← Book details Rubutaccen Alamari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 77

Sashe 12

Rubutaccen Alamari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

5:00 pm zugar ago da abokanshi suka ido farfajiyar gidan Ya Usman ne a gaba yayinda sauran abokon ke binshi a baya ,
Hamma Umar kuwa yana tsakiyar su yasha sutura ta al'farma ya fito cikin haiba da cikar zati sajenshi sai wani irin shek'i yakeyi farar fatarshi ta fito ras tamkar balarabe sumar kanshi kuwa. yayi luf gwanin sha'awa ya murza hula a kan nashi yayinda gashin nashi yabi k'eyarshi da zagayen fuskar shi,
idanun shi kuwa wani d'an siririn glass ne mai haske irin na Doctors ke manner a fuskar sa.

dai-dai lokacin da suka fito a dai-dai lokacin kuma matayen abokan aggon suna suka fito ,
gaba d'aya wani taku suke a jere kamar yadda kujerun ke Jere kowa da matarsa a gefen Hamma Umar ne ya fara zama sai babban abokin shi ,
Hamma Yusuf da Ayshar sa sai Hamma Hassan da Fateemar shi sai kuma. Hamma Bashir da Ruk'ayyar shi
Sai Hamma Mahmoud da Khadija shi sai kuma Hamma Aliyu Haydar tare da Minalin shi,
A d'aya gefen kuwa
wasu manyan abokan Hamma Umar d'in na gani da matayen su, Amadi da Nadiyar shi,
sai Abuturrab da Batul d'in shi sai kuma Salim da Tawa
Sai Abdullahi tare da Maryam d'in shi,
daga gefen su kuwa Fauziyya ce da Al'ameen sai Aisar tare da
Bintun shi
sai kuma Abbah da Ruky pinkyn shi,
ga kuma Ridwan da Zakiyya
can kuma kusa dasu Ahmad Ana Muslim ne tare da khadijan shi
sai kuma Assadiq da Safiyyar shi tare Hibbah da Faheem.

Gaba d'aya sun zauna cikin nitsuwa da al'farma suna zaune cikin cikar haiba sun fito tamkar taurari sai shek'i sukeyi da wani irin k'amshin da suke zubawa zamane sukayi na masoyan gaske.

Bayan sun zauna da kamar minti 5 Dangi da k'awayen Amarya da sauran mutane sukazo suka zauna,
cikin nitsuwa da lumana,
Jim kad'an,
suka fara jiyo wani irin k'amshin na k'ara ratsa hancin su gaba d'aya sai wani irin shauk'i ya ziyar cesu ido suka lumshe tare da jin dad'in k'amshin dake k'ara bud'e su wanda Anty shuwace ke rik'e da kaskon turaren wuta,
Anty Halima kuwa na biye da Ita a baya tana rik'e da hannun Ummul wacce tasha gyara iya gyara an yaneta cikin laffaya mai tsadar gaske ta fito a shuwa'arab d'in sak ta fito tamkar tauraruwar zarah dake kusa da wata,
Anty Halima na rik'e da hannun ta suka iso farfajiyar gidan yayinda ita kuwa Ummul kanta ke sunkuye idanun ta na zubda wasu irin wahaye masu zafi da tafasa zuciya tafiya takeyi tamkar hawainiya,
suna isowa Ya Usman ya mik'e cikin happy yaje gabansu ya tsaya cikin wani irin salon al'darsu ya d'an kife guiwarsa d'aya a k'asa sannan ya d'an d'ago hannunsh sama kad'an ya ware tafin hannushi cikin sanyi yace.
"Halima samin hannun matar Hamma na cikin tafin hannuna ni zan kaiwa Hamman matarsa kusa dashi."

