← Book details Rubutaccen Alamari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 77

Sashe 9

Rubutaccen Alamari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Binta yayi suka shiga cikin gida kai tsaye kitchen d'in Nenne suka shiga , gaban sink ta tsaya tare da
wonke su tsab sannan ta jawo wata yar roba mai kyau ta zuba mishi,
suna fitowa Aliyu ya kalli Ummul yace.
"In anga kina kiciniya dai toh kinga kayan zak'ine,
nanne za'aga k'wazon ki."

"Eh d'in me ruwan ka da ni d'an sa ido kawai."

Kitchen d'in ya shige yana cewa.
"Uhum shazumami kawai kin iya shan zak'i kin iya yi mana kuka in cikin ki ya fara ciwo,
kita b'are mana baki."

Kanshi tayi da sauri zata kai mishi duka,
shi ko zillewa yayi ya koma bayan Ya Adam dake harararta yace.
"Ai gaskiya ce Aliyu ya fad'a kike wani fiffik'ewa ke zakiyi duka."

Shi dai Ya Usman dariya yayi ya jawo hannun ta ya nufi parlour Hajjajo da ita yana cewa.
"Ko Hamma Umar mai son kalota miki laifi bazaice fruits zai saki ciwon ciki ba,
k'anwata sha abinki."

ba tare da tunanin su Abba na cikan d'akin ba suka shiga tare da sallama.

Suna shiga Hamma Umar ya d'ago kanshi fuska a tsuke ya d'an harari Ummul dake rik'e da Apple a hannun ta tana ci,
baki ta tura tare da kauda kanta da sauri a ranta tana.
"Mugu ko yaushe fuska a tsuke."
Shi ko Usman cikin dariya yace.
"Abba yau mitin kukeyi da Hajjajo da d'an jikinta a gefe ne."

Kallon shi kawai su Abba sukayi zuk'atan su cike da alhinin irin son da Umar keyi mishi,
shiko Usman ganin yadda suke zaune daga dukan alama magana mai mahimmanci sukeyi sai ya d'an zauna tare da gaida su,
itako Ummul dama tuni ta fita ta tsaya a barandar ganin bai fito bane tace.
"Ya Usman bari in kai maka robar cikin motar ko."
"Toh muje nima gani nan zuwa."

Juyawa tayi ta nufi harabar gidan nasu,
shima yana gaida su ya fito yabi bayan ta,
robar ta ajiye mishi sannan ta koma cikin gida, tana shiga Mustapha ya kira dan shaida mata ya isa lafiya,
daga nan kuma sukaci gaba da hira,
shi kuwa ya Usman wurin abokin shi Nuru ya nufa,

A parlour hajjajo kuwa cikin zurfin tunani Abba yabi bayan Usman da kallo a hankali ya sauk'e ajiyan zuciya sannan ya kalli Hamma Umar cikin nitsuwa,
shiko Hamma Umar kanshi ya sunkuyar,
kai Abba ya juya ya fuskanci Daddy da Hajjajo ajiyar zuciya ya kumayi sannan cikin yanke hukunci yace.
"D'an uwana Hussani da maifiyata Ku zama shaida a gareni na bada auren Ummul khairi ga d'an d'an uwana ,
na bada auren ta ga shi.....

By
*GARKUWAR FULANI*
📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*RUBUTACCEN AL,AMARI*

Page 8⃣

*NA*
*AYSHA ALI GARKUWA*

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*Fans na fatan alkhairi a gareni baki d'aya ina mai Baku hak'uri kwana biyu zaku jini shiru sakama kon tafiyar da zanyi gobe zanyi tafiya YOLA 2 KANO kuma biki zani ba damar yin typing sai Allah ya dawo dani lafiya ina barar addu'arku gareni*

*INA kuke masoyan yan gaskiya Firdausi Sodaggi tare da Hassana d'an larabawa Wannan shafi nakune INA al'fahari daku*

*TABITAL FULAKU group GARKUWAR FULANI group AYSHA ALI GARKUWA fans GARKUWA AYSHA&UMMEE novels tare da BANDIRAWO fans kun zamoni na zamo Ku Kusani kab groups na inajin daku kamar yadda kuke ji dani bani da kamarku a duniyar gizo-gizo🤝😍😘*

*"N*a bawa Umar auren Ummul khairi,
ku sani na bashi auren ta na kuma yanke hukuncin za,ayi bikin nanda wani d'an lokoci domin aurar dasu ga juna shine mafita da zamu sama musu ."

