← Book details Rubutaccen Alamari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 77

Sashe 21

Rubutaccen Alamari Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Sai kuma ya k'ara rugumoshi jikin shi cikin rawan jiki,
Abba ne yasa hannu ya jawo Usman d'in jikin shi cikin k'arfin hali irin na manya ya cewa Daddy.
"Hussaini kawo wuruwa."
jiki na rawa Daddy ya shiga cikin gidan,
Ammi kuwa tunda Usman ya fad'i gaba d'aya sai jikin ta ya fara rawa kar-kar ko ina na jikin ta ya sake k'afafun ta suka k'asa d'aukar nauyin ta zuciyar ta sai bugawa take tara-tara cikin wani irin rashin kuzari ta zame a wurin ta zauna ta jingina da kujaran da Usman yake kai cikin sanyi baki na rawa take cewa.
"Ya Allah ka rufa min asiri Allah ka dub'eni da idon rahama Allah ka hanani ganin mugun abu Allah ka jinkirtawa wannan bawa naka kabashi lafiya Usman Allah ya hanani ganin gawarka ganin na mahaifinku ma har yau bai bar idanuna ba."
Inna ce ta dafa ta cikin sanyi tace.
"Kiyi mishi Addu'a Amina addu'arki gare shi ba hijabi insha Allah karb'ebb'iya ce ."
jin haka sai zuciyar Ammi ta kara karaya cikin sanyi ta kontar da kanta a cin yar Innarta ta kamo hannun Usman ta rink'a wani irin kuka mai cike da fargabar faruwar wani abu,
Hajjajo ma sai kukan takeyi ya Sadip da Aliyu ma gaba d'aya sun k'asa saida hawaye su Anty Halima kuwa cikin gida ta shiga tana kuka cur-cur,
Daddy kuwa yana zuwa ya d'auko goran ruwan mai sanyi ya dawo Abba ya mik'a wa,
yana karb'a ya b'alle marfin gorar sannan ya tuttulo ruwan sanyin a tafin hannun shi da k'arfi ya watsa a fuskar Usman d'in,
a take sai yayi wani irin ajiyan zuciya mai k'arfi sai kuma yayi shiru numfashi sa na harbaqa ,
cikin kuka Ammi ta rik'o hannun shi tana.
"Usman ! Usman! Usmaaaan!." sai kuma ta fashe da kuka,
Shi kuwa can sama-sama yake jin sautin kukan mahaifiyar shi da sauran yan uwa,
cikin tsananin mutuwa jiki ya bud'e idanun shi kuma sai ya lumshe su ganin baya ganin su sosai ,
su kuwa ganin haka yasa Ya Adam ya zaro woyarshi da sauri yace.
"Abba bari in kira Hamma Umar yazo ya duba shi."
jin hakan yasa Usman d'in ya k'ara bud'e idanun shi cikin rawan. Murya yace.
"Ah,Ah a a Adam kar ka gayawa Hamma Umar komai ka barshi ,
naji sauk'i."
meda woyar Adama yayi cikin jin dad'i ya kamashi ya rugume murya na rawa yace.
"Usman meyasa kake wasa da lafiyar ka me kake tunawa me damuwarka a duniyar nan Usman?."
cikin k'arfin hali ya d'an ture Adam sannan ya d'an jingina da jikin kujerar ya kamo hannun Ammin shi ya kalli Hajjajo da inna dake ta zubda k'ollah yace.
"Kai da Allah ni ku dena min kuka lafiyata lau ji tsoffin nan fa aini ras na ke sai namu rakiya kafin nima a min rakiya zuwa gidana na gaskiya,
Abba kace su dena kuka ni na worke."
Sai kuma ya kalli Ammin shi cikin sanyi yace.
"Ammi shi komai da kika gani a duniyar nan toh Rubutaccen al'amari ne so karki damu ki sawa ranki dangana insha Allah ba zakiyi kuka ba matukar Hamma Umar na yana raye,
karki damu shi d'aya ne tamkar da mu biyu kinji ko Ammi na."
kanshi ta shafa cikin rawan murya tace.
"Ku duk ina fatan ku rayu har bayan rayuwa ta."
dariya ya d'an yi sannan ya kalli Abba da Daddy dake binshi da ido cikin fidda numfashi mai nauyi yace .
"Dan Allah Abba kar a gayawa Hamma na kunga kar hankalin shi ya tashi."
Nenne ce ta kalleshi a hankali tace,
"Kasha maganin ka yau?."
Kai ya gyad'a mata sannan yace.
"Hamma Umar ya bani kafin ya tafi."
so haka yayi ta basu k'arfin guiwa ya kuwa hanasu su gayawa Umar,
a haka sukayi ta mishi nasiha kan shan maganin shi, sannan Abba yace daga yau shi da Adam zasuke kwana tare,
haka kuwa akayi,
shi kuwa Usman,
suna shiga d'akin nasu ya zame ya shiga toilet k'ofar ya maida ya rufe cikin tarin takaici dajin haushin kanshi da zuciyar shi ya kife kanshi jikin gini ya rink'a wani irin kuka maicin rai kuka yake yana d'an dukan saitin kahon zuciyar shi cikin kukan yake cewa.
"Kai tona da Wannan zuciya tawa mai zuwa hurumin daba nataba."
haka yasha kuka har saida yaji kamar numfashi sa zai yanke sannan yayi al'wala ya fito ya shimfid'a sallaya ya fuskanci gabar,
Adam ne ya kalleshi cikin kula yace.
"Usman zaka iya tsayuwa ? ka konta mana ka d'an huta."
Murmushi yayi cin juya fuskar sa dan baya son Adam yaga idanuwan shi da sukayi jazir suka kumbura,
cikin yanayin wasa yace.
"Kai nafa fika lafiya kuma zanyi wa Hamma na da Ummul addu'ar Allah ya basu zaman lafiya dakuma 'yan biyu."
dariya Adam yayi tare da cewa.
"A a yan ukune ba yan biyu ba."

