Sashe 10
Rubutaccen Alamari Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Kai ta juya yayin da idanun ta sukayi tab da k'olloh cikin sanyi tace.
"A a me zance ba komai sai fatan Allah ya sanya alkhairi Allah yasa sanadin haka zumunci ya k'ara k'arko."
sai kuma tayi shiru sannan tace.
"Lallai Mustapha yayi halin kirki,
sai kuma ita Ummul."
Cikin kula Abba yace.
"Ummul kam ai dole tabi umurni na."
Kai Nenne ta gyad'a tare da tarin zulumi.
Daga nan sukaci gaba da hirar yadda bikin zai kasan ce.
Shi kuwa Hamma Umar su Abba na fita ya koma kan 3 str ya konta yayi shiru tafin hannushi yasa ya rufe fuskar sa,
gaba d'aya zuciyarshi ta cushe ta cika da tausayin Mustapha da Ummul shi kam gani yake tabbas ba'ayi musu adalci ba,
d'aya rumtse idonshi sai ya rink'a ganin yadda Mustapha ke kallon Ummul zuwanshi na k'arshe,
Hajjajo ce ta matso shi gefen shi ta zauna a hankali tace.
"Umaruh Farouqu farin cikin ka iyayen ka ke bid'a shi yasa suka yanke wannan hukuncin da su sama maka dad'in rayuwa,
ba k'inka sukeyi ba."
ido ya d'an bud'e sannan yace .
"Na sani basa nufin cutar dani."
daga nan kuma ya mik'e jikin a mace yace.
"sai da safe."
"Allah bamu alkhairi."
Part d'in su ya nufa yana zuwa ya samu Usman yana konce sanyi da 3qtr shi a jikin shi matso shi yayi a hankali ya kalli B'iyayen nashi ganin yayi bacci ne yajawo blanket ya rufeshi,
sannan yayi addu'a ya shafa mishi sannan yaje yayi wonka yayi al'wala yazo suka konta..
A hankali Abba ya kammala shirye-shiryen auren Ummul da Umar hatta kayan d'akin Ummul Abba ya had'o mata a saudia ba abin daya rege,
abin mamaki shi kam Hamma Umar daga ranan basu kuma maganar dasu Abban ba,
Abin da ke bashi mamaki kuwa hatta kayan d'akin an kaishi gidan da yake zama a damaturu cikin gida jen ma'aikatan an shirya komai tsab ba abin da ya rege da bobu a gidan hatta kitchen d'in an shirya komai tsab.
Ita ko Ummul duk abinda akeyi bata da labari,
shak'uwa tsakanin Hamma Umar da Usman kuwa kullum k'aruwa yake Hamma Umar sam baya yarda ya kwana a damaturu yana tashi daga office nashi zai kama hanyar potiskum,
Ummul da Mustapha kuwa suna soyewa son ransu shima Mustapha har manta maganar su Abba yakeyi wasu lokutan.
Yau jumma tun da safe Ummul ta tashi da ciwon cikin da mararta kad'an-kad'an,
haka yasa bata samu tayi aikin da Hamma Umar ya k'indaya mata ba,
shi kuwa Umar Faruoq tun da sassafe ya shirya tsab shida Usman tea kawai suka d'an sha sannan suka fita a tare Usman ya nufi wurin aikin shi shima Hamma Umar ya nufi cikin damaturu,
kasan cewar ya jumma'ace aikin ba yawa sosai.
11:00 Am kiran Adam ya shiga woyar Hamma Umar d'in,
yana d'agowa yace.
"Adam ya akayi ne?."
"Yauwa Hamma Umar dama Abba ne ya aikoni da masu gyaran labulaye yace a canza labulayen toh munzo kuma baka gida gashi gidan a rufe."
"OK gani nan zuwa yanzu ku jirani kad'an bari in k'arisa aikin dan tare zamu koma cikin potiskum d'in."