murmushi Anty Halima tayi tare da kamo hannun Ummul d'in ta d'aura cikin tafin hannushi,
wani irin nanauyan ajiyan zuciya ya sauk'e tare da
rumtse idonshi da k'arfin,
yatsun hannushi ya cusa cikin nata ya rik'o hannun ta sannan ya mik'e tsaye ya fara taku a hankali itama Ummul takun takeyi tamkar hawainiya a haka har suka isa gaban kujerar da zai zaunar da ita suna zuwa ya kamo kafad'unta ya juyota tana fuskantar shi yayinda ta bawa kujerar baya,
cikin sanyi ya zaunar da Ita kan kujerar dake manne data Hamma Umar,
a hankali ya fara tasowa daga sunkuye da yayi a kanta,
Ita kuwa Ummul kanta ta kuma sunkuyarwa tare da sakin wani narkekken sautin kuka can k'asa,
Sai kuma tayi shiru cikin sauri ta d'ago kanta tana kallon Ya Usman d'in nata jin kamar y'an watsa mata ruwa,
abin mamaki da Ummul ta gani ba ruwan bane ya Usman ke watsa mata ,
Hawaye ne ke bin fuskar sa har yana diga cikin tafin hannun ta ,
ido ta zuba mai cikin yanayin tabbaya da tsantsar. mamaki a fuskar ta,
shi kuwa cikin jarumta yasa tafin hannushi ya goge k'ollah dake zuba a idanun shi,
murya na rawa yayi murmushin da yafi kuka k'una a zuciya murya can k'asa yace mata.
"Allah ya d'aiyiba."
itama murmushi tayi cikin zubda k'olloh murya a disashe tace.
"Ya Usman ina son ka".
ido ya lumshe da sauri cikin raunin murya yace.
" Ummul nima ina sooonki."
Ido Ummul kam ta kuma rumtsewa dan tasan ba haka suka saba cewa juna ba,
Ita tasan in tace mai ya Usman ina sonka shiko sai yace Allah ya d'aiyiba Amman Yau kuma shima sai yace mata "Ummul nima ina sooonki " a madadin yace Allah ya d'aiyiba Sannan ga hawaye dake bin fuskarsa,
tana cikin nazarin ne taji ya fara yi mata lik'in da Sabin kud'i na gudan dubu-dubu'
gaba d'aya wuri aka fara tafi marok'a na .
"Kaji k'anin aggo Usman d'an Maliki mai ruwan nare."
lik'in sosai Ya Usman yayi mata yanayi yana zubda k'olloh cur-cur sai yasa tafin hannushi yana gogewa ganin haka yasa Ummul tayi murmushi cikin d'an d'aga murya kad'an yadda zai iya jinta tace.
"Allah ya d'aiyiba min ya Usman dina."
jin haka sai ya rink'a murmushi tare da kallon fuskar ta,
a haka ya gama yi mata lik'in sannan Ya Adam da ya Sadik tare da Aliyu auta suma suka shigo sukayi mata lik'in ,
daga nan manyan abokan Aggo kuma jarumai suma suka fito sukayi lik'in ban girma,
daga nan y'an uwa da abokan arzik'i sukayi nasu. lik'in,
bayan duk an gama kowa ya koma mazaunin shi wuri yayi haske,
cikin wani irin yanayi Hamma Umar d'in ya mik'e tare da juyowa gaban Ummul d'in sannan kanshi a sunkuye cikin sanyin muryar shi ya kalli marok'an yace.
"Ku shaidawa Jama'a yanzu zanyiwa Ummul lik'in ne a matsayina,
na babban Yayanta d'an uwanta."
aiko a take marok'an nan suka rink'a shela suna fad'in.
"Aggo yace a shaida muku yanzu zaiyi lik'in ga Amarya a matsayin shi na babban yayanta kuma d'an uwanta."
gaba d'aya sai wuri ya ciki da shauk'i ,
abokan Hamma Umar da matan su sai murmushi suke,
shi kuwa Hamma Umar lik'in kawai yake mata da rafa-rafa na dubu-dubu,
haka ya rink'a zubawa Ummul kud'i tamkar ruwan sama,
bayan ya gama ne sai ya kuma komawa kan kujera ya zauna,
sannan k'awayen Amarya suka rink'a tattara kud'ad'en.

Bayan sun gama ne Hamma Umar d'in ya sake tashi tsaye cikin cikar haiba da kamala gaban Ummul d'in ya kuma tsayawa cikin k'asaita yace.
"Yanzu a matsayin aggo zanyi lik'in."
marok'an ko tuni suka cika wurin da kirari suna.
"Ummaru sand'a babuga mai nera Ummaru mai ado da zinari Ummaru Farouq mai K'amshin al'miski
kunji Umaru Farouq babban adali doctor mai tausayi da jink'ai."

