← Book details Rubutaccen Alamari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 77

Sashe 20

Rubutaccen Alamari Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Washe gari misalin k'arfe 11:00 Am dai-dai
dubban al'umma suka shaida daurin auren Umar Ibrahim Umar Shuwa tare da Rabi'atu Hassan Umar Shuwa Ummul kenan,
d'aurin auren d'aya samu halartan manya-manyan bak'i kama daga gwamnan Yobe Ibrahim gaidam dan Hamma Umar shine doctor dake duba lafiyar gwamnan nasu na jihar Yobe tare da sarkin su,
bayan an gama d'aurin auren ya Usman ne yazo ya rugume Hamma Umar d'in cikin happy yace.
"Ina cin farin ciki Yau Allah ya nuna min auren d'an uwana Allah ya tayaka rik'o."
murmushi Hamma Umar yayi tare da cewa.
" Amin."
daga nan abokan shi suka rink'a yi mishi musabaha suna tayashi murna,
cikin zugar mutanen dake tayashi muryar ne yaga Mustapha ya mik'a mai hannu cikin sanyi sukayi musabaha sannan Mustapha yace.
"Hamma Umar inayi maka fatan al'khairi a Rayuwar auren ka kaida Ummul ina taya ka farin ciki a matsayinna na d'an uwanka musulmi."
sai kuma muryar shi ta fara rawa sai hawaye cur-cur a fuskar Mustapha,
cikin tausayawa Hamma Umar ya rugume shi a hankali yace.
"Mustapha ka gafar ceni na shiga rayuwar ka kai da Ummul Amman bayina bane Mustapha wannan rubutaccen al'amari ne bani da niyar rabaku,
su Abba ne suka had'a aurena da Ummul,
ku gafar ceni Mustapha domin na zame muku bak'in jakada a Rayuwar ku Mustapha ka gafar ceni."
Cikin rawan murya Mustapha yace.
"Hamma Umar na yarda da kaddar ta fatana ka rik'e min Ummul bisa amana."
kara rugume shi yayi sannan ya sake shi cikin sanyi Mustapha ya juya ya tafi,
shiko Hamma Umar haka yayi ta sallama da abokan shi dan duk yaune zasu tafi tunda biki ya kare gashi kuma abokan duk y'an nesane,
Hamma Haiydar har Kaduna
zai koma Hamma Yusuf kuwa Taraba Hamma Mahmoud Adamawa Yola Hamma Hassan Gombe yayin da Hamma bashin kuwa zai koma kano,
haka Hamma Umar da ya Usman suka tsaya a harabar gidan nasu suna ta ban kwana da bak'on nasu,
bayan duk sun tafi ne,
saura baki matama dake cikin gida duk sun tattafi sai y'an kad'an da suka rege.

Da daddare bayan Anyi Sallan maggariba da ishah Abba ya Tara family d'in shi harda Ammi da Inna da sauran mutanen gidan bayan sun zazzauna Daddy ya bud'e musu taron da Addu'a ,
sannan daga nan Abba kuma yayita musu nasiha mai ratsa jiki da zuciya,
Ummul kuwa zuwa yanzu kuka ya zame mata jiki.

Bayan Abba ya gama musu nasihar ne ya mik'e tsawon sa gaban Ummul yaje ya tsaya cikin bada umurni yace.
"Ummul taso kizo."
mik'ewa tayi cikin zubda k'ollah,
shi kuwa Abba hannun ta ya kama yaja har gaman Hamma Umar d'in cikin kula ya kamo hannun Umar d'in ya tsaida shi sannan cikin girma da jagoranci yasa hannun Ummul cikin tafin hannun Umar d'in a hankali yace.
"Farouq ga matar ka rik'e hannun ta ku tafi gidan Ku."
kallon Abban yayi cikin sanyi sannan ya manner tafin hannun shi ya rumtse hannun Ummul d'in kamar yadda Abba ya umur ceshi,
shi kuwa Abba Ummul ya kalla cikin tsuke fuska yace.
"Kibi mijin ki ku tafi Allah ya baku zaman lafiya."
"Amin Amin." sauran mutanen dake wurin suka amsa,
shi kuwa Hamma Umar hannun Ummul d'in ya jawo cikin yin k'asa da guiwowin shi suka durk'usa gaban Abba a hankali yace.
"Abba nagode Allah ya k'ara zumunci."
"Amin Amin."
Abba yace tare da shafa Kansu ,
sannan shi kuma Hamma Umar ya sake jan hannun Ummul gaban Daddy ya mishi godiya a haka ya rink'a jan Ummul suna zagaya wa har suka iso gaban Ammi da Nenne kamar kullum Hamma Umar hannun shi d'aya yasa ya ciro hularshi sannan ya jawo ummul suka durk'usa a gaban su cikin sanyi yace.
"Ammi ! Nenne ! nagode Allah ya saka muku da al'khairi."
dafa kanshi Ammi tayi kamar ko yaushe sannan tace.
"Allah ya sanya haske a wannan Aure naku Allah ya taya ka rik'o Allah yayi muku al'barka."
haka tayi ta musu Addu'a sannan tayiwa Abba ma godiya da kyautar y'ar shi d'aya bawa d'an ta.

