← Book details Rubutaccen Alamari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 77

Sashe 4

Rubutaccen Alamari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Alhaji Umaru Shuwa'arab asalin sa shi da matarsa Rabi'atu Hajjajo kenan su Shuwa'arab ne asalin ma zauna garin patiskum cikin unguwar tudun wada yamma da fce,
kowa yasan shuwa'arab kyewawane kuma masu jin larabci ne,
Alhaji Umaru da Hajjajo suna da yaran su 3 duk mazane babban d'ansu Alhaji Ibrahim Umar shuwa sai k'anneshi biyu tagwaye ne Hassan da Husaini sun tashi cikin gata da tsantsanr k'aunar juna,
Alhaji Ibrahim shine babba kuma ya kasan ce mutun mai tausayi da k'aunar k'annenshi yana musu so mai tsanani,
iyayensu kuwa sun basu tarbiya mai inganci tare da ilimin addini da na zamani
sun tashi cikin tsabtacecciyar rayuwa,
da kulawar iyayen su bayan sun girma ne Alhaji Ibrahim yayi aure ya auri matarsa Amina ba fullatanar potiskum d'in,
mace mai mutunci da kara da sanin ya ka mata,
bayan anyi auren bada jimawa ba Allah yayiwa Alhaji Umaru Shuwa rasuwa,
daga nan ragamar gidan ya zama a hannun Alhaji Ibrahim yake ya rik'e k'anneshi da amana ya basu dukkan abinda uba zai bawa ya ranshi sunci gaba da karatu su .

Yana zaune da matarsa da mahaifiyar shi a gidan shi da k'annenshi baki d'aya,

Ranar da Alhaji Umaru Shuwa ya cika shekara d'aya da rasuwa a ranar Amina matar Alhaji Ibrahim ta haifi d'anta fari tas kekyawa dashi mai kama da babanshi,
ran suna yaro yaci sunan kakanshi Umar Faruoq kenan.

Yaro ya tashi cikin gata da kulawan mahaifiyar shi da kakarshi da k'annen mahaifinshi Hassan da Husaini,
yaro mai farin jini da kwarjini.

bayan shekara 4 Alhaji Ibrahim, yayiwa k'annenshi Aure rana d'aya,
suka tare a gida jen da ya gina musu a gefen nashi.

Bayan watannni 5 da auren Khadija matar Hassan ta fara laulayin cikinta na fari a lokacin kuma Amina matar Alhaji Ibrahim itama tana da cikin d'anta na biyu,
matar Hussani kuma bata da ciki tukun ,
Bayan wani lokacin Amina matar Alhaji Ibrahim ta haifi d'anta na biyu mai suna Usman a lokacin Umar Faruoq kuwa ya cika shekara 5 da y'an watanni, Khadija matar Hassan kuma ta haifi d'anta na fari mai suna Adam wanda tsaka ninshi da Usman kwana 12 ne Usman d'in ya girmi Adam da kwana 12 haka yaran suka tashi cikin shak'u da juna ko mai tare akeyi musu,
Umar Faruoq ya tashi da k'aunar k'annenshi.

Usman da Adam suna da shekara d'aya a duniya Allah yayiwa Alhaji Ibrahim maifin Umar da Usman rasuwa.

Rashuwa da ta shiga jikin Hassan da Hussain da Hajjajo sunyi kukan rashin d'an uwansu wanda shine madadin mahaifinsu a garesu.

Amina matar Alhaji Ibrahim mahaifiyar su Umar wacce yaran ke karanta da Ammi tayi kukan rashin mijinta da rabuwa da yaranta dan tana gama ta kaba ta koma gidan iyayen ta,
Alhaji Hassan wanda suke kira da Abba ya karb'i Umar da Usman ya dank'asu a hannun matarsa Khadija wacce yaran ke kira da Nenne sannan kakarsu Hajjajo itama tana gidan suka taru suka raini yaran cikin kulawa da tsantsar gata ta yadda su Umar basu san zafin maraici ba.

Nenne kuma bayan ta haifi Adam ta kuma haihuwa yaran 4 Sadiq sai Sadiya sai Rabi'atu wacce take takwarar Hajjajo ce amman suna kiranta da Ummul khairi sai kuma d'an autanta Aliyu.

