← Book details Rubutaccen Alamari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 77

Sashe 68

Rubutaccen Alamari Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Wata ranar asabar da tayi dai-dai da saura kwanki bakwai d'aurin auren Aunty Shuwa ta jiko abunda suka saba bawa Ummul kullum tafito palour Hajjajo inda suke zaune ita da Aliyu da Aunty Halima sai Nanne da Ammi da uwar gaiya Hajjajo,
aiko tana ganin ta da cup ta ɓata fuska ta marairaice kamar zatayi kuka tajuyar da kai tace,
"Ni gaskiya nagaji wallahi cikina a k'oshe yake yanzufa Aunty Halima taban wani nasha".
Itama Anty Shuwa É—aure fuska tayi ba wasa tace,
"Kuma wannan ma yanzu zaki shanye shi ba,
ni banson shirme ki amsa kishs kawai".
Bubbuga ƙafa tafarayi a ƙasa tana yarfa hannu da ƙunƙuni ƙasa-ƙasa dai-dai lokacin shigowar Usman da Adam da Sadiq sun dawo daga gaida Inna,
Dasauri Usman ya ƙaraso cikin palour yace,
"Wai meye, Halima ce ko?".
ÆŠauke kai Aunty shuwa tayi kamar bata jiba itako Aunty Halima cewa tayi,
"kai ya Usman to bani bace itada Auntyn ta". É—an juyawa yayi ya kalli Aunty Shuwa data É—aure fuska babu alamun wasa tace, "kyaleni da ita, abu nabata wai bazata shaba ta k'oshi".
ɗan leƙa cikin kofin yayi sannan ya tambaya,
"Magani ne?".
"eh maganin ciwon ciki ba".
Inji Halima,
ganin yadda yajuyo yana kallonta yasa Nanne tashi ta fice dan ta gane sarai Usman ya gane maganin menene ake batan,
dan tasan halin shi zai iya faÉ—an komai,
a hankali ya ƙarasa inda take zaune yace, "Ummu na yi haƙuri kisha mana kinji kinga yanada amfani".
Noƙe kafaɗa tayi alamar taƙi a hatsale Aunty Shuwa tace,
"Matsamin dan Allah intafi ana baki kinawa mutane yanga wazai amfana? ni ko Halima ko ke?".
Dasauri yamiƙe ya karɓi kofin ya tsura mata ido fuskar shi babu alamun wasa yace,
"Ke wallahi sai kinsha ko in É—ura maki, wannan ai shirme ne,
au tukun ma wai shin ko dai baƙin ciki zakimin?".
da jin haka Ammi ma ta tashi ta fice tabarsu ganin taƙi karɓa yace, "Sadiq riƙe min cup ɗin Allah saina ɗura maki zakiwa mutane asara da baƙin ciki inke bakya so ni inaso kuma dole kishi".
Yana faɗa yana matsowa kusa da itan sanin halinshi yasa ta miƙa hannu Sadiq ya miƙa mata kofin tana ɓata fuska takai bakinta,
"Gwara miki dan wallahi ba abinda zai hana in d'ura maki shi". Saida ta shanye tas sannan tasauke kofin tana dama fuska kamar zatai amai,
kallon Aunty Shuwa yayi wacce kunya ta rufeta har ta kasa ɗaga ƙafarta wato Usman yama gano me ake bawa Ummu,
shiko ko a jikin shi yace daga yanzu in taƙi sha dan Allah ku kirani".
Yajuya zai fita Hajjajo datake kallon ikon Allah tace,
"fitsararre".
Juyowa yayi kafin yaba ta amsa idon shi yasauƙa kan Ummul da taketa kakarin amai kallon ta yayi tare cewa,
"Kada kiyarda ki amayar da abinnan dan sai an ƙara maki wani".
Ficewa yayi suko duk sukayi shiru suna kallon juna itako tashi tayi tafice tana buga ƙafa.

Yau asabar da misalin ƙarfe 10:30am na safe dubban jama a suka shaida daurin auren USMAN IBRAHIM UMUR SHUWA da amaryar shi RABI'ATU HASSAN UMAR SHUWA ciki da abokan Hamma Umar wanda dayawa suka sami gayyata daga Dr Bashir da kuma Mustapha shima da mahaifinshi,
Ango kuwa Usman lokaci ɗaya tunanin ɗan uwanshi ya faɗo mai a take ida nunshi suka fara zubda ƙolla mai tsananin zafi yana tuna a yau ds Hamman shi na raye da zaifi kowa farin ciki da yau zaiga gata mai tarin yawa cikin kuka yake gaisawa da abokan Hamman nashi,
bayan ya shiga cikin gida kuwa Ammin shi ya tasa a gaba suna wani irin kuka mai cike da ƙuna a zuciya da kyer aka samu Abba da Hajjajo suka tausasu.

