← Book details Rubutaccen Alamari Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 77

Sashe 24

Rubutaccen Alamari Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

a hankali ya sunkuyar da kanshi cikin sauri ya manne bakin shi da nata lips d'in ta yayiwa rik'on taushi ida nunshi ya lumshi tare dasa hannun shi d'aya ya zagayo k'ugunta ,
ita kuwa ido ta zazzaro woje cikin tsantsar firgita da tsoro ga tarin mamaki Hamma Umar ne ke manne bak'in shi da nata ,
gaba d'aya ya rufe bak'in manata ya hanata kukan bare rakin da takeyi da son tara mishi mutanen,
shi kuwa Hamma Umar idon shi a lumshe ya sab'ule lips d'in ta a bak'in shi cikin lumshe ido ya juya ya koma bedroom d'in shi ,
wonka ya sake yi sannan ya canza kaga ,
ya fito parlour kan dinning table yaje phone d'in shi ya d'auka kanshi a sunkuye yazo gefen ta ya tsaya yana jin yadda take yin kuka a hankali yace.
"Ayyah Khairi kiyi hak'uri kibar kukan nan kinji bari inje in dawo ki gaya min me kike son in miki."
mik'ewa tayi ta nufi bedroom d'in tana kukanta na rashin gaskiya,
haka ya fita yana mai tuhumar kanshi daya gaza rik'e amanar daya d'auka.

Tunda ya fita bai samu ya dawo ba sai 9:34 pm ,
yana shiga cikin gidan bedroom nashi ya shige wonka yayi sannan ya fito d'aure da towel a parlour ya d'an zauna jin gidan shiru kamar ba kowa a ciki,
mik'a yayi tare da lumshe ido tabbas yana buk'atar kulawar Ummul amman haka ya faskara zuwa yanzu ya fara k'asa yin control d'in kanshi,
a yanzu kuwa ya gane cewa shi mutunne mabuk'aci mai son kulawar matar sa,
a hankali ya mik'e ya nufi d'akin nata cikin sa'a ya samu k'ofar a bud'e take a hankali ya murd'a hannun k'ofar tare da turawa ,
yana shiga ya haggota kwance kan gadon,
k'ofar ya maida ya rufe cikin sanyi ya zauna gefen ta a hankali ya kwanta tare da sauk'e ajiyan zuciya jikin shi ya manna da nata a hankali yasa hannu ya jawota jikin shi ,
kan k'irjin shi ya kifeta a hankali ya fara shafa gadon bayan ta murya can k'asa cikin rad'a yace.
"Ummul khairi ! Khairi ki tashi."
ido ta bud'e cikin yunk'uri tare da yin mutsumutsu tana.
"Wallahi bana so ni ka fita harkata."
A hankali ya k'ara matsota bak'in shi ya saita cikin k'annen ta iska ya d'an hura mata cikin rauni da rawan murya yace.
"Ki tausawa min Ummul khairi ki jik'aina ki tallafa min ki bani hak'k'ina Khairi karki zamto silar sani cikin wani hali."
tureshi takeyi tana
"Ni ba ruwana da halin da zaka shiga in saka cikin wani halin ko kasa kanka ka sakeni in auri wanda nake so kamai kaje can ka nemi wacce zata soka."

cikin rawan murya kamar zaiyi kuka yace.
"Khairi ki tausayawa mijinki Ummul nifa d'an uwanki ne zakiso na cutu plzz kiyi hak'uri ki amince dani Ummul bazan cutar da keba karki cutar dani ki barni na rab'i jikin ki ,
in ban rab'eki ba wa zanje in rab'a?."
jin yadda yake magana yana cakud'ata da juyata yasa ta rink'a kuka tana birgima har saida ya saketa sannan ya zauna gefen ta yana mai karkarwa,
ita kuwa ganin haka ta mik'e ta koma parlour.