Yaran sun tashi cikin k'aunar juna baka gane cewa Nenne ba ita ta haifi su Umar ba,
Sai dai kowa da halinsa dan shi Umar mishkili ne baya wasa da yara kuma kasan cewarsa shine babba a family d'in su yasa k'annenshi suna girmamashi
shi kanshi Umar yana jin haushin yadda yake halinshi, yayinda hakan ya jamishi kiyeyyah a uzuciyar Ummul ita kuma gani take yana takura rayuwarta a, zahiri Umar yana jin zafin yadda wasu lokutan ake gaza gane cewa wannan halin fa ba yin kanshi bane Allah ne ya halicce shi a hakan.

Sun tashi cikin gata da kulawa inda Umar a yanzu haka shi babban doctor ne yana d'aya daga cikin yerdeddun governor damaturu shine doctor dake duba lafiyar governor nasu kuma shine babban doctor dake aiki a general hospital damaturu,
Usman kuwa shi accounter ne sai .

Sai
Adam Airforce ne yanzu haka a Kaduna yake
sai in yazo ziyara.

Sai Sadiq shi kuma yana aiki a ministry of justice.

sai Halimatu Sadiya ita kuma nurse ce tana aiki anan cikin garin potiskum.

Sai
Ummul khairi ita kuma bayan ta gama primary school d'in ta aka jona mata secondary school GGC damaturu inda ta koma cikin damaturu da zama a cikin makaran ta,
yayin da shi kuwa Alhaji Hassan Abban Ummul kenan shi yana aikine a offishin gwamna a damaturu hakan yasa Abba yana da gida a can inda yake zama yana aikin shi sai alhamis ya taho week end cikin garin patiskum d'in,
hakan yasa idan anyi hutu Ummul takan zauna a gidan shi dake gidan jen maikata na ministry of works and housing dake gashua road damaturu dan jira ya gama aikin sa sai su tafi tare su koma cikin potiskum tare.

A hakan ne wata rana Ummul ta fita ita da k'awayen ta suna d'an zagawa cikin uguwar,
anan ta had'u da Mustapha saurayin da suke soyayya a yanzu haka,
shima yazo gun abokan shine a unguwar,
dan shi Mustapha gidan su na commissioners quarters dake Maiduguri road damaturu,
haka sukayi ta soyeyya in sunyi hutu yana zuwa har gidan su Ummul d'in dake potiskum,
Haka yasa
ya saba da ita ya saba da y'an uwanta suna yiwa juna so mai tsabta.

Shi kuwa Umar sosai ya zuba ido kan lamuran Ummul, gashi in Abba baya nan kusan shine uba a gidan,
so yana tsanani sa mata ido dan kare tarbiyar ta ita kuwa hakan yasa ta k'ara tsanarsa da jin tsoronshi,
dan baya mata da sauk'i.

Usman kuwa mutun ne mai fara'a da sakin fuska yana watsa da kawo dan shi ko da Abba wasa yake mishi kamar kakanshi,
haka yasa Usman ya kasance wani jigo na gidan in ya fita ko na awa d'aya ne sai anyita ceki yarshi,
shi da Umar kuwa suna yiwa juna wani irin so mai tsanani Umar yana k'aunar Usman fiye da komai a rayuwarshi suna yawan kaiwa Amminsu ziyara a gidan kakannin su.

Usman tun yana k'arami ya tashi da ciwon zuciya mai tsanani inda Abba da Daddy Hussain in Abban kenan sukayi ta jin yarshi,
a haka abin tashi hankali da fari an gane cewa zuciyar Usman tana da d'an hujin dake sashi ciwon zuciya so anyi ta bashi kula,
amman kuma Usman na girma abin na k'aruwa haka yasa zuciyarshi ta zama ta tsage ,
dole aka fitar dashi Egypt so acan akayi mishi aikin tare da kulawar d'an uwanshi Umar Faruoq aikin da akayiwa Usman a cikin zuciyar shi aiki ne da yasa an bar wasu na'urori a cikin k'irjinshi d'an zuciyar tashi tayi raunin da bazata iya harba jininshi ba sai da wannan na'uran haka kuwa aka k'inda ya mishi dokokin aka hanashi cin duk wani abu green dan abubuwa green suna sa jinin d'an adam kauri shi kuwa zuciyarshi nada raunin harba tsinkekken jinima bare mai kauri sai na'urar ke iya harba jinin ,
haka duk bayan shekara 5 yake zuwa a canza na'urar,
ko kusa da kai Usman ya zauna zakaji yedde na'urarnan take aikin a jikin shi tana,
*cak-cak* yana harba amman sai ka matso kusa dashi sosai zakaji sautin a hankali.

