← Book details Rubutaccen Alamari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 77

Sashe 64

Rubutaccen Alamari Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

A parlour kuwa dakyar shima ya yunk'ura a daddafe yashige bedroom din ya fad'a kan gado hannun shi rik'e da marar shi yayita mirginawa yana juyi hawaye na bin fuskarshi pillow ya jawo Ya rungume da k'arfi yanajin wani irin yanayi na shigar shi,
yad'au lokaci a haka sannan ya tashi dak'yar yafad'a bathroom yasakarwa kanshi ruwa sannan yafito ya shirya tsaf ya d'au mukullin mota yayi b'angaren Nanne .

Kwance yasami Ummul kan gado kamar me bacci Ammi kuma da shigowarta d'akin kenan tana ajiye kayan data shigo dasu ya rusuna k'asa yasake gaida ta amsa tayi sannan tasami bakin gadon ta zauna saida yayi kamar zai tashi sai kuma ya zauna yace,
"Yauwa Ammi akan maganar rubuta littafin da Ummul takeso d'azu munkira ita marubuciyar munyi magana shine nace mata zan had'aku da ita tasake ji daga bakin ki saboda tad'au abin da muhimmanci duk da dai daga yanayin yanda mukai magana da ita baza a samu wata matsalaba kuma bisa ga dukkan alamu Ummul ta k'ara samun Aunty dan bakiga yadda tayita rarrashinta d'azuba".
Nan da nan Ammi taji k'aunar marubuciyar na ratsata kasancewar a yanzu bata da burin daya wuce ganin samun kwanciyar hankalin Ummul d'in ta da murna tace,
" To madallah kirata muyi magana kaga sai nasake mata godiya". D'an d'agowa yayi ya lek'o kan gadon yace, "Khairi mik'omin wayar ki".
Dana sauri Ammin tace, "Haba Usman kace in mik'omaka mana saika tayarmin da ita daga baccin tun d'azufa kuka take yi da kyer na samu tayi shiru".
A hankali ta d'an d'ago kanta wadda daman tana jin duk zancen nasu ta d'auko wayar tayi ta mik'o mai,
Kanshi a sunkuye yasa hannun zai karb'i woyar cikin hikima ya had'e wayar da hannun ta ya rik'e yana murza yatsunshi biyu kan yatsunta cikin salon lallashi da so,
da sauri ta zame hannun ta tana kallon Ammi,
Itako Ammo batama ga abinda suka yiba, Dialling number yayi bata jima tana ringing ba ta d'auka sannan ya mik'awa Ammi ta karb'a tasa a kunnen ta sannan tace,
"Assalamu alaikum". Cikin muryarta mai sanyi da saisaita zuciya ta amsa sallamar sannan tace,
"Wa alaikissalam ina kwana".
gyara zama Ammin tayi tana fara a tace,
"lafiya lau d'iyar albarka, ya yaranki ? da mai gidan ? ya kuma gurin manya?".
Cikin ladabi ta amsa da, "lafya lau Alhamdulillah".
cikin girma Ammi taci gaba da cewa,
"Y'an nan Ammin Ummul ce".
jin hakan Garkuwar cikin tausayawa tace, "Ayyah Ammi kece ya hakurin mu na rashin Hamma Umar? Allah ya jik'an shi yamai rahama yasa can yafi masa nan ku kuma Allah ya k'ara maku juriya da hak'urin rashin shi".
Cikin sanyi Ammi ta amsa mata da,
"Ameen nagode Allah ya bada lada".
sannan tayi ajiyan zuciya tare da ci gaba da cewa,
"Usman ya sanar dani yadda duk kuka yi akan rubutun littafin kuma yace kinaso ki k'ara tabbatar da sahihancin labarin shiyasa nasa baki kuma nake fatan zaki karb'i abun dan taimakawa".
Shiru tayi dan sauraren amsarta inda cikin girmamawa tace,
"Insha Allah Ammi babu matsala zanyi iya k'ok'arina inga munbada sak'on da labarin yake d'auke dashi, duk da ina da wasu ayyukan banda wanda nakeyi a yanzu amma da yardar Allah zan aje komai idan na k'arasa wanda nake aiki akai yanzu Insha Allah shi zan fara."
Cikin jin dad'i tace,
"To y'ar nan Allah yamiki albarka ya jib'anci dukkan lamuranki yakuma biyaki da gidan aljannah".
Daga ita har Usman da Ummul da,
" Amin Amin Ameeeeeeeeeeeeeeeen ya rabbil izzati ".
suka amsa cikin sakin fuska Ammi tasake cewa,
"To sai hakuri da k'anwar taki gatanan kuka koyaushe takasa daina shi sai ki cigaba da d'orata kan hanya dan tabbas had'uwar ta dake ya kawo canji a yanayin ta da".
"Insha Allahu" Garkuwa tace sannan Ammi taciga da cewa,
"Yauwa Aisha nagode sosai Allah ya bada sa a Allah yabaki ikon aikin alkhairin da kikayi niyya Allah ya miki al'barka".
"Ameeen". da haka sukayi sallama Ammi ta mik'awa Ummul wayar ta mik'e tana kallon Usman cikin k'aunar d'an nata tace,
"Fita zakayi ko?".
yana inda yake zaune yace,
"eh me kike buk'ata? in kawo miki?".
tana tafiya tace, "bakomai Allah ya kiyaye ka ya dawo dakai lafiya".
Yana sosa kai kamar mara gaskiya yace,
"Amin".
Tashi yayi yakoma bakin gadon ya zauna ya k'ura mata mayan idauwan shi sannan cikin rad'a yace,
"Wai ina yarona ne?". Kanta a k'asa tana wasa da yatsunta tace, "Yabi Daddy tunda yazo gaida Hajjajo".
K'ara sunkuyowa kanta yayi cikin lumshe ido yace,
"To amma dai bawata matsala ko?".
Murya na rawa tace, "bakomai".
hannu shi yasa ya ruk'o nata yana d'an murza yatsunta a hankali yace, "To aimin rakiya mana irinta masoya".
nan da nan ta kwab'e fuska ta tayi rau-rau da ido alamar zatayi mishi kuka,
Ganin haka ya sake daburcewa jiki na tsuma mik'ewa yayi sannan ya sunkuyo dai-dai kunnen ta ya tsurawa k'irjin ta ido murya a cushe yace,
"Kiyi baccin ki mai dad'i tare da mafarki na ina lasar wad'an nan lips en na ki masu taushi Ummu na ina begen randa zaki zamo mallaki na".
Fusge hannun ta tayi ta rufe idonta cikin kinda da mamakin ya Usman d'in,
shiko ko ajikinshi dan daman haka yake baya b'oye abinda yakeji,
juyawa yayi har yaje bakin k'ofa yace,
"please ki ajiye wayarki a kusa".
Sannan yasa yatsunshi biyu a kan lips d'in shi yai kissing d'insu ya hura mata da bakin shi sannan ya fice.