"Toh" yace sannan suka koma cikin mota suka zauna.
Jimawa k'adan Hamma Umar d'in ya iso ya bud'e musu gidan nashi suka shiga ,
a take su Abdul suka canza labulayen gidan kab sannan suka kimatsa komai suka shimfid'e carpet masu lau shi da taushi gaba d'aya gidan ya d'auki k'amshin da shek'i ga k'amshin sabon penti ga k'amshin sabbin kayan d'akin ga k'amshin kasan cewar Hamma Umar ma abocin tsabta da k'amshin ne komai yayi ras sai shek'i da k'amshin yake zubawa,
shi kam Hamma Umar yana tunanin me Abba yake shirin yi tunda yasan har yau Ummul bata san da zancen ba haka dai ya bar abin a ranshi tunda shi bashi da yawan magana,
su Abdul na gamawa suka d'auki hanya tare da Hmma Umar..
Suna zuwa gida sallan jumma'a suka tafi,
Bayan an taso masallacin ne Dr Umar ya wuce chemist d'in shi,
Abba kuwa da sauran gida suka dawo,
Itako Ummul zuwa yanzu ciwon cikin ta ya fara tsananta,
tana zaune a parlour Nenne tana d'an juya kai Aliyu ya shigo parlour kallon ta yayi cikin kula yace.
"Sannu Anty Ummul ko inje in kira Hamma Umar ne?."
a d'an wahalce ta harareshi tace.
"Barni in mutun."
Dariyan tsokana yayi sannan yace.
"Kije Abba na kiran ki."
Da sauri ta d'an zaro ido gami da dafe k'irji cikin tsoro tace.
"Ni? da gaske Abba na kirana?."
"Ehh wallahi da gaske ne,
toh menene dan Abba ya kiraki ji yadda kike zaro ido."
"A a wallahi Aliyu Abba baya kirana ko batun makaran ta ne Nenne yake gayawa ta gaya min,
ni dai naji tsoron kiran nan nashi."
"Toh koma dai menene kije maji daga baya."
cewar Aliyu kenan.
A bak'in kofar parlour Abban ta tsaya tare da yin sallama ,
Daddy ne ya amsa tare da cewa .
"Ummul na shigo."
Kai ta sunkuyar cikin jin tsoro ta shiga a hankali can gefen Daddy ta zauna yayin da zuciyarta ke luguje,
a hankali ta gaida su,
sannan tace.
"Abba Aliyu yace kana kirana."
Kallon ta yayi cikin k'aunar y'ar tashi a hankali yace.
'"Ehh ina kiran ki."
Sai kuma duk sukayi shiru,
can dai Abba yayi gyaran murya tare da cewa.
"Ummul ni wayene a gareki?."
Kai ta d'ago cikin k'arin firgici a hankali tace.
"Mahaifina."
Kallon ta ya kumayi sannan yace.
"A duniya bayan mahaifi yarki akwai wanda ya fini sonki?."
Baki na rawa tace.
"A,a babu."
"Na tabbatar kina da sanin cewa shariya ta bani damar zab'a mik'a majin aure ko."
"Ehh."
ta bashi amsa hawaye na bin fuskarta.
Shi kuwa gyaran murya yayi sannan yace .
"Abin da ban saniba ko zaki iya min biyeyya kan zab'in da nayi miki."
Zuwa yanzu kam ta k'asa magana sai kai take gyad'a wa tana wasa da yatsun ta.
Cikin bada umurni Abba yace.
" toh nayi miki miji,
kiyi biyeyya a kanshi ko bana raye shine mijin ki, mahaifiyata da d'an uwana sune shaida,
na bada auren ki ga d'an uwanki Umar Faruoq."
Kalaman Abba sun maida Ummul kurma sun sata wani irin razani da firgici gaba d'aya jikin ta rawa yakeyi bugun zuciyar ta kuma kamar zai b'allo ya fito woje kunya yayi mata wani irin nauyi cikin rawan baki tace.
