← Book details Rubutaccen Alamari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 77

Sashe 73

Rubutaccen Alamari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hankali Ummul take buÉ—e idonta har suka gama buÉ—ewa idon ta k'urawa sumar kan Usman daya fara bacci, tausayin shi ne ya kamata sosai dan tabbas tasan ya Usman yana sonta gashi ita kuwa ta kasa sakarmai jikinta ta sama mai nitsuwa yana bata tausayi dan ya resa mai kula dashi na hak'ik'a ido ta lumshe a ranta take fad'in,
"Zan kula da kai kamar yadda nasan Hamma Umar nason a kula da kai zan saka cikin farin ciki kamar yadda d'an uwanka yake fatan ya ganka cikin farin ciki".
hannunta ta cusa cikin sumar kan nashi tana murzawa tare da mishi salon lallashi a hankali tana shafawa,
kamar a mafarki yaji kamar ana mai susa É—ago hannun shi yayi yakai kan sumar tashi hannu Ummul yaji dan haka yayi sauri É—ago kanshi sukayi tozali da ita,
A hankali ta sakar mai murmushi tana d'an lumshe ido,
Hannu yasa ya shafi fuskarta sannan ya d'an taso ya sunkuyo kanta ya haÉ—a goshinsu guri guda harshe yasa ya d'an laso lips enta a hankali yace,
"Hubby karki sake min haka please zuciya ta zata buga in mutufa". Girgiza mai kai tayi sannan tafara magana da saida ya matso da kunnen shi kusa da bakinta sannan yaji abinda take cewa,
"Ya Usman Insha Allah bazaka mutu ka barni cikin maraici biyu ba bazaka mutuba ina sonka zamu rayu tare mu bawa Farouq tarbiya da kanmu ya Usman ina sonka har abadan bazan sake yin rowar kalmar soba zan dauwama ina cema ina sonka'
mutafi gida na samu lafiya ka kontar da hankalin ka mu koma gida na kula da farin cikin ka kaji?".
Lonk'oso kai yayi cikin lallashi da jin dad'i yace,
"Kiyi hak'uri likitan zai dubaki yace inkin tashi nayi mishi magana kinga sai muji ya zaice karki damu Ummu na zamu koma Insha Allah muna tare".
Kai ta gyad'a mai shiko ya sumbaci bakinta ya fita,
tare suka shigo da likitan ya sake duddubata sannan yasake jan kunnensu kan ɓacin ranta sannan yabasu damar tafiya gida.

Yau kwanan su biyu da dawowa asibiti Ummul ta k'ara worworewa,
bayan ta fito wonka ne ta zauna gefen gado tana shirin konciya bacci,
Usman ya shigo shima wonka yayi sannan ya kimtsa blanket ya jawo sannan ya juya zai koma parlour,
ido Ummu ta zuba mai tana kallon shi har yaje bakin k'ofar fita tace,
"Ya Usman".
"Na'am".
yace da ita ba tare da yajuyo ya kalleta ba,
ita kuwa keyanshi ta zubawa ido cikin mamakin yadda tun randa suka dawo asibiti ya Usman yake komawa parlour ya kwana a can zuwa yau kuwa abun ya fara soya mata zuciya,
shiko jin shiru batayi magana bane yace,
"lafiya dai ko? ".
shiru tayi tana rau-rau da ido alamar zatayi kuka sai kuma ta daure a hankali ta mik'e tazo bayan shi murya can k'asa tace,

"Ina zaka je? ".

"Parlour zan tafi mana bacci zanyi".

"Nan kuma cikin d'akin ba wurin bacci ne?
ko dai zama kusa da nine baka so? ".
ta k'arishe maganar tana zubda k'ollah,
a hankali ya juyo suna fuskantar juna jin yadda muryarta ke rawa kai ya d'an kawar sannan yace,
"Toh ya zanyi? Ummu ya zanyi da raina dolece take sa nakeyin nesa dake Ummu nifa ba waliyi bane,
kinga dole inbar zama kusa dake tunda in na zauna kusa dake dole na buk'aceki ke kuwa yanzu baki shirya zama da niba toh ya zanyi kinga dole nayi nesa dake".

