← Book details Rubutaccen Alamari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 77

Sashe 69

Rubutaccen Alamari Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

*H*annu yasa ya jawa Ummul ɗin ta faɗo jikin shi cikin sauƙe ajiyan zuciya ya haɗasu da Farouq ya ruggume su tsam a jikin shi yana jin wani irin yanayi mai cike da tarin rauni,
tabbas wani abu sai mutuwa inba mutuwaba ya za'ayi ya auri Ummu matar É—an uwanshi gaba É—aya begen É—an uwanshi ya rufeshi zuciyarshi ta cika da rauni a hankali wani irin kuka ya kufce mai,
kuka mai cin zuciya har jikin shi na rawa sai ƙara ruggume ta yake yana sheshsheƙa hawaye na bin fuskar shi,
itama Ummu sai kara lafewa tayi a jikin shi tacigaba da kukan dama tun safe take yinshi,
Kuka suke sosai bame rarrashi wani a cikin su sai ruggume juna sukeyi suna kuka mai cike da ƙuna a zuciya,
sun ɗau lokaci mai tsawo suna cikin yanayin tuno da jigonsu gaba ɗaya zuƙatansu sun cika da rauni,
Cikin kukan Ummu ta ɗago kanta fuska cike da ƙollah ido ta ɗan firfitar ganin yadda numfashin ya Usman ke fusga yana neman ɗaukewa sai karkarwa yake ida nunshi sunyi jazir ƙirjinshi na bugawa da ƙarfi ,
janye jikinta ta tayi hankali ta miƙa hannun ta karɓi Farouq dake ta bacci daga hannun shi tamatsa a hankali ta kwantar dashi akan 2 seater,
sannan tadawo jikin shi ta ruggume shi a hankali takamo hannun shi ta jashi suka zauna kan 3 seater,
ruggume shi tayi cikin kuka da rawar murya tafara magana a hankali tace,
"Hamma Umar baida wani fargaba daya wuce ya ganka cikin tashin hankali,
kullum burinsa ya ganka cikin farin ciki,
fatan Hamma Umar baya wuce samun lafiyar ka ya Usman,
ko a lokacin da zai rasu sunan ka dana Ammi ya kiramin amman Allah bai bashi damar karisa min maganar da yake son faÉ—a minba sai yayi kalmar shahada,
Abunda ban saniba wata ƙil amanar ku zai barmin ko cemin zai na kula da kune ban saniba".
Tana kaiwa nan suka daÉ—a rungume juna suka sake fashewa da kuka jiki na rawa ya kuma matseta a jikin shi murya na rawa yace,
"Ummu na ni kam Hammana yabar min amanar ki keda Farouq randa yayi zuwanshi na karshe a gidan nan,
saida duk ya bar mana wasiya amman a lokacin bamu ganeba,
Ummu kituna meyace min nida Adam".
sai kuma ya sake matsota jikinshi yana zubda ƙolla sannan yaci gaba da cewa,
" Hamma na cemana yayi,
"Da inada damar tafiya da Ummul duk inda zanje,
da ko ina zanje zan tafi da ita,
sai dai kach bani da damar yin tafiya da ita dole in barmaka ita Usman kaine É—an uwana kuma dole ka kula da family na,
Ummu
kin tuna abinda yacewa Adam
yace Adam zantafi da ita amman zata dawo in tadawo duk maison ɓata min rai ko tozar tani to ya ɓatawa Ummu rai niya ɓatawa!
Ummu kin tuna abinda Hamma yacewa Aliyu,
yacewa Aliyu kai kuwa Aliyu a zatona kaine abokin kukan ta kaine abokin shawarar ta Aliyu ko duk zasu dakarmin Ummul a zatona kai zaga zame mata katanga abun jingina azatona kai mai tayata kuka ne".

Sai kuma ya sake ruggumo Ummun cikin tarin ƙunci ya sauƙe nannauyan ajiyar zuciya yace,
" Kin tuno me yacewa Sadik
Cemai yayi
"Sadiq inta dawo ka kasheta don dole zata dawo badon ina soba dole zata dawo cikin ku ba yadda na iya,
ya kuma cewa Nanne Ummul fa madadin mutum 3 ce ni Usman da Ammin mu dakuma É—an cikin ki ya ware kanshi a lissafi ashe zai tafi ya barmune bamu saniba tafiyar da bazai dawoba ashe duk maganganun shi wasiyace a garemu,
Ummu dana sani dana hana Hamma na tafiya a wannan ranar,
ashe shike nan mun rabu har abadan,
ashe shike nan yayi zuwanshi na ƙarshe a gidan nan,
Ummu ki tuna a ranar Hamma yace min,
Usman nauyin farin cikin Ahlina yana kanka in bananan".
Sake matsota yayi yaci gaba da kuka har yana shiÉ—ewa,
Cikin tsana nin kuka itama ta ruggumoshi tana cewa,
"Ya Usman kayi hakuri mubar yiwa Hamma na kuka muyi mishi addu'a zaifi farin ciki damu, kabar kukan nan Hamma bayason kukanka nima banason kukan ka,
ya Usman ina sonka ina son farin cikin ka ka dena kuka".
Cikin kukan ya tallabo kanta ya kalleta da kumburarrun idanun shi ya sakar mata murmushin dayafi kuka ciwo a hankali yace,
"Allah ya É—aiyaba min Ummuna,
nima ina sonki".
Itama murmushin tayi wanda hawaye ke bin fuskarta a hankali tasa tafin hannunta tashare mai hawayen,
shima haka yasa hannu ya share mata nata ya ruggumo ta yana sauƙe nannauyan numfashi a hankali yace,
"Ummuna zan dawo miki da farin cikin ki keda Farouq ko Hammana zaiyi farin ciki dani".

