← Book details Rubutaccen Alamari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 77

Sashe 46

Rubutaccen Alamari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A gida kuwa Hamma Umar d'in yana fita,
itako ta koma ta zauna kan kujera,
shiko Ya Sadik shiru yayi a kitchen d'in har saida yaji tashin motar Hamma Umar d'in yana jin ya fita gidan,
shima ya fito parlour Ammin kai tsaye gaban Ummul ya tsaya hannu yasa ya kamo nata
ya tsaida ta,
itako da take lumshe da ido jin an d'agota ta bud'e ido cikin firgici baki na rawa tace,
"y...! ya....! ya.. yaya Sadik".
k'ara ta cilla da k'arfi tare da dafe kuncinta dan jin wani irin gigitaccen marin da Sadik d'in ya sakar mata,
shi kuwa da iya k'arfin sa ya rink'a zuba mata maruka a jere a jere ba k'ak'k'autawa marinta yake cikin fushi da jin haushinta yama manta tana da ciki ji yake kamar ya karya ta,
tuni ya fasa mata baki,
itako sai kuka take tana kiran ,
"Wayyo ya Sadik kayi hak'uri wallahi bazan sakeba wayyo Hamma Umar ka tafi ka barni zasu kasheni wayyo Nenne na wayyo Abba na wayyo ya Usman ".
haka ta rink'a kuka da kururuwa ba wanda yayi yunk'urin k'arbarta sai da sukaji kukan yayi yawane suka fito duk sukazo,
ganin marinta kawai Sadik keyi sannan ya gaya musu abinda yaji tana gayawa Hamma Umar hakan yasa gaba d'aya suka k'i kwatarta,
sai Adam ma daya k'ara zuba mata maruka duk aka resa mai karb'arta a gidan Usman ma sosai yaji zafin yadda take nuna bata son d'an uwan nashi,
shiko Sadik mammaketa yayi har saida fuskarta ta kumbura tayi jazir,
sannan ya barta Abba ma yazo yayi ta fad'a kamar zai ari baki Nenne kuwa fushi tayi da ita tak'i ta kulata,
Usman ma fushin yayi da ita,
haka ta wuni a wannan ranar cikin kuka da k'unci ga zazzab'i mai zafi ga ciwan kai gaba d'aya ta jeme tak'i taci komai tak'i tasha komai sai kuka har muryarta ta disashe hatta cikin nata saida ya yayi k'asa motsinshi ya d'an ragu,
hajjajo ce mai d'an bata abinci duk da itama fushin take da ita a haka ta kwana har washe gari har zuwa yamma bataci komaiba duk gidan sun juya mata baya hatta Aliyu fushi yake da ita.