Wannan larura da Usman yake da ita yasa gaba d'aya zuriyarsu suke tausayawa mishi duk wata kulawa suna bashi,
yayinda Umar Faruoq kuwa a duniya baida wata matsala sai damuwar ciwon B'iyayen shi,
shi yasa duk wata kulawa ta duniya wacce uwa da una zasu bawa d'an su ya had'eta yana bawa k'aninshi Usman.

Ummul kuwa da Usman suna rayuwa tamkar abokai,
Anty Halima kuwa tana gidan mijin ta amman duk wata kulawa tana yiwa Ya Usman d'in nasu.

Ya Adam da Usman kuwa su tamkar tagwaye suke tunda dama kwana 12 Usman yake bawa Adam.

Ya Sadiq kuwa mutumin Hamma Umar ne.

Auta Aliyu kuwa abokin fad'an Ummul ce shima yanzu ya kusa gama secondary school d'in shi ita kuwa Ummul sune suka gama this year so yanzu tana gida ana sama mata admission a FCE (T) potiskum zatayi NCE d'in ta akan maths and computer.
toh fa a d'an wannan zaman da takeyi a gidanne take k'ara fuskantar takura fad'a da Umar ke mata hakan yasa ta k'ara tsanarshi.

Haka Ita kuwa Ummul take da wani irin ciwon mara a duk lokacin da zatayi al'adarta kasan cewar a makaran ta tafara ciwon cikin sai ba'a santa dashi sosai ba tana dai fad'a tana ciwon ciki amman Nenne bata san ciwon mai tsanani bane.....
*Tak'aitaccen labarisu kenan*

Mun dawo kan labarin yanzu.

Nenne na dawowa ta lek'a kitchen tana kiran Ummul tana fad'in.
"Ummul kin gama ne?."

Ido ta d'an zaro ganin ba abin da tayi a kitchen d'in cikin sauri ta fito parlour kan dinning table d'in ma ba komai agogo ta kalla da sauri ta fita ganin har 2:00 pm tayi.

Parlour Hajjajo ta nufa tana kiran Ummul d'in.
tana shiga Parlour ta kalli Umar Faruoq d'in cikin b'acin rai da fushi tace........

By
*GARKUWAR FULANI*
📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*RUBUTACCEN AL'AMARI*

Page 4⃣

*NA*
*AYSHA ALI GARKUWA*

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*Fatan alkhairi a gareku masoya na da wannan littafi nawa ina godiya da k'aunarku gareni 🙈🙈 kuyi hak'uri nasan wasu zasuce ba zasu fara karatu yanzuba sai nayi nisa sabida basa son farawa suzo suna jira toh dan Allah kuyi hak'uri duk wacce tasan sai anyi nisa zata fara toh ta Tarawa kanta kar sai nakai 20 ko 30 azo ayita bina P/C a nace ana so ni banzan iya hanaku ba sabida ina son mai sona kuma bana iya fiffik'e ido nayi banza da d'an Adam sabida d'an Adam abin karramawa ne Amman wallahi ina takuruwa gashi inada eyes problem kuyi hak'uri Ku tarawa kanku ngd Allah bar zumunci da k'auna GARKUWAR Fulani tana al'fahari da masoyan ta*

Rai a b'ace cikin yana yin kai k'ararta tace
"Umar kaga Ummul tafiya tayi bata yi aikin komai ba ko,
yanzu-yanzun nan kira min Halima kace maza ta turota gida."

Kallon Nenne yayi yace.
"Tafiya tayi gidan Haliman ne? kuma batayi aikin ba?."
Chapter 4 · 0% Book details