Shi kuwa Hamma Umar Dolas ya zaro ya rink'a yiwa Ummul b'arinsu a kanta,
Ya Usman kuma na tsaye a gefen shi rik'e da turaren mai suna *du'a'ul jannarh* mai tsananin k'amshin,
bayan Hamma Umar ya gama lik'in sai ya kuma mik'a hannu ya karb'i turaren dake hannun Ya Usman,
sannan ya d'an sunkuyo kan Ummul d'in ciki kallon fuskar ta ya fara fesa mata turaren yanayi yana k'ara matsota har ya isa gab da Ita sannan ya mik'ewa Usman turaren ,
a hankali ya rokk'fo gaban ta sannan ya sunkuye dai-dai kanta,
mutanen wurin kuwa gaba dayasun maida hankalin su sukayi kan Hamma Umar d'in domin son ganin me zai aika ta,
Hajjajo kuwa da Inna tuni sun fara mamakin abinda Umar d'in yake shirin aika tawa,
sauran mutane kuma gaba d'aya kallon shi suke cikin tarin mamaki dan gano abinda yake shirin aika tawa,
Ammin kuwa lokaci d'aya taji wasu siraran hawaye na bin fuskata tana kallon Abin da Babban d'an nata zaiyi,
Abokan Hamma Umar kuwa ido suka zuba mai cikin mamaki su Hamma Yusuf duk an cika da mamaki sai k'ara rik'e hannun Ayshan sa yake.

Itako Ummul gaba d'aya jikin ta sai kerma yake ido kawai ta zubawa Hamma Umar d'in fuskar ta cike da k'olloh,
Nenne ma ido ta zuba mishi dan gano abinda zaiyi.

Shi kuwa Hamma Umar cikin wani irin yanayi yasa hannushi ya cire hular kanshi sannan ya k'ara sunku yowa kan Ummul d'in tare da manna....

By
*GARKUWAR FULANI*📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*RUBUTACCEN AL,AMARI*

Page 9⃣

*NA*
*AYSHA ALI GARKUWA*

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*Alhamdulillah ala kulli halin nayi tafiya lfy na dawo lfy yanzu zanci gaba da typing insha Allah har k'arshe*

```NI na jinjina muku y'an KADUNA bamai rabani daku jama'ar KANO kui hak'uri ga shafinku ya iso mun jinjina muku reedars damu writers daku d'ayane bamai rabu daku sai Allah kui hak'uri ga pagenku ya fito kanawa sunce mini GARKUWAR a baya kinyi wani kuskure duk novels da kinkayi a social media dad'in su yayi ta kewaya nahiya sun shiga sak'ok'in Nigeria shin meyasa kika ware hausawa bakya yin novels da su sai FULANI? Hausawa ne sukayi min wannan tabbayar shaidar suna k'aunata gaba d'aya, NIKO NACE MUSU , dole naje duk inda rebo yake dan bani Rena masoya na kuma ban raina ranar da novel yayi mini ta sanadi an sannu garuruwa INA alfahari da Gombe Taraba ADAMAWA YOLA gida nake tun fari su sukayi mini GARKUWA😘 tunda nazo a cikin y'ay'an Adam duk ajizi an sanshi da kuskure kuyi hak'uri novelna na gaba da hausawa yana nan tafe, dan ni garin mosoya nisa bai mini da na fad'a kuma yanzu ina tuni Allah ya kaddara in zamto Zuma dana fito ai tayi mini sansani, yau hak'uri zan bawa hausawa dan sunfi so na tsaya tamkar gini, RABBI nufeni silar novel da zanyi mutan k'asarmu su zauna lfy,
Forko mutan KANO zanai kira wanda fagen nema basa jira maza da mata Manya da k'ank'ana a gsky na sansu da Hattara sunce nazo naga yadda abin yake sannan na tabbaya ni sukayi jira na mori so da k'aunar da suke mini sannan sunce na dage fannin k'irk'ira🤝😘Kanawa wannan shafi naku ne```
Chapter 12 · 0% Book details