← Book details Rubutaccen Alamari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 77

Sashe 65

Rubutaccen Alamari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kamar yau aikin hajji ya k'are dan haka suka d'unguma sai Dubai inda zasu kwana kafin da safe suwuto gida Nigeria,
Wannan yaba Ummul damar bud'e data ta tayi sa a Auntyn ta tana online taji dad'in ganin ta saboda hakanan taji tana buk'atar su tattauna akan abunda yake damunta,
sallama ta yimata bayan su gaisa sosai ne Ummul tafara tambaya kamar haka, " Aunty dan Allah dagaske ne yanzu idan nasake aure shikenan na rabu da Hamma Umar na rabu da aurensa na tashi a matsayin matar Hamma Umar?". Tambayar ta bawata tausayi duk da tasaba da shirmen Ummul d'in, cikin sigar lallashi data saba da yimata tace, "Meya kawo wannan tambayar dear?". Shagwab'ewa tayi kamar zatai kuka tace, "Ya Usman ne yadameni kan maganar aure nikuma gaskiya banason kowa kuma banaso inzauna da kowa sai Hammana Aunty Aysha wallahi ina son Hamma na duk duniya yanzu shi nake so".
Ajiyar zuciya tasauke sannan tace,
"Haba Ummuna, tun kafin kiyi tafiyar nan muke magana guda d'aya kuma kinga dukkan mu burin mu mu samar maki da farin ciki wannan shiyasa zakiga kowa nada burin kiyi aure saboda auren shine kad'ai hanyar da zaki sami nutsuwa kuma kisamar wa Hamman ki kwanciyar hankali dan in kinyi aure zaki rege zubarmai da hawaye,
kuma ta hanyar auren Usman ne zaki samu farin ciki mai d'orewa, k'anwata auren Usman shine kwanciyar hankalinki dana iyayenki dakuma na yaronki kai harma dana Hamman ki Allah yamai rahama".
"Amin" ta amsa sannan taci gaba,
"Zai kasance cikin farin ciki kina kulamai da d'anshi da k'anin shi sannan iyayenku su kasance cikin farin ciki kuma su manta da duk abinda ya faru a baya da yafe maki kuskurenki na bijire musu da kikayi a baya".
Sannan taci gaba cewa, "Ki d'aure zuciyar ki nasan dole zakiji babu dad'i kuma dole akwai ciwo a zuciyar ki amma ki daure kiyi hak'uri kinji k'anwata ki yarda da auren Usman".
Hannu tasa tashare k'ollah dake zubowa daga idonta sannan ta fara typing amsa,
"To Aunty Aysha insha Allah zanyi hakan sabida farin cikin Hamma na da iyayena, nagode da kulawarki gareni".
hakanan daga nan kuma hirar takoma rarrashi saboda kukan da dukkansu sukeyi.

K'arfe 12 na dare jigin su yasauka a filin sauka da tashin jirage na Aminu kano a cikin birnin kano,
a Tahir guest palace suka kwana sannan da safe suka d'auko hanyar Potiskum, ya Usman da ya Adam ne sukaje d'aukosu haka suka dungumo misalin k'arfe 10:08 suka iso gida,
Sunsami kowa cikin k'oshin lafiya Umar Farouq tunda suka iso ya haye jikin mahaifiyarshi yanata bata labari na abubuwan da suka faru bata nan haka suka wuni cikin nishad'i sai bayan sallah isha'i ya Usman yamaida Halima da yaranta gida shima Adam yamaida Aunty Shuwa da Inna tunda unguwarsu d'aya,
Adam na dawowa yawuce b'angarensu dan yana buk'atar hutu, shiko gogan Ummul daman Allah-Allah yake bak'in su tafi ya gana da masoyiyar shi tun yana mota yakira wayarta tana d'auka yace,
"Ki jirani a palour Nanne baijira amsartaba ya katse kiran.