Daga wannan ranar haka suke rayuwa kullum da salon azabar da Ummul ke shirya wa Hamma Umar d'in shi kuwa gaba d'aya yana rayuwa ne cikin tarin bukarta yayinda hakan ya k'ara bawa Ummul damar juya shi haka kwana ki suna tafi mokonni sunja har sun fara irga watanni,
Hamma Umar kuwa har yau baisan menene dad'in aure ba shi kuwa bai iya kai k'araba bare ya kai karanta,
Anty Halima na yawan kiran Hamma Umar tace ya Ummul ta nitsu ko? sai yace mata ehh ba komai fa,
ita kuwa Anty Halima bata gamsuwa hakan yasa tana yawan zuwa weekend toh hakan yasa kab ta lura da zaman da suke yi.

ya Usman kuwa tunda akayi auren yak'i zuwa a cewarsa sai Ummul ta dena kuka,
Hamma Umar kuwa rana d'add'aya ne baya zuwa cikin pataskum shida k'anin shi sunyi ta hira yana kula dashi kamar da sukan je gun Amminsu,
su wuni.

Yau Saturday tun safe Anty Halima da Hajjajo da inna da Aliyu suka shirya zasu je gidan su Hamma Umar d'in ,
Hajjajo kuwa ta dage sai dai Ya Usman ya kaisu ,
dolen shi a hakan badon yaso ba ya kalli Hajjajo tare da cewa.
"Toh sai ku jirani na shirya ai Hajia Yawo."
murmushi tayi tare da cewa.
"Zamu jira jeka shirya,
dan ni nafi yarfa da tuk'in ka kaida Umaru,
Adam gudune dashi Abubakar ko motarsa kamar zai fire in mutun ya shiga."

Murmushi kawai yayi ya tafi part d'in su,
yana zuwa wonka ya shiga amman ya kasa sai kife kanshi da yayi a jikin gini ya rink'a wani irin kuka mai cin rai zuciyar shi na harbawa da k'arfi zuwa yanzu Ya Usman shi kad'ai yasan idan yayi tarin yakan ga jini amman yak'i gayawa kowa dan ya naga shi lokacin sane ya kusa.

Haka yasha kukan shi sannan ya shirya ya fito suka tafi idanun shi na cike da begen ganin Ummul d'in.

A gidan Hamma Umar kuwa yau kwana yayi cikin takura haka ya wayi gari a buk'ace
bayan ya dawo masallaci d'akin shi ya wuce da niyar ko zai samu yayi bacci amman ina baccin yak'i zuwa,
dole ya fito ya nufi d'akin nata yana shiga ya haggota tana zaune bakin gado cikin sanyi ya zauna gefen ta,
shiru yayi yana kallon ta,
ita kuwa tab'e baki tayi tare da harara shi k'asa k'asa dan ta rigada tasan damuwar shi ita kuwa ta naga ta nan zata cuzguna mishi,
ajiyan zuciya ya sauk'e tare dasa hannun shi ya kamo nata cikin rawan murya yace.
"Ina cikin matsala dan Allah ki taimaka min wallahi na fara cutuwa da rashin kulawar ki Ummul."

cikin ko in kula ta mik'e taje gaban dressing Mirror ta tsaya tana gyara gashin kanta,
mik'ewa yayi tare matsowa bayan ta suna kallon juna ta cikin madubin
hannun shi yasa ya tattara gashin nata a hankali yace.
"Ki tsammin aron lokacin ki da jikin na d'an wani lokacin ta haka zaki ceci lafiya ta."
juyawa tayi a tsiwace zatayi magana kenan ya fizgota jikin shi,
cikin rawan jiki ya had'e bakin su wuri d'aya,
ido Ummul ta zare jin yadda Hamma Umar d'in yake mata wani irin hort kissi ,
cikin zafin nama ta tureshi ta koma jikin mirror ta tsaya tana rawan jiki tare da kallon yadda Hamma Umar d'in ya birkice gaba d'aya lips d'in shi sunyi jazir sai shek'i suke ida nunshi ma sai shek'i suke alamun sun ciko da k'ollah,
ido ta kuma zarowa ganin ya zare jallabiyan jikin shi ya nufi kanta yana cewa.
"Zan karb'i hak'k'ina Khairi tunda na lura baki da tausayi so kike ki kashe ni."
kai ta rink'a juya mishi tana cewa.
"Karka matsoni wallahi bana so."