Haka abin ya kasance a cikin gida mata nata nasu hidimar ga matar Dr Bashir da matar Mustapha da Ummanshi,
ita kuwa Ummul yau mutuwar Hamman ta takuma dawo mata ruggume Farouq tayi ta durƙusa gaban Adam da Sadik tana kuka mai tarin nadama da dana sani,
Shima yaro ganin yadda mahaifiyarshi ke kuka sai ya fashe da kuka mai ƙarfi
ayyah Adam shma gaba É—aya ya kasa control en kanshi sai hawaye cur-cur ya kasa magana
Aliyu kuwa jawo Farouq yayi ya riƙeshi gam a jikin shi suna kuka,
Sadik ne da Anty Shuwa sukayi ƙarfin halin lallashin su da yi mudu nasiha,
saidai Amaryar kam da kyer aka samu aka rarrasheta saboda kuka da takeyi mai tsanani dan tunawa da masoyinta Hamma Umar.

Haka jama'a sukayi ta tayasu murna har zuwa dare aka fara watsewa.

Ango yanata sintiri dan yana son ya lallashi Ummul enshi da kanshi kuma shima yana buƙatar ta tausayawar ta a gareshi dan yau gaba ɗaya begen Hamman shi yake,
karo na 3 yashigo yasami Nanne da Ammi sai Aunty Shuwa da Aunty Nafisa yasami gefe yazauna gaisawa sukayi tare da ƙara yimai addu'a kai yafara sosawa yakalli Aunty Shuwa cikin rauni yace, "Ina take?".
HaÉ—e fuska tayi sannan kuma abin nashi ya bata dariya ya kuma bata tsusayi a hankali tace,
"To anace tanada bak'i".
D'agowa yayi ya kalleta sannan ya saci kallon Ammi daketa ƙoƙarin maida ƙollar ta a hankali yace,
"Dere yayi fa kuma zamuje wani wuri da ita Ayyah dan Allah a bani matata".
Ammi ce ta karb'i zancen da cewa,
"A,a baza a baka ba Usman,
ainan ba gidan ka bane kuma da bakinka kace sai kaje course kadawo zata tare".
Da hannu ta nuna mai hanya alamar ya tafi, marairaice fuska yayi kamar zaiyi kuka yace, "Nanne".
Bai ƙarasaba tace,
"Jeka kayi wanka ka huta babu mai hanaka matarka".
Ɗan murmushi ya ido cike da ƙollah yatashi yafice yana ƙoƙarin cire babbar rigar jikin shi, Ammi ta kalli Nanne tace,
"Bafa zan yarda da wannan tsarin ba". ƙasa Nanne tayi dakai cikin girmamawa tace,
"Kiyi haƙuri Addana dan tun ɗazu Abban su yace kada a hanashi matar shi ,
dan duk su biyu kukan da sukeyi na abu É—aya ne tuno Umar ne kuma su duka kowa zai tsaida hawayen shi dan É—aya yayi shiru,
kuma ai banga laifin hakan ba tunda mutune dayawa suna aure su tare gidan iyaye nasu kinga shima yanada damar hakan kuma kinga yama kusa yin tafiyar".

Aunty Shuwa ce ta kalli Ammi tare da cewa, "Ammi ki kyale ɗan Abba yasha sha anin shi dan wallahi dagashi har Ummul sun ban tausayi ga yadda ƙaddara ta haɗasu bawan Allah Farouq shima yau yayi kukan rashin Uban da bai saniba".
Itako Ammi baki ta d'an rumtse hawaye na bin fuskarta tace,
"Hmmm to Allah yayi musu albarka Allah ya jiƙan Umar Allah ya mishi rahama Allah ya raya abun da ya bari".
"Amin Amin Ameeeeeeeen ya rabbil izzati"
suka amsa baki É—ayan su,
Aunty Nafisa matar Daddy wacce tunda aka fara magana tayi shiru tace,
"Au shiyasa naga Adam da Halima sunata shirya Ummul É—in".
Ammin ce ta miƙe tana tafiya tace,
"eh mana ai duk bakinsu É—aya har da Adam kamar mace,
nidai baruwana kuma bame takuramin yarinya.

A É—akin su Usman kuwa Adam ne da Nuru sukayi ta lallashin Usman,
miƙewa sukayi
jin muryar Anty Halima wacce ta shigo ruggume da Farouq Ummul na biye da ita a baya,
A hankali tace,
"Ga Farouq tun É—azu yake kuka sai a kawoshi gun Abeen shi".
hannu Usman yasa ya karɓeshi sannan ya ruggemeshi
suko Anty Halima da Adam da Nuru fita sukayi suka bar part É—in gaba É—aya.

Shiko Usman suna fita yasa hannun ya ruggum.....

*By*
*GARKUWAR FULANI*

[12/5, 9:42 PM] ‪+234 808 364 9787‬: 📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*RUBUTACCEN AL,AMRI*

Page 3⃣7⃣

*Na*
*AYSHA ALI GARKUWA*

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*MOH ALLAH WUJI FURÆŠA TA FULLO BE FULAKU KOSAM EH DAN GOL*

*Wannan shafi naki ne ke kadai k'anwata ta kaina Queen Hafsi Allah bar zumunci da k'auna dear 🤝*
Chapter 68 · 0% Book details