A parlour ya sameta tana kwance akan kujera yana shiga da sallama tamik'e zaune ta amsamai kusa da ita yaje yazauna yasauke ajiyar zuciya sannan ya kure ta da ido cikin tsananin so yace,
"gaskiya kin rame baby, dama nayita tunanin hakan".
d'an murmushi tayi sannan ta sunkuyar dakai k'asa tace,
"ya Usman tunda naje a wuraren Ibadan nake tarewa ina yiwa Hamma na addu'a da nema mishi rahamar Allah ko cin abinci bana son fita,
ranar na d'an fara gyagyad'i sai nayi mafarkin Hamma na yana nuna min kai yana cemin inje gareka kar in bari ka zubda hawaye".
sai kuma tayi shiru tana zubda k'ollah,
sai kuma tace,
"ya Usman ka gafar ceni".
A hankali ya sake matsota yakamo hannayen ta duka biyu ya rik'e da kasalalliyar murya shi yace, "bantab'a jin b'acin rai akan duk abinda kike fad'a kinyi ba,
nasha fad'a miki komai kikayi birgeni yake kuma komai kyau yake miki nagode da kulawarki ga d'an uwana".

Shiru sukayi dukkansu yanata matsa hannunta dake rik'e a hannun shi ya katse shirun da cewa,
"Fatana ki yarda da aurena".
sai kumu yasa hannu ya d'ago fuskarta tare da cewa,
"Kamar kinada magana ko?".
K'asa tayi dakai murya na rawa a hankali tace,
"inaso ".
da sauri yace,
"kina son me"?.
ido ta lumshe cikin zubda k'ollah tace,
"Ince son ince maka na amince da maganar auren".
Kasa k'arasawa tayi tafashe da kuka,
jiki na rawa ya janyota jikinshi ya had'ata da kirjin ya ruggume ta da k'arfinshi ta yanda har tana jiyo bugawar da zuciyar shi takeyi ido ya lumshe yanajin wani irin yanayi da bai tab'a jiba hakan yasa yakasa daurewa shima yafara k'ollah,
kamar ya tuna wani abu yasa tafin hannu shi ya goge k'ollar idon shi yasake matso ta yace,
"Yi hakuri kinji, kinga narasa mezance maki dan murna amma dai nasan yau matsalata ta k'are".
Sakinta yayi ya sauka daga kujerar ya durkusa yayi sujjada yayiwa Allah godiya sannan ya juyo yazauna gabanta ya d'ora kanshi akan cinyarta kamar k'aramin yaro yasauke nannauyar ajiyar zuciya yace, " inasonki ina k'aunarki". A hankali takai hannun ta d'aya kan gashin kanshi ta tusa yatsun ta ciki tana d'an tureshi, runtse ido yayi da k'arfi yanajin wani irin abu da baitab'a jiba kuma bazai iya kwatan tawaba,
itace ta dawo dashi daga halin dayake ciki dacewa,
"Naji dad'in samun Aunty Aysha Garkuwa domin ko yaushe shawararta irin ta Ammi da Nenne ce kuma in nabi ina jin dad'i".
d'ago kanshi yayi ya kureta da ido hakan yasa tai shiru cikin kunya tafara wasa da yatsunta,
shi kuwa sake tashi yayi ya zauna gefen ta sannan ya ruk'o hanna yenta murya a raunane yace,
"Nasani my life nasan wannan yafaru da ikon Allah da taimakon ta hak'ik'a ni dai GARKUWA tayi min rana".
sai kuma ya d'an fizgota cikin tsananin shauk'i yace,
"inna fad'a miki toh ki rik'e mini duk tsanani da wuya zana sakar miki sona kiyi rik'ona don Allah kar naga kin gajiya,
in dai kikayi haka so zai habaka zamuga kyen tafiyar,
da shak'uwa aka samu yarda har so yassanya muna kama da juna".
shiru tayi tana jin salon son ya Usman d'in ta mai cike da kalamai masu sanyi gaba d'aya ya kashe mata jiki sai k'ara narke mishi takeyi cikin Shauk'i ya tallabo fuskarta ido ya kashe mata tare da kashe murya cikin rad'a yace,
"Bisa dukkan alama an yabamini Kumar nasan zanga kyen yanayi domin kinmin halin mutuntawa duk kin gwada mini su tunda kin amince na zama mijin ki ni kuwa dole na k'arfafa so da k'auna nayi miki rik'on da ba shayi,
gurin zaman auren mu in kyautata miki domin muyi zama na faran tawa juna rai".
cikin jin kunya murya can k'asa tace,
"Ni nace maka kwarai ina so dan haka karka fidda rebo,
me kake so ya zama alamar sona a gareka don akwai sabo a tsaka ninmu inko yarda ta kake buk'ata to ka sanya a ranka ka samu,
dan kai gudane da bani da kamar ka nida Hamma na da Farouq a zuk'atan mu".
Murmushi yayi cikin jin dad'i yace,
"Ummu na ina da matsala fa ban sani ba ko zaki iya d'aukar nauyin yawan buk'atata gaskiya gwara na shaida miki tun yanzu kar sai munyi aure kice na matsa miki ko na fiye jaraba,
kuma ko a Shari'ance dama in gaya miki kisan irin mijin da zaki aura".
kanta ta sunkuyar cikin jin tsananin kunya hakan yasa ta kasa maga sai kai ta gyad'a mai murmushi yayi cikin tsananin jin dad'i yace,
"Dole in gwada miki farin cikina gaskiya kinyi na yaba miki al'k'awari kuma zan rik'e miki wurin zaman aurenmu wallahi bazan matsa mikiba zan sakaki a cikin farin ciki zuciyar ki na cire mata bak'in ciki da duk wani k'unci tunda kema kin yimin halacci domin kinyi rik'o da amana tunda kin amince dani".
ido ta lumshe cikin sanyi da jin kasala da kalaman ya Usman d'in nata,
a hankali tace,
"Lallai shak'uwa tana sanya yarda a tsakanin mu tabbas idan nace maka a zuciya ta kai na zab'a ka gaskatani ka bani dama,
amman in dai sone har gobe Hamma nane kawai nake so a raina ya Usman sai kayi hak'uri dani".
Ajiyar zuciya ya sauk'e sannan ya kamo hannun ta ya tsaida ita cikin mayen so da juyewar idanu yace,
"zan rayu dake cikin aminci son da kikeyiwa Hamma na ma kawai ya wadatar dani ko baki soniba ba matsala tunda kinso d'an uwana Kuma nasan nima wata rana zaki soni".