Jikin shi ta fad'a tare dasa hannunta ta ruggumoshi tana kuka tana juya kai tace,
"Kayi hak'uri ya Usman ka gafar ceni Insha Allah bazan sake irin kuskuren da nayi a baya ba ni na shirya zama da kai".

Ajiyan zuciya ya rink'a sauk'ewa tare da ruggumota a jikin shi cak ya d'ageta sai kan g......

*By*
*GARKUWAR FULANI*

📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*RUBUTACCEN AL,AMARI*

page 3⃣9⃣

*Na*
*AYSHA ALI GARKUWA*

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*MOH ALLAH HOKKI B'URI MOH BABA HOKKI*

*Hahaha 😎😀😜👸🏻 ina kuke ne BAREBARI bayin FULANI toh kuzo ku matso kusa kun san mu FULANI sarakunane masu adalci a gareku toh yau dan haka bisa adalcinmu a matsayi na uwar giyiyarku na Baku kyautar wannan shafi nawa nabakushi gaba d'ayan shi kuyi yadda kukaga dama dashI in kunga dama ku seda wannan shafin ku saro kanwa kud'in😜💃🏻SIRATI SIRTA MOD'O TO SALDORI TAGGA MOD'O babarbare cinna kane tunba wurin idonba💃🏻😜😂 maza kuyi mubaya'a dan GARKUWAR kuce ke gaidaka*

*K*an gado ya direta a hankali ya kontar da ita,
Sannan shima ya haye kan gadon gefenta ya d'an rab'a ya haÉ—e jikin shi da nata wuri guda sai kuma ya rink'a sauk'e ajiyar zuciya yana lumshe ido da furzar da numfashi mai sanyi,
k'arar da wayar shi keyine yasa Ummul lek'a wayar dake kan side drower gadon,
sai kuma taÉ—an zame jikin ta gani baida niyyar ko kallon wayar yasa tayi k'arfin hali murya can k'asa kamar mai rad'a tace, " ya Usman Abbane fa".