Toh hakafa rayuwa tayi ta juyawa Usman kullum yakan b'uya yasha kuka har sai yayi gyatsa ya kuma ji numfashi sa na carkewa sannan ya fito,
ba kuma wanda yasan halin da yake ciki.

*Gidan Hamma Umar da Ummul kuwa*

Bayan sun shiga cikin gida Hamma Umar na rik'e da Hannun Ummul d'in a haka ya jata har bak'in k'ofar shiga cikin asalin gidan bak'in k'ofar parlour ya tsaya key ya zaro a haljihun shi sannan ya bud'e k'ofar cikin bada umurni yace.
"Kiyi Addu'a ki kuma shiga da k'afar dama."
bata kulashi ba sai k'ollah da take zubda wa sannan tayi yadda yacen,
suna shiga cikin Parlour Ummul tayi fizge hannun ta cikin kallon yadda Abban ta ya binne mata dukiya a parlour fuska cike da k'ollah tayi cikin bedroom da gudu tana zuwa shiga ta maida kamar ta rufe kan gado ta fad'a cikin disashewar murya taci gaba da sana'arta,
shi kuwa Hamma Umar shiru yayi a parlour ya tsurawa k'ofar d'akin ido yana jin sautin kukan can k'asa-k'asa kai ya juya ya fito kai tsaye motar shi ya shigar cikin gida ya ajiye ta a harabar gidan sannan ya bud'e bayan motar ya d'auko lodojin da ya ciko da abubuwan cin da sha,
kai tsaye parlour ya shigo kan dinning table ya ajiye ledojin sannan ya bi d'an corridor dake gefen d'akin da Ummul ta shigan nan ma wani d'aki ne babba wanda yasha gyara da shimfid'u daga dukan alamu dama nanne d'akin da yake rayuwa in yazo Damaturun daga can d'aya b'arin kuma nan ma akwai wani bedroom d'in dan gidane mai yalwar d'akuna parlour ne guda d'aya babba wanda ke d'auke da dinning area mai girma da tsarina sai daga gefen shi wani d'an corridor ne da zai sadaka da kitchen sai sito dake manner a gefen shi,
ta bayan kitchen din kuwa d'an k'aramin wurine mai cike da tsirrai masu kyau ,
cikin parlour kuwa yana d'auke da 3 bedroom,
so yana shiga d'akin sa wonka yayi sannan ya fito yayi shirin baccin sa,
parlour ya fito cikin nitsuwa yana taku mai cike da haiba a hankali ya jawo kujara ya zauna a dinning table d'in kanshi ya jingina jikin kujerar sannan ya d'ora k'afafun shi kan table d'in yana d'an kad'a su a hankali ida nunshi ya lumshe tare da kamo lips d'in shi ya matse yana jin yadda Ummul ke yin kuka cikin sauti mai cike da rauni da wahala da alamun gajiya daga kuma jin sautin kukan da alamun zazzab'i a jikin ta,
ido ya k'ara rumtsewa dan yana jin kukan nata na ratsashi dan window d'akin ta yana ta saitin dinning area d'in,
cikin sanyi ya mik'e a hankali yaje bak'in k'ofar, cikin murya mai cike da tausayawa yace.
"Khairi kiyi hak'uri ki dena kukan nan ya isa kizo ki bud'e k'ofar kinji kibar kukan kar ya saki zazzab'i ki fito kici abinci kinji ko Khairi?."
kukan Ummul ta kuma k'ara yi cikin dishewar muryar tace.
"Bazan fito ba,
ka barni nayi kukana in banyi kukaba me zanyi ? bazanci abincin ba inya so yunwar ta kasheni kowa ya huta tunda dama ba,a sona."
Shiru yayi sannan ya d'an yi ajiyan zuciya tare da cewa.
"Khairi baki da lafiya fa ki bud'e kizo kici abinci kisha maganin inyaso kyaci gaba da kukan tunda shi kikeso ."
bata kuma kula shi ba haka tayi ta kukan ta yayi ta lallashin ta a banza,
haka ya hakura ya barta ya koma bedroom d'in shi ba tare da yaci abincin ba,
ita kuwa haka ta kwana kuka har Allah ya wayi gari.
Chapter 21 · 0% Book details