Sashe 45
Rubutaccen Alamari Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
*A* kan fuskar Nenne ya dire ida nunshi,
kallon shi itama takeyi tana juya mishi kai cikin zubda k'ollah,
shi kuwa komawa yayi ya zauna ya kife kanshi jikin kujera ya rink'a kuka mai cin zuciya,
kusa dashi Nennen ta zauna a kan kujera,
jinta a kusane yasa Usman ya d'aura kanshi guiwowinta sannan ya ci gaba da kuka,
hannun tasa kan kafad'unshi cikin sanyi tace,
"Usman ashe bazaka yiwa kanka fad'aba shin haka zaka bar rayuwarka cikin garari Usman ka manta illar abin da kakeyi shin haka zakaci gaba da son matar d'an uwanka Usman kai har sai yaushe zaka ruggumi k'addarar ka ashe bazaka zamo mai yarda da k'addarar rayuwar kaba".
Kai ya d'ago ya rik'o hannun ta sannan ya rink'a juya kai cikin rawan murya yace,
"A, a Nenne a a na yarda da k'addarata na bar son matar d'an uwana na cireta a raina bana son Ummul Nenne Hamma Umar da Ammina nake tausayawa Nenne zan tafi tafiyar da ba dawowa zan bar Hamma na bari na har abadan,
Nenne Hamma na baida aboki sai ni Hamma baida mashawarci sai ni Hamma baya gayawa kowa matsalarsa sai ni Hamma yafi sona fiye da kanshi,
Nenne ya Hamma na zaiji randa babuni ya Ammina zataji wazai lallasarmin su wazai sasu dariya wazai shiga rayuwarsu a madani dan ya sasu farin ciki Nenne tausayin Hamma nane ke sani kuka da k'uncin zuciya".
kuka sosai yakeyi hawaye har gemunshi itama Ammi kuka takeyi sosai dan tausayin halin k'addarar rayuwar Usman da Umar kuka ta kumayi dan tausayawa Umar yaro ya tashi cikin maraicin Uba amman duk da haka ya hana Usman maraici ya zame mai madadin Uba ga kuma wata sabuwar kaddarar da zata rabashi da Usman d'in
Murya na rawa tace,
"Haba Usman ka dena fad'in haka ciwo ba mutuwa ba kuma Insha Allah zaka rayu da d'an uwanka kuma Allah ne gatan bawansa Umar,
Usman ka kontar da hankali ka".
kai ya gyad'a tare da share hawayen nashi sannan ya kalli Nenne a hankali yace,
"Nenne kukana kikaji har cikin gidane yasa kikazo?".
kai ta juya cikin sanyi ta mik'o mai magungunan shi tace,
"Abban kune ya bani maganin ka in bawa Aliyu ya kawo maka so dana fito sai na samu Aliyun ya tafi gidan Ammin ku shine na kawo maka dan kasha sai kuma na samu kana cikin wannan halin".
Ajiyan zuciya ya sauk'e sannan yace,
"Nagode Nenne da kike tayani b'oye sirrina dan Allah ko bayan raina kar Hamma Umarna yasan wannan matsalar tawa".
kai ta gyad'a mai cikin zubda k'ollah tace,
"Insha Allah bazai saniba".
haka ta zauna tayi ta mai nasiha har saida taga ya d'an sake sannan ta bashi maganin yasha ta fice ta tafi,
shiko wayarshi ya d'auka cikin k'aunar Hamman nashi ya kirashi yana d'agawa sai cewa yayi,
"Hamma na ina sonka! ina sonka! ina soka! bana son kayi nesa dani ina sonka d'an uwana ina son Ammin mu bani da kamarku a duniya Hamma na duk son da nakewa Ammi wanda nake maka yafi yawa ina sonka fiye da kaina".
Shiru Hamma Umar yayi jikin shi a mace da kalaman Usman a take yaji kamar an rufe mishi jikin shi da d'anyen fata wani irin sanyi ya ziyarci rayuwarshi hannun shi ya fara rawa tuk'in da yakeyi ya fara gararsa dan wani kasala da yaji cikin firgici yace,
"Usman meke damun ka zuciyar ka ko? Usman ka gaya min meke damun ka".
dariya Usman yayi cikin calikanci yace,
"Ni Hamma matsalata da kai Kenan kai saurin tsoro gareka ashe dan nace ina sonka sai ya zama banda lafiya toni lafiyata lau aradu".
murmushi Hamman yayi duk da har yanzu yanayin sanyin na jikin shi,
a hankali yace,
"Nima ina sonka ina sonka sama da yadda nike son kaina d'an k'anina".
dariya sukayi baki d'aya a dai-dai lokacin kuma yayi parking a cikin gidan nashi sannan ya katse Kiran,
ya shiga cikin gida.