Sakinta yayi yasa hannu yaÉ—auko wayar ya koma kan pillow ya kwanta yana sauk'e numfashi sannan yakai idanunshi da suka k'ank'ance kan wayar ganin sunan Adam yasa ya aje wayar yajuyo gareta yana shirun ruggumo ta,
da sauri ta yunk'ura zata gudu shima cikin hamzari ya kamota ya fara mata cakul-kuli yana cewa,
"Daman dan ki gudune yasa kikace Abba ne ko?".
Dariya take har tana shiÉ—ewa tana zulle-zulle tana d'an tureshi,
jin wayar na sake yin ringing yasa ya kyaleta ya É—auki wayar yasa a kunne sallamar da Adam yayi ya amsa sannan dagacan Adam É—in yace,
"Ga su Ammi da Nanne zakuyi magana".
"Uhummmm".
yace a tak'aice sannan yasa wayar a handsfree ya ajiye woyar akan pillow sannan yasa hannu ya tallafo Ummul ya haÉ—ata da jikin shi yana shafata da lumshe ido a hankali yace,
"Nanne na".
Ammi ce ta katse shi dacewa,
"Ina autata Ummu?".
Da sauri cikin happy ta d'an ture kan Usman da yake tsakin wuyanta da kafad'arta yana shak'ar k'amshin cikin d'an d'aga murya tace,
"Gani nan Ammina ina wuni?".
Gaisuwa sukayi harda Aliyu sannan Nanne tace,
"Usman daman matar Mustapha ce ta haihu jiya akayi suna,
tomu bamu jiba sai jiyan Ummie shi ta kira take faÉ—a min ansami Umar Farouq,
Mustapha yayiwa Hamma Umar enku takwara,
jiyan lokaci ya k'ure shine yau zamu je muyi barka gashi Adam da Sadiq sun haÉ—o mana kayan barka zamu tafi yanzu muje muga Umarun mu".
Tana maganar Usman yakai duban shi ga Ummul yaga ta shagwaɓe saura kaɗan tasa kuka,
bakin shi yasa kan nata yai mata kiss sannan ya É—aga yatsan shi yasa kan bakinta yana jujjuya mata kai hannun shi d'aya kuma yana cikin rigarta,
sannan ya amsa da cewa,
"Alhmdulillah, kai amma mungode sosai lallai Mutsapha yayi mana halacci tabbas ya cika d'an uwa musulmi,
ku gaidashi in kunje sosai nima zan kira nayi barka da godiya kafin mu dawo muma muje".
Aliyu ne ya katse maganar sanin halin Ummul zata iya kuka akan maganar yace,
"Aunty Ummu albishirin ki?".
Kamar bazata amsa ba saida Usman yakai hannu zai mata cakul-kuli tayi maza ta rik'e hannu shi tana zaroshi daga kan k'irjin ta a hankali tace,
"goro".
Cikin raha Aliyun yace,
"Bakiga yadda Abba ya gyara ɓangaren ya Usman ba,
yace yanzu yazama na Ammin ki".
tuni ta mik'e zaune tasaki dariya tace, "Haba, Yanzu ta koma can tabar d'akin mu?". Sai kuma ya d'an kad'a kai cikin halin shi na tsokana yace,
"Ina kuma ai badan zamu je unguwa bama da yau zamu rakata zata koma gidan Innar ta itama,
tunda dama ke kika hanata tafiya da shagoɓa,
yanzu kinyi tafiyarki kin mak'alawa miji dad'i kin manta damu,
dan haka itama tafiya zatai".
Adam ne yasa hannu ya É—an bigi kan Aliyun cikin wasa,
Itako harta faÉ—a jikin Ya Usman tana ta tumurmusheshi zata fara halin,
da sauri Usman yace, "kai Aliyu ina wasa dakai ne? zaka samin ita kuka ko?".
Ammin ma cikin Dariya tace,
"Karkiyi kuka Ummuna, babu inda zanje zolayarki yakeyi harma na koma part d'in Usman d'in yanzuma a nan muke,
ai inda kike so nan zan zauna Ummu na sai kun dawo harda Innata zaku tare".
A hankali tasa tafin hannunta ta goge k'ollah dake shirin zubo mata taci gaba da cewa,
"Amma fa idan na tambaya kina yawan kuka kuma bakicin abinci to zan tafi zan koma gun Innata".

Tasowa tayi daga jikin Usman ta sunkuyo kan wayar yayin da ta kife k'irjin ta kan fuskar Usman tace,
"Ammi banayi kuma ina cin abinci da yawa ko?".
Tajuya tana tambayar Usman daya zura hannun sa cikin rigarta yana shafa kirjinta zuwa saman wuyan ta yana ta murza fuskarshi kan k'irjin yanayi yana lumshe ido, murmushi yayi cikin jin dad'i da tsananin shauk'i ya d'an gyad'a kai tare da cewa.
"Ehhhhyyy Ammi ta d'an rege kuka yanzu kam".
cikin jin dad'i Ammin tace,
"Yauwa yarinyar kirki". Ita kuma a shagwaɓe tace,
"Ammi kar kuje da Aliyu gidan Mustapha tunda yana tsokana ta".

Adam ne yasa hannu yaÉ—au wayar sa tare da cewa,
"To sarkin shagwa ɓaɓɓu da sakalci sai anje dashi tunda ba motarki bace".

"ba inda za aje dashi tunda yana tsokano min ita".
cewar Ammi,

Usman ne ya katsesu da cewa,
"Ina Boy ne ban jishi ba?".
Murmushi Adam yayi yace,
"Yatafi daÉ—i mota mana sun fita da Sadiq tun É—azu".
dariya sukayi dukansu
Da haka sukai sallama kowa na cikin jin daÉ—i.

Shiko Usman É—aga Ummul yayi suka shige bayi alwala sukayi sannan suka fito,
ya jasu suka gabatar da sallah nafila raka'a 2 sukai addu'a ya kama kan ta yayi mata addu'a sannan ya cire mata hijabin ya É—auketa cid'ak sai kan gado .
Chapter 73 · 0% Book details