"Hamma Umar Faruoq?."
Kai Abba ya gyad'a mata tare da cewa.
"Ehh shi d'in dai."
Hannu tasa cikin tsoro ta kama kanta ta bud'e baki zatayi magana Abba ya dakatar da ita cikin tsuke fuska yace.
"Tashi ki tafi bana buk'atar jin komai daga gareni ba shawara bace umurni nane wannan."
Tanaji Abba na cewa tashi Amman ta k'asa ko d'aga yatsarta,
sai da taji ya zuba mata tsawa,
cikin firgici ta mik'e ta fita ,
tana fita kai tsaye part d'in Nenne ta ta nufa ,
tana zuwa a parlour ta samu su Ya Usman su ya Adam ya Sadik da Aliyu kai tsaye cikin bedroom ta shige,
Usman na binta da kallon ganin yadda take a firgice.
Tana zuwa ta zauna gefen Nenne dake kan sallaya cikin wani irin yanayin ta kifa kanta kan k'afafun Nenne cikin cushewar sauti ta saki wani irin galabaicen kuka mai cike da tausayi kuka takeyi mai tsuma zuciyar mai sauraro kukan take da sauti,
Nenne kam tana ganin haka tasan me yasa ta kukan gaba d'aya sai zuciyarta ta cika da tausayawa y'ar tata,
su Ya Usman kuma suna jin kukan da takeyi cikin sauri suka shigo d'akin ,
cikin tarin tausayawa Usman ya zauna gefen ta baki na rawa yace.
"Ummul meke faruwa? meya sameki? meke miki ciwon?."
Ba amsa sai kukan da takeyi,
Nenne kuwa tsuke fuska tayi cikin fad'a tace.
"Ke ni tashi a kaina tunda abin naki iskanci ne ana miki magana kina kukan banza bazan kiyi magana ba."
Cikin kuka mai cushe zuciya ta d'ago kanta baki na rawa tace.
"Wayyo Allah wayyo Nenne kiji abin da Abba yace min Nenne wallahi ina son Mustapha ina sonshi yana sona dan Allah Nenne ki bawa Abba hak'uri wallahi ina son Mustapha."
Wani irin dogon tsaki ya Adam yaja cikin buga mata tsawa yace.
"Ai Mustapha yafi miki kowa a duniya tunda har kike kuka da umurnin Abban mu,
ni wallahi kin saman na k'ara tsanar sa."
Juyowa tayi cikin kuka tace.
"Ya Adam kasan da waye Abba zai had'a ni?".
A hatsala yace.
" Na sani mana kuma yafi Mustapha da komai."
Cikin kad'uwa da bugawar zuciya Ya Usman ya kalleta tare da cewa.
"Waye za'a had'a ki dashi?."
Kuka ta saki tare da cewa.
"Ya Usman waifa Abba da Hamma Umar zai had'a ni aure."
Ido Usman ya zaro cikin wani irin yanayin yayi wani irin.....
By
*GARKUWAR FULANI*
ðŸ“ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡
*RUBUTACCEN AL,AMARI*
page 1⃣1⃣
*NA*
*AYSHA ALI GARKUWA*
ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡ðŸ‡
*Zan abbato mutanen sokkoto su y'an kwaraine basu da tsoggoma idan kaje ka sanya fad'a musu zasu rik'eka da kyau harda lallamah k'warai-k'warai na gane duniya mai sonka shike yi maka hiddima masoya na na sokkoto kun gaman gata gaisheku ðŸ¤ðŸ˜ðŸ˜˜ðŸ‘ðŸ»ðŸ¤nakeyi domin kuke raba gardamaðŸ‘ðŸ»ðŸ¤ sokkotawa ina al'fahari daku domin baku da hassada a zuk'atan ku shiyasa na sadaukar da wannan shafi gareku sokkotawaðŸ¤ðŸ˜˜ðŸ‘ðŸ»*