Kai tsaye bedroom nashi ya wuce,
yana shiga ya fara rege kayan jikin shi wonka ya sha yana shiga
Ummul ta shigo d'akin a bakin gado ta zauna tasa k'aton cikin ta a gaba,
shiko fitowa yayi k'ugunshi d'aure da towel yana ganin ta ya matso gabanta hannun yasa ya shafa cikin ajiyan zuciya yayi tare da kallon idonta yadda suka kumbura alamar tayi kuka zama yayi ya jawota jikin shi a hankali ya mannan kanta a kirjinshi dake da d'an damshin ruwa jin sanyin jikin shi yasa ta k'ara manna kanta sannan ta fara magana cikin muryar kuka da rauni irin na masu tsofaffin ci,
"Hamma sai yaushe zaka ciremin cikin Hamma kullum sai kace min sai gobe gobe sai goben shi gashi yanzu kullum k'uguna ciwo yake min dan Allah ka rabani da cikin nan naka".
k'ara ruggumeta yayi cikin sanyi yace,
"Ummul na kiyi hak'uri ki haifa mana shi da kanki kar in cireshi inya girma yaji kinsa an cireshi a cikin zaiyi kukan bakya sonshi kinga fa yau saura kwana uku rak cikin ya cika wata takwas kinga kenan saura wata d'aya ki haifamin shi ni zan raini abuna".
Rigarta ta d'aga sama ta nuna mai cikin sai kuma ta fara kuka tare da yarfa hannu tana buga k'afa tana,
"Wallahi ni dai na gaji nayi iya taimakon da zanyi kawai ka cire min cikin tunda kai kana son abunka ka ciremin shi wallahi ko nasha gishiri na fiddashi".
k'ara ruggumeta yayi cikin sanyin da kalaman Usman suka sakar mai yace,
"Toh na yard'a zan cireshi amman kiyi hak'uri sai gata dan gobe da safe zan kaiki potiskum gun Nennen ki dan zamuje Abuja nida govnr akwai wasu gwaje-gwajen da zamuyi mishi da wasu doctors d'in kwana d'aya zamuyi muna dawowa zanje in d'aukoki mu dawo sai na cire cikin ko".
kai ta gyad'a cikin jin dad'i tace,
"Toh na yarda".
murmushi yayi cikin kasala ya k'ara jawota jikin shi a hankali ya shafa cikin sannan yace,
"d'ana ina sonka ina son mamanka".
sai ya kuma tura hannun shi kan kirjin ta da suka k'ara ciccikowa a hankali yace,
"Khairi na a d'an barni nayi pakala mana wata k'il daga nan ma baby ya fito".
baki ta tura tace,
"Na gaji ni na gaji da wannan jarabar".
kai ya sunkuyar tare da cewa,
"ya isa na barki kiyi baccin ki ina dai kinci abinci? ".
"eh". tace sannan ta konta gefenshi shiko al'wala yaje yayi sannan yazo yayi nafilfilinshi tare da karatun qura'an ya rok'owa d'an uwanshi lafiya sannan ya rok'awa Ummul enshi sauk'a lafiya tare da mata fatan samun gajeriyar nak'uda,
Sai k'arfe 2 na dare ya konta.
Washe gari da safe bayan sun gama
shirin su,
suka nufi hanyar potiskuma dan yana sauri zai dawo su tafi Abuja,
suna isa gidan A parlour Hajjajo suka zauna gaba d'aya gidan sai ya Sadik dake kitchen din Nenne, bayan sun gaggaisa ne ya kalli Abba cikin girmamawa yace,
"Abba zamuje Abuja nida govnr kwana d'aya zamuyi toh gida ba kowa shine na kawo Ummul gida sai na dawo goben zanzo in d'auketa".
Kallon shi Abban yayi tare da cewa,
"Toh Allah ya kaiku lafiya Allah ya bada sa'an tafiya".
"Amin Amin". suka amasa baki d'aya sannan ya mik'e tare da cewa,
"sai na dawo".
kusan duk a tare suka ce,
"Allah ya dawo da kai lafiya".
"Amin".
yace sannan ya fito har yaje bakin kofar fitan yace,
"Ummul zo".
ba musu tabi bayan shi ganin hararakin da take sha,
kai tsaye parlour Nenne suka nufa,
suna shiga ya jawota jikin shi
ya ruggumeta kanta ya tallabo ya had'e bakinsu wuri d'aya kissing nata ya rink'ayi cikin salon so da k'auna,
itako tureshi ta rink'ayi har saida ta zame bakinta tana haki shima yana hakin,
cikin tsiwa tace,
"Wallahi ka fiye jaraba da wannan jarabar taka ka d'irkamin cikin nan kawai ka tafi kana dawowa ka ciremin cikin nan na huta da fitina".
duk maganganun da takeyi kab a kunnen Sadik da yake dafa indomi a kitchen d'in Nenne,
shiko Hamma Umar shafa fuskarta yayi sannan yace,
"ba matsala Ummul wata ran zakiso wannan d'an naki fiye da kowa a duniya".
baki ta tura tace,
"Bana sonka bana son cikin".
kai ya kad'a sannan ya fita ya tafi,
kai tsaye Damaturun ya koma bayan sun gama shiri da tawagar govnr suka nufi babban birnin taraiya.