← Book details Rubutaccen Alamari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 77

Sashe 41

Rubutaccen Alamari Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

a gidan su Ammi Kuwa yana isa yai paking a k'ark'ashin bishiyar kofar gidan ya fito yashige cikin gidan,
da Inna yafara had'uwa tafito daga kichin tana ganin shi tayi murmushi cikin jin dad'i da k'aunar jikan nata tace,
"kaga Ummaru faruq, mai tagwayen suna, kaga d'an Ammin shi da Nanne yayan shehu Usmanu, angon Rabi'atul Adawiyya likita bokan turai".
Duk kirarin da Inna keyi ya na tsaye ya na kallon ta yana shafa sajenshi ganin ba zatayi shuru bane ya katseta da cewa,
"To ya isa haka zo muje inbaki tukuici dan kinyi aikin maroka".
hannun ta ya kama suka shiga cikin parlour inda Ammi ke zaune tana ninke y'an kayayyakin data data woke,
sai murmushi takeyi tana jin dad'i da shauk'i da k'aunar d'an nata dariya ta d'anyi dan jiyo kirarin da Inna kewa d'an nata,
suna shiga yasamu ya zauna a gaban ta ya cire hular shi kamar ko yaushe in yana gaban Ammin nashi , ya kwantar da murya yace, "Ammi na ina kwana?". hannunta takai ta shafa kanshi tace,
"lafiya lau, ya aikin, ina Ummul dina?".
K'ara matsawa jikin ta yayi yace,
"lafiya lau Ammi na tare muka zo da ita bacci tai kafin in fito shiyasa bamuzo tare ba".
sai kuma yasa hannu ya karb'i zanin hannun ta yaci gaba da ninkewa,
Ido Ammin ta zubawa d'an nata tanajin kaunar shi na ratsata tace ,
"Umar inajin dad'in yanda kake tafi da rayuwar auren ka da k'anwarka amanar ka". Ajiyar zuciya ya sauke ya lumshe ido yana jin dad'in yadda Ammin nashi ke Al'fahari dashi da kuma yadda take gamsuwa da rik'on amanar daya d'auka, murya can k'asa yace "koyarwarki ce Ammi ina alfahari dake ko yaushe".
Tattare kaya yayi yaje ya jere kowanne a mazauninshi sannan ya fito yad'akko abin yankan farce ya dawo ya russuna gaban Ammin sa, itako hannu ta mik'a mai yafara aikin shi na yankemata farce Kamar yadda ya saba dai-dai sanda ya gama yankan ffarcen Ammin nashi akayi kiran sallah dan haka yai alwala yawuce masallaci dan gabatar da sallah azhar,
bayan an idar da sallan ne ya koma cikin gida gaban Ammin nashi ya zauna tare da zaro woyarshi yace,
"Ammi bari in kira autanki ayi hira dashi".
"toh".
tace tare da yin murmushi.

A b'angaren Ummul kuwa tun tana zaune har ta kwanta bacci b'arawo ya saceta shiko ya Adam da ya Sadiq daya shigo bayan fitan Hamma suna nan zaune a palour Nanne suna jiran fitowarta, baccin da tayi ne yasa bataji tafiyar su masallaci ba bare taking dawowarsu , Anan sukaci abinci cewarsu ko shekara zatai a d'akin suma zasu shekara a gurin.

Ya Usman Kuwa mutan india, yana zaune a k'asan capet ya kifa kan shi a kujera hannu shi dafe da kirjinshi yana wani irin kuka mai cin rai da k'ona zuciya kamar yadda kukan ya zame mai sabo duk da ga tarin magungunan da ko ya shasu baya jin sauk'in zogin da zuciyarsa keyi kullum son Ummul da k'aunarta K'aruwa suke a zuciyarshi,
kukan yakeyi kamar yadda ya saba har numfashin sa na fizga, Kid'an da wayar shi keyi ne yasa ya dago rinannanun idanun shi yakai hannu ya janyota daga kan table d'in dake tsakiyar palour, har kiran ya yanke yanata kallon ta yana k'ok'arin saita kan shi gudun kada yad'au kiran yayi abinda B'iyayen nashi zai gane yana cikin damuwa,
Shiko Hamma Umar dake zaune gaban Ammi yace,
"barin in sake kira". Bugu d'aya Usman ya amsa da,
"Amincin Allah da rahamar sa gareka d'an uwana jinina".
ba Hamma Umar ba hatta Ammi da tasawa wayar ido saida ta lumshe ido dan jin dad'in kalmar autan nata, aiko ita ta amsamai da,
"Amincin Allah ya tabbata gareku y'a y'an albarka".
wannan kalmarce ta tabba tarwa Usman da Hamman shi na tare da Ammin su, sai da ya k'ara dai daita kanshi sannan yace, "Ammina, Hammana, da y'ar tsohuwa Inna ina wunin ku?".
Kafin su amsa kuwa ya sake katse su da cewa,
"ina nan lafiya lau, dan nasan yanzu Hamma na zaita bincike ni da tuhuman ina shan magani".
dukkansu sun manta da amsa gaisuwar tasa suka fashe da dariya sannan Inna tace, "wato dai angona kana nan da halinka na ban dariya ko?".
sai da yayi gyaran murya sannan yace, "waye angon ki? kinga barni karki cikani da surutu gwara nayi magana da Ammina dan nayi missing voice d'in ta".
Ammin ce ta katse shi tace,
"Meyasa bazaka dawo ba in dai hakane, muna buk'atarka a kusa damu".
Sai da ya sauk'e ajiyar zuciya sannan ya furta, "Afwan ya Ammi na ki tanadi abun dad'i dan nan da sati biyu zan taho".
bai gama rufe bakin shiba Hamma Umar ya d'an juyo ya kalli wayar cikin nutsuwa da murmushi d'auke a fuskar shi ya ce,
"Ajiye wasa B'iyayena, da gaske hakan zaka dawo?".
Murmushi mai sauti yayi yace,
"Insha Allah".
Shima murmushin yayi cikin tsananin farin ciki da k'aunar d'an uwan nashi yace, " Alhamdullahi Usman yau naji dadin jin zaka dawo, Allah ya dawomin da kai lafiya nayi kewarka matuka".

