Sashe 16
Rubutaccen Alamari Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
shi kuwa Hamma Umar ko inda take bai kallah ba ya fice yana d'ingisa k'afar,
ya Usman kuwa karb'a laptop d'in Hamman nashi yayi ya rik'e cikin raunin fuskar sa kamar zaiyi kuka dan tausayawa d'an uwan nashi,
har zasu fita ya juyo ya kalli Ummul d'in cikin raunin da yanayin tuhuma dan ya gane itace silar ciwon Hamman nashi,
itama kallon shi takeyi cikin sanyi ta rumtse idonta,
shi kuwa juyawa sukayi suka tafi.
Suna zuwa part d'in su Hamm Umar d'in yayiwa yatsar tashi dressing sannan yawa kanshi allurar ya kuma sha magani.
Ita kuwa Ummul suna fita Anty Shuwa da Anty Halima suka jata d'akin dake gefen na Hajjajo suka rink'a yi mata gyare-gyare tare da tsumata da irin tsumukansu na shuwa'arab ,
Anty Shuwa ce ta b'alle marfin wani roba sannan ta jijjiga tare da mik'ewa Ummul d'in cikin tsuke fuska tace.
"Karb'a ki shanye yanzu ki bani robar."
Kai Ummul d'in ta karya cikin kuka da gajiya da d'ure-d'uren da suke mata tace.
"Ni dai amai nakeji dan Allah a barni hakanan."
A fad'ace Anty Shuwa tace .
"Sai kinsha muguwar banza yadda kike mishi mugunta haka zai rama kiji tsoron mutumin da baya magana inya tashi ramawa zaki yabbawa aya zakinta."
kai Halima ta jinjina sannan tace .
"Gaya mata dai Anty wallahi wata rana zakiyi nadama abinda kikewa Hamma Umar d'in."
Haka suka rink'a yi mata fad'a da nasiha sunayi suna tsumata tare da dilketa da murjeta.
Haka nan kullum Sai sun murjeta sun tsumata,
ta fito tayi rasa sai wani shek'i take tamkar tarwad'a fatar jikinta kuma tamkar auduga komai nata yasha gyara sai wani k'amshin mai sanyi take fiddawa ko wucewa tayi k'amshin ta sai ya ratsa wurin
gashin kanta kuwa ba'a maganar gyaran d'aya sha, an gyareshi gyara na mussamman k'afafun ta da hannayen ta kuwa an musu zanen Lalle na mu samman komai na Ummul ya fito rasa ta fito a shuwa'arab d'in sak.
A gefen ago Hamma Umar kuwa ,
komai Ya Usman ne yake gudanarwa gaba d'aya ya gayyato abokon Hamma Umar d'in nashi ...
Yau ta kama Jumma haji babbar rana Wanda ya kasance gobe asabar ne za'ayi d'aurin aure Ummul da Hamma Umar .
Toh a rayuwar shuwa'arab akwai wata al'adar da sukeyi a duk lokacin da zasuyi bikin su ,
suna yin wannan al'adar tasune kamar gone za'a d'aura aure ,
kuma wannan al'adar tasu tana kunshe da wata al'adar kuwa Wanda a halin gaskiya a yanzu haka gaba d'aya shuwa'arab sunbar yin wannan al'adar ta biyun na farin dai sunyi Amman na biyun kam ,
a shuwa'arab d'in ma na zamanin yanzu da yawa basuma san al'adar ba dan tuni anbar yin al'adar duk da dai a zamanin da d'in ma a cikin aggwaye 100 da wuya a samu aggwaye 5 masu yin wannan al'adar domain al'adace mai nuni da d'auka alk'awari da kuma rik'o da amana suna kiran al'adar da sunan *Nad'in uwar gida*
So shiyasa aggwayen yanzu basa wannan al'adar ta biyun kenan fa,
Amman na farin kam har yanzu shuwa'arab sunyi kuma in an gama na farinne akeyin na biyun,
so Yau jumma'a tun safe aketa shirin wannan al'adar tasu na. farin wanda dama asan dashi shi kuwa na biyu ba wanda yake da tabbacin za'ayishi a cikin shuwanma wasu basu san da wannan ba,
tun safe aka k'afa tantuna a harabar gidan nasu aka shimfid'a kilisai na al'farma aka ajiye kujera na gani na fad'a kujera masu taushi gaba d'aya an zagaye wurin da kolliyoyin zamani tare dana al'adun shuwa'arab d'in,
cikin kujerun kuwa a tsakiyar kujerun akwai na aggo da amarya wanda sunayen su ke rubuce a Kansu sai na k'awayen Amarya da abokin aggo suma duk sunayen su na rubuce akan kujerun nasu.
Yadda ake al'adar tasu kuwa bayan an gama kimtsa wurin aggo zai fara zuwaya zauna da zugar abokan shi sai bayan ya zauna da mintuna kad'an sai a fito da amarya,
fito da amaryarna kuma 'Yar uwar amaryar ce ta jini zata fito da amariyar rik'e da hannun ta ,
sai ta mik'a hannun amariyar ga hannun y'ar uwar aggo ko d'an uwan aggon,
daga nan sai shiko d'an uwanshi ago yaja hannun Amarya ya kaita kusa da aggon ya ajiyeta,
so y'an uwa da abokin arzik'i zasu tashi sunyi ta yiwa Amarya lik'in kud'i da gudumowowinsu,
bayan duk an gama lik'inne sai shi kuwa aggo ya tashi yayi nashi lik'in,
shike nan itace al'adar su ta farin .
