Sashe 32
Rubutaccen Alamari Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
A part d'in Nenne kuwa suna shiga kai tsaye bedroom suka wuce kan gado Ummul ta konta ta kife kanta tana kuka,
ita kuwa Nenne toilet ta shige ruwan d'umi ta had'a mata mai k'unshe da sinadarai na gyaran jiki sannan ta had'a mata wani juk'o na musamman a cikin buta,
tana fitowa taje kusa da ita cikin kulawa da tausayawa irin ta uwa da yarta ta kamo hannun ta ta zaunar da ita kafad'an ta ta dafa a hankali tace.
"Ummul Allah ya miki albarka kiyi hak'uri mamana ki d'aure kinji ko ki denan kukan nan ya isa yanzu kin girma ya kamata kiyiwa kanki fad'a tashi kije kiyi wonka ki zauna cikin ruwan d'umin sannan kiyi amfani da ruwan butar nan."
kukan ta kumayi cikin shogwob'a dan ganin Nennen ta na lallashin ta,
da kukan ta shiga tayi wonkan sannan ta k'asa kanta lokaci d'aya taji jikinta duk ya wore,
tana fitowa ta samu Nennen ta jona borner a ajikin wuta tana fitowa ta zuba mata wasu turaruka masu tsananin k'amshi sannan ta kalleta cikin kulawa tace,
zoki tsuguna kiyi hayak'i da wannan."
"toh " tace sannan ta matso gaban borner ita kuwa Nenne ta fita parlour,
tsuguna wa tayi a kanshi hayak'in na shiga jikin ta wani irin k'amshi na ratsata,
tana mik'e wa ta Jita garau hakan yasa ta kimtsa sannan ta koma bak'in gadon ta konta cikin jin wani irin baccin gajiya,
Tana konciya Nenne na shigo wa had'in kaza ta karb'a mata wanda Hajjajo tayi mata sai ruwan tsumi mai dad'in sha,
ajiye wa Nenne tayi sannan tace.
"Taso kici abinci saiki kontan."
ba musu ta sauk'o taci tasha dan tana jin yunwa,
kuma yau tana jin dad'in yadda Nennen ta ke kula da ita wanda tunda ta nuna bata son Umar Nenne ta dena kulata sai yau d'in,
tana gamawa ta koma ta konta tana kallon Nenne dake shirin shiga wonka cikin sanyi tace.
"Nenne zazzab'i nake ji da ciwon kai."
ba tare da ta kalleta ba tace.
"Toh bari in gayawa Umar d'in yazo ya dubaki."
fuska ta tsuke dan bata son abinda zai had'a ta dashi inuwa d'aya kuma gashi ta jawa kanta,
bayan Nenne tayi wonkan ne ta shirya ta nufi d'akin Abba a tsakar gidan ta kalli Aliyu yana shirin shiga part d'in Hajjajo kiran shi tayi sannan tace.
"Jeka kira Hamma Umar d'in ku kace Ummul bata da lafiya yaje ya dubata."
"Toh" yace sannan ya nufi parlour Hajjajo yana zuwa ya samu Hamma Umar d'in yana zaune gefen Usman yana b'are mishi lemu,
gefen shi ya zauna a hankali yace.
"Hamma Anty Ummul bata da lafiya Nenne tace kaje ka dubata."
kai ya gyad'a sannan yaci gaba da bawa Usman d'in kulawa,
bayan ya gama bashi abinci ya bashi maganin sannan suka tafi part d'in su suna zuwa ya had'a mishi ruwan wonka,
har cikin bathroom d'in ya rekashi kamar zaiyi mishi wonkan,
murmushi Usman yayi tare da cewa.
"Hamma yau wonkan ma zaka min ne?."
"Kanaga ka girma ko?."
kai ya sosa sannan yace.
"Gaskiya dai Hamma na girma mai min wonka zai iya makancewa."
K'eyan shi ya d'an buga sannan ya fita,
shi kuma Usman wonkan yakeyi yana zubda k'ollah cikin tausayawa kanshi da d'an uwan nashi,
bayan ya fito Hamma Umar ya shirya shi sannan ya kontar dashi kan gado ya zauna gefen shi yana shafa kanshi cikin sanyi yace.
"Ammmi ta kiraka kana wonka nace mata kace min yanzu ka girma."
ido ya lumshe yana jin dad'in yadda d'an uwan nashi ke kula dashi k'aunar shi na ratsa mai zuciya,
ido ya lumshe cikin jin bacci yace.
"Hamma ?."
"Na'am Usman d'an uwana."
kai ya jinji na sannan yace.
"Ina sonka d'an uwana."
kanshi ya rink'a shafawa yana cewa.
"Usman duk duniya bani da tamkar ka ina sonka k'anina bani da buri a duniya daya wuce inga ka samu lafiya fatana a koda yaushe in ganka cikin farin ciki."
ruggume juna sukayi sannan a hankali Umar ya kontar dashi sannan ya rink'a yi mishi karatu qura'ani a cikin kunnen shi murya cike da rauni,
lokaci d'aya bacci ya tafi da Usman d'in,
shi kuwa Hama Umar a hankali ya gyara mishi konciya sannan ya fito kai tsaye harabar gidan ya koma motar shi ya bud'e ya d'auki magungunan Ummul sannan ya nufi part d'in Nenne,
yana shiga parlour ya samu ba kowa sai kuma yaji muryan Ummul dake magana da Anty Halima da woyar Nenne,
cikin yin sallama ya shiga yana shiga ya zauna gefen Ummul d'in sannan yasa hannu ya karb'i woyar ya katse kiran ,
ita kuwa a fusashe ta juyo gare shi a nufin yin tsiwa,
sai kuma tayi shiru jin yadda ya jawota jikin shi ya ruggume ta tsam a jikin shi sai sauk'e ajiyan zuciya yakeyi murya can k'asa yace.