Da haka sukaita hira cikin so da k'aunar juna har lokacin sallah la asar sannan sukai sallama kowa yatashi dan gabatar da sallah shiko Hamma daga masallacin gida ya nufo dan ya sallami su Ammi shi.

Yunwa ce ta tashi Ummul da rawar jiki da kyar ta mik'e ,a daddafe tai sallah la asar sannan ta zira kunnenta a bakin kofa, shirun dataji ya bata damar bud'e kofar ta leko kanta bakowa babu motsin kowa a palour dan haka da fito kai tsaye tai kicin, abinci ta zubo ta dakko ta fito kenan sukai arba da ya Adam jiki na rawa tai k'asa ta ajiye plate d'in ta durkusa jiki na kerma tace,
"Ya Adam". Damgota da yayi ne yasata sakin wata irin gigitacci yar k'ara tana,
"kayi hak'uri yaya, nadena, bazan sakeba". Aiko saukar marukan da taji yasa ta k'walla k'arar data janyo hankulan mutanen gidan ciki harda Hamma Umar wanda fitar shi daga mota kenan,
da Nanne dake b'angaren Abba tana d'an gyare-gyare,
da Hajjajo wadda suke zaune palour ita da Ya Sadiq da Aliyu da gudu sukayo b'angaren Nanne Hamma Umar ne a gaba, shigowar shi tai dai dai da marin da Ya Adam ya k'ara mata,
a fusace ya janye Ummul bayanshi cikin fushi ya d'ago hannunshi tas, ya kifawa Adam mari ,
hakan yasa kowa k'amewa a inda yake sannan kowa da irin tunanin shi, Hamma Umar d'inne ya katse shiru cikin tsananin takaici yace, "metayi maka?".
Kanshi a kasa yana rik'e da kumatun daya sha marin yace, "Hamma inaso inmata fad'ane akan maganar d'azu".
Hannu Hamma Umar d'in ya d'aga ya dakatar dashi da cewa,
"waya saka? na kawoma k'ararta ne?". Ya Sadiq ne ya matso kusada Hamma Umar d'in yace,
"Hamma".
Dakatar dashi yai yace, "ya isheni, kuban waje".
fita su kayi dukkan su sukabi bayan Nanne da Hajjajo wanda tunda Hamma Umar ya mari Ya Adam d'in suka fita suka barsu,
batare daya juyaba yasa hannu ya dawo da Ummul dake manne a bayan shi tunda ya karb'eta daga hannu Ya Adam ya ruggume ta tsam kamar za a kwacemai ita yana shafa bayanta ya sun kuyo da kanshi kan wuyan ta yana hura mata iska a kunne ta, dad'a narkewa a jikinshi tayi tana shashshekar kuka k'ara matseta yayi yace,
"shiittt, ya isato, kinyi sallah ne?".
da kai tabashi amsa, a hankali ya rabata da jikin shi yace, "muje mutafi gida".
Maida kanta tayi kan kirjinshi tace,
"Hamma yunwa nakeji". Matsawa yayi ya zaunar da ita akan kujera ya juya, kicin d'in ya shiga jim kadan yafito da plate d'in abinci da kofin shayi, zama yayi a kusa da ita ya ajiye plate d'in abincin a hannun kujerar ya rungumota ta kwanto jikin shi ya kafamata kofi shayin a bakinta aiko nan da nan ta shanye ya kuma mika mata abincin ta ta fara ci,
sannan yajuya ya nufi b'angaren Hajjajo, Sallama yai ya shiga a gaban Nanne yazauna ya sunku yar dakai k'asa yace,
"Nanne kiyi hakuri, bata da lafiya ne,
shiya sa nakasa hakuri da hukuncin da Adam yayi mata, kuma ba wata babbar matsala bace shiyasa nace yabar maganar
duka".
yana maganane kanshi a kasa,
itako Nanne fuska a sake tace,
"bakomai babana, wannan ai tsakanin ka da k'annenka ne".
Ajiyar zuciya ya sauk'e sannan yace,
"zamu koma kar dare yayi".
murmushi Nennen tayi sannan tace,
"to barin d'akkoma man shanun ka".
Hajjajo ce ta mik'e ta d'akko fura da kindirmon nono tace mai,
"gashi in kunje shagwab'abbiyar matar taka ta dama muku". Kanshi a k'asa yace, "nagode".
ya Sadiq ne ya karb'a yayi gaba Adam ma tasowa yayi Hamma Umar ya dafa kafad'ar shi cikin k'aunar juna suka nufi inda motar take,
anan suka sami Nanne da Ummul tsaye dagani magana sukayi. Cikin k'aunar juna sukai sallama suka kama hanyar Damaturu.
Chapter 41 · 0% Book details