Daddy kam da Hajjajo kallon Abba sukeyi cikin jin dad'i Daddy sai murmushi yake yi ita kuwa Hajjajo kai take ta jinjina wa,
gaba d'aya sai farin ciki ya cika zuk'atan su,
Shi kuwa Hamma Umar tunda yaji furucin da Abba yayi,
gaba d'aya yaji jikin shi na rawa gabb'an jikin shi kab kamar an sassare su,
sai zufa yaji yana ketomai tako ina ido ya d'ago ya kalli iyayen nashi sai kuma atake yaji wata iriyar kunya mai tarin yawa ta rufeshi nauyin Abba yaji gaba d'aya ya kama shi,
cikin tsananin kunya ya sunkuyar da kanshi k'asa yatsun hannushi ya rink'a murzawa tare da yin shiru sai bugun zuciyar shi da ya tsanan ta,
Daddy ne ya kalli shi cikin kula yace.
"Farouq kaji ta inda Allah ya kawo mana mafita ko?,
tunda dama kai tunanin ka matar da zaka aura ta kasan ce mai tausayawa Usman ta taya ka kula dashi kar tazo ta rabaka da d'an uwanka,
kaga a sauk'ak'e ita Ummul yar uwarsa ce kuma ko yanzu tana kula dashi."
Shiru yayi bai d'ago ya kalli Daddy ba sai gyad'a mishi kai yakeyi,
haka yasa Abba ya zuba mishi ido cikin kula yace.
"Farouq."
Shiru bai amsa ba sai gyad'a kai ya kumayi alamar amsawa, shima Abba kai ya jinjina tare da k'ara kiran shi a karo na uku yace.
"Farouq."
Jin Abban nata jerama mishi kiran yasa ya d'ago kanshi kad'an cikin raunin murya yace.
"Na'am Abba."
a hankali Abba yace.
"Farouq d'ago kanka ka kalleni."

Kai ya jinjina a hankali ya d'an kalli k'anin mahaifin nashi,
sai ya kuma yin k'asa da idanun shi,
kafad'an shi Abba ya dafa murya a tausashe yace.
"Farouq kai da banne a cikin yaran mu kowa da halinsa kowa ana fahimtar ina ya dosa amman kai haka Allah ya halicce ka kana da zurfin ciki ba'a gane abin da kake so da abinda baka so kuma bakin ka baya furtawa,
toh ka sani duk da haka bazan cutar da kaiba,
dan kafin ka zama maraya mu muka zama marayu kuma d'an uwanmu Abbanka shi ya zame mana uwa da una bai regemu da komai ba yakan hak'ura da farin cikinsa dan ya sama mana farin ciki,
haka zaisa Farouq bazan k'untata rayuwar kaba,
yadda Ummul take y'ata haka kaima d'anane jininane ni da maifinka uwa d'aya uba d'aya Farouq ina sonka son da bana yiwa y'ay'an cikina,
Farouq ni ubane a gareka kuma aboki kuma amini kuma mashawarci,
Farouq bazan yimaka doleba sai da son ranka karkaji kunyar shaida min baka son Ummul in har baka sonta ka gaya min ,dan bazan yimaka auren cusheba bare na dole,
ka furta min kana son Ummul? ko baka sonta?."

Kai ya rink'a jujjuyawa yana sauk'e numfashi a ranshi yake juya kalaman Abba a fili kuwa cikin raunin murya yace.
"A,a
A,a Abba a,a ba kaina nake tunawa ba , Abba Ummul bata sona,
ko cikin yayunta ni da ban ta d'aukeni kuma gashi tana da wanda take so,
Abba me za'a cewa Mustapha? Ummul da Mustapha nake tunawa kar sanadi na a cutar dasu hakan zaisa Ummul ta k'ara tsanata bana son na zama bak'in jakada a Rayuwar Ummul da Mustapha."