Bai kulata ba sai k'ara matsota yakeyi ganin haka yasa cikin sauri ta lalubo kolban turaren dake kan mirror,
tana nuna mishi tana cewa.
" karka isoni Hamma Umar ka fitan min a d'aki."
bai kulata ba don shi a zaton shi ko buga mishi kolbar zatayi,
ita kuwa yana iso ta cikin tsoro da mugunta ta saiti idanun shi ta dannan bak'in turaren feesssh sai cikin I....

By
*GARKUWAR FULANI*
📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*RUBUTACCEN AL,AMARI*

Page 1⃣6⃣

*NA*
*AYSHA ALI GARKUWA*

🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

*S*ai cikin idanun shi,
da k'arfi ya rumtse idanun tare dasa hannu ya damk'e kanshi da hannu. bibbiyu kai d'in ya rink'a juyawa tare da yin layi cikin wani irin azaban da bazai misal tuba gaba d'aya jikin shi b'ari yakeyi duk ta inda hudar gashin jikin sa yake zuface ke tsatstsafowa kwayar idanun shi tamkar zasu zazzago su fad'o k'asa ji yakeyi tamkar rushin wuta aka cusa mai a cikin idanun,
ba abin da jikin shi keyi sai rawa daya bud'e bakinshi zaiyi magana sai ya kasa sai lips d'in shi suyi ta rawa tamkar maijin sanyi a haka ya rink'a juyu a cikin d'akin har yaje bak'in gado lokaci d'aya kuma ya rink'a murza kanshi a jikin gadon dan azabar da yakeji,
Ita kuwa Ummul da fari murmushi tayi ganin yadda ya rumtse idanun shi jikin shi na rawa,
amman zuwa yanzu tsoro ya rufeta ganin yadda Hamma Umar d'in yake cikin azaba da gigita gefe ta tsaya jikin ta na rawa cikin tsoro a hankali ta fara cewa.
"Hamma! Hamma!."
Yana jinta amman bashi da damar amsawa ba abinda yake yi sai murzan kan nashi da yakeyi,
cikin dauriya da k'arfin hali ya d'an bud'e idon
ihu Ummul tayi cikin firgicin ganin yadda kwayar idanun nashi sukayi jazir tamkar zasuyi aman wuta sun fiffito woje sun hargitse,
shi kuwa Hamma Umar bud'e idon daya d'an yi sai da yaji k'ahon zuciyarshi tamkar zata dare dan iskar da ta d'an shiga cikin ido
cikin sauri ya sake rumtse idanun ya k'ara danna kanshi a kan gadon,
Ummul kuwa gaba d'aya ta tsinke sai kuka ta saki da iya k'arfin ta tana kiran shi tana,
"Hamma Umar ka tashi! ka tashi mu tafi hospital. "
Ganin yadda gaba d'aya ya fara sakewa ne yasa ta sake sakin wani k'ara mai k'arfi.

Dai-dai lokacin Ya Usman kuwa yayi parking a harabar gidan jin yadda Ummul ke kuka da k'arfi yasa cikin zafin nama ya fito da sauri ya nufi cikin gidan yayin da Aliyu ke binshi da gudu,
suna shiga parlour Ummul kuwa tana fitowa a nufin ta zata d'ebo mai ruwan sanyi ya woke idon,
ganin ya Usman d'in ne tayi sauri taje gareshi cikin kuka da tsananin tsoro da firgici ta rik'e hannu Usman tana buga k'afafun ta da k'arfi tana kuka murya na rawa take cewa.
"Ya Usman Hamma Umar!
ya Usman Hamma Umar."
Chapter 24 · 0% Book details