So haka aka tsaba wannan al'adar bayan an sauk'o sallan jumma'a Hamma Umar da abokanshi duk suka dawo gidan suka d'an huta sannan matayen su kuwa suna cikin gida ,
bayan anyi sallan la'asarne sannan aka fara shirin fita wurin taron,
abokon Hamma Umar manyane masu cikar kamala abokai ne daku masu karatu kun sansu haka kuwa matayen su,
haka sukayi shiga ta al'farma shiga irin ta shuwa'arab d'in sukayi baki d'ayan su suka fito rasa tamkar larabawa,
Suma matayen su da k'awayen Amarya Ummul shiga sukayi ta shuwa'arab d'in gaba d'ayan su laffaya suka yane jikin su dashi suma dama gasu kyawawa. Haka yasa wurin taron ya zama tamkar a k'asar larabane ,
wani abin burgewa kuwa duk woni sak'o da luggu har cikin fulawowi na gidan an ajiye kaskon turaren wuta sai wani irin k'amshin ke tashi hakan yasa nishad'i a zuk'atan duk wani bani adam dake zaune a wurin.
5:00 pm zugar ago da abokanshi suka ido farfajiyar gidan Ya Usman ne a gaba yayinda sauran abokon ke binshi a baya ,
Hamma Umar kuwa yana tsakiyar su yasha sutura ta al'farma ya fito cikin haiba da cikar zati sajenshi sai wani irin shek'i yakeyi farar fatarshi ta fito ras tamkar balarabe sumar kanshi kuwa. yayi luf gwanin sha'awa ya murza hula a kan nashi yayinda gashin nashi yabi k'eyarshi da zagayen fuskar shi,
idanun shi kuwa wani d'an siririn glass ne mai haske irin na Doctors ke manner a fuskar sa.
dai-dai lokacin da suka fito a dai-dai lokacin kuma matayen abokan aggon suna suka fito ,
gaba d'aya wani taku suke a jere kamar yadda kujerun ke Jere kowa da matarsa a gefen Hamma Umar ne ya fara zama sai babban abokin shi ,
Hamma Yusuf da Ayshar sa sai Hamma Hassan da Fateemar shi sai kuma. Hamma Bashir da Ruk'ayyar shi
Sai Hamma Mahmoud da Khadija shi sai kuma Hamma Aliyu Haydar tare da Minalin shi,
A d'aya gefen kuwa
wasu manyan abokan Hamma Umar d'in na gani da matayen su, Amadi da Nadiyar shi,
sai Abuturrab da Batul d'in shi sai kuma Salim da Tawa
Sai Abdullahi tare da Maryam d'in shi,
daga gefen su kuwa Fauziyya ce da Al'ameen sai Aisar tare da
Bintun shi
sai kuma Abbah da Ruky pinkyn shi,
ga kuma Ridwan da Zakiyya
can kuma kusa dasu Ahmad Ana Muslim ne tare da khadijan shi
sai kuma Assadiq da Safiyyar shi tare Hibbah da Faheem.
Gaba d'aya sun zauna cikin nitsuwa da al'farma suna zaune cikin cikar haiba sun fito tamkar taurari sai shek'i sukeyi da wani irin k'amshin da suke zubawa zamane sukayi na masoyan gaske.
Bayan sun zauna da kamar minti 5 Dangi da k'awayen Amarya da sauran mutane sukazo suka zauna,
cikin nitsuwa da lumana,
Jim kad'an,
suka fara jiyo wani irin k'amshin na k'ara ratsa hancin su gaba d'aya sai wani irin shauk'i ya ziyar cesu ido suka lumshe tare da jin dad'in k'amshin dake k'ara bud'e su wanda Anty shuwace ke rik'e da kaskon turaren wuta,
Anty Halima kuwa na biye da Ita a baya tana rik'e da hannun Ummul wacce tasha gyara iya gyara an yaneta cikin laffaya mai tsadar gaske ta fito a shuwa'arab d'in sak ta fito tamkar tauraruwar zarah dake kusa da wata,
Anty Halima na rik'e da hannun ta suka iso farfajiyar gidan yayinda ita kuwa Ummul kanta ke sunkuye idanun ta na zubda wasu irin wahaye masu zafi da tafasa zuciya tafiya takeyi tamkar hawainiya,
suna isowa Ya Usman ya mik'e cikin happy yaje gabansu ya tsaya cikin wani irin salon al'darsu ya d'an kife guiwarsa d'aya a k'asa sannan ya d'an d'ago hannunsh sama kad'an ya ware tafin hannushi cikin sanyi yace.
"Halima samin hannun matar Hamma na cikin tafin hannuna ni zan kaiwa Hamman matarsa kusa dashi."