"Kun bani tsoro keda Usman in na rasaku bansan makomata ba Ummul Khairi ina tsoron abinda zai rabani daku,
In babu Usman bansan ya rayuwa zata juya min ba."
sai kuma ya k'ara matsota jikin shi d'umin jikinta na ratsa shi,
ita kuwa tureshi takeyi tana k'ok'arin matsawa,
jawota ya kumayi a hankali ya tallabo kanta kissing d'in ta yayi da kyau sannan yace.
"Kiyi hak'uri my Khairi bazan sake wahala da keba."
shiru tayi tana jin yadda yake fidda numfashin da sauri-sauri a haka har ya fara sauk'e ajiyan zuciya a hankali nitsuwarsa ta dawo jikin shi sannan ya bata maganin ya kontar da ita ya shafa fuskar ta sannan ya fita.
A haka Hamma Umar ya wuni kula da k'anin shi da matar shi da derema haka ya kwana kula da Usman yayin da kewar Ummul ke cin jikin shi da zuciyar shi,
koda gari ya waye haka ya wuni kula dasu,
kuma Alhamhadullih duk sun mik'e musamman Ummul dan shi kam Usman k'arfin haline da son kontar da hankalin Hamman nashi,
bayan Anyi salla isha ne Abba yace Hamma Umar su tafi tunda duk jikin su da sauk'i,
bayan ya fita ne ya d'auko jakar Ummul ya bawa Aliyu ya kai mata cikin gida sannan yace .
"In kaje kace tazo."
"Toh" yace sannan ya nufi cikin gidan,
a parlour Nenne ya samu su ya Adam cikin mamaki ya Sadik yace .
"Jakar nanfa daga ina.?."
"Ta Anty Ummul ce."
Ya bashi amsa ya Adam ne ya kalli Ummul d'in cikin tsuke fuska yace.
"Ba yanzu zaku tafiba?."
Kai ta juya ido cike da k'ollah tace.
"A a ni bazan komaba bani da lafiya."
A hatsale ya bugawa Aliyu tsawa .
"Maza ka meda jakar cikin motar Hamma Umar d'in ke kuma tashi kibi mijin ki ku tafi."
shi kam Aliyu tuni ya juya da jakar ita kuwa hannun ta rink'a yarfa wa tana buga k'afafun ta tare da bud'e baki da k'arfi tana.
"Ai Hamma Umar d'in ya yarda kuma bani da lafiya shike nan dan an tsaneni sai ayi ta korata a gidan mu."
Kanta yayi da sauri yana zaro bel d'in k'ugunshi,
ya Sadik kuma cewa yake.
"Yauwa zaneta tunda bata jin magana."
Ihu ta saki jin sauk'ar bel d'in a jikin ta a guje ta fita tana kuka,
bayan Hamma Umar d'in ta tsaya tana tsalle da dire-dire tare da rik'e hannun shi ,
Abba ne ya fito dan jin kukanta yana zuwa ya kalli yadda takeyi sai murmushi yayi dan a fili yarintar Ummul take ganuwa,
shi kuwa Adam tsawa yake buga mata yana.
"Ki wuce ki shiga cikin mota."
Abba ta kalla dan ko zaice ta dawo sai kuma ta shiga motar ganin yadda ya had'a fuska yana kallon ta,
shi kuwa Abba cikin bada umarni yace.
"Farouq shiga ku tafi.
"toh."
yace sannan ya shiga,
Aliyu kuwa dariya yayi tare da d'aga tafin hannun shi ya saitasu da kanshi yana kad'a hannun tare da zaro harshen yana kad'awa Ummul cikin tsokana yace.
"Bana gaya mikiba yanzu ke ba y'ar gida nan bane yanzu dagani sai Nenne na."
ya k'arishe maganar yana rawa,
Usman ne ya d'an roggoshi keyarshi yace.
"Aliyu wato kaine d'an tada zaune tsaye ko."
ita kuwa kuka tasa tana cewa.
"Ya Usman ba kaga Aliyu ba."
Murmushi yayi yace.
"Muna sonki Ummul d'in mu ke y'ar gidan nance har Abadan."
K'ollah ta zubda tare da cewa.
"ya Usman kai kad'ai kake sona, nima ina sonka."
Ido ya lumshe sannan yace.
"Allah ya d'aiyiba."
murmushi sukayi dukan su,
shi kuwa Hamma Umar hannun Usman ya jawo ya d'an sunkuyo kanshi a hankali yace.
"Ka kula da kanka d'an uwana ina son ka ina tsoron abinda zai cutar da kai."
Murmushi yayi tare da cewa.
"Nayi lafiya fa."
Haka sukayi sallama suka tafi,
Ita kuwa suna fita harabar gidan ta bud'e sabon shafin kuka,
sunyi tafiya mai d'an nisa,
Hamma Umar yana tuk'in hankalin shi na cikin tunanin halin da k'anin shi ke ciki,
kamar a mafarki yaji Ummul tasa hannunta ta d'amk'o........
By
*GARKUWAR FULANI*
ðŸ“ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡
*RUBUTACCEN AL,AMARI*
Page 2⃣0⃣
*NA*
*AYSHA ALI GARKUWA*
ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