Kai tsaye yawuce FCE(T) inda yake koyar da masu koyan computer duk juma a da asabar.

Office d'in Mallam Bashir Bala abokin aikin shi yashige kai tsaye kasan cewar nan yake zama in yaje saboda yakan jene sabida nemanshi da sukai yarink'a taimakawa,
bayan sun gaisa Malam Bashir yace,
"To bari inje kafin ka huta".
Yana fita shiko ya d'aga kafafuwan shi ya d'ora akan kujerar dake kallon wadda yake zaune ya ciro waya yakira number Ummul ya saka a kunne,
saida ta kusan katsewa sannan ta amsa murya can k'asa tai mashi sallama,
"wa alaikissalam Hubby, ykk".
Jin abin tai wani iri sabida ganinta yanzun nan yafita amma yana tambayar ya take,
shiya dawo da ita daga tunanin da take da cewa,
"Allah yasa ba bacci kika fara na tasheki ba, kiyi hak'uri wallahi soyayyar ki ce take d'ibana nake kasa jurewa shiyasa zakiga ina irin wannan abu buwan".
baki ta tura tare da cewa
"hmmm". Kawai shikuma yaci gaba,
"Gaskiya Baby ki dena min rowar muryarki dan Allah ki karb'eni kiban dama nashigo rayuwarki na cika zuciyar ki da farin ciki pls".
Yasan da wuya tabashi amsa dan haka yaci gaba da cewa,
"Kice wani abu dan Allah, indai kinaso nayi aikin danazo yi".
shiru dayajin ne yasa d'an sauke k'afar shi k'asa yazura takalmin shi ya mik'e yana mak'ale da wayar yafara tafiya yana cewa,
"Ganinan dawowa tunda bazaki min magana ba nima babu abinda zan iya yi gwara indawo inta zamana a gida". Dai-dai nan yabud'e murfi motar shi yashiga ya rufe kofar,
k'arar rufe motar yasa ta tabbatar dagaske zai dawo da sauri cikin sanyin murya tace,
"Ya Usman dan Allah karka dawo". Komawa yayi ya jingina da jikin kujerar motar yayi murmushin jin dad'i yace,
"kin barni na fito bakimin addu'a ba kuma yanzu nakira kink'i kimin magana gashi duk a matsa nake wane irin aiki kikeso nayi a hakan?".
Katseshi tai da,
"Kayi hakuri Allah yabada sa'a ya kiyaye ka".
Wani irin sanyi yaji a zuciyar shi yasa hannu yabud'e motar ya fita ya maida murfin ya rufe sannan yace,
"Amin, to ko kefa, yanzu ne zanyi aiki ki kulamin da kanki saina fito".
"Adawo lfy".
tace sannan ta katse kiran tabi wayar da kallo tana jinjina hali irin na ya Usman shi sam ya fiye zalama daga dukkan alamu shi ba irin Hammanta bane mai hak'uri.

Shak'uwa mai k'arfice take shiga tsakanin Ummul da sabuwar Auntyn ta Aysha Aliyu Garkuwa, wanda sukan yi waya sannan suna dadewa suna chat, hakan na debewa Ummul kewa kuma tasami nutsuwa saboda irin rarrashi da shawarwari datake samu daga gareta saidai kusan koda yaushe dukkansu da kuka hirar tasu take k'arewa musamman idan GARKUWAR tayi mata wata tambaya game da rayuwarta ta baya,
ranar wata asabar Ummul ke fad'awa Auntyn nata zasu tafi Saudi dan gudanar da aikin Hajji ita da Ammi da Ya Sadiq kuma zasu tafine ta international air dan haka Dubai zasu wuce sannan daga can su dawo k'asa mai tsarki. Addu'a tayi mata sannan suka rabu.
Chapter 64 · 0% Book details