Haka suka kasance cikin hirar su ta soyayya duk da bakomai take amsamai ba amma saida suka raba dare suna hira sai k'arfe 3:15 ya rakata har bakin kofar d'aki ta shiga yanajin kamar kada su rabu sannan ya juya ya tafi part ensu.

Yana shiga bedroom ensu yasami Adam yayi d'ai-d'ai a gado yana baccin gajiya kasa hak'uri yayi yasa hannu yad'an bugi k'afar shi, da k'yar ya bud'e ido yad'ago kai yace,
"yadai?".
zama yayi kusa dashi a kan gadon yace,
"Tashi kasha labari naci zab'e Dr Bashir da Mustapha duk sun fad'i jam'iyata ta kafu k'ark'ashin jam'iyar Hamma na naci albarkacin d'an uwana duk da baya raye amman a sana dinshi nake farin ciki".
"a a dan Allah ka barni nai bacci na kaban labarin da safe".
Adam yafad'a yana gyara kwanciya,
da sauri shiko ya rik'oshi ya k'arasa zaunar dashi yana cewa,
"Gwarama ka tsaya kaji wlh dan bazan barka kayi baccin nan ba". Adam da yakeson yacigaba da bacci yace, "To menene?".
"Ummul ce". yace shiko katse shi yayi da cewa,
"ai dama nasani koyaushe maganar kenan".
hannu yasa ya toshemai baki yace,
"Kai ba irin wannan labarin bane,
yau da bakinta tace ta amince da aure na".
"congrat Allah sanya alkhairi". daga haka ya juya yaci gaba da baccin shi,
shiko mik'ewa yayi yaje yayi wanka da alwola yazo yayi ta nafiloli da karatun Qur'ani har aka kira sallah asuba.
Chapter 65 · 0% Book details