkuyar da kai tana ƙoƙarin rufe fiskar ta da gyale saboda kunya.

"Lokacin da Najdah ke shekara tara ba abinda ta sani sai sakalci. "Lets go for ice cream Dad" ko "are we going to Disney this summer?" " Dad i want a pink teddy not brown" yai murmushin yaƙe sannan ya cigaba.
"Allah ya ba ki baiwa Aisha ki gode ma sa bisa wannan ni'ima. Ba zan takura mi ki ba amma ni akaran kai na ina so ki jagoranci kamfanin Najeeb, Allah kuma zai taimake ki a kan hakan"...

"Allah ka taimake ni bisa wannan jagoranci, ka bani ikon sauke nauyin da ya rataya a kai na, ka ba ni ikon yin gaskiya da adalci, Amin" abinda ta faÉ—a kenan kafin ta fara buÉ—e tarin files da ke gabanta.

.............................

Ƙarfe biyar da rabi ta isa asibitin, bayan an tashi sai da ta tsaya su ka tattauna da Anas kafin ta taho.
Tana shigowa ta samu Najma da Najdah a É—akin.
Chapter 53 · 0% Book details