Sashe 5
Rubutaccen Alamari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Cikin takaici Nenne tace.
"Ehh tafiya tayi mana tunda bata gidan nan tun dazu nake kiranta ban jita ba,
gacan kitchen d'in kuma ba abinda ta tsinana."
Hajjajo ce tayi tsaki dan ko ita bata san Ummul na cikin d'akin nata ba,
cikin mita irin ta tsofaffi tace.
"Wannan yarin ya akwai lalaci da k'in aiki,
fisabillahi yanzu a haka za aurar da ita a kaiwa wani yayi ta famar yi mata bauta."
Wani dogon tsaki Hamma Umar d'in ya ja,
sosai yakejin zafin rashin jin maganar ta.
Ita kuwa Ummul tuni ta fara had'a zufa dan tun dazu take son fita jin Hamma Umar d'in a parlour Hajjajo ya hanata fita,
gashi yanzu kuma tanaji Nenne ta kawo kararta gun shi dama ya lafiyar kura a dawa bare an tab'oshi,
hannu ta yarfa cikin sanyi da rawan murya tace.
"Nenne nifa gani nan ba inda naje fa,
kuma wallahi zanyi girkin."
A hatsale Nenne tace.
"Toh me kikeyi a cikin d'akin da kika kasa fitowa?,
me kike aika tawa?
wato ke har kullum indai batun aiki ne sai kin b'ata min rai ko?."
Taku ta farayi a hankali tana fitowa parlour murya a hankali tace.
"Ayyah Nenne kiyi hak'uri wallahi zanyi aikin yanzu zan gama."
Hajjajo kam salati ta rink'a yi tana tafa hannu cikin mamaki tace.
"Ke takwarata yanzu yaushe kika shigo ban ganki ba? kuma uwar me kikeyi a d'akin?."
Baki ta d'an tura cikin kallon kakar tasu tace.
"Wani abu nake yi."
Harara Nenne ta watsa mata cikin jin haushi tace.
"Bar min aikina zanje nayi abina,
ki zauna nan ki gayawa Hamman ku dalilin ki na k'in yin aikin."
Tana kaiwa nan ta fice part d'inta ta koma
kai tsaye kitchen ta wuce ta fara aikin ta cikin sauri da tsanaki.
Shi kuwa Hamma Umar tunda Ummul ta fito bai kalli inda take ba har Nenne ta fice ,
yana komce kan 3 str sai y'ar k'aramar k'orya da ke gaban shi mai cike da kindirmo mai kyau fari tas,
konce yake rigin gine sai laptop d'in shi dake kan ruwan cikin sa ya hard'e k'afafun shi.
Ita kuwa Ummul cikin tsarguwa ta tsuguna gefen shi kad'an tayi k'asa da kanta tana d'an satan kallon shi,
Hajjajo kuwa mik'ewa tayi ta kalli Hamma Umar d'in cikin kula tace.
"In dama maka da furane? ko insa maka dakkere ne?."
Baiyi magana ba sai lumshe
ido yayi,
ita kuwa ganin haka ta shige d'aya d'akin ta fara dama mishi da fura.
Shiru parlour su duka biyu ba wanda yayi magana har zuwa wani lokacin ganin haka Ummul ta gyara durk'usuwan da tayi don guiwowin ta sun fara tsami,
fuska ta marairaice ta lokk'oshe kanta a kafad'ar ta tai rau-rau da ido murya can k'asa tace.
" Hamma kayi hak'uri wallahi bazan sake ba".
Shiru bai kula taba,
itama shirun tayi dan ta sani da ta k'ara magana toh ta k'ara laifine dan zaice ta cika mishi kunne da hayani yarta."
Haka yasa kawai sai ta rink'a jujjuya guiwowinta dan sun tara jini,
gashi ta fara jin ciwon marar da yake mata duk wata,
haka yasa ta fara zubda k'ollah tana d'an gogewa da tafin hannun ta,
murya na rawa tace.
"Hamma kayi hak'uri."
Sai yanzu ya bud'e idanun shi a hatsale yace.
