Sashe 19
Rubutaccen Alamari Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Daga nan kuma sai ta mik'e ta fice ta nufi part d'in Abban ta,
ita kuwa Ummul kuka take da bak'in ciki mai yawa a ranta a fili take gani duk an tsaneta tunda babu ko mai lallashin ta inba Ya Usman ba kowa harara ke had'a su ganin yadda su Anty Shuwa ke cilla mata harara yasa ta mik'e cikin kukan ta nufi part d'in Hajjajo,
a parlour ta samu su Hamma Umar d'in da ya Usman dasu Hajjajon da Ammin su,
har yanzu Hamma Umar kanshi na kife kan cinyar Ammin yana kuka k'asa-k'asa dan gaba d'aya jikin shi da zuciyar shi Abban shi kawai suke tuno mishi a yau d'in,
shi kuwa Usman kukan Hamma Umar ne yake sashi kukan,
itama Ammi ta kasa d'aure zuciyar ta sai k'ollah dake ta bin fuskar ta,
itama Ummul nata kukan take ta wuce bedroom d'in Hajjajo kai tsaye kan gadon ta konta ta kife kanta cikin pillow taci gaba da kuka,
ita kuwa Anty Halima a baki k'ofar parlour Abba tayi sallama cikin muryar kuka,
cikin sanyi ta shiga bayan Abba ya amsa mata sallamar , Abban ta samu shida Daddy suna zaune sai fufun goro kusan guda 12 da katon-katon na sweet da k'oren dabino dake gaban su,
gefen Abban nata taje ta zauna cikin sanyi ta gaida su sai kuma ta fara magana cikin raunin murya tace.
"Abba Hamma Umar!
Abba Hamma Umar da ya Usman sunata kuka sun tuno Abban su,
Abba Hamma Umar ya bani tausayin Ammin suma sai kuka takeyi,
Daddy kuje ku rarrashe su,
Hamma Umar ya bani tausayin yanata kuka ya Usman ma yana kuka."
kusan a tare Abba da Daddy suka mik'e suka fita kai tsaye parlour mahaifi yarsu Hajjajo suka nufa Anty Halima na biye dasu a baya,
suna shiga parlour suka zauna gefen Ammi da yaranta Daddy ne ya jawo hannun Usman cikin kula yace.
"Ya isa kukan ya isa haka habba Usman k'afa san zuciyar ka bata da cikekken lafiya."
A hankali Usman ya kalli Daddy cikin sanyi yace.
"Daddy kalli yadda Hamma Umar yake kuka ,
hawaye na bazasu bar zuba ba muddin idanun Hamma Umar na zubda k'ollah."
Abba ne ya kalli Hamma Umar d'in cikin sanyi yace.
"Farouq Kaine nake ganin kana da k'arfin zuciya sai gashi ka k'asa iya daurewa ga yadda kake kuka kalli yadda kukanka yasa d'an uwanka yin kuka kalli mahaifiyarku yadda kuka sata a rud'ani,
shin ka manta zuciyar d'an uwanka ne?
Farouq a yanzu ba abinda mahafinku keso daga gareku da mu da mahaifiyar mu sai Addu'armu."
da sauri yasa hannu ya share hawaye shi cikin k'arfafa zuciyar shi yace.
"Abba na bari,
Usman kayi hak'uri ka koyi dauriya kajiko d'an uwana?."
Kai Usman ya rink'a juyawa tare da goge k'ollah,
daga nan su Abba sukayi ta musu nasiha sannan suka fita tare dasu dan jin an kira sallan maggariba,
har sun fita gaba d'ayan su ,
sai kuma ya Usman ya juyo cikin sanyi ya shiga d'akin Hajjajo kai tsaye bak'in gadon da Ummul ke zaune yaje ya zauna cikin sanyi ya zaro hankicif d'in shi ya mik'a mata,
bata karb'a ba sai d'ago kanta tayi ta zuba mishi ido cikin kuka tace.
"ya Usman shike nan Hamma Umar zai rabani da Mustapha har *Abadan* shike nan nayi ban kwana da farin cikina,
ya Usman kalli al'k'awarin da Hamma Umar yayi dan tsabar mugunta ya Usman shike nan Hamma Umar ya zame min k'arfen k'afa Ya Usman kasan ina son Mustapha gashi Hamma Umar ya rabamu gashi Abba na ya kwace woyata shike nan ya Usman ko muryar Mustapha baza a barni Mayo ba,
ya Usman Hamma Umar ya binne min rayuwa ba Mustapha ba karatu na."
sai kuma taci gaba da kuka,
shi kuwa Usman ido ya tsura mata ,
sannan ya d'ago hannun shi ya dafe kahon zuciyar shi cikin tsura mata ido yace.
"Ummul kece sanadin bugawar zuciyata zaki kasheni ki huta ki sani idan na mutu kece sila."
cikin tsoro da mamaki ta zaro ido woje baki na rawa tace.
"Ya Usman ni kuma? ni dai? in kasheka kuma? sabida me zan kasheka?."
Kai ya jinjina mata cikin sanyi yace.
"Ehh kasheni kike son yi tunda na lura bazaki bar koke-koken nan ba,
na kuma gaya miki bana son inji kina kuka,
Kukan ki nasa zuciya ta tayi nauyi bana son kina kira min sunan Mustapha in kina ki ranshi ji nake zuciya tana harbawa da k'arfi, kamar zata fashe."
da sauri tasa hannu ta karb'i hankicif d'in sannan ta goge k'ollah cikin rawan murya tace.
"Nayi shiru ya Usman na bar kukan ,
bana son ka mutu."
Murmushi yayi sannan yace.