Shi kuwa Umar yana rik'e da hannun Ummul yaje ya rugume ya Usman cikin sanyi da k'aunar k'anin nashi murya na rawa yace.
"Kamin al'k'awarin zaka kula da kanka, kasha maganin ka karkaci duk wani abu green kaji B'iyaye na,
nanda kwana 5 Kaima zaka koma gidana inci gaba da kula da kai."
murmushi Usman yayi cikin yanayin shi na abin dariya yace.
"Nayi ma al'k'awarin zan kula da kaina kafin nima na auru matata taci gaba da kula dani,
kaima ka kula da matarka Allah ya d'aiyiba."

gaba d'ayansu dariya sukayi sannan Abba yace.
"Farouq ku tafi dare yanayi."
"toh" yace sannan suka rekosu harabar gidan Usman ne ya bud'e musu mota bayan sunyi saida safe sannan Hamma Umar yaja motar suka tafi.

Tunda suka shiga motar ummul taci gaba da kukan ta,
shi kuwa Hamma Umar tuk'in kawai yakeyi hankalin shi na kan titi haka sukayi tafiyar tasu Ummul daga Potiaskum har cikin Damaturu kuka take batayi shiru ba,
suna isa k'ofar gidan ba tare d'aya shiga cikin gidan ba yayi parking sannan ba tare d'aya kalleta ba ya fito gefen da take ya zagayo marfin motar ya bud'e sannan ya jawo hannun ta,
ita kuwa sai fizge hannun take tana k'ok'arin kwancewa,
shiko sai matse hannun yayi da k'arfi cikin sanyi ya jata zuwa bak'in gate d'in juyawa yayi ya kalleta cikin bada umurni yace.
"Ki nitsu kisan abinda kikeyi karki kuskura ki shigar min gida da k'afar hagu ,
sannan kiyi Addu'a kafin ki shigar min gida, dan na lura akwai shaid'anu a tsakiyar kanki,
so ki watsar dasu anan kan titi karki kuskura ki shigar min gidana da su."
kai ta sunkuyar cikin zubda k'ollah dan ta tuno Nenne tama ta horeta da tayi addu'ar kafin ta shiga gidan,
k'ollah ta zubda sannan a hankali ta d'aga k'afar ta dama wanda kusan a tare suka d'aga k'afafun nasu,
a hankali sukayi addu'ar shiga gida sannan suka shiga cikin gidan.

A gida kuwa bayan Hamma Umar yaja motar sun tafi,
Usman ne ya dafe k'ahon zuciyar shi da sauri jin yadda zuciyar shi ke bugawa da sauri-sauri idon shi ya rumtse da k'arfi lokaci d'aya yaga wani irin duhu cikin k'arfin hali ya juyo ya kalli Nenne sai yayi murmushi ya bud'e baki a hankali yace ,
"Shike nan yau kam ni kad'ai zan kwana ba Hamma Umar,
da safe kuma ba Ummul wazan tsokana?."
Dariya su Ammi sukayi mishi sannan suka juya zasuyi cikin gida kenan a dai-dai lokacin Usman yayi wani irin numfashi tare da dafe k'irjin shi yayi taggal-taggal ya fad'i kan kujerun jiki ba.....

By
*GARKUWAR FULANI*
📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*RUBUTACCEN AL,AMARI*

Page 1⃣4⃣

*NA*
*AYSHA ALI GARKUWA*

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*Y'an uwa abokai k'awaye yayu k'anne yara manya maza da mata masoya na da sab'anin haka writers da reedars dan Allah don soyeyyar mu da Annabi ina barar addu'arku ga mahaifiyata bata da lafiya dan Allah kusa min ita a addu'arku da bakunanku masu albarka Allah ya bata lafiya rabbi ya tashi kafad'an ta Allah yasa zakkan jiki ne a wanan gab'ar kuma zan shaida muku ba tabbas kuci gaba da samun posting nan kullum in nasamu nayi fani'imal in ban yiba la'basa nasan zaku min uzuri, DEDDE Am Allah ya baki lafiya 😭👏🏻*

*A baya nace Usman Accounter ne so na batane Usman Lecturer ne a Yobe state university so daga yanzu a lecturer sa zamu tafi dan shine aikin sa na gaskiya*

*B*a numfashi ya konta kan kujarar ba inda yake motsi a jikin shi, gaba d'aya su Nenne da Abba dasu Hajjajo a tare suka juyo kanshi ya Adam ne yayi sauri ya tallabo shi jikin shi cikin tsananin firgici ya rink'a juya kanshi yana d'an tab'a fuskar shi cikin d'imuwa yana .
"Usman ! Usman ! Usmaaaaaaan! ka tashi ka tashi Usman , Abba Daddy ku gani Usman baya numfashi."
Chapter 20 · 0% Book details