"Uban me ya hana ki yin aikin?,
wacce tsiyar kike aika tawa a cikin d'akin tun da safe?."
Baki na rawa ta d'an matsa baya a hankali tace.
"Hamma har na fara aikin fa,
sai Mustapha ya kirani shine na zo nan d'in."
Daga koncen yasa bayan hannushi ya yarfa mata mari da bayan hannun nashi,
sannan ya tashi zaune ido ya kafa mata tare da cewa.
"Amsa kiran Mustapha yafi aikin da zaki yiwa mahaifiyar ki ko?."
Kai ta rink'a juyawa cikin toshe bak'in ta dan karta saki kuka,
tana juya kai tace.
"Kayi hak'uri Hamma bazan k'ara ba."
Tashi yayi ya mik'e fuska a murtuk'e ya watsa mata harara tare da cewa.
"Mik'e kije kiyi aikin kar in b'ab'b'allaki fitinenniya kawai mara jin magana."
Da sauri ta fice tana zubda k'ollah tare da k'uk'k'ini k'asa-k'asa kai tsaye kitchen d'in ta shiga.
tana zuwa tace.
"Ayyah Nenne kiyi hak'uri'
ki kawo aikin zan k'arasa."
Rai a d'an had'e tace.
"Je kici gaba da baccin ki,
nayi aiki na,
in bakiyi na gidan kuba ai zakiyi na gidan miji inda ko godiya baza'ayi miki ba."
Haka Nenne tayi ta mata fad'a har suka gama aikin,
itako tana bata hak'uri,
Shi kuwa Hamma Umar nonon ya karb'a sannan ya koma part d'insu.
Nenne kuwa suna gama aikin rana taje tayi wonka ta kimtsa d'akin Abba dan yau zai shigo potiskum d'in,
haka yasa ta barwa Ummul sauran aiyu kan girkin dere da kuma abincin Usman da ban.
Su ya Adam kuwa da ya Sadiq da Aliyu duk suna tare a parlour Nenne suna kan dinning table suna cin abinci.
Aikin take yi cikin k'arfin halin dan ciwon da mararta keyi ya fara yawa sai ta shiga kitchen d'in ta d'an yi aikin in matar ta murd'a sai ta dawo parlour ta konta kan kujera tayi ta murk'ususu sai tayi jigib da zufa dan azaba.
Shi kuwa Aliyu duk abin da take yi hankalin shi na kanta,
dan yana matukar son yar uwarshi haka yasa yana lura da yadda take zuwa ta kontan .
8:00 pm Abba ya iso gida cikin family d'in shi su ya Adam da ya sadik duk suka nufi part d'in Hajjajo suna zuwa suka tsame shi shida Hussain in shi wato Daddy suna ta hira da dariya Hajjajo
na zaune a tsakiyar su Hamma Umar kuma yana gaban su Abban kanshi a sunkuye yana zaune tsakiyar k'annen mahaifin shi,
Abba ne ya kalleshi cikin kula yace.
"Farouq ya ina k'annen naka? ban gansu ba."
Ya d'ago kanshi zaiyi magana kenan su Adam suka shigo cikin girmamawa suka gaidasu sannan suka zauna sukaci gaba da hira,
kallon Hamma Umar Abba ya kumayi tare da cewa.
"Usman da ummul fa ina suke?."
Aliyu ne yayi carab yace.
"Abba Anty Ummul bata da lafiya tun d'azu kuka takeyi,
ya Usman kuma yanzu ya dawo bai shigo ba tukun."
Daddy ne ya kalli Hamma Umar d'in cikin yana yin tabbaya yace.
"Farouq meke damun Ummul d'in.?"
Kai ya sunkuyar a hankali yace.
"Daddy ni ban san bata da lafiya bama sai yanzu."
Nenne ya kuma kalla a hankali yace.
"Nenne meke damun ta.?"
Fuska ta d'an tab'e cikin kula tace.
"Hmmm Umar kafa san Ummul da raki tun bayan sallan magariba take kuka wai cikin da mararta ke ciwo ko tashi tak'i tayi wai bazata iya ba."