Shiko Hamma Umar a Abuja tunda sukaje bai samu sukuni ba haka yasa bai kirasuba sai dare daya kira Kuma sai akace Ummul tayi bacci hakan yasa basu gaisa ba koda gari ya waye ya kira duk woyoyin gidan basa shiga,
haka yasa suna dawowa ko gidanshi bai komaba ya kama hanyar potiskum d'in,
yana shiga cikin garin sai kuma yaji kewar Ammin shi da begen son ganin ta hakan yasa ya nufi gidan Ammin yana zuwa ya samesu ita da Inna da uncle ensu suna tsakiyar gidan suna ta hira,
kamar ko yaushe gaban ta ya zauna ya tonk'oshe k'afafun shi sannan ya cire hular kanshi,
itako Ammin ido ta tsura mai cikin murmushi da Happy tasa hannun ta kan gashin kanshi murya cike da k'auna tace,
"Allah yayi maka Albarka Allah ya tsaremin kai da d'an Uwanka Allah ya sanya alkhairi a rayuwarku ubangiji yayi muku rahama duniya da lahira".
Murmushi yayi cikin jin dadi yasa hannun shi ya dafa hannun ta dake kanshi yace,
"Amin Amin Ameeeeeeeeeeeeeeeen ya rabbil izzati Ammina".
sai kuma ya juya ya Kalli Uncle en cikin girmamawa yace,
"Uncle ina wuni ya gida".
"Lafiya lau Farouq ya hanya yanzu Ammin ka ke cemin jiya kazo ka sallameta zaka tafi Abuja".
"Alhamdulillah".
yace da uncle d'in sannan ya kalli Inna yace,
"sarkin surutu yau ya naganki shiru ko dan banzo da ogan naki bane".
dariya tayi sannan tace,
"ai kaima oganane".
kallonta yayi a hankali yace,
"kin Kama gaibu gwara miki Usmanun ki".
dariya sukayi duka shiko Hamma murmushi yayi sannan ya kamo hannun Ammin shi yace,
"Ammina farcenki ya d'an taru bari in yanke miki".
murmushi tayi tace,
"toh Allah ya ma albarka Allah ya tsaftace rayuwarka kamar yadda kake tsabtace min farcena".
"Amin Amin".
ya amsa sannan ya yanke matasu ya kankare mata,
bayan ya gama ne ya kalleta cikin karya wuya yace,
"Ammina yunwa nake ji kuma yau abin cikinki nake son ci".
mik'ewa Ammi tayi da sauri ta nufu kitchen,
abincin ta kawo mai tare da roban wonke hannun,
tuwan farar shinkafa da miyar ganye yasha man shanu da nama,
gaban shi ta ajiye mai a hankali tace,
"matso kaci ka d'ena zama da yunwa bana so".
"toh". yace sannan ya bud'e abincin murmushi yayi yace,
"Tab Ammi ai wannan yamin yawa gsky bazan iya cinyewa ba sai dai in zamuci tare zanfi jin dad'in cin".
murmushi Ammin tayi sannan ta matso sukaci a tare sannan suka dan yi hira Inna da uncle suna ta musu dariya,
sannan ya salla mesu ya tafita,
har yaje kofar gidan ya dawo ya kalli Ammin nashi itama shi take kallo a hankali yace,
"Na manta ban gaya miki ba na kusa na samowa autanki mata muyi mishi aure yafi zaman hakan matar zata kulan mana dashi".
murmushi tayi sosai sannan tace,
" toh Allah sanya Al,khairi".
"Amin Amin Ammina kiyiwa k'anina fad'a ya rink'a kula da kanshi".
"toh zan mishi kaima ka mishi ".
A haka suka sallami juna,
yana fita kai tsaye gidan Abban ya nufa.

Bayan yayi parking kai tsaye ya kutsa cikin gidan parlour Nenne ya wuce inda ya samu ba kowa har zai juya ya fita sai yaji sautin kukan Ummul a cikin bedroom d'in,
da sauri ya Koma cikin d'akin kan gado ya hangota konce tana ta rawan sanyi da kuka,
cikin sauri da furgici ya k'aroso gabanta hannu yasa ya d'agota ruggumeta yayi cikin kad'uwa yace,
"Khairi! Khairi na meke damun ki? Ina Nennen? ya gidan shiru basa nanne? ".
ruggumeshi tayi cikin kuka ta d'ago kanta,
da sauri ya tallabe kanta cikin tsoro yace,
"meya samu fuskarki inasu Nennen? ".
cikin kuka da tausayawa kanta ta, kwashe labarin abinda sukayi mata ta gaya mishi ta k'ara da cewa,
"Nenne ma bata min magana Abba ma fushi yakeyi dani ko Aliyu sun hanashi yamin manana ya Usman ma fushi yake dani duk basa sona basa zama kusa dani yanzu duk suna parlour Hajjajo".
hannun ta ya kamo cikin tsananin bak'in ciki da takaici waje ya fito da ita kai tsaye part d'in Hajjajo ya nufa da ita,
kicinb'is sukayi da ya Sadik a tsakiyar gidan,
yana ganin Sadik d'in yaja hannun Ummul d'in ya tsaya a gaban Sadik d'in cikin tarin bak'in ciki murya na rawa idanunshi sunyi jazir sai shek'in hawaye yakeyi cikin fad'a da d'aga murya yace,
"Zo nan".
jin muryarshi yasa gaba d'aya mutanen gidan suka firfito tsakiyar gidan dan basuma san ya dawoba,
shiko ido ya zuba musu d'aya bayan d'aya cikin rawan murya da fad'a yace,
"Sadik amman dai dama can haushina Kake ji ko? bazaka iya duka na bane shiyasa kai ma Ummul duka dan ka huce a kanta ko? ".
Gaba d'aya shiru sukayi ganin yadda jikin shi ke rawa dan basu tab'a ganin wannan bacin ran a fuskar shiba,
shi kuwa cikin fad'a yaja hannun Ummul zuwa gaban Adam baki na rawa yace,
"Adam ka tsani Ummul ko meyasa baza kayi min adalci da kawaici ba ka tsane ni shiyasa ka tsani Ummul tunda aka Aura minta ko?".
shi kam Adam da Sadik sai jujjuya kai sukeyi alamar a, a,
shiko k'ara jawo hannun Ummul d'in yayi zuwa gaban Nenne cikin rawan murya da k'ok'arin maida hawayen shi yace,
"Nenne ki rink'a ganina a jikin Ummul na tabbata a ko wanne hali kike zaki kulanmin da Ummul Nenne ya za'ayi kina ji kina gani a doki mutun hud'u Nenne Ummul a gareta Ammina a gareta d'an Uwana Usman a gareta d'ana da zata haifa a gareta ni kaina".
Nenne kam kasa cewa komai tayi.