Sai kuma yayi shiru yana murza yatsun sa tare da kamo lips d'in shi na k'asa yana d'an ciza.

Abba da Daddy kuwa ido suka zuba mishi yayin da Hajjajo kuwa gaba d'aya take kallon shi da suffar maihaifinshi ,
Umar Faruoq shi haka Allah yayi shi baya son shiga hakk'in kowa .

Kai Abba ya jinjina sannan yace.
"Farouq amsa min tabbaya ta,
shin kana son Ummul ? ko baka sonta?."

Kai ya k'ara sunkuyar wa cikin cushewar tunani a ranshi yake tuna.
"Abba ya zanyi in kalli tsabar idanun ka nace bana son y'arka ta cikin ka?."

A zahiri kuwa kai ya girgiza murya a raunane a hankali yace.
"A,a Abba ya zanyi ink'i y'ar uwata."

Nannauyan ajiyan zuciya Abba ya dire sannan ya kalli Daddy cikin jin k'arfin guiwa da kara yace.
"Hussaini ina nemawa d'ana Umar Faruoq auren d'iyar mu Ummul."

Murmushi Daddy yayi tare da yin hamdala yace.
"Na bada auren Ummul ga d'ana Umar Faruoq."

Hajjajo ko murmushi tayi da hamdala sannan ta sanya alkhairi a acikin abin,
shi kuwa Hamma Umar kai ya d'ago a hankali yace.
"Abba nagode Daddy Allah ya biyaku."

Da sauri Abba yace .
"A a Farouq godiya kuma a tsakanin mu ai nauyin mu ne mike sauk'e wa."

Kai ya kuma sunkuyar wa murya a raunane yace .
"Abba ya za'ayi da Mustapha? Abba me za'acewa Mustapha? Abba ya Ummul zata d'auke ni?."

Gyara zama Daddy yayi sannan a nitse yace.
"Farouq wannan magana bamu gaya maka itaba har saida mukaje muka samu iyayen Mustapha mu kayi misu bayanin Ummul zamu bada ita ga d'an uwanta,
Alhamdulillah iyayen Mustapha masu mutun cine sun fahim cemu inda anan take suka kira Mustapha a gaban mu akayi mishi baya ni,
tabbas Mustapha yana son Ummul kuma ita tana sonshi d'an Mustapha ya san haka d'an tunda mahaifinshi ya mishi bayani Mustapha kuka yake tamkar yaro,
Amman kuma hakan bai hanashi ya fahimci abinda mik'e nufi ba,
d'an haka yace ,
yaji kuma ya yarda amman don Allah kar a hanashi zuwa gun Ummul tunda ba'asan Rubutaccen AL'AMARI da zai wakana ba yace zaici gaba da neman ta in ita rebonshi ne zaka bar mishi ita,
haka yasa yake zuwa gunta har yanzu kuma munce karya gaya mata yakuma yarda munkuma ce ya rege kiranta da zuwa duk ya yarda."

Allah sarki Umar Faruoq mai sadaukar da farin cikin sa ga wani gaba d'aya sai yaji ya tsani kanshi dan yanaga ya shiga hurumin wasu ya tsaga soyeyyarsu,
gaba d'aya jikin shi ya mutun a haka suka tashi taron su,
Daddy ya tashi ya koma gidan sa shi kuwa Abba yayi part d'in sa a parlour shi ya samu Nenne tana zaune rik'e da carbi hankalin ta na kan tv tana kallon tashar sunnah tv,
zama yayi gefen ta cikin sakin fuska da halin girma ya kalleta tare da cewa.
"Khadija rege sautin tv nan akwai maganar da zamuyi."

cikin girmamawa ta rege sautin sannan ta juyo gareshi cikin nitsuwa tace.
"Fatan alkhairi."
kai ya jinjina cikin girma da isa da gidan shi ya shaida mata yadda sukayi da y'an uwanshi kab.
sannan ya d'ora da cewa.
"Kinji hukuncin da muka yanke."
shiru Nenne tayi cikin zulumin abinda zai biyo baya a hankali kamar cikin rashin fahimta tace.
"Umar ko Usman?."
cikin zuba mata ido yace
"Umar dai ba Usman ba ko kina da magana ne?."
Chapter 9 · 0% Book details