Cikin mamaki Abba yace kai Khadija mamana bata da lafiya kice raki ,
duk rakin Ummul indai taji na dawo toh zata zo tamin sannu da zuwa ,
tunda kikaga har ta k'asa tashi toh gaskiya tana jin jiki."
Hajjajo tace.
"Gaskiya kam gwara a dubata."
Daddy ne ya kalli Hamma Umar din cikin bada umurni yace.
"A gaskiya bata da lafiyan ne,
Farouq kaje ka dubata."
"Toh" yace tare da mik'ewa ya fita a ranshi yana cewa.
"Mara lafiya ke zuwa gun doctor ita kuma uwar sakalci da raki doctor ne zaije ya sameta dan tsabar samun sake."
A tsakar gida ya had'u da Usman murmushi Usman d'in yayi tare da sosa k'eya yace.
"Hamma tun d'azu fa na dawo,
yanzu sai naci abinci zanzo insha maganin."
Kafeshi yayi da ido cikin k'aunar k'anin nashi da tausaya mishi,
hannu yasa ya d'an bugi k'eyarsa tare da matse kunnenshi yana.
"Usman baka jin magana ,
baka kula da lafiyar ka,
baka jin tsoron da nake ji akan ciwon nan naka."
Shi kuwa Usman d'an kara ya saki tare da cewa.
"Wayyo Abba na Daddy kuzo Hamma na zai tsinke min kunne."
Abba ne yayi dariya jin muryar Usman yace.
"Da ka iso wuri ko ido bai ganka ba kunne zai shaida zuwan ka Usmanu shehu sarkin barkwanci shi kowa kakan sa ne."
Daddy ne yayi murmushi tare da cewa.
"Usman kenan shi shiya d'auki halin Baban mu komu y'ay'anshi bamuyi irin yanayin shi ba kamar yadda Usman yayi. ,
shiko Farouq koman shi. na Yaya Ibrahim ne har tausayin shi da kulawan shi a kan k'annenshi."
Usman kuwa dariya ya rink'a yi yana juyawa Hamma Umar na binshi da ido yana kallon yadda k'anin nashi ke harkokin sa tamkar baisan ciwon da ke jikin shiba.
A haka ya wuce ya nufi parlour Nenne,
shi kuma Usman ya tafi gunsu Abba yana zuwa.
Ya gaida su sannan ya kalli Aliyu cikin murmushi yace.
"Kai Auta ina Ummul ban ganta ba?."
Hajjajo ce ta kalleshi tare da cewa.
"Bata da lafiya mai baka duk abinci da kake so kaci d'in,
yau anan zakaci abinci."
Cikin zillewa zancen yace.
"Ni duk abinda doctors suka hanani bana cin karki wani had'ani da su Abba,
kuma ko Nenne ma shaida ce bana cin komai matuk'ar dai green ne,
dan haka karma kiyiwa Ummul lak'el kice ita ke bani komai naci,
kowa yasan ina bin doka."
Aliyu ne yayi carab yace.
"A a kam ya Usman wallahi ko jiya kaci miyar ganye."
Kai ya sunkuyar yana murmushi ganin yadda Abba da Daddy suka tsareshi da ido cikin tsoro Daddy yace.
"Usman meyasa baka kiyaye lafiyar ka Usman ka rufa mana asiri kake bin dokokin doctors ko zamu samu ka rabu da ciwon nan."
Murmushi yayi cikin k'arfin guiwa ya kalli Abba da gaba d'aya ya karaya jikin shi yayi sanyi hannun Abban dana Daddy ya d'an rik'e a hankalin yace.
"Cuta ba itace mutuwa ba ,
lafiya kuma bata hana mutuwa nasan abinda kuke tsoro,
ba haushe yace,
nisan kwana maganin annoba,
karku damu yanzu nayi lafiya jin zuciya ta nake kamar ta k'arfe."
Murmushi su duka sukayi tare da sauk'e ajiyan zuciya sannan sukaci gaba da hirar.