shiko jawo Ummul d'in yayi gaban Abba dake tsaye a k'ofar parlour shi suka durk'usa cikin rauni da karya wuya yace,
"Abba kayi hak'uri abin ne yayi yawa gara in fad'a musu yadda nake ji in sun tozarta ta,
Abba nasan sonane yajanyo kai watsi da Ummul,
Ayyah Abba in dai soyayya tace to na rok'ek'a dan Allah ka kulanmin da ita ka hana su Adam dukan ta Abba kallifa da tsohon cikin nan suka daketa in sun mata illafa me zasu cemin".

ita kanta Ummul yau ta fara gano wani irin son da Hamma Umar ke mata hakan yasa ta cika da mamaki ziryan.

Shiko Hamma k'ara jawo hannun Ummul yayi ya tsaya a gaban Usman, cikin tuhuma ya kafe Usman da idanu sai kuma hawaye car-car na bin fuskarsa,
murya na rawa cikin kuka yace,
"Ashe Usman bazaka iya kula da iya lainaba in bana nan ?
Usman ashe baka damu da abinda ni d'an uwanka nake soba? shin in ban barmaka amanar Ummul ba wa zan barwa amanarta a wannan duniyar?,
wallahi wallahi bazan yafewa duk wanda ya takura min itaba hankalina bazai kwantaba,
Usman hakan yana nufun
kenan in nayi tafiya zatasha wuya a gaban ka?."
kai Usman ya rink'a kad'awa cikin kuka da tashin hankalin ganin yasa Hamman shi kuka cur-cur shima kukan ya rink'ayi yana matsowa jikin Umar d'in dan wani irin suka da zuciyarshi tayi a take jikin shi ya rink'a rawa,
shiko Hamma Umar kamo hannun Ummul din yayi yace,
"Khairi na mu tafi kai kuma Aliyu azatona ko kowa zai juyawa Ummul baya ai kai abokin kukanta ne dole ka lallasheta in kana son inji dad'i,
Nenne wallahi gata d'aya zakumin inji dad'i ku kulanmin da Ummul in bananan Adam! Usman! Sadik! wallahi da kunsan yadda nake ji a kan Ummul da ko hararta baza kuyi ba".
sai kuma yaja hannun ta ya nufi harabar gidan da ita tare da ce musu,
"Adam! Usman! Sadik! kuci gaba zata dawo in yaso saiku kashemin ita ku huta".
sannan yaja hannun ta suka fice
suko gaba d'aya bayanshi sukabi da sauri Usman yana kuka har jikin shi na rawa yace,
"Ayyah Hamma Umar kayi hak'uri ba hannuna a dukan Ummul Hamma bazan sake barin ayi mata komaiba kar kayi fushi dani d'an uwana ."
Chapter 46 · 0% Book details