"Allah ya d'aiyiba."
itama murmushi tayi sannan tace.
"Ina sonka ya Usman."
cije lips d'in shi yayi da k'arfi sannan ya juya cikin sauri yayi hanyar fita har yaje bak'in k'ofar fita sai kuma ya tsaya cikin sanyi yace.
"Allah ya d'aiyiba,
nima ina sooon ki k'anwata Ummul."
daga nan kuma sai ya fita,
part d'in su ya nufa yana zuwa ya samu abokan Hamma Umar d'in duk sunyi al'wala shima al'walan yayi sannan suka nufi masallaci,
bayan sunyi sallan maggariba basu dawo ba saida akayi sallan ishah sannan suka dawo gidan.
9:00 pm Hamma Umar ne da abo kanshi suke ta hira a parlour shi hira sukayi sosai cikin shak'uwa da sabo Abdallahn Maryam ne yayi murmushi cikin tsokana ya kalli Hamma Haiydar din Minali yace.
"Kai General Aliyu wai ina Hamma Yusuf d'in Aysha ne ban ganshi ba?."
Amadin Nadiya ne yayi murmushi tare da cewa.
"You ai Hamma Mahmoud d'in Khadija ma ban ganshi ba."
Salim d'in Tawa ne yayi murmushi tare da cewa.
"Toh sa idawa."
Abun batul kuwa murmushi yayi sannan yace.
"Mutun da matar sa ai sai adena sa musu ido."
Hamma Bashir d'in Rukayya ne yayi murmushi tare da nuna Hamma Hassan d'in Fateema yace.
"Kaima ko zaka zillene kayi gaba da matar ka?."
Hamma Haiydar d'in Meenarl ne ya d'an yi murmushi sannan yace.
"Kai Aisar d'in Bintu sai dariya kawai kake kuma kaima anjima za'a nemeka a rasa zaka tafi gun matar ka."
Al'ameen d'in Fauziyya ya mik'e cikin raha yace .
"Nima nayi gaba."
Ridwan d'in Zakiya kuwa shima sai murmushi yake yana woya da zakiyarsa Ahmad ana Muslim kuma shima dariya kawai yake.
Suna cikin hira da dariyar su Hamma Yusuf ya shigo hannun shi rik'e da robobin inabi dasu Apple da reke sai kwakwa da dibino,
ajiye su yayi a tsaki yarsu ya zauna gefen Abuturrab cikin murmushi ya kalli Aisar yace.
"Ga inabi nan kusha ,
Aysha ce ta kirani tace in seyo mata shine kuma na kawo muku ku d'ana."
dariya sosai Abban Rukky pinky yayi yace.
"Aysha ta kiraka ko kai ka kirata."
murmushi Hamma Umar d'in Ummul yayi tare da cewa,
" Ku dai kuci kar kuyi tone -tone."
dariya sukayi baki d'ayan su sannan sukaci gaba da hirarsu,
suna hira suna cin lodin fruits din da Hamma Yusuf ya kawo musu,
can sai kuma Hamma Umar d'in ya mike cikin sauri Key din motar Aisar ya zara sannan ya fice da sauri yana fita yaje ya lodowa Ummul fruits d'in da yacin gaba d'aya sannan ya dawo gida,
Parlour nashi ya shiga inda ya samu su Abu har yanzu suna hira,
Amadi ne ya kalleshi cikin tsokana yace.
"Kaima Ummul tayi kira ne kaje ko?."
murmushi kawai Hamma Umar d'in yayi tare da juya kai sannan ya zaro woyar shi auta Aliyu ya kira,
Jim kad'an Aliyu ya shigo rik'e da hannun Hannah yarin yar Hamma Haiydar da Meenarl,
robobin fruits d'in Hamma Umar ya mik'a wa Aliyu cikin yana yin aike yace.
"Gashi ka kaiwa Ummul kace abokin nane ya seyo mana mukaci shiyasa itama na seyo mata nata."
"Toh" Aliyu yace sannan ya karb'i robobin yayi cikin gida,
kai tsaye parlour Hajjajo ya nufa, yana zuwa ko ya samu Ummul d'in tana zaune fuska duk a jeme ,
a hankali ya ajiye mata fruits d'in cikin kula yace.
"Anty Ummul sarkin son zak'i gashi wai inji Hamma Umar wai abokin shi ne ya seyo sukaci shine kema ya seyo miki naki."
ido ta d'ago cikin tsuke fuska ta buga mishi harara sannan tace .
"Bana so ka meyar mai da abunshi."
Kallon ta yayi cikin sanyi yace.
"Kai Anty Ummul kinfa san ba kyau meda hannun kyauta."
K'afa tasa ta ture robobin,
Shi kuwa Aliyu hannu yasa ya d'auki robaa inabi guda d'aya ya fice tare da cewa.
" ni dai zanci."
Hajjajo kuwa tire ta d'auko ta tattara fruits d'in duka ta lodasu kan tiren cikin yin hamdala ,
ta rink'a nuna wa mutane tana cewa.
"Ku gani Ku shida Farouq ya fara cika al'k'awarin d'aya d'aukar wa kanshi."
suko sauran mata sai sunyi ta yabawa halin Hamma Umar d'in,
ita kuwa Ummul ji take kamar taje ta shak'e shi ya mutu ta huta da bak'in cikin sa,
kamar wasa Hajjajo ta dage tana bin d'aki-d'aki tana nuna musu abinda Umar ya aiko wa Ummul harsu abba sai da taje ta nuna musu,
Ummul kuwa haka ta kwana cikin k'unci shiko Hamma Umar yana tare da abokan shi..