Sashe 70
Rubutaccen Alamari Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Gari na wayewa misalin 8:00 Usman ya shirya tsab yaje yagaida Abba da Hajjajo sannan ya shiga ɓangaren Nanne, a kitchin yaji motsin Nanne dan haka ya tsaya ya gaidata sannan ya wuce ɗaki, zaune yasami Ummul a kan sallaya Ammi kuma na bakin gado ta zuba mata idanu, kamar jira take ya shiga tana ganin shi ta zuba mai ido cikin son gano halin da ɗan nata ke ciki,
Shiko Usman a hankali yazo ya zauna a gefen ta yana gaida ta,
É—ago kai tayi tana kallonshi,
sai kuma ta sunkuyar da kanta ido cike da kolla a hankali ta fara zub da hawaye sai sautin kukanta dayake fita a hankali dasauri sukayo gabanta suka durkusa suna tambayar ta ko meya sameta suma idonsu tab kollah, cikin kuka tace,
" Usman wato wannan shine gatan da zakuyiwa Umar kenan ko Usman? sai ku taru kuyita mishi kuka?
An haÉ—aku aure dan a nazaton zaku samawa juna sanyi da sassaucin zafin rashi shi amman ashe bamu saniba hakan an baku damar ku zauna kuyi ta mishi kukane".
Usman ta kuma kalla da duk jikinshi yayi sanyi tace,
"Usman bakaso hankalina ya konta ko? Kasan bana son tashin hankalin ku kaida Ummu kuma shine kake ƙarawa ga yadda fuskokin ku suka kubbura,
Usman har sai yaushe zamu bar kukan rashin Umar?
Usman ai kukan rashin shi bazai kare manaba har sai randa muka konta damarmu daurewa zamuyi mubar zubda ƙollah muyita mishi Addu'a,
amman hakan ya gagara da sai ka tasa Farouq a gaba kaɓuya kayi ta kuka yanzu kuma Ummul zakake tasawa a gaba kana kukan kenan?".
Shiru sukayi cikin sanyi da yarda da nasihar Ammin,
A haka Abba da Adam suka shigo suka samesu suma suka É—ora tasu nasihar har saida sukaga sun sake suka je sukayi break cikin wolwola.
A ranar bayan sunci abincin dare ne suka zauna a palour Nanne dukkansu suna kallon news a tashar TVC News suna zaune kowa da abinda yakeyi amman ita Ummul gaba É—aya hankalin ta na kan tv sai Aliyu dake zaune gefenta ta saman hannun kujerar da take zaune Usman kuwa yana gefen ta a kan kujerar
suna cikin hirar kawai sai sukaga Ummul
ta miƙe cikin tsananin razana da firgici gaba ɗaya jikinta sai rawa yake cikin gigita ta damki hannun Aliyu dake kusa da ita sannan ta nuna tv da hannunta ɗaya baki na rawa murya a hargitse take nuna tv tare da cewa,"
"Ammi gasu Ammi sune ya Usman kallesu wallahi sune Ammi sune suka k..".
Bata ƙarasa maganar ba tayi baya a sume ta faɗa kan Usman,
wanda ya taso tunda yaga yanda jikinta ke rawa,
dukkan su kanta sukayo kowa yana addu'a da jimamin damuwarta da gudu Sadiq yaÉ—ebo ruwa ya mikawa Ammi jikinta na rawa ta yayyafa mata sannan ta shafa mata a fuska,
Lokaci É—aya tayi wata irin ajiyar zuciya sai takuma razana tana É—ago kai idanu wanta a zazzare
cikin tsoro Ammi tace,
"Wai meke razanata ne haka fa in baku mantaba hakan yafaru da ita cikin azumi ta suma".
sai ta kuma kallon ta cikin tausayawa tace,
"Ummu na faÉ—amin me ke faruwa?".
Cikin firgici jiki na rawa tare da rera kuka mai cike da ƙuna a zuciya ta nuna fuskokin da ake nunawa a tv tace ,
"Ya Usman kallesu sune suka yankamin Hamma na a gabana sune suka kasheshi wallahi har abadan bazan manta waÉ—an nan fuskokin ba bazan manta fuskokin suba wallahi sune".
Gaba É—aya jikinta na rawa,
sosai Usman yasake matsota ya tare mata fuskar ta daga kallon tv shima yana rumtse idanun shi da ƙarfi dan har abada bazai so ƙara kallon waɗannan mutanen da suka kashe mai Hamman shiba,
Adam dayake tsaye jikin shi yana rawa yafara musu bayani,
"Hakane cikin azumi wani azumi daya wuce ankama waɗanda suka kai harin bomb a Jos! Kano da Zaria a gurin da ake verification na malaman makaranta, an kamasu ne a hanyar komawar su a Daɗin Kowa ta jahir Gombe, wannan da take nunawa yanzu dashi a cikin su yanzu kuma dasune akayi musaya suka bada y'anmatan Chibok da aka sace sukuma aka badasu wa uƙiyar tasu".