Shiru tayi tana kallon shi cikin jin tausayin shi,
Shiko ido ya lumshe cikin sanyi yasa hannun shi yana shafe fuskarta tare da gashin kanta hannun yasa ya ƙara jawota jikin shi cikin salon lallashi yasa hunnun shi yana shafa jikinta yana sunsunarta tare da goga sajen shi a kumatun ta,
a hankali ya rinƙa fese mata iska mai sanyi cikin kunnen ta,
hannun shi yarinƙa cusawa cikin rigarta yana yiwa kirjinta wani irin salo mai wuyar faɗuwa yana sunsunar wuyanta yana wani irin numfashi gaba ɗaya ya gigitata ya gigita kanshi,
itama sai sake narkewa take jikin shi tana mika tana ɓoye fuskarta a jikinshi cikin tsananin kunya,
haka suka kasance cikin yanayin rarrashin juna da kyar ta zame jikinta,
ta koma gefe tana gyara rigarta da ya cukuikiye a hankali takai dubanta ga agogon dake manne a palour 12 dai-dai
shiru tayi a wurin tana satan kallon shi yadda
ya kife kanshi a jikin kujerar yana maida numfashi gaba É—aya yayi wani iri,
da kyar itama ta saita kanta a hankali tace,
"Ya Usman tashi ka rakani zan koma cikin gida kar Ammi ta farka taga Farouq baya kusa da ita".
riƙo hannun ta yayi murya na rawa yace,
"a,a dan Allah kibar shi mu kwana anan". miƙewa tayi tana girgiza kai,
"a,a gaskiya nidai tafiya zanyi wallahi ni kunya nakeji bazan iya kwana anan ba".
Shima miƙewa yayi ya kamo hannun ta ya lonƙoso kai yace,
"Ki taimaka min habibty zan shiga wani hali in kika barni cikin wannan yana yin ina buƙatarki kusa dani,
ki kaishi saiki dawo in kinga kowa yayi bacci kinji plssss".
Dakai ta amsa mai alamar "Toh".
dan ya Usman yana bata tausayi kuma tana tsoron karta kuma irin kuskuren da tayi a baya A hankali ta É—auki Farouq É—in ta fita kai tsaye ta wuce É—akin su inda ta samu tuni Ammi tayi bacci.

Kwantar dashi tayi akan gado a kusa da Ammin,
sannan taje tayo wanka tashafe jikinta da turaruka masu ƙamshi da sanyaya zuciya sai kuma
itama tazo ta kwanta gefen shi,
Addu'a tayi ta tofa mashi ta tofe kanta sannan ta kwanta tajanyo wayarta ta buÉ—e data dan taga ya Usman nata kiranta kuma bata son É—agawa kar Ammi ta tashi,
tana buÉ—e datan
saƙon shi ta gani,

"ina jiranki a kofar Nanne ki fito mutafi kinga kowa yayi bacci".

Amsa tamaida mai,

"kayi haƙuri kaje ka kwanta saida safe".

"gaskiya bazan iya baccin ba kizo ki taimaka min in kuma bakizo ba kuka zanyi tayi har gari ya waye, daman ni nasani ba mai sona sai Hammana".

Jiki na rawa ta kashe wayar gaba ɗaya ta lallaɓa dan kar Ammi tafarka ta fice,
a bakin ƙofar palour ta taddashi tana fita yasa hannu ya ɗauketa cak ya ruggume ta a jikin shi,
bai sauketa ko inaba sai sai akan gadon shi,
A hankali ya kontar da ita cikin wani irin yanayi ya konta gefenta a hankali ya jawota jikin shi yana maida numfashi hannun shi ya cusa cikin rigar baccin jikin ta yana mata wani irin salo mai taɓa zuciya a hankali yake sarrafata da salo mai cike da so da ƙauna haɗe bakinsu guri guda yayi yana mata wani irin tattausan kiss,
hannun shi nakan kirjin ta yana murzawa dukkansu sun rikice sunyi nisa cikin duniyar masoya a haka sukai ta fama har bacci ya É—aukesu suna ruggume da juna cikin happy.

A zabure Ummu ta farka,
aiko tare suka mike yana daÉ—a matseta kamar zaa kwace mai ita,
"Ya Usman kabarni intafi kafin kowa ya farka kaga an fara kiran salla ".
Wani irin kallo yake mata kamar zai haÉ—iye ta baice komaiba ya saketa,
dasauri ta fice bayanta yabi da kallo badan yasoba banÉ—aki yashiga yayi wanka sannan ya fito ya fara nafilillin shi.
Chapter 69 · 0% Book details