Sadiq ne yakar ɓi zancen da cewa,
"Ammi waɗannan dukkansu y'an asalin nan potiskum ne fa wata ƙil".
Usman da tunda aka fara maganar baice komaiba sai addu'a da yaketa tofa mata,
ganin har yanzu bata dawo hayyacin taba yasa yamiƙe hankali itama ya ɗagota duk jikinta na rawa suka fita yanufi ɓangaren shi da ita tana makale dashi tana rawar jiki da zazzaro idanuwa,
Suko su Ammi da su Adam É—in gaba É—aya haka suka zauna sunata jajantawa da yiwa Hamma Umar É—in addu'a.
A ɓangaren su Ummul kuwa kukan taketa yi a kiɗime,
ganin haka yasa Usman ya wuce da ita part nasu kan kujera ya jawota suka zauna
rarrashin ta ya rinƙayi amman ina ya rigada Ummu ta buɗe shafin kuku dan ganin fuskokin waɗanda suka kashe mata ɗan uwanta kuma mijin ta,
jawota jikin shi yayi a hankali ya tallabo haɓarta cikin sanyi da zubda ƙollah ya haɗe bakin shi da nata wuri ɗaya kissing ɗinta ya rinƙayi cikin salon son tsaida kukan nata daga nan ya gama rikitata da salon soyayyar shi mai tsanani duk da kuwa shima yanayi yana zubda hawaye,
haka suka kwana ranar ma yanata ririta ta da son sama mata nitsuwa,
sai dai duk yanda yaso daya samu damar raɓarta bata bashi damar kusantar taba shikuma baida niyyar takurata haka dole ya haƙura kamar yadda ya haƙura jiya,
Asubar fari ta tashi ta gudu kamar yadda tayi jiyan.
Usman ne yasami Abba da Daddy a safiyar litinin a palour Hajjajo yake sanar dasu cewa tafiyar shi zata kama cikin satin nan zuwa ranar juma a, kuma zaitafi da matar shi dakuma yaronshi Farouq duk da ba daÉ—ewa zaiyi ba aiki ne kawai zaije na watanni uku yadawo,
Addu'a sukayi mashi cikin jin daÉ—i sannan Abba yace,
"Usman bazan hanaka ɗaukar matar ka da yaron kuba amma inaso ka fahimci hakan zai iya taɓamai karatu shi kada kayi tunanin dan yanzu yafara bazai sami matsala ba amma kaga ko zuwa kayi ka sakashi makaranta acan watanni 3 kawai zaiyi kasake ɗaukoshi kudawo kaga canje-canjen makaranta baida daɗi ga yaro dan haka kayi hakuri kutafi kubarshi anan yana zuwa makaran tar shi har kudawo ku sameshi ina ganin baza a sami wata matsalaba tunda daman yasaba da iyayen ku gakuma Adam da Sadiq sannan ga abokinshi Aliyu".
Kanshi a kasa idonshi yafara ƙollah ya daure ya danne halin da yake ciki gudun kada su Abba su gane a hankali yace,
"To Abba shikenan saimu barshi".
sai ya kuma É—an gyara zama cikin sanyi yace,
"Abba dama Ummu tace min tana son zuwa gun AYSHA ALIYU GARKUWA marubuciyar dake rubuta labarin tannan to dama mun gama shiri kafin mu tafi Malesia sai munje garin su Garkuwar toh shine nake so in zamuje can É—in kam a barmu mu tafi da Farouq dan itama Aysha tana son ganin Farouq É—in".
Daddy ne ya É—an kalleshi cikin murmushi yace,
" ba damuwa Usman Allah yayi muku albarka yasa ayi tafiyar a sa'a Allah ya kuma dawo daku lafiya".
Da "Ameeen duka suka amsa sannan sukayi ta tattaunawa kafin suka watse.
ÆŠaki Usman ya koma yafaÉ—a kan gado yanajin wani irin zafi a zuciyar shi idanuwan shi na zubar da kollah a hankali yajanyo wayar shi yakira Ummul tana É—agawa yace,
"Kisameni a É—aki".
yana faÉ—in haka ya katse kiran,
jin muryarshi yasa jikinta yin sanyi dan ta fahimci akwai damuwa tattare dashi dan haka ba ɓata lokaci ta fita ta nufi ɗakin nashi.
Sallama tayi a parlour taji babu motsin shi dan haka ta murÉ—a kofar bedroom É—in a hankali da sallama ta shiga,
kwance yake yana kife a haka ya amsa sallamar ta yaɗago hannu ya kamota sannan ya juyo ya janyota jikin shi zamewa tayi ganin ƙollah a idanun shi tasa hannu ta goge mai a hankali tace,
"Menene kuma?".
Shima tashi yayi ys zaune ya ɗora kanshi akan kafaɗarta duk ya narke a jikin ta cikin shogoɓa yace